SHAFI NA BIYAR
by @ummishatu
©️Love story 2025
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA....!
NA
*UMMI A'ISHA*
5
***Tsawon kwanaki biyu ya shafe bai zo gidan ba tun bayan da ya dawo daga police station ya shirya ya fice,daren kwana na uku sai gashi ya dawo amma kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci a buge yake saboda da kyar yake iya bude idanuwansa, kasancewar ranar da wuri ya dawo dan ba afi karfe 9 na dare ba yasa kusan kowa dake cikin gidan yasan dawowar tashi banda mommy wacce ke cikin bedroom dinta, Imaan har tayi shirin bacci ta kwanta ta juyo ƙugin motar sa dan tukinsa dabanne indai ya shigo sai ta san ya shigo saboda bedroom dinta yana kusa da parking space,
Tashi tayi daga kwancen da take ta leka window nan ta ganshi ya fito ya nufi part dinsa, hijabinta ta saka ta fita duk da ba wai shi ya dauke ta aiki ko kuma shi take yiwa aiki ba amma yana cin albarkacin mommy cikin abubuwa da yawa, banda mommy da ko kallo bai isheta ba domin ta tsane shi mutukar tsana. Abinci ta zuba mishi tuwon semo miyar agushi ta dauka ta nufi part din nasa, kwance ta ganshi yashe a falonshi bayan da ta bude kofa ai take jikinta ya soma rawa yana ɓari dan da alama yanke jiki yayi ya fadi, a rude ta ajiye kwanukan anan sai kuma taga ya fara yunkurin amai amma kuma ya kasa yin aman,
"innalillahi.... Karfa a bawa Anaam guba...." ta fada cikin zuciyata har lokacin jikinta yana rawa, a guje ta fita ta nufi side din mommy, bata yi wata wata ba ta banka cikin dakin mommy inda take kwance duk da ba wai ta fara bacci bane dan idonta biyu,
"mommy.... Mommy Anaam ne na ganshi ya faɗi acikin part dinsa, kuma yana ta yunkurin amai amma ya kasa.... Da dukkan alamu mommy babu lafiya a tare dashi"
Ko gigau mommy bata yi ba maimakon haka ma sai gyara kwanciyarta da tayi sannan cikin halin ko in kula tace,
"ki kyale shi zai yi ya gama, shi yasan me yaje yasha tafi karfin cikinshi.... Ku rabu dashi kar wanda ya sake zuwa kansa bare yace zai taimaka masa, ko compound nan gaba ya fadi kar wanda yayi yunkurin ɗagashi ku barshi a inda yake acikin kazantarsa....." daga haka mommy ta kashe bedside lamp dinta alamar ta gama magana kuma ta sallameta, jiki a sanyaye kuma har lokacin yana rawa ta juya ta fita,
" kai anya kuwa mommy ta san halin da tilon ɗanta ke ciki? Kai gaskiya da ta sani ba zata fadi haka ba, koda yake cikin ɓacin rai take shi kuma bacin rai babu abinda baya sakawa......" haka take fada cikin ranta dan ta rasa ina zata dosa kuma, shin zata koma wurin mommy ne ta sake yi mata dalla dalla ko zata fahimci halin da yake ciki ko kuma zata wuce bedroom dinta kamar yadda mommy din ta bada umarnin kada wani ya sake raɓarsa da sunan taimako ko kuma tsallake umarnin mommy din zata yi taje ta taimaka masa dan tana ganin kamar zai iya mutuwa cikin wannan halin, ta san duk da wannan abun da mommy ke yi tana tsananin ƙaunar ɗanta haka kuma tana son sa kawai damuwa ce da bacin rai ke sata yin hakan, da sauri ta fita ta sake komawa part din nasa,sake tarar dashi tayi yashe yana murkususu cikin amai wanda har lokacin bai gama shi ba, da gudu taje ta tsugunna a gabansa, wannan shine karo na farko da ta iya kallonsa har hannunta ya kai jikinsa, riƙe shi tayi tana yi masa sannu nan ya soma kelaya amai kamar zai amayar da hanjin cikinsa gaba ɗaya,
Da ƙyar ta iya dagashi bayan ta cire masa fararen takalman da ke kafarsa, haba mutum kamar karamin yaro sam babu tunani ko hangen nesa atare dashi? Wani sashi na zuciyar ta ke karanta mata hakan sai dai bata kula ba taci gaba da taimaka masa dan gaba daya rigar dake jikinsa ta jike da amai haka itama nata hijabin dake jikinta, jikinta duk a mugun tsorace haka ta soma balle masa botiran jikin t shirt din dake jikinsa gabanta na faduwa ras ras,
Kama shi tayi bayan ta cire masa rigar da ƙyar ya iya tashi suka nufi cikin bedroom dinsa, gyara masa kafafuwansa tayi bayan ya tafi a rub da ciki ya fada kan gadon ta ja duvet ta rufe masa jikinsa dan sai taji kamar har ya fara bacci, durkusawa tayi gaban gadon tana kallon komai dake cikin bedroom dinsa duk da ba yau ne ta fara shigowa ba, dakin babban gaske ne mai fadi da tsayi yasha fararen furnitures ƙirar ƙasar Italy, takalma, suttura, agogo, turaruka abin ba a cewa komai domin gasu nan kamar ba mallakin mutum ɗaya ba,
"Dan Allah ka daure mommy tayi alfahari da kai a rayuwa koda sau ɗaya ne....." ta fada a hankali sannan ta mike daga gaban gadon ta kashe masa haske dake gauraye da ɗakin ta fita, sai da ta gyara inda yayi aman tas ta goge sannan ta koma bedroom dinta ta je ta kwanta sai dai abin mamaki sai ta nemi bacci ta rasa a idanuwan ta dan wani irin tausayin mommy ke sake shigar ta Allah sarki ita kadai ta san irin baƙin cikin da take shaƙa akan Anaam saboda kowa ya san irin soyayyar da take yi masa, ta jima bata yi bacci ba daga karshe sai bacci ɓarawo ne ya saceta amma dasu ta kwana cikin ranta.
Lokacin da ya farka bayan asubah ya ganshi kwance kan gadonshi lullube cikin duvet kokarin tuno abinda ya faru ya fara yi amma sai dai ya kasa tuno komai shi dai kawai abinda zai iya tunawa faɗan da suka yi da jazzy akan cocaine daga nan ya manta komai kuma ba hakura yayi ba ya zama dole sai ya dauki fansa, cigaba yayi da kwanciyar sa dan dagaske bashi da lafiya.
Bayan ta kammala shirya breakfast kamar koda yaushe tray ta samu ta shirya na cikin mutum ɗaya ta kinkima ta nufi sashen Anaam duk da ta san ba lallai ta sameshi ba musamman ma idan ya samu lafiya amma abin mamaki sai ta sameshi tukunkune cikin duvet kamar yadda ta tafi ta barshi jiya dan wani matsanancin ciwon kai ke damunsa tun bayan da ya farka bayan asubah,breakfast din ta ajiye masa ta juya ta fita ta koma part din mommy, tana shiga mommy din na fitowa daga cikin bedroom dinta a shirye tsaf da alama akwai inda zata je,
"ina kika je?" mommy din ta bukata bayan ta nufi dining batare da ta amsa gaisuwar da take yi mata ba,
"mommy kamar fa Anaam bai da lafiya sosai gaskiya....."
"Allah ya bashi lafiya"
"amin, amma mommy ki daure ki kira masa likita..... Mommy hakuri zaki yi saboda babu yadda za ayi dole sai hakurin" har lokacin mommy bata tanka ba asali ma wayar ta ce a hannunta tana kokarin neman layin malam bala driver, wuri ta samu ta zauna kamar yadda taga mommy ta zauna domin karyawa, sai da ta jira mommy ta gama wayar da take yi sannan ta sake yin ƙasa da murya tace,
"mommy dan Allah ki taimaka ki kira Dr yazo ya duba shi....."
Tsam mommy tayi tana kallonta na dan wani lokaci kafin cikin zafin rai tace "wai imaan ba nace kar wanda ya sake zuwa inda Anaam yake ba mutukar ya shigo gidan nan cikin maye ko wani abu mai kama da haka ba? Nace kar wanda ya sake yunkurin taimaka masa ko yi masa wani abu muddin a buge yake, faɗa ta ce.... Idan ya bukaci jin dalili a sanar masa nice nan na hana..... "
" mommy ai yanzu ba maganar yanayin da ya shigo gidan ake yi ba, magana ake yi ta lafiyar sa, wallahi mommy bashi da lafiya....... Kije ki ga halin da yake ciki idan har baki yarda dani ba "
Shuru mommy tayi sai kuma ta dauki wayarta ta soma kiran Dr, ajiyar zuciya Imaan ta sauke a hankali dan sai yanzu ne taji ta dan samu nutsuwa duk da basa wani shiri dashi amma ai jinya ita ake dubawa. Mommy bata fita ba sai da ta jira zuwan Dr Najib suka shiga wurin Anaam tare wanda har lokacin bai tashi ba a kwance yake ya tukunkune wuri ɗaya, duba shi Dr yayi sannan ya bashi magunguna ya fita, kallon mommy yayi dake tsaye tana kallon dakin nasa,
"Mommy fita za kiyi ne?"
"ehh wani abu ne?"
"mommy dama ina so ne zan kai motana wurin mechanics........"
"yanzu ba kwance kake baka da lafiya ba? Ka bari sai ka samu lafiya tukunna...."
Daga haka mommy din ta juya ta fita, da ido ya bita har ta fice, yana ganin ta fita ya lallaba a yadda yake ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito da kyar yaci abincin ya sha magani yasa kaya ya fita zuwa part din mommy, Imaan na zaune falon mommyn ya shiga ya nufi bedroom dinta amma a rufe, to ko dai mommy dince ta rufe dakin nata? Bai yiwa Imaan magana ba saboda dama ba maganar suke yi ba ya juya ya fita, binsa tayi da kallo dan ta san abinda ya kawo shi duk yadda aka yi wani abu yazo dauka dama kuma ta san za ayi hakan shiyasa ta rufe bedroom din tun kafin ya shigo, fasa fita yayi ya koma bedroom dinsa ya kwanta kuma yana kwanciya Najla ta kirashi a waya,
"hello babe...." ya fada cikin kasala,
"love ya najika haka.... Are you ok?"
"baby bani da lafiya..."
Ai tana jin haka taja akwati ta fara shirya kaya za ta taho zaman jinya, zuwa yamma sai gata kuma kai tsaye part dinsa suka wuce bayan da ya fito ya taryeta, babu wanda yasan ta zo sai masu gadi amma ko Imaan bata san ta zo ba bare mommy da ba a gidan ta wuni ba,
Dambun acca da zogale yau ta yiwa mommy sai farar shinkafa da miya sannan ta hada mata lemon kwakwa, zubawa Anaam shima tayi ta shirya komai akan tray ta nufi part dinsa saboda ta hango motarsa alamun yana nan bai fita ba, wani kamshi ne ya cika mata hanci tun bayan da ta doshi part din nasa wanda ta san dai ba kamshinsa bane saboda shi nasa kamshin ba irin wannan bane, zuciyar ta ɗaya ta buda kofar falon ta shiga, tana shiga idanuwanta suka hango mata su shida Najla zaune kan 1 sitter Najla na zaune kan cinyarsa ta wani rungume kansa a kirjinta kamar wani baby shikuma idanuwansa a rufe kamar mai bacci, cak ta tsaya ta diririce dan ta rasa ina zata dosa shin komawa zata yi ko kuma karasawa zata yi ta kai abincin?
"Baby ita kuma wannan fa?" taji Najla na tambayarsa cikin lankwasa harshe, a hankali ya bude idanuwansa ya kalleta ya mayar ya rufe kafin yace,
"ke...... Idan zaki zo ki ajiye ki zo ki ajiye idan kuma komawa zaki yi ki juya ki koma...... Ban son ganin ki"
A hankali tayi kasa da kanta ta karasa gabansu kan center table ta ajiye musu tray din ta juya ta fita zuciyarta na bugawa saboda yanda yace baya son ganin ta itama wallahi bata son ganin nasa, wato abin nasa ya sake bunkasa ba raguwa yake yi ba gaba yake yi yanzu harda kawo mace gida duk da dai dama kowa ya san neman mata halinsa ne, tana komawa ta iske mommy ta dawo kuma jin daga part din Anaam yake yasa mommy tambayarta ya jikin nasa tace da sauki daga haka taja bakinta tayi shuru, wanka mommy tayi taci abinci ta kwanta bata kara bi ta kan Anaam ba har sai da dare yayi bayan ta idar da sallar isha kafin tayi shirin bacci ta fita zuwa part dinsa dan gano halin da yake ciki, tana shiga ta gansu falo shi da Najla kamar yadda Imaan ta gansu sai dai wannan Karon shisha suke sha tana zaune bisa cinyarsa idan ya zuka sai ya bata itama ta zuka a haka mommy ta shiga ta samesu, tsawa mommy ta daka masa cikin bacin rai,
"Anaam...... Wannan kuma fa? Rashin kunyar taka har ya kai haka?"
"mommy itace fa babe din da nace miki ina son zan aura kiyi min aure kika ki....."
"ke.... Tashi ki fita, kar na sake ganin kafarki acikin gidan nan..... Marar tarbiyya, marar mutunci,wadda bata san ciwon kanta ba, a hakan kake so in barka ka auri wannan abar? Ke tashi ki fita....."
Fuuhhhh Najla ta tashi Anaam na riketa amma ta fusge ta wuce cikin bedroom dinsa ta janyo trolley dinta tazo ta fita,
" haba mommy... Yanzu da kika koreta ina zata je da wannan daren? "
" koma ina ne taje, sannan kai kuma ina son ka sani daga yau sai yau duk ranar da ka sake yarda ka kuskura ka kawo min wata ballagaza gidan nan wallahi sai naci mutuncinka..... Shashasha wanda bai san ciwon kansa ba.... " daga haka mommy din ta juya ta fita, shima cikin sauri ya tashi ya fita domin bin bayan Najla............ ✍🏻
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.
Ummi Shatu👌🏻