🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻(GIDAN AURENA) BOOK 1.
Page 61
🌻🌻MATSALAR GIDAN MIJI🌻🌻
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU💞💞💞
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION📚
BOOK 1:CHAPTER 121-122
_________________________Kika kuskura kika matso kusa da ni wlh sai na sharara miki mari.
Shiru Lubna ta yi ta dafe kuncin ta tana bin shi da kallo har ya bacewa ganin ta,kara shafa kuncinta ta yi tana jinjina girman lamarin.
Direct emergency room aka nufa da ita dan bata taimakon gaggawa,sai safa da marwa kawai Ummi take ta rasa abin yi,ko kadan babu alamun natsuwa a tare da ita,idan ta yayi jazir kamar an zuba mata barkono,sai huci take tana haki kamar wacce ta yi gudun kilometer 500.
Bayan minti talatin da bakwai likita ya fito yana sharce zufa,da gudu Ummi ta karaso kusa da shi tana haki tace"likita ya ake ciki?,kar ka ce min ta rasu dan Allah,wlh ita kadai gare ni,ba ni da wata yar uwa sai ita,ka taimaka min dan Allah",sai a lokacin kuka yayi nasaran kufce mata,ajiyar zuciya likitan ya sauke yace"ki kwantar da hankalin ki,yar uwar ki tana raye bata mutu ba".
Ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tare da fitar da huci mai zafi daga bakin ta ta yi baya ta zauna dabas a kan kujeran dake bayan ta tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun kilometer 100.
Murmushi likitan yayi yace"na ga alamun kina san yar uwar nan ta ki sossai".
Hawayen dake gangaro mata ta share tace"ba dole ba,ita kadai gare ni,ita kadai ce yar uwa ta ta jini".
Murmushi likitan yayi yace"muje office dina dan na miki bayani",ba musu Ummi ta mike ta bi shi a baya.
Bayan ta zauna ya bude fridge ya dauko mata ruwa da coke mai sanyi ya aje mata a gaban ta yana murmushi yace"bismillah kanwata".
Murmushi Ummi tayi tace"nagode sossai".
Bayanin abinda ke damun ta yayi mata sannan a karshe yace"tana cikin matsanancin damuwa wanda yasa jinin ta yayi mugun hawa,kuma ta yi bari ta zubar da jini sossai amman an yi nasarar samo jinin da yayi dai-dai da nata,yanzun she's unconscious,za ta iya fargadowa nan da awa Arba'in da takwas,kuma bulalar da aka bige ta da shi ya ji mata ciwo sossai,amman insha Allahu komai zai dawo dai-dai,yanzu zan baki list din magungunar da za ki siyo mata da cream din da za ta shafa wanda zai goge tabon jikin ta".
A mugun fusace Ummi ta mike ta bigi table din dake gaban ta tace"he must pay for it",fita ta yi daga office din ba tare da ta amshi takardar da yake mika mata ba.
Maimaita abinda ta fada ya yi fuskar shi kunshe da mamaki,da sauri ya mike dan ya tare ta,ko kafin ya karso har ta shige napep.
Buga kafar shi ya yi a kasa yace"shitttt!".
Bata zarce ko ina ba sai gidan Hauwa,ko sallama bata yi ba ta bangaje kofar gidan ta shiga kaman za ta tashi sama.
Tana shiga parlor ta iske Lubna zaune a kan kujera ta harde kafa daya kan daya tana kallo da plate a gaban ta.
"Keh ina mijin ki ya ke?".
Juyowa Lubna ta yi ta kalle ta a wulakance tace"kin ba shi a jiya ne da kike nai"...........
Dauke ta da mari Ummi ta yi tana huci tace"dan uban ki ina mijin ki yake?".
Dafe kuncin ta Luban ta yi tana kallan ta tace"ni kika mara?".
Kallan sama da kasa Ummi ta yi mata tace"tantama kike ne?".
Hannu ta dago da niyyan ramawa Ummi ta rike hannun tace"kika kuskura hannun ki ya taba ni yau wlh sai na miki dukan da sai an miki dauri tun daga kan dan yatsar ki har kan ki".
Murya a kausashe tace"ina gantalallan mijin na ki yake?",tana hura hanci ta turo dankwalin ta gaba tace"yana inda kika aike shi".
Wani marin Ummi ta wanka mata sannan ta hau dukan ta kaman Allah ya aiko ta,sai da ta yi mata lilis sannan ta barta ta bincika duka dakunan ta ga baya ciki,fita ta yi ta tsaya a tsakar gida tana sintiri ran ta a bace,sossai ranta ya baci da bata sami Sani a gida ba,ta fi minti ashirin a tsakar gidan tana ta safa da marwa idan ta kyar a bakin kofar gidan tana jiran dawowar shi amman shiru.
Ganin babu alamun zai dawo a lokacin yasa ta barin gidan cikin bacin rai da kunar zuciya na rashin ganin shi.
Tana fita daga gidan ta nufi bakin titi ta shiga a dai-dai ta sahu,sai a lokacin ta tuna cewa bata sanar da Mama ba,bugu biyu Mama ta daga tace"ina Hauwa take?",ajiyar zuciya Ummi ta sauke tace"tana asibiti Mama ba ta da lafiya".
Jiri ne ya kusa kwasar ta,dafe bango ta yi tace"mai ya same ta ne Ummi?",ajiyar zuciya kawai Ummi ta sauke tace"zazzabi ne kawai",ta fada tare da dauke hawayen dake idan ta tana kokarin shanye kukan dake kokarin kufce mata,gaya mata sunan asibitin ta yi ta katse wayar.
Cikin awa daya Mama ta isa haraban asibitin ta kira Ummi suka shiga tare.
Murya a sanyaye Mama tace"mai ke damun Kulu ne Ummi?,sam ban yarda da abinda kika fada min ba,na ji a jiki na cewa Kuluwa na cikin damuwa,na san kin san halin da take ciki,ki gaya min dan Allah ko Allah zai sa hankali na ya kwanta".
Sharce hawayen dake idan ta ta yi tace"tabbas abinda na fada miki ba gaskiya bane,ta fada tana share hawayen dake idan ta,bazan iya sanin gaskiyar zanchan ba sai dai daga abinda na gani na tabbata an dau tsawon lokaci ana fama da wannan matsalar,ina shiga gidan dazu na iske yana dukan ta,ko kamin na yi wani kwakwaran motsi naga ya tokare ta a ciki,daganan kuma bata kara motsi ba har yanzu,likita ya ce tana cikin matsanancin damuwa kuma jinin ta ya hau sossai sannan ta yi bari,yanzu likita yace"bata cikin hanyacin ta amman ana sa ran zata iya farfadowa nan da awa Arba'in da takwas...
Dauke hawayen dake idan ta Mama ta yi tace"Allah ya saka mata,mun bar shi da Allah".
Wani irin murmushi Ummi ta yi tace"sai ya girbi abinda ya shuka da hannun shi dan bazan yarda ba".
Dafa ta Mama ta yi tace"bana san fitina Ummi ki bar zanchan kamar yanda nace,mijin na ta ya sake ta ne!"
Girgiza mata kai Ummi ta yi alamun a'a sannan ta dora da fadin amman zanje na amso takardar dan ba komawa za ta yi ba,indai shi kadai ne miji a duniya toh wlh sai dai ta mutu ba aure.
Girgiza mata kai Mama ta yi tace"bar shi karki amso,Allah zai dai-dai ta tsakanin su".
Girgiza kai Ummi ta yi ta mike tace"inaaaa! Mama,baki ga abinda idona ya gane min ba,wlh na tabbata idan aka bari Hauwa ta kara wata daya mai lafiya a gurin shi ina ga sai dai a kawo muku gawan ta,yau din ma i da ba dan na zo ba i da sai dai kawai sakon mutuwar ta ya riske mu".
Murmushi Mama ta yi tace"dama zaman aure ya gaji haka,wata rana sai labari".
Mikewa Ummi ta yi ta taka zuwa bakim window dake kusa da ita tace"wlh Mama sai na amso takardar nan,na san abinda kike tsoro,sabida haka ki bar komi a hannuna zan ji da shi........................................
By Gimbiya Ayshu💞💞💞.