ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA

SHAFI NA SHIDA

by @ummishatu

©️Love story 2025

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA...!

NA

*UMMI A'ISHA*

6

***Duk irin rarrashi da ban bakin da Anaam ke yiwa Najla bata saurare shi ba har suka je hotel inda suka saba zama, zama yayi gefen ta inda ta juya masa baya tana jin kamar ta rufe shi da duka ko zata samu ta huce daga haushin abinda mommynsa tayi mata, ta yaya zata farfada mata wadannan maganganun kuma ta kirata da sunaye kala kala marassa kyau dan kawai taje dakin shi ta zauna?

"baby..... Please here me out at least baby....."

"wai mai kake so in ji daga gareka? A gabanka fa komai ya faru Anaam, ashe ni duk zamana da kai bata lokaci na nake yi? How could I be so foolish...... For all this time I been wasting my time....." ta fada idanuwan ta na cika da kwalla,

"am very sorry baby, you know i love you right? Kiyi hakuri ki kyale maganar mommy, kawai bacin rai ne but I promise you she will come around.... Zata so ki kuma zata kaunaceki....."

Shuru tayi masa bata tanka ba saboda bata da abin cewa sai dai amma tana jin dadin kalamansa.

Rai a ɓace mommy ta koma part dinta tana kokarin shiga bedroom dinta Imaan na shirin fitowa, saurin matsawa Imaan din tayi mommy ta shiga ciki ba tare da tayi magana ba, shuru ta zauna ta gagara bacci sai faman tunane tunanen da basa karewa take ta faman yi a haka har asubah tayi gari ya waye, sam bata da niyyar fita ko falo dan gaba daya ta gaji da komai bata son ganin kowa bare magana,

Imaan tun bayan da ta tashi take ta faman aikace aikacenta har tayi ta gama bata ji motsin mommy ba bare taga fitowar ta, breakfast din mommy din ta shirya kan tray ta bita dashi cikin bedroom inda mommy ke zaune idanuwanta biyu amma ta tafi duniyar tunani,

"mommy ina kwana....."

Sai lokacin ta san cewa Imaan ta shigo cikin ɗakin, cikin sanyin murya ta amsawa Imaan gaisuwar,

"mommy breakfast dinki ne na kawo miki tunda naga baki fito ba, kici ki sha maganin ki....."

Girgiza kai mommy tayi cike da takaici tace "a wanne dalili zan sha magani Imaan?"

"mommy dan lafiyarki mana...."

Sake girgiza kai mommy tayi ta kalleta "bani da bukatar shan wani magani a halin yanzu Imaan, ai ina shan maganin ne dan in samu lafiya kuma in rayu ko? To na gaji da rayuwar gara in koma ga Mahalicci na ta yuyu acan in samu hutu....."

"innalillahi haba mommy.... Da rayuwa da mutuwa ai duk na Allah ne" Imaan ta fada jikin ta na rawa,

"Imaan bana son in cigaba da rayuwa ina kallon wannan bakin cikin da Anaam ke ƙunsa min...... Bin mata? Koda yaushe yana tare da mace...... Abin nashi yanzu har yayi tsananin da zai shigo da mace cikin gidan nan babu kunyar idona? This is very unfortunate........"

"to ai mommy in dai hakane kamata yayi kici ki koshi kisha magani dan ki samu lafiyar da zaki yaƙi wadannan muyagun halayen nasa tunda ke kadai zaki iya tsawatar masa haka kuma ke kadai zaki iya hana shi ya hanu......"

"Imaan na gaji..... Na gaji gaba daya da halayen Anaam....."

"kiyi hakuri mommy.... Muci gaba da yi masa addu'a Insha Allah wata rana sai labari, Insha Allah ba zai dawwama ahaka ba Allah zai ganar dashi gaskiya kuma zai daina duk wadannan abubuwan, zai zamo miki ɗa na gari kuma sanyin idaniya, da yardar Allah sai kinyi dariya kuma sai kinyi alfahari da shi"

Cigaba da bata baki tayi har ta sauko domin cin breakfast din bayan ta umarce ta akan ta dauko nata itama su ci tare, murmushi Imaan tayi ta dauko natan ta zo ta zauna kusa da mommy suka fara karyawa, tana jin mommy tamkar uwar da ta haife ta saboda kyawawan halaye da kuma nagartattun dabi'u irin na mommyn. Tunda Anaam yayi fushi ya bar gidan sai da yayi kwana biyu sannan ya dawo nan mommy ta sake saka shi a gaba tayi masa faɗa tamkar zata doke shi, ransa yayi mutukar baci saboda a gaban Imaan ne shi kuma ya tsani yarinyar nan ya sake kulewa da ita kuma daga ranar bai sake fita ba saboda mommy tace kar ya kuskura ya sake saka ƙafarsa ya fita waje, ya za ayi shi ba mace ba a fara yi masa kulle a hana shi fita? Yana tsaka da wannan haushi da bakin cikin mommy ta kira shi a waya yana kwance ya rasa me yake yi masa dadi wai yazo yanzu yanzun nan,

"Imaan me da me kika ce ana da bukata a kitchen?"

"mommy shinkafarki ta kare, sannan babu wake sai dan kadan, semovita saura leda daya sai kuma sauran abubuwan bukata irin su spices da sauransu....."

"ok babu matsala zaku je yanzu ki siyo duk abinda babu...... Yau Kinga Anaam ya fita kuwa?"

"mommy gaskiya banga fitar shi ba, kuma ina ganin kamar wannan matakin da kika dauka a kansa yayi daidai saboda idan bai fita ba to ba zai hadu da abokai ko sauran yan matan dake zuga shi yana dauko magana ba...."

Shuru tayi sakamakon jiyo kamshinsa da tayi wanda ya gauraye cikin bedroom din cikin kankanin lokaci,

" ke....... Ke...... Ke yar aiki " ta jiyo yana kwala mata kira, babu shiri ta fita, yana zaune falon mommy ya dora kafa daya akan daya fuskar shi a daure,

"gani"

"ke ya sunanki ne? Indo kike ko inna.....?"

"Imaan..."

"whatever, kawo min ruwa mai sanyi...."

Kitchen ta shiga ta dauko masa ruwan ta kawo, kallon sama da kasa yayi mata kafin yace,

"maida wannan ruwan, ɗauko min coke mai sanyi...." Juyawa ta sake yi zuwa kitchen ta mayar da ruwan ta dauko masa Coke din kamar yadda ya bukata ta kawo ta ajiye a gabansa kuma daidai lokacin mommy ta fito daga cikin bedroom dinta,

"Anaam kuje da Imaan zata iyo min cefanen gida......"

Gyara zamansa yayi kafin ya fara magana cikin kunar rai bayan ya ajiye Coke din dake hannunsa,

"mommy yanzu nine zan dauki yar aiki in tafi in kaita kasuwa dan kawai zata iyo cefane? Yanzu mommy kaskancin nawa har ya kai haka? Me su malam bala suke yi da su ba zasu kaita ba ko kuma ta hau taxi amma sai ace ni....."

"saurara, malam bala tun jiya baya nan ko ka ganshi a gidan nan? Ai ba ita zaka yiwa ba ni zaka yiwa saboda abinda zanci zata je ta siyo min...." shuru yayi yana kunkuni sai kace karamin yaro,

"ta fito mu tafi...." daga haka ya tashi ya fice ita dai Imaan duk a tsorace take dashi dan harga Allah ba dan ba zata iya yiwa mommy musu ba da wallahi ba zata yarda ta bishi ba saboda tun tana yar karama take bala'in tsoron yan shaye Shaye kuma ta tsane su ko inda suke zama bata yarda tabi ta hanyar amma yanzu gashi zata fita tare da Anaam, wadatattun kudi mommy ta bata wadanda zasu isa ta siyo duk abubuwan da zata siyo, a cikin motar shi ta hango shi zaune amma yabar kofar a bude bai rufe ba, diriricewa tayi ta rasa ina zata shiga ta zauna gaba ko baya saboda bata son tayi laifi,

"ke zaki shigo ne ko yaya?"

Gaba ta bude ta shiga ta zauna a takure ya figi motar suka fita daga cikin gidan sai faman tsaki yake yi shi kadai. Tashin farko wurin da suke buga snooker ya fara zuwa yayi parking tana zaune aciki tana kallon sa ya fita ya barta aciki yaje ya zauna tare da karbar sigari a hannun wani ya fara busawa zuwa can ya tashi ya karbi sandar snooker din ya fara yi a takaice dai sai da ya shafe sama da awa ɗaya awurin sannan ya dawo cikin motar lokacin har ta gama ƙosawa da zaman da take yi tana ta faman jan tsaki a zuci da fili, kasuwa suka je ta shiga ta sissiyo duk abubuwan da suke da bukata, lokacin da ta dawo samunshi tayi yana waya da Najla wato LOML kamar yadda yayi saving no dinta, tana jinsa suna cigaba da hirar su shida masoyiyar tasa bayan sun canza harshe daga hausa zuwa turanci kuma ta yuyu yayi hakanne saboda ita watakila baya son taji abinda suke tattaunawa, maimakon gida sai taga ya sake kaisu wani wuri wanda bata san ko inane ba nan ya sake fita ya barta cikin motar sai faman kalle kalle take tana kallon masu shiga da fita amma jikinta ya bata duk yadda akayi wurin hotel ne sai dai ita babu wanda yake ganinta kasancewar gilasan jikin motar duka bakake ne daga wajen, tayi zaman a kalla rabin awa kafin ta hango shi suna fitowa shi da wata wadda kamar ta taba ganin fuskar ta, kafin su karaso ta ganeta dan kamar itace wadda ranar ta samesu a part dinsa tana zaune kan cinyarsa, yanzun ma gashi nan sai sake narkewa take yi a jikin sa kamar zata koma cikin cikinsa, sunkuyar da kanta tayi sakamako jin ya bude kofar motar zai shigo, ji tayi mararta tayi wata irin murdawa sannan ta kulle nan take, bata fahimtar me suke cewa saboda da turanci suke yin magana kuma anan dinma sai da suka ɓata lokaci kafin suka iya hakura suka rabu yaja motar suka nufi gida, suna zuwa bakin gate ya tsaya yace,

"fita...." bata yi magana ba ta soma tattara kayan ta bude kofa ta fita ta rufe masa kofa, ganin sa tayi ya fito da sauri ya sha gabanta har yana kokarin yin tuntube,

"shiga mota.... Shiga mota nace miki kin tsaya kina kallona, baki jin hausa ne.... Are you dumb?"

"ka barshi zan karasa..."

"ke dalla bana son bata lokaci nace ki shiga...."

Juyawa tayi ta bude murfin kofar amma kuma me gani tayi kan kujerar da ta tashi ya baci da jini wanda sam bata san da zuwan sa ba ita dai kawai taji mararta ta murda ta juya shikenan ashe bakonta ne yazo, wata matsananciyar kunya taji ta rufeta dan ta san shima abinda ya gani kenan shiyasa ya matsa da sai ta shiga ya shigar da ita ciki saboda kada sauran mutanen gidan su gani, zama tayi cike da kunya ta rufe kofar motar ya yi horn ya tura hancin motar ciki yana jan tsaki saboda harga Allah baiyi niyyar shiga gidan ba, wani wurin zai je amma wannan ta rusa masa lissafi. Parking yayi tana kokarin fita taji yace,

"ke shekarunki nawa?"

Kallonsa tayi amma taga ba ita yake kallo ba kawai gabansa yake kallo,

"27...."

"Amma shine dan tsabar dakikanta baki san lokacin da period dinki zai zo ba...... Zaki zo ki bata min sit din mota...... Ki shiga ki fito ki zo ki wanke min sit...." ba tace komai ba ta fita bayan ta kwashi kayan nan ya bita da kallon tsana da jin haushi aransa yana sake jaddada shirme da gidadanci irin nata banda haka ya za ayi kina abu shekara da shekaru amma ki kasa sanin time din da zai zo miki bayan yanzu gashi nan an waye harda su app ake amfani, fita yayi daga cikin motar ya nufi part dinsa yana jan tsaki........ ✍️

Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.

*Ummi Shatu*👌🏻