🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Page 42
🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1: CHAPTER 83&84
________________________Kwanan ta biyu a asibiti tana samun kulawa wurin likitoci.
Turo kofar dakin likita yayi ya shigo,bayan ya gama duba ta yace"Masha Allah jikin patient yayi sauki sossai".
Bayan ya gama duba ta yace"yanzu za muje dan a mata scanning sabida musan watannin cikin".
Kallan Jalal tayi ta kalli Dr fuskar ta cike da mamakin abinda Dr yace.
Binsu take kamar solobiyo har suka shiga dakin scanning,bayan an gama suka koma dakin da aka kwantar da ita.
Ajiyar zuciya Jameela ta sauke tace"Noor kalbi wai mai Dr yace ne ban gane ba kamin bayani".
Murmushi Jalal yayi ya karasa kan gadon ya rungume ta ya manna mata peck a goshin ta yace"kin kusa zama Mummy my luv"ya karasa maganar shi yana shafa cikin ta har zuwa marar ta.
Shiru tayi bata ce komai ba,daura hannun ta tayi a kan na shi hawaye na tsiyaya daga kwaryar idan ta.
Muryar ta na rawa tace"wai da gaske na kusa zama Mummy".
Girgiza mata kai Jalal yayi yasa harshen shi yana lashe hawayen dake zuba daga idan ta.
Lumshe idan ta tayi tana amsar sakon shi.
Rungume ta yayi yana shafa bayan ta yace"Allah yayi miki Albarka,ina kaunar ki sossai matata,Ubangiji Allah ya saukeki lfy kuma ya baki ikon rainon babyn mu lafiya Ameeeen".
Sossai Jameela taji dadin Addu'ar da yayi mata,shafa gashin kanshi tayi tace"ina Kaunar ka sossai Hubby na,ina alfaharin samun ka a msatsayin mijina,ina rokon Allah ya barmu tare,sai dai kashhhh! ina ji a jiki na bazan yi tsawon rai ba".
Rufe mata baki yayi da hannun shi yace"haba mana wani irin magana ce wannan,mai yayi zafi shi ba wuta ba,ki daina fadin haka pls bana so".ya karasa maganar shi ranshi a bace.
Murmushi daya karawa fuskar ta kyau tayi tace"yi hakuri Abban unborn na tuba bazan sake ba",ta fada hannun ta rike da kunnan ta.
Murmushi yayi jikin shi a tsanyaye dan sossai ta karyar mai da gwiwa.
Bayan awa daya Dr ya shigo daki hannun shi rike da paper,murmushi yayi yace"result ya fito"ya fada tare da mikawa Jalal yace"Alhamdulillah tana dauke da ciki na tsawon wata uku".
Rike marar ta tayi hawaye na tsiyaya daga idan ta yana shiga kunnen ta dan a kwance take.
Sujjadar godiya ga Allah yayi sannan ya dau waya da sauri ya fara trying layin Mami amman is not reachable.
Ya gwada ya kai sau goma amman not reachable.
Washe gari aka sallame ta bayan an hada ta da magunguna.
*****BAYAN WATA UKU*****
A yanzu cikin Jameela na da wata shida cikin yayi girma kaman wata maman twins,zama da kyar tashi da kyar,idan ta naimi wuri ta zauna bata tashi sai sallah.
Zaune suke a parlor Jalal na matsa mata kafar ta daya kumbura,tura kofar da suka ji anyi ne yasa su kai duban su zuwa wurin kofar.
Da sauri Jalal ya mike ya nufi bakin kofar kaman kiftawar ido fuskar shi da mamaki,baiyi wata-wata ba ya rungume ta.
Kokarin tashi Jameela take amman ta kasa.
Kallan su take fuskar ta dauke da murmushi.
Shafa kanshi Mami tayi tace"Son ykk nayi missing naka,ya matar ka?".
lafiyan mu lau Mami,munyi missing dinki sossai
Da haka suka karaso parlor,sai a lokacin Mami taga Jameela da tulelen ciki a gaba haihuwa yau ko gobe,janye Jalal tayi daga jikin ta fuskar ta da alamun mamaki take kallan ta.
Murmushi Jameela tayi kanta a kasa tace"Mami ina wuni,sannu da zuwa ya hanya",ta fada tana kokarin mikewa.
Dakatar da ita Mami tayi tace"yi zaman ki ba sai kin taso ba".
Yaushe aka samu karuwa ban sani ba,tsabar rashin mutunci babu wanda ya iya kira na a cikin ku,i kun kyauta i.
Dariya Jalal yayi yace"na kira ki a ranar da muka san da cikin lokacin cikin na da wata uku,na kira ki ya kai 10 times bai shiga ba,shine kawai na fasa gaya miki kuma na bari sai kin zo nayi miki suprise".
Dariya Mami tayi ta karaso inda take ta mana mata peck a goshi tace"Allah yayi miki Albarka ya sauke ki lafiya ya baki lafiyar shayarwa Ameeen".
"Yanzu fisabilillahi da kun gaya min da ban siya kayan baby a chan ba,gaskiya baku kyauta min ba gaskiya".
Dariya Jalal yayi yace"i yanzu ma bai baci ba zaki iya siyowa Mami,i da sauran lokaci at least 3 month plus".
Masha Allah,insha Allah hakan za'a yi Allah ya kaimu lokaci lafiya Ameeeeen................................
By Gimbiya Ayshu 💞💞💞.