Chapter 2
by @khairatup01
Karamci Writers Association
(Karamci Shi ne tushen mu'amala tagari)
ZUCIYAR MUTUM
NA
Ummulkhair Sani Panisau
(Khairatup)
No.2
Tun jiya ake son ayi tashin hankali tsakanin Suwaiba da amaryarta Atika amma basu ga fuska ba daga mijinsu Yaya Amado mutum ne masifaffe shi ma baya daukar raini kusan kowa ma na tsoronsa gaskiya.
Can na jiyo dariya daga barin Aisha Indo da Maryamu suna ta karadi nan da nan aka cika sashensu ana kallo wannan ma sabon yan gidan ne ba a raba fada kuma ba a shiga tsakani sai dai in Baba ne ya shigo ko yayyunsu.
A kwance suka tarar da Aminu yana karkarwar da ya Saba. Ba damar a tambayeshi kudin cefane sai ya soma jijjiga wai za a kashe Shi an San ba shi da lafiya hawan jininsa ya tashi . Sai dai matan su nemo dan ko kofar gida baya fita wai hawan jini gareshi.
Su nemo su dafa ya ci yayi nak kuma ya kushe yace babu dadi.
To yau ma hakan ce ta kasance. Innarsu Menaali ce tayi wankau ta Samu kudinta dubu hudu rigis ta lallaba Tayo cefane tayi musu tuwu. Ya lamushe abinci tas ya kuma koma dakin Maryamu ya kushe abincin tas Ashe Indo taji sai fada ya barke shi ne ya zube a kasa yana musu makarkatar da ya saba su kuma suna ta fada a tsakaninsu da tsinewa junansu. Haka aka rasa mai raba wannan fada aka barsu da halinsu.
A barin Hadiza ma hakan take daman yau Baffah zai yi shari'arsu sun kama mijinsu sun mai bugun kashi har hakoransa biyu ma sun zube ya zama wawulo tamkar dai yaron da yake famfara.
Hadiza ta dauje masa baki da tabarya ta gurje masa shi wai aljannunsu ne suka tashi.
In zan fara lissafin abubuwan al'ajabi da dariyar da yake a cikin gidan gandu sai kun Sha dariya kun kuma kume takaici kala-kala.
Ni Uwanin Inna marainiyar Allah. Tunda na tashi nake Jin ana aibatani ance iyayena ba a san asalinsu ba lokaci daya suka shigo garin da zama maigarin wancan lokacin ya karbesu da hannu bibiyu har suka zama mazauna garin. Amma duk da haka ba a fasa yi musu gorin rashin asali ba. Tunda na tashi ban taba ganin wani yazo da sunan zuwa gidanmu ba wai ga yan'uwan mahaifana yau sun zo ba . Kwatsam Baba ya kwanta ciwo duk wani arziki da ya mallaka ya kare a neman magani kuma bai ma wani jima yana jinyar ba ya rasu. Sai aka bar ni daga ni sai Innarmu duk da ba wani sosai zan iya wassafota ba. Saboda ina da shekaru biyar ta rasu ita ma sai aka rasa mai daukata daga karshe abokin Abbana ya dauke ni ya maida ni gidansa. Sai dai tsugunne bata kare mini ba.
Matar Abba Halilu bata kaunata saboda yadda yake nuna mini kulawa. Ita kuma tana kishin hakan sabo da bata haihu ba ita. Komai ya samo zai kawo min ko furar dare ya sha sai ya rage mini. In za shi cin kasuwa tare muke tafiya da shi ya sai min kayan kwalliya da atampa wannan abu na bakanta ran Hajjo. In dai Abba yayi doguwar tafiya kafin ya dawo na fita daga hayyacina sai an san Abba baya nan. Don kayan nawa ma kwacewa take yi ko ta boye ko ta siyarwa dilalliya tayi ta aibatani. Sabulun wanka ma hanani take yi , haka zan yi ta walagigi duk in zama kazama. Abincin kuwa sai na yi mata ayyukan gida tsaf Shara,wanke-wanke,debo ruwa harda talla in aka yi rashin sa'a ban yo ciniki ba ranar bana samun na sawa a bakin salati sai dai in makota sun tausaya su bani.
Babu arabi babu boko. Ina da shekaru goma sha biyu komai na yanmatanci suka bayyana a jikina ina da jikin daukar ido kuma ina samun manema sosai. Sai dai a ciki na fi son Nata'ala a kan sauran saboda ya iya tsara magana da iya zance kamar wanda ya karanci yadda ake tsara zance.
Ganin shakuwarmu ya saka Abba nuna masa ya fito ayi bikinmu dake akwai sannaya tsakanin Baffah da Abba ba bata lokaci aka yi bikinmu musanmman ma da Abban zai yi kaura daga garin ya koma Minna.
Bayan aurena da Nata'ala muka fara fuskantar matsalar abinci saboda ba wata kwakwarar sana'a gareshi ba sai yan buga-buga don ma Yaya Habulle abokinsa amininsa na kawo mana abinci. Inno mahaifiyar Nata'ala tana kaunar shi sosai ta fi son shi da sauran 'ya'yanta. Masifaffiya ce ta bugawa a jarida bata dauke Kai akan yaranta matan gidan ma tsoranta suke ji sai abinda tace a gidan duk da yawanci ita tazo ta same su. Ba a son ranta aka yi auren Nata'ala da ni ba kawai dai bata isa ta ja da Baffah bane. Hakane ya saka ta ja wa Nata'ala kunne ba zai kasance ni ba har sai an samo asalina dan ba zata hada jikoki dani ba ko ya yarda ko ya sake ni akan dole ya yarda da hakan.
Wattaninmu biyar ya yanke shawarar fita daga garinmu neman kudi ya zo ya daukeni mu koma birni. Duk garinmu bani da wani gata sai na Allah sai na mijina sai dai ban san dalili ba ina ji a jikina akwai abinda zai faru sai dai ina fatan alkhairi ne.....
Ihun Inno ne da Sa'ade suka fargar dani hayyacina. Jikina nan-nan ya soma rawa saboda ina matukar tsoron baiwar Allahn nan ba kadan ba.
"Yau naga sabon abu kin shigo daka kin makale sauran ayyukan ubanki ne zai dawo yayi ko uwarki?"
Hawaye naji yana min zarya akan fuskata saboda yadda take zagin iyayena da kasa ta rufe musu idanuwa. A hankali nace "Kiyi hakuri Inno ban san an kawo ba." Haka ta ja tsaki ta kama haba tace "Sa'ade ji min kinibibi da makirci kuka salon ace wani abin na miki to ko za ki hadiyi yawu sai kin yi aikin nan ba mai ciyar dake a banza Wallahi me kashin tsiya."
Tashi nayi na daura dankwalina na fita. Shafaffen silifas dina na zura na soma harhada kan kayan amfani kafin magariba na kamalla. Tuwon ma na dora zuwa isha'i zan kira masu rabon su hattama kowa ya dauki na shi.
Sageeru ne ya shigo a make dama shi kadai ya fita zakka a gidan saboda shaye-shaye.
Kamar zai fado kaina haka ya nufo ni daman ya saba yi mini kallon banza tsoro ma yake bani aiko yana yo wa kaina nayi sauri tashi cikin rashin sa'a kuwa yayi taga-taga zai fado kaina ya fada da fuska kan robar tuwon da nake kwashewa ihun azaba ya saki ihun da ya jawo hankulan jama'ar gidan kaf kasancewar lokacin ne na dare kowa yana nan hatta da mazan ma.
Salati Inno ta soma rafkawa tana tafa hannayenta biyu ta kasa karasa ko da kalma guda ce .
"Uwani mai kika yi masa ke kuwa?" Inji Sabira.
Na soma murza hannayena biyu "Ban masa komai ba Allah. Zuwa yayi zai tabani na matsa sai ya fada kan robar tuwon."
"Zai taba ki"? Inji Gwagwon Zaure.
Inno ta sha mur "eh ikon Allah sharri za ki yi masa? "
Baffah ya tsawatar aka dauke shi aka yi daki da shi gefen fuskar sa ta tashi saboda zafi kun san dai konuwar tuwo Yadda take?(Jiki magayi)
Ranar dai Inno bata bari na sha ko ruwa ba. Can wurin garken dabobi ta kai ni wai a nan zan kwana tunda nayi wa danta haka. Sauro da zarnin fitsari da warin Kashi sun cika mini ciki ga yunwa ina ji gashi yau Yaya Habulle bai zo ba na fara yarda ya soma gajiya ne don da gajiya kullum babu fashi sai ya kawo amma yan kwana biyun nan baya zuwa matarshi ma ta sauya mini fuska. Allah ne kadai ya sa na tashi da safe sallah kawai nayi na kama aiki duk wadda na gaidar sai ta gwabamin bakar magana wai Ina kokarin lalata gan gida sharri nake yi masa na kona shi da gayya.
*
Washegari Nata'ala ya shirya tsaf yayi wanka ya kuma take cikinsa tsaf ya riga ya Gama tsara yadda zai samu mafaka a gidan nan dan shi ya ga wurin zama.
Wurin karfe biyu na rana Hajiya ta aika a
kira mata Nata'ala don sallamarsa kamar yadda suka alkawaranta.
Nata'ala ya zama dolo dan kauyen asali ya koma gidan ya tafi da imaninsa gabadaya. Baki sake idanuwa a ware yake bin ko ina da kallo ji yake a aljanna yake a fili yace "Kam lallai kudi suna birni ji wata aljannar duniya wannan wane irin gida ne?"
Mato ya kama hannunsa ya danke "Kai nutsu ,Hajiya bata son gidadanci Kar Ka ja min da ranar nan."
Nata'ala bai ce komai ba. Ya cigaba da bin Mato yaga an wuce falo biyu a wani karamin wurin mai dauke da kujeru guda biyu suka tsaya falon ya hadu ba hayaniya a ciki amma ya sha tsadadun Kaya.
Tsugunnawa yayi a kasa. "Hajiya barka da rana."
A yatsine ta kalle shi hakoran na yellow fatau sai taji amai ya taso mata da sauri ta dauke Kai daga kallonsa tace "Zaka bar min gidana yau kuma yanzu ba anjima ba Kada Ka kuskura Ka Kara zuwar mini gida...."
"Hajiya! Kiyi min rai ki bani aiki ko shara ne zan yi. Wallahi Ina da iyali iyayena masakai ne nine karfin gidan kuma bani da aikin yi ga mata kuma tana da ciki dole ta saka na bar gidan na fito neman kudi ki tausaya min...."
"Dakata Malam aiki Ka Kalli Kan Ka kuwa kazami da Kai. Ka juya Ka Kalli gidan nan da ma masu aikin gidan ka kuma kalli Kan Ka. Saurare ni da kyau baka isa ba..."
Tuni ya saka kuka ya hade hannayensa biyu yana roko.
Kan Hajiya ya fara ciwo ta daka masa tsawa ta nuna masa hanyar kofa "Ka tashi Ka bi ta inda shigo ka koma ta can."
Nata'la yaga da gaske dai korarsa za ayi ya ko tashi tsaye ya jujuya yaga ba a kallonsa kawai ya soma juyin karya karshe ya kife a kasa wai ya suma.
Ta kalli yan dakin tace "Suma again?"
Suka yi kasa da kawunansu. Ta saki tsaki tace " A fitar min da shi. A zo a goge mini wurin nan a saka hypo da turaren kamshi a gyaran wurin ya bata mini falo." Daga nan ta haye sama.
Suka cicibe shi suka yi waje da shi. A bakin gate suka zubar da shi da kayansa suka kulle gate.
Suna rufewa suka koma shi kuma ya tashi ya zauna yana takaicin wannan korar da aka yi masa amma ya saka a ransa ko ba nan ba sai na ya shiga jikin masu kudi ,kuma zai yi kome zai yi don ganin ya samu kudin.