DINGISHIN KWADO

4

by @surayyaibrahim

4

*Bojuwa herbs*

*Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?*

*Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?*

*Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?*

*Muna dafa ciccibin da yake ciki da mace, yake kyautata matuncin mace komin tsufanta*

*Kazalika muna sayar da saiwowin dahuwar idan ke kike so ki dafa da kanki*

*Muna dafa kazar sababi gangariya,mai saukar da niima da kuma hade mace*

*Akwia kuma saiwowin dahuwar idan zaki dafa da kanki*.

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida maijego*

*Bazawara package*

*Man ayun Chad da Marwa Wanda Babu algus, zumar silki kola*

*Hakkkn daka emergency na mussaman*

*Tightening set*

*Kudai ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin aminci da rahusa, bana siyar da abin da bashi da inganci*

*A Dade ana yi sai gaskiya*

**** what'sapp only*

A hankali ta yiwa motar ki ta hau titin da zai kaimu gidana da yake cikin Shagari lowcost.

Zuciyata ta buga ganin motarsa a harabar gidan tabbacin ya dawo.

Bamu tarar da shi a falo ba. Muka zauna Alawiyya ta kawo mata kunun. Ta sha, sannan ta mike tana gyara mayafin ta. Ta dauki jakarta ta kalle ni ina shirin tashi dan yi mata rakiya. Ta ce "Wallahi na yafe miki. Zauna ki huta, tunda kin sha magani ki kwanta ki yi barci idan kika tashi In sha Allah you will be better"

Na ce "Zan kokarta."

Ta tafi tana fad'in"Sai mun yi waya, ki sha magani, ki kuma kwanta ki huta sosai.

Fiye da shudewar sa'a ina zaune a falon ni kad'ai. Gyangyadi ya fara cafka ta. Na tabbatar a cikin magungunan akwai wanda zai saka ni barci. Baya ga hakan ma na ci bashin barci jiya.

Da k'yar na yunkura na yi dakina, ina yaki da sashen zuciyata da take son na je na gano halin da yake ciki.

Amma na daure na kwanta. Na fara barci na ji muryarsa tamkar a mafarki. Na bude idona da suka canja launi saboda barci da kuma rashin isasshiyar lafiya.

Fuskarsa babu fara'a ya ce "Tunda Basma ta zo ai yau kuma sai abin da na ga ni a gidan nan. "

Murya babu amo na ce "Babu kyau zato fa".

A hanzarce ya ce "menene zato a cikin maganata? Na ce zan kai ki asibiti kin k'i, saboda kin raina k'ok'arina! Amma da yake tana da tasiri ta shigo har gidana ta dauke ki, ta kai ki asibiti ta dawo da ke bayan ta gama yi miki hudubobin da na yi amanna na hure kunne ne. Kinsan ina gidan, amma ki kasa zuwa ki ga halin da nake ciki, ko ki tambayi ba'asin dawowar da na yi, sai kika yi kwanciyar ki saboda kin riga kin fara gina katangar karfe a tsakaninmu! Ya fad'a cikin bacin rai da ya bayyana a fuskarsa da gangar jikinsa gabad'aya.

Na zuba masa ido, na kasa ce wa komai. Domin ya riga da ya bari na fara fahimtar ainihin kalarsa. Ba abin da yake buguna irin idan na tuna yadda ya kaikace yake fad'awa yarinya k'ankanuwa maganata. Wai ni ba yarinya ba ce bare ya lallaba ni. Sa'a d'aya da na yi dai duk tsufana ya kere mini.

Na murmusa kad'an na dauke idanuwana akan kyakkwar fuskarsa da ta fara bak'ancewa a idanuwana. Na kuma yi amanna kishin da yake yagalgala ni ya janyo na ga bakinsa. Na kuma gamsu ba za'a dauki lokaci mai yawa ba zuciyata zata yafe masa, ta cigaba da ganin farinsa.

Ganin na yi shiru kuma ina kallonsa sai ya fahimci akwai al'amarin da yake zuciyata mai nauyi.

Ya matso ya zauna murya babu sukuni ya ce "Maman Amrah wannan kallon na ki, ina buk'atar fashin baki"

Na dauke idanuwana, na lumshe su ba tare da na ce kanzil ba.

Ya numfasa ya ce "Fad'a mini matsalar ki, ban gamsu da kallon da kike bina da shi. Haka nan ban gamsu da yadda kike mu'amalanta ta ba."

Na sake yin shiru. Don bansan abin da zance masa ba. Domin duk yadda na tunzura bazan iya bude baki na yi masa gatsali ba. To na ce masa me ma? Tunda ni na binciko kuttu da kaina.

Da na cigaba da dauke idanuwana daga kan wayarsa da ban ga abin da ya gigita ni ba.

Ya yi k'wafa ya ce "Basma ba zata ga alheri ba in sha Allah."

Har cikin zuciyata na ji rashin dad'in kalamansa.

A sanyaye na ce "Basma na cikin jerin masoyana, tana cikin wadanda suka damu da damuwa ta. Ban zaci zaka iya mata mugun fata haka ba."

Ya mik'e a kausashe ya ce "Yadda kika gamsu masoyiyar ki ce haka na tabbatar makiyata ce. Kuma ni Wallahi ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli ya ci riba."

Ya fice cikin sauri tare da bugo k'ofar da k'arfi tabbacin ya yi fishi sosai.

Na sauke nannauyen numfashi. Na furta "Subhanallah! A bayyane.

Zuciyata ta sake nauyi wato ko mun rabu ba shi da kaico. Na fara gasgata da gaske yanzu babu soyayyata a tare da shi tunda har ya yi irin wannan furucin tare da rantsuwa.

Ina kwance lamo ba abin da nake yi sai tunanin rayuwarmu. Tunanin k'alubalen da na ratsa. Hawaye ya silalo mini a dalilin mahaifina da ya fad'o mini.

Badakalar da ke faruwa a cikin zumuncin zamani na matukar tsorata ni.

Na sha jin labaran damalmalewar zumunci daban daban amma ban tab'a cin karo da irin na gidanmu ba

Ban tab'a ganin rashin kunya da mutunci irin wanda na ga ni a zuriarmu ba. Idan na tuna abin da ahalinmu suka yi sai na ji kunya da tashin hankali na rufe ni irin mai saukar da zazzabi da kasala.

*Bojuwa herbs*

*Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?*

*Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?*

*Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?*

*Muna dafa ciccibin da yake ciki da mace, yake kyautata matuncin mace komin tsufanta*

*Kazalika muna sayar da saiwowin dahuwar idan ke kike so ki dafa da kanki*

*Muna dafa kazar sababi gangariya,mai saukar da niima da kuma hade mace*

*Akwia kuma saiwowin dahuwar idan zaki dafa da kanki*.

*Bridal package*

*Maijego package*

*Uwargida maijego*

Bazawara package*

*Man ayun Chad da Marwa Wanda Babu algus, zumar silki kola*

*Hakkkn daka emergency na mussaman*

*Tightening set*

*Kudai ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin aminci da rahusa, bana siyar da abin da bashi da inganci*

*A Dade ana yi sai gaskiya*

**** what'sapp only*

Hakan na cikin dalilin da ya sanya bana kaunar aurena ya samu tasgado domin bana fatan na koma gidanmu da zumar zama mai tsayi.

Don kuwa ina cikin jerin mutanan da aka jarraba da rashin dacen uwa. Mahaifiyata wata irin uwace mai wuyar sha'ani. Mai yada bacin rai a tsakaninmu, mai yayata kuskuren da jama'a suka yi mata. Shiyasa gabad'aya mu y'aya'nta bamu da kwarjini ko farinjini a cikin dangi. Munanan dab'iun da ta cusawa mana ya sanya ake yawan rikici da mu. Domin duk wadda ta fad'a mana ya mata kaza zamu kullece shi tare da k'ulla adawa da shi, ba tare da tunani ko shakkar komai ba.

Hawaye ya silalo mini, domin ni da kaina na tabbatar muna shan zagi a idon duniya. Duk da ni kad'aice ban bi ra'ayin mahaifiyata da yan'uwana ba, amma hakan ba zai hana na shiga sahun y'aya'nta ba.

Na muskuta ina jin makakin bacin rai har cikin zuciyata don kuwa ina cikin matan da basa son tuna da d'insu. Domin ni gabadaya bacin rai da kuttu yafi yawa a kafatalin rayuwata. Tun daga rayuwar gidanmu har zuwa rayuwar aurena.

Amma dalilai masu yawa suka sanya na yi nufin yin bitarsu tiryan tiryan dan na lura bayar da labarin nawa na iya zama izna hadi da hannunka mai sanda ga mutanen yau, mussaman mata da sune iyayen al'umma. Ina kuma fatan duk wacce ta ji labarina zata yi duba na tsanaki ta laluba wacce irin dabia take aikatawa, shin kina cikin mutane masu manta tarin alkairai, akan kuskure guda daya tak?

Ku biyo ni sannu a hankali, ta yadda zaku fahimci inda na dosa domin kuwa mai tsananin aiki da lura ne zai fahimci Dingishin K'WADO.

Sunana Bilkisu Isa Funtua.

Ni y'ar asalin k'aramar hukumar Funtua ce ta jihar Katsina.

Ina matukar son garina, ina alfahari da kasancewata y'ar asalin Funtua. Shiyasa a duk sadda na samu sukuni na kan yi bita tare da nazarin garin namu.

Dan haka kafin na kutsa cikin labarin nawa sai na fara fayyace yadda garin namu yake.

K'aramar hukumar Funtua

Tana daya daga cikin manyan Kananan Hukumomin Najeriya da aka samar tun bayan gyaran tsarin kananan hukumomi da akayi a shekarar 1976. Ita ce kuma hedikwatar mazabar Katsina ta Kudu, wadda ta kunshi kananan hukumomi har guda goma sha daya (11) wadanda suka hada da: Bakori, Danja, Dandume, Faskari, Sabuwa, Kankara, Malumfashi, Kafur, Musawa, Matazu da kuma ita kanta Funtua.

Tana da girman murabba'i 448 km² da yawan jama'a (225,571 a bisa ƙidayar 2006) sannan kuma mutum 570,110 bisa ga ƙiyasin 2016. Shugaban shine shugaban karamar hukuma a hukumance. Mazauna karamar hukumar hausa Fulani ne akasarinsu, sana’o’insu kasuwanci, noma da kiwon dabbobi ne. Funtua tana da yanayi mai kyau yayin da take kan latitude da longitude 11°32′N da 7°19′E bi da bi. Garin yana da matsakaicin zafin jiki na 320C da zafi na 44%

Funtua tana cikin iyakar kudancin jihar Katsina. Shi ne birni na biyu mafi girma a jihar bayan Katsina. Tana iyaka da karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a kudu, Bakori daga gabas, Danja a kudu maso gabas, Faskari a arewa maso yamma da Dandume a yamma.

Har ila yau garin namu bashi da matsalar ababen more rayuwa irinsu ruwa da wutar lantarki.

Funtua tana da tashar watsa lantarki ta kasa mai karfin 132KV na National Grid da ke zuwa daga Mando tasha ta Zariya daga nan ta wuce Gusau ta tsaya a Talata Mafara. Yana da kyau a lura cewa tashar watsa wutar lantarki mai karfin 132kv/33kv da ke Funtua tana gudanar da ayyukan kananan hukumomi 9 daga cikin kananan hukumomi 11 da suka kunshi Gundumar Sanata Funtua. Yayin da rashin wutar lantarki ya zama ruwan dare gama gari a fadin kasar. Funtua ba ta da irin wannan matsalar saboda garin na samun wutar lantarki na tsawon sa'o'i 12-20 a kullum. Don haka duk mai sha'awar zuba jari zai iya zuwa ya saka hannun jari.

Dangane da Samar da Ruwa; An albarkaci Funtua da madatsun ruwa guda 2, wato; Mairuwa da Gwagaye da suke hidima da birnin da wasu sassa na majalisar Faskari da yankin Bakori.

Har ila yau, akwai gonar Songhai da ake amfani da ita don horarwa da noman wasu kayayyakin gona.

Haka nan Funtua ta haifi manyan mutane da suka yi shura a fannoni daban daban a jihar Katsina da k'asa gabad'aya. Bayan haka garina ne ya samar da tsohuwar marubuciya *Haj Bilkisu S Funtua.*

Allah ya kara lafiya uwar marubuta da makaranta.

Wannan kenan.

*MalaysianFabrics*

*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*

*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*

*7020695644