03
by @nkds
SON ƘAUNA...🔥🏃💔
Story & Written by: Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡
03
“Kaɗaici ba?.”
Muryar Aani ta daki dodon kunnenta yayin da take zaune ta zuba wa tagar Ɗakin da take ciki ido tana hangen tsakiyar gidan marayun da irin girmansa gini ne da shi mai burgewa hakan ya ɗauki hankalinta daga nan ta faɗa duniyar tunani har batasan lokacin da Aani ta shigo Ɗakin ba sai saukar muryarta da taji.
“Tunanin Rayuwa kawai nakeyi.”
Emem ta bawa Aani amsa tana kallonta fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma Aani murmushin ta yi tana mai tsayuwa gefen tagar ya kasance gaba ɗayansu sun zubawa harabar gidan marayun idanu suna duba.
“To tun da kin ce haka faɗa min tunanin rayuwarki kike ko kuwa yadda yanayin Rayuwar gidan nan yake mai burgewa nasan kin fahimta duk da kasancewar ki ba Musulma ba amma na fahimci Rayuwar gidan yana burgeki kamar dai ni.”
Cewar Aani tare da mayar da dubanta ga Emem da ta ɗan yi shiru cikin nazari sai kuma ta ɗan girgiza kanta tare da faɗin.
“A rayuwata ta baya babu wani abu mai daɗi da zan iya tunawa har naji daɗi shi ya sa bana so ma na tuna, sai dai kamar yadda kika faɗa ina tunani a kan irin Rayuwar gidan nan da kuma addininku ji nake kamar na san wani abu dangane da addinin kamar dai nima irinku amma kuma idan nayi duba da wacece ni da wurin da na fito sai na kyale wannan tunanin a matsayin ni ce kawai ke ƙoƙarin ɗaura wa kaina kasancewar komai na addinin na burgeni a taƙaice dai ina da ra'ayin kafin na haihu ya kasance na zama ɗaya daga cikin mabiya addinin zan yi farin ciki idan abin da na haifa ya taso ƙarƙashin addinin musulunci koda a ce ban rayu ba domin bani da tabbacin zan ci gaba da rayuwa.”
Emem ta kai ƙarshen maganar tana kai hannu ta shafa ƙaton cikinta hawayenta na ɗiga a saman hannun nata haka kawai takejin karayar zuciya.
Ita kam Aani ta rasa farin ciki zatayi da jin kalaman Emem na faɗin zata musulunta ko kuwa ta a je farin cikin a gefe ta tausaya mata a kan kokwanton ci gaba da rayuwa da take ciki musamman duba da halin da take ciki rasa abin yi yasa ta rungumo Emem ɗin cikin wata kalar murya mai cike da annushuwa take faɗin.
“Da gaske ƴar uwata kin amince zaki shigo wannan addini namu na gaskiya addinin musulunci? Gaskiya naji daɗi maƙura na kuma tayamu gaba ɗaya murna na samun ƙaruwa ina yi miki fatan Alkhairi a sabuwar rayuwa sannan Dan Allah ki dena damuwa in sha Allah babu abin da zai faru dake zaki haihu kuma zaki tuna abin da kika gagara tunawa sannan zakiyi rayuwa na farin ciki tare da abin da kika haifa in sha Allah.”
Sakin Emem daga rungumar da ta yi ma ta Aani ta yi tana share hawayen tausayinta ta kamo hannun Emem ɗin suka zubawa juna ido kowacce idanunta cike tab da kwalla amma a hakan murmushi suke.
“Na gode sosai da kulawa Ƴar uwa Aani Ubangiji ya baki ikon tuna naki Rayuwar kema domin kin fini kasancewa cikin duhu amma da sannu komai zai wuce da yardar Ubangiji.”
Emem ta faɗa tana jinjina kai cikin son ƙara wa Aani gwarin gwiwa.
Aani ta share hawayen fuskarta tare da janyo hannun Emem tana faɗin.
“Ya kamata Maman Yara taji wannan daddaɗan albishir na musuluntar da zakiyi nasan zatafi kowa farin ciki zo muje.”
Ta ƙare maganar lokacin da suke fita daga Ɗakin, tafe suke tare har suka ƙari sa wurin da Aani ta tabbatar zasu sama Maman Yara wato cikin Office nata na gidan marayun, da sallama suka shiga ciki sai dai ganin Maman Yara zaune ga kuma wasu mutane mata da miji dake zazzaune ga kuma yaronsu, da alama magana mai muhimmanci suke yi da Maman Yara hakan ya sa suka ja burki Aani ta ce.
“Ayya, ashe bake kaɗai bace da baƙi kike tare bari mu jira daga waje.”
Ta faɗa suna ƙoƙarin komawa domin ita Emem har ta kusa ficewa, a tare mata da mijin tare kuma da Maman Yara suka juyo suna kallonsu sai dai banda wannan yaron dake zaune a cinyar matar.
“A haba ba komai ku shigo mana sai mun ma kammala dama ina shirin nemanku.”
Cewar Maman Yara cikin nutsatstsiyar muryarta mai cike da kamala.
Takawa suka fara domin ƙari sawa ciki yayin da salon bugun da ƙirjin Aani yake ya tsananta lokaci guda kuma jaririn dake cikin cikin Emem ya yi wani motsi mai ƙarfi da hakan ya tilasta wa Emem saurin dafe cikin nata cikin wani irin yanayi domin ji ta yi kamar yana shirin zazzagowa, a hankali kuma kyakkyawan yaron da kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yaro ne mai kyau da ya yi gadon kyau ya ɗago lumtsatstsun idanunsa kamar bayaso ya kuwa sauke su a kan ƙaton cikin jikin Emem ya ɗan zubawa cikin idanu na wani lokaci sauyin bugun zuciyarsa na canzawa kamar wanda ake kira haka ya sauka tsam daga jikin Matar tare da ƙari sawa wurin Emem da suke tsaye gefen Maman Yara dake zaune, tun da suka shigo idanun Aani yake kan yaron tana yi masa wani duba ga zuciyarta na azalzalarta game da yaron, lokacin da ya miƙe ya nufa Emem kuwa sai duk suka bisa da ido har iyayen, shi kam ko'a jikinsa ya ƙari sa ba tare da ya duba Emem da ta bishi da kallo tana jiran ganin abin da zai yi ba ya kai hannu ya ɗaura a kan cikin nata ai kuwa take cikin ya ƙara motsi mai ratsa zuciya sai ya yi murmushi tare da kai kunnensa saitin cikin kamar wanda za'a faɗa wa wani abu. “Assalamu Alaikum Ƙauna!”
Shi ne abin da yaron ya faɗa cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗin saurare bai kuma dena sakin murmushi ba.
Tun da ga kan mata da mijin da suke matsayin iyayen yaron da ido kawai suke bin sa suna mamaki musamman da ya kasance da wani boƴaƴƴen sirri a tare da su suka kalli juna ganin abin da ya yaron ya aikata domin sun sani tun da suka baro gidansu dalilin ƙaddara tare da wasu sirrika masu razana tunani, yaron bai yi ma kowa magana ba bare murmushi duk irin abin da za'a yi masa kuwa, haka ita ma Maman Yara kallon mamaki take yiwa yaron domin lokacin da iyayen suka zo da shi ba irin abin da ba'ayi ba yaƙi magana ita ta yi zaton ma kurma ne shi baya ji sai gashi yanzu ya yi abin da ya kawar ma ta da kokwanto ya kuma bata mamaki, Aani kuwa zuciyarta, ƙwaƙwalwarta da tunaninta ne suka nema dena aiki na ɗan wani lokaci jin saukar amon muryar yaron a tsakar kunnenta ta lumshe idanunta tare da buɗe wa cikin wani yanayi ji take kamar tana da wata alaƙa ta jini da yaron, Emem kam abin ya ɗaure ma ta kai musamman da ya kasance abin cikin nata ya ƙara wani motsi mai kyau lokacin da yaron ya yi masa sallama tare da kiransa da 'KAUNA' abin dai gunin al'mara.
Shafa sumar kan yaron mai santsi da taushi ta yi tana murmushi ta ce.
“Yaro ai ba mace bace a cikina da aka yi scanning an tabbatar da namiji ne.”
Yaron da ba zai wuce Shekaru uku ba ya ɗago yana kallonta da alamar kokwanton maganarta a fuskarsa sai kuma ya ce.
“Kauna ce wannan zaki haifa min ƙauna kuma ina SON KAUNA.”
Ɗakin ya ƙara shiru na ɗan lokaci kafin Matar da take matsayin uwar yaron ta miƙe tare da faɗin.
“Muhib! Menene kake yi haka? Dawo nan kaji?.”
Juyawa yaron ya yi yana kallonta kamar yadda su ma su Aani suka zuba ma ta ido.
Ba musu yaron ya koma tare da tsayawa wurin uwar sai dai bai dena kallon cikin jikin Emem ba tamkar numfashinsa ko kuma rayuwarsa ne tare da cikin.
“Kuyi haƙuri fa shirmen yaro ne kawai ba wani abu ba.”
Uwan da uban suka haɗa baki wurin faɗa. Da hakan ya dawo da hankulansu Emem kan su.
Ajiyar zuciya Maman Yara ta sauke tare da faɗin.
“Bakomai da alama so yake abin da ke cikin nata ya zama ƙawa ko abokinsa idan Allah ya kawo shi Duniyar lafiya...”
“Ko kuma ta zama abar Ƙaunarsa ba.”
Cewar Aani tana murmushi duk cikin son ganin ta dawo daidai ta bar tunane-tunane dake ƙoƙarin addabarta. Duk suka yi murmushi.
“Baƙi ne su a gare mu suna buƙatar taimakonmu a halin yanzu mata ne da mijinta sai ɗansu ɗaya kamar yadda kuke gani, Matar sunansa Ammiey mijin kuma Barau sunansa sai kuma ɗan kamar yadda kukaji uwar ta ambata sunansa Muhib, musulmai ne sai dai ƙaddarar da ta faɗa musu ya sa suka zo garemu domin neman taimako, ina fata kun fahimta yanzu zaku rakasu zuwa masauki da zai kasance nasu su kaɗai.”
Maman Yara ta ƙare bayanin ga su Emem tana yi musu nuni da mutanen sai a lokacin Emem da Aani suka tsaya suka ƙare ma mata da mijin kallo ba sa ce sun ga wata mugun kama tsakanin mata da mijin da ɗan ba, sai dai ganin yadda Matar take da hasken fata haka shima ɗan fari ne sosai sai hakan ya cire musu kokwanto da mutunta wa suka gaisa sannan kamar yadda Maman Yara ta buƙata suka kai su masauki mai kyau da zai wadacesu domin zuwa yanzu ita ma Emem ta san abubuwa da dama na gidan marayun kuma tana taimakawa sosai.
__
“Ma sha Allah, ma sha Allah amma naji daɗi sosai na kwana biyu ban shiga farin ciki kamar wannan ba kai Alhamdullilah.”
Maman Yara ke maganar cikin zumuɗi da farin ciki irin wanda Emem bata taɓa gani ba a tare da ita tsawon zamanta a gidan sai yanzu, da bayan dawowarsu daga kai mata da mijin masauki Aani ke sanar da Maman Yara a kan cewar Emem ta amince zata musulunta shi ne ta shiga wannan farin ciki mai girma tana kuma godiya ga Allah abin har kwalla sai da ya saka Emem kuma taji da ace tasan wannan hukunci da ta yanke zai saka wannan baiwar Allah cikin farin ciki kamar haka to tabbas da ta daɗe da faɗa musu amma yanzu ma ta yi farin ciki da ya kasance Maman Yara ta karɓe ta hannu bibbiyu kuma tsaban farin ciki Maman Yara har rungumarta ta yi ta rasa ina ta saka ina ta a je abin dai gunin burgewa.
Ai kuwa nan take ba tare da ɓata lokaci ba Maman Yara ta saka aka kira ɗan uwanta wato Alhaji Muzzafar da yake gidansa babu nisa da gidan marayun ai kuwa tun a waya ta sanar da shi wannan daddaɗan labari ta kuma umarce shi da ya taho da abokinsa Babban Malami da yake taimakawa sosai a gidan marayun wato Sheikh Sha'aban Isiyaka.
Koda ba wata magana sosai ko wani abu ne ke shiga tsakanin Emem da Alhaji Muzzafar ba amma sosai yaji daɗin musuluntar da zatayi ya kuma ƙara alfahari da ƴar uwar tasa Maman Yara domin ya san duk cikin ƙoƙari da jajircewarta ne ai kuwa ba tare da ɓata lokaci ba sai gasu shi da Sheikh Sha'aban Isiyaka sun hallara a gidan marayun, a taƙaice dai a wannan Ranar Emem ta karɓa addinin Musulunci a wurin Sheikh Sha'aban sannan kuma ya saka ta zaɓa sunan Musulunci a inda ta zaɓa Hauwa'u kowa ya yi farin ciki da hakan bayan wani lokaci gaba ɗayansu zazzaune suke cikin Office na Maman Yara a ta can wurin palo Maman Yara ce ta sai Alhaji Muzzafar da Sheikh Sha'aban da kuma Aani sannan sai mai gayya mai aiki Emem da ta koma Hauwa'u a yanzu.
Sheikh Sha'aban ya buɗe zaman da addu'a sannan ya ci da kiran sunan Allah da yabo garesa da kuma godiya ga Allah da salati ga Annabi ﷺ.
“Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Alhamdulillahi rabbil 'alamin. Wassalatu wassalamu ala Sayyidina Muhammadin wa ala alihi wa ashabihi ajma'in.”
Ya ci gaba.
“Yar’uwa, mun yi maraba da ke cikin wannan addini na gaskiya, addinin Allah, addinin Annabi Muhammad ﷺ. Mun yi murna da shigarki Musulunci, kuma muna roƙon Allah Ya tsare ki Ya daidaita ki, Ya sa ki a cikin sahun bayinSa na gari.”
Gaba ɗaya suka amsa da Amin. Sannan Sheikh ya ci gaba da tuna mata da rahamar Allah da muhimmancin sabuwar rayuwa.
“Kin yanke hukunci mafi girma a rayuwa — kin zabi Musulunci. Wannan zabi ne da ke nuna cewa Allah Ya nufe ki da alheri. Ki sani cewa dukkan zunuban da suka gabata sun shafe, kin fara sabuwar rayuwa mai tsabta. Allah Mai rahama ne, kuma Yana ƙaunar bayinSa.”
Sannan ya gangaro zuwa ga faɗakarwa da nasiha a gare ta.
“Yanzu kin zama ’yar’uwar mu a cikin Musulunci. Mu duka bayin Allah ne, kuma Musulunci yana koyar da ƙauna, taimako, da kyautatawa. Ki dage wajen koyon salla, karatun Al-Qur’ani, da sauran ibadoji. Idan kin buƙaci taimako, akwai mu anan.”
Ya ƙara da addu'a a gare ta.
“Allah Ya ƙarfafa ki a kan wannan hanya ta Musulunci, Ya ba ki zaman lafiya da natsuwa a zuciyarki, Ya sa ki a cikin bayinSa na ƙwarai. Allahumma thabbit qalbaha ‘ala deenika. Amin.”
Sannan daga ƙarshe cikin murmushi na kamala ya kammala da faɗin.
“Maraba da ke, ’yar’uwa. Muna farin ciki da ke. Allah Ya tabbatar da ki a matsayin Musulma har zuwa ranar da zaki hadu da Shi.”
Amin ya Allah duk suka amsa. Sannan Sheikh ya buƙaci Maman Yara a kan ta dage a kan nuna wa Hauwa'u (Emem) abubuwa da suka dace kamar yadda ake al'wala salla da sauransu duk da ya san ita ɗin gwana ce kuma zata dage kai da fata akan Hauwa'u, daga nan Sheikh bai wani jima ba ya yi musu sallama ya tafi kasancewar yana da tafsiri da zai yi a yammacin.
_____
To ma sha Allah Hauwa'u (Emem) Barka da shigowa Muslunci muna taya murna. Masu karatu labari fa yanzu zai fara zafi wai kuwa kun lura cewa labarin ba akan Emem (Hauwa'u) bane ba kaɗai kacokan a kan abin da ke cikinta ne da kuma wannan yaro Muhib! 🔥 Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin Nainarh KD domin jin yadda zata kaya. Mu kasance a shafi na gaba. Na gode.