🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Page 40
🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚
BOOK 1:CHAPTER 79&80
________________________"Congratulation sir,matar ka na da ciki sai dai bamu san wata ko sati nawa bane amman yanzu zan tura ta X-RAY dan a gane mana".
Tunda Dr ya fara magana Sani ya kasa ko da kyafta ido har sai da Dr ya dire maganar shi kafin ya samun damar fadin"dan Allah Dr da gaske kake kana nufin ma....ta...ta na da cikiiiiiiii!"ya karasa maganar shi yana nuna Hauwa bakin shi har kunne tsabar farin ciki.
Dariya Dr yayi yace"hmmm!taya zan maka wasa da hankali,abin da gwajin ya nuna mana kenan kuma yanzu zan tura ku X-Ray room dan musan watan cikin ko sati nawa ne cikin",ina fata ka gamsu.
Girgiza kai kawai Sani yake sai kace dan kadangare.
Yace"Dr nagode da wannan Albishirin daka bani,da badan bani da karfi yanzu ba da na maka kyauta na ban mamaki,nagode nagode nagode"ya fada tare da mikewa tsaye hannun shi rike da paper gwajin,da murnar shi ya dago Hauwa ya rungume ta ya suburbudo mata Addu'a tare da sa mata Albarka.
Sossai Hauwa ta ji kamar ta shige kasa sabida tsabar kunyar rungumar daya mata a gaban Dr ko kunya babu,dan karami. tsaki taja ta turo dan karamin bakin ta.
Yana sake ta tayi saurin janyo hijabin ta ta kulle fuskar ta da shi suka fice daga dakin.
Bayan minti Ashirin suka dawo,mikawa Dr paper yayi yana zumudi tare da Addu'ar Allah yasa cikin ya kai wata,dan shi har ya fara lissafin wata nawa ya rage mata.
Amsa Dr yayi ya warware takardar,bayan ya gama dubawa yace"masha Allahu Madam na da ciki na tsawon wata biyu da sati daya".
Kabbaran daya firgita su duka Sani yayi sannan ya kai goshin shi kasa yana godiya ga Allah.
Sakin baki Hauwa tayi galalaaaa..... tana kallan ikon Allah.
Dariya Dr yayi yace"tabdi",sai daya bari Sani ya sarara da murnar da yake sannan ya gaya musu dabarun da za su yi wurin kula da cikin sannan ya gaya musu mahimmancin zuwa awo da cin abinci mai gina jiki.
Godiya sossai Sani ya mai sannan ya cire agogon dake hannun shi da kudin shi zai kai kimanin dubu talatin yace"ga wannan Dr goron Albishir ne,wlh ina ga tunda nake babu Albishirin daya taba dadada min rai kamar wannan,nagode sossai Dr".
Kin karbar agogon Dr yayi yace"ka tafi aiki na ne i kuma na aiwatar karka damu jeka kawai,i ko farin cikin daka nuna kawai ya isa ba kamar wasu mazan ba".
Kin yarda Sani yayi har sai daya tabbatar Dr ya amshi agogon kafin suka bar Asibitin,ba su zarce ko ina ba sai gidan su Sani,ko sallama bai iya yi ba ya fada dakin Ammin shi, rungume ta yayi sossai yace"Albishirin ki Ammi".
Murmushi tayi tace"goro".
"fari ko baki".
Fuskar ta da alamun tanbaya tace"fari sidiq ma kuwa,wannan murnar naka da alamun tanbaya akan shi".
Dariya Sani yayi ya rufe fuskar shi yace"na kusa zama Baba Ammiiiiii......na girmaaaaa
...."ya fada tare da boye fuskar shi da hijabi yana dariya.
Murmushi Ammi tayi tace"shine baka taho da ita ba?".
Da sauri ya dago ya karewa dakin kallo yace"tare muke fah Ammi,i daga Asibitin ma muke,ina ga tana waje"ya fada tare da mikewa tsaye ya fice daga dakin.
A rakube ya same ta jikin kofa ta yi narai-narai da ido kamar kazar data fada ruwan zafi.
Riko hannun ta yayi dan su shiga ciki amman ta turje tace"ka gaya mata kohhhh!".
Murmushi yayi yace"i wannan wajibi ne,ke dai zo mu shiga ciki"ya fada tare da yin sama da ita.
A fili Hauwa tace"na shiga uku na lalace,dan Allah ka rufa min asiri ka sauke ni wlh zan shiga".
Mukus yayi kamar bai san tana yi ba.
Bai dire ta ko ina ba sai a gaban Haijiyar shi.
Yana ajiye ta ta rufe fuskar ta da Hijabi,bata taba sanin bai da kunya ba sai da ta sami cikin nan,lallai kam yanzu ta yarda cewa maza ba su da kunya sam.
Katse mata tunani Ammi tayi da fadin"diya ta ykk ya jikin naki?".
Kara sunkuyar da kai Hauwa tayi tace"ina wuni Ammi".
Ji take kamar ta fashe da kuka tsabar takaicin abinda Sani ya mata.
Amsawa Ammi tayi da murmushi,kunyar yarinyar na birge ta sossai.
Hannu Ammi tasa ta ja hijabin ta baya.
Kara sunkuyar da kanta kasa tayi,ji take kamar ta nitse kasa dan kunya.
Kwalawa diyar ta kira tayi,ba jimawa tazo.
Tana ganin Hauwa tayi ihu ta nufe ta da gudu ta fada kanta.
Ihu Sani ya saki yace"kehhhhh! mai haka,so kike kimin asara"ya fada tare da janye ta daga jikin ta.
Murmushi Ammi tayi tace"zaki ji mata ne,baki san ba ita kadai bace".
Zaro ido tayi tace"Ammi baby zamu samu".
Girgiza mata kai Ammin tayi alamun eh.
Ihu tayi ta mike ta fara tikar rawar da ba kida..................................
Kuyi hakuri da wannan,bazan muku Post gobe da jibi ba sabida ina da test har biyu ran monday so ina bukatar yin karatu,amman insha Allah za'a samu Monday ko Tuesday.
Comment
Vote
&
Share
By Gimbiya Ayshu 💞💞💞.