🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Page 51
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 101-102
___________________________Ganin wanda ke tsaye a bakin kofar yasa cikin ta bada wani kara kulllllll!.
Wani miyau mai daci ta hadiye da kyar tana hada kalmomi kamar mai koyon magana tace"in....ina...kwa...kwa...........
Malama yi min shiru dan Allah,ba wannan ya kawo ni ba.
"Ina abinci na?"
Baki na rawa tace"em.....dama umm......yanzu umm....ban ban tashi da wuri bane shi yasa amman yanzu zan zan".................
Tsawa ya daka mata ya karaso dakin a fusace,bai yi wata-wata ba ya dauke ta da wani zazzafar marin daya sata sakin Ameeen ba tare data shirya ba.
Kukan daya fashe da shi ne yasa ta dawowa hanyacin ta.
Dukawa tayi zata dauke shi yasa kafa yayi wurgi da shi.
Ihu Hauwa tayi ta dago a fusace ta dauke shi da mari hagu da dama tana huci tace"kamin komai amman wlh banda yaro na".
Da mamaki yake kallan ta baki bude,cikin zafin nama ya kwance belt din dake jikin shi ya fara zabga mata ta ko ina.
Ihu take tana kuka tana rokon shi amman fir yaki,sai daya tabbatar ta daku tayi laushi kafin ya barta a kwance ya fice daga dakin.
Da rarrafe Ameen ya karaso ya kwanta a jikin Mamar shi yana kuka.
Ko dan yatsar ta ta kasa dagawa balle tayi kwakwaran motsi.
Ba ita ta iya jan jikin ta ba sai bayan la'asar.
Ameen ko yaci kuka har ya gode Allah,karshe barci yayi gaba da shi.
A hankali ta saukar da Ameen daga jikin ta,a daddafe ta mike ta jingina da bango tana sauke ajiyar zuciya kamar wata mai chutar asthma.
Sai data yi minti biyar kafin ta iya daga kafar ta daya,a haka ta daddafa har ta isa kitchen,ruwan dake flask ta juye sannan ta daura wani a kan gas,sulalewa tayi ta zauna a kasa hawaye na zuba daga idan ta.
Sai da ruwan ya tafasa sannan ta mike ta kashe ta juye ruwan tana haki.
Daukar ruwar tayi a hankali tana tafiya tana hutawa har takai bayi ta sirka ruwan.
Daukar Ameen tayi ta nufi bayi ta gasa mai jiki da ruwan zafi yana kuka yana ihu har ta gama mai wanka ta nade shi a towel ta kai shi daki ta shinfide shi a kan gado ta koma tayi nata.
Bayan ta yi wanka taji karfin jikin ta, kitchen ta nufa ta hada musu breakfast mai sauki a daddafe,hada nasu tayi ta daura a tray ta nufi dakin ta da shi,sai data tabbatar Ameen yaci ya koshi kafin taci,bayan ta gama ta bashi maganin rage zugi da paracetamol itama tasha,jin bata ji alamun motsin shi ba yasa ta kwantawa ta rungume yaron ta,Allah yasa tana fashin sallah,nan danan barci yayi awon gaba da ita sabida tsamin da jikin ta yayi.
Ba ita ta farka ba sai bakwai da minti hamsin na dare,da sauri ta mike bakin ta dauke da Addu'a.
Tana yin ido hudu da agogo tayi tsalle ta dira daga kan gadon tana salati,tuni jikin ta ya dauki mazari sakamakon tuna abinda ya faru dazu da safe.
Ba shiri ta nufi kitchen tana hada hanya, kayan Karin daya rage ta duma ta kai daki,tana shiga ta iske Ameen ya tashi,ajiye abincin tayi ta dauke shi ta kai shi bayi ta mai brush yayi fisari sannan ta dawo da shi ta bashi abinci da ruwa ta wuce kitchen.
A gurguje ta dafa jelof din taliya ya ji kayan hadi sai kamshi ke tashi ta ko ina.
Bayan ta kammala ta gyara kitchen tayi wanke-wanke.
Parlor ta nufa ta gyara shi dan babu abinda tayi a gidan.
Bayan ta gama ta rungume yaron ta suka zauna a parlor suna kallo amman rabi da quarter hankalin ta naga Sani,sam ta kasa yarda da abinda ya faru,gashi tana jin dacin marin shi data yi,ita a ganin ta bata kyauta ba.
Haka tayi ta zaman jiran dawowar shi amman shiru har tara da rabi bai shigo ba,gashi tana jin barci kuma tana tsoron ta kwanta ya zama matsala.
Daukar Ameen tayi ta kaishi daki ta kwantar da shi ta kashe wutar dakin ta dawo parlor.
Tun tana kallo Tv tana kallon agogo har barci ya kwashe ta,ba ita ta farka ba sai goma da minti hamsin da biyar.
Ganin inda take kwance yasa ta mikewa da sauri tana zare ido.
Mayar da kallon ta tayi ga bakin kofa tagan shi a bude.
A fili ta furta mai hakan ke nufi,juyawa tayi ta nufi dakin shi idan ta cike da hawaye,tana shiga ta iske babu kowa a dakin,a hakali ta karasa bayin ta tsaya tsawon minti biyu amman bata ji alamun saukar ruwa ba,tura kofar bayin tayi taga wayam babu kowa.
Juyawa tayi ta fice daga dakin.
Kara duba agogo tayi taga shadaya da minti daya,kwafa tayi ta zauna tana karkada kafa,ta cika tayi famm!,jira kawaii take a taba ta ta fashe.
Bata jima da zama ba taji shigowar shi gidan,har ya shigo parlor bata motsa ba.
Kamab kiftawar ido ta dira a gaban shi,sai huci take ta kasa magana.
Kallan ta yayi daga sama har kasa sannan yace"meh haka?,ba kida hankali ne za kizo ki tsaya min a gaba,kina hauka ne?".
Murmushin takaici tayi tace"ehhh!rashin hankali da haukar ce ta jawo haka",ta fada hannun ta rike da kugun ta tana karkada jiki.
Kara hada rai yayi kaman bai taba dariya ba yace"keh wlh tun muna mu biyu ki matsamin da gani in ba haka ba wl"........
Taran nunfashin shi tayi da fadin in ba haka ba ka kashe ni baaaa!,shine karshe.
Cizan labban shi na kasa yayi yana kada kai,ba tare daya ce komai ba ya bi ta gefen ta ya wuce.
Cikin bacin rai tace"ga abincin ka".
Tsayawa yayi kafin ya juyo ya kalle ta daga sama har kasa sannan yace"ki dube ni da kyau kinga na miki kama da mai jin yunwa".
Shiru Hauwa tayi kamar an dauke wuta,yana gabda shiga daki ya tsinkayi muryar ta tana fadin"toh ya kake so nayi da abincin?".
A hassale ya juyo yace"za ki iya kwalliya da shi a daki mtswwwwww",ya fada tare da shigewa daki ya murza makulli dan karma tayi gigin biyo shi.
Sulalewa Hauwa tayi ta zauna dabas a kasa hawaye na zuba daga idan ta tana karanto duk wata Addu'ar daya zo bakin ta...............................
COMMENT
VOTE
SHARE
BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.