🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Page 44
🌻🌻 MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
WATTPAD:Aishamaaruf1
I.G: Official_gimbiya_Ayshu
TWITTER: Gimbiyaayshu
BOOK 1:CHAPTER 87-88
_______________________"Mun yi nasaran ceto rayuwar ta amman ta zubar da Jini sossai,yanzu she's unconscious but muna sa ran farfadowar ta maybe cikin dare ko zuwa gobe insha Allah".Bayan ya gama magana ya koma dakin dan ya duba aikin da Nurses suke,bayan ya shiga ya ga sun gama shirya babyn tare da gyara dakin.
Baby ya amsa ya fito da shi ya mikawa Mami yace"ga yaron Mami Allah ya raya mana shi tafarkin Addin islam Ameeeen".
"Amsar yaron Mami tayi bakin ta har kunne,hawaye farin cikin ne ya zubo mata,wai yau gata dauke da jikar ta,ganin abin take kamar almara".
Sai Da ta dau tsawon kwana biyar a Asibiti kafin aka sallame ta.
Bayan Kwana biyu da dawowar su aka yi shagalin suna inda yaro yaci sunan Abie Abdulkareem amman za'a kira shi da Affan,anci an sha kuma an raba kyaututtuka na ban mamaki,su Mami sun kashe kudi sossai a wannan taron sunan kaman shine na farko kuma na karshe.
Su Mama sun Hallaci taron dan da ita aka yi komai na hidamar suna,Hauwa da Ummi kuma suna dakin mai jego,Ummi ta kanainaye baby kaman ita ta haife shi,duk wanda ya zo ganin baby in dai ba kawayen Mami bane da wa'inda suka fita ba toh ba taba kowa,sai dai ta ce a ga baby a inda yake kwance amman ban da dauka.
Kwanci tashi asaran mai rai,a kwana a tashi ba wiya in da rai da rabo,Hauwa tayi shekara daya da wata biyu da haihuwa,in kaga Muhammad Al-Ameeen(Amin) baza ka taba cewa dan shekara daya da dan kai bane sabida girman jikin shi,Amin Yaro ne mai shiga rai sabida tsabar kyan da Allah ya mai,babu ta inda ya baro Ammin shi,komai nata ya dauko.
Sossai Sani yake kula da matar shi da yaran shi,sai dai har lokacin bai da wani tsayayyan aiki yan bige-bige kawai yake ya ciyar da su,duk randa bai samu ba kuma haka za su lallaba.
Wani kyakyawan yaro ne zaune a kan kujerar yara da tebur a gaban shi,an mishi shiga ta alfarma,takalmin kafar shi sai kyalli yake,tebirin dake gaban shi ko shake yake da kayan ciye-ciye,an zagaye dika barandar da balloons da wuta mai kyalli,ba ka jin komai a wurin face kida.
Wata matashiyar mata ta fito hannun ta rike da cake mai hawa uku an rubuta Happy birthday Affan a jiki tare da hoton shi da aka dan makala da dan tsinke.
Tana ajiye cake din aka saki shine-shine wani saban kida ya tashi,nan aka fara shagalin birthday,ba su suka gama ba sai gab da magrib.
Jameela ta gayyaci Hauwa birthday dan ta amman bata sami zuwa ba sabida yaran ta baida lafiya an kwantar da su a Asibiti.
Ummi ta samu Admission a A.B.U tana karanta Medical Lab,duk ta rame sabida wahalan karatu,sati daya ya rage suyi jarabawar barin 100L.
Tun bayan suna Hauwa bata koma gidan Mami ba amman suna waya,ko Hauwa bata kira ba Mami zata kira.
Mama bata taba zuwa gidan Hauwa ba,Ummi tayi-tayi suje tare amman kememe Mama taki wai ba da ita za'a yi abun kunya ba.
In Mama ta fadi haka sai Ummi tayi dariya tace"Haba Mama sai kace yar kauyen da bata yi boko ba,ke fa yar birni ce dan kinyi karatu,dan Allah Mana ki watsar da wannan al'adar taku ta fulani kizo muje".ko kusa Mama bata kula ta sai dai tace"in kin gaji za ki bari ni dai baza ni ba atoh.
"Tabdi ni kam ba da ni ba,ni kila ma ni zan kai diya ta dakin ta,kuma duk bayan kwana biyu zan je in dubo ta".
Tsaki Mama ta ja tace"ke i dama na dade da sanin ba ki da hankali,i har abin da ya fi wannan ma za ki iya,ni kam ba abinda zan iya miki face Addu'ar Allah ya shiga lamarin ki ya sa ki yi hankali ki natsu".
Dariya Ummi tayi tace"Ameeeen Mamana amman ni gaskiya ta nake fada wlh sai na je dakin diyata muddin ina da rai da lafiya insha Allah".
"Ni kam tashi ki ba ni wuri na gaji da ke kin fiye surutu".
Kwanan su uku a Asibiti aka sallame sutare da tarin magunguna.
Ana haka rayuwar ta juye ya zamto ko abin da yake kawowa a dama ya gagara,idan suka samu abincin safe da rana aka ci,ba lallai a ci na dare ba.
Akwai wata ranar da ko abincin safen ma ya gagara,dan abinda take da shi a gida ya kare kuma mijin ta bai bata komai ba,gashi ta kasa tanbayar shi dan tasan bai da shi,ga yaron ta ya addabe ta da kukan cikin shi na ciwo,ita kuma ta san ba ciwo bane yunwa ce kawai amman ba ta da abin yi,da dai taga ba sarki sai Allah sai ta nufi kitchen,dama bata kai ga yin wanke-wanke ba,tukunyar tuwon data yi jiya ta nufa ta tsiyayar da ruwan ciki ta kankare kanzon tasa a roba ta zuba mai da yaji ta motsa ta bashi,da sauri ya amsa ya fara ci Kaman wanda yayi kwana biyu bai ci komai ba...........................................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.