KARAGAR MULKI

Page 2

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*

*YOTA*

Book 2:Page 2


"Na yarda na amince Ashe dai da gaske ka ke mashayarku ta amsa sunanta na babbar mashaya dubi yanda ta cika ta batse ,dad`in gushi kuma ga shi na samu wacce ta ke cakar da ni cikin k`ank`anin lokaci", Narshad ya ce cikin muryar wanda ya sha yai mankas,muryarshi kanta ba ta fita yanda ya kamata.
      " Ai dama na gaya ma ka za ka samu duk wata kalar Giya da ka ke nema inda a cikin wannan mashayar ta mu ce kai har ma da tsala-tsalan mata mu na da su in ka na da buk`ata sai mu je in kai ka"......
     Da sauri ya katse shi ya na mai tashi a kusa da shi ya na tafiya ya na rangaji tamkar zai kifa,ya ce da shi ciki raba kalmomin bakin sa,"Tir Allah wadai da irin wannan zancen na ka me zan yi da wata mace ,ni ba ruwana da su ,Babu wata alak`a tsakanina da su kai ko hanya ba na buk`atar had`awa da su na fi buk`atar abun da zan sha in yi marisa, in rik`a jin kaina tamkar ina yawo a cikin gajimare,wannan shine burin Narshad, shine abinda ya ke so ya yi a duk sanda ya samu dama ya ganshi a cikin fad`in duniyar nan,da zaran na ganni a cikinta ba abinda na fi so irin in ganni da tulun giya a gabana",ya k`are zancen ya na mai kai ma k`ok`on da ke kusa da shi raruma da zumar ya k`ara sha. 
       Da sauri d`an tsohon ya kwace ya na mai cewa, "Ya Isa haka in ba haka ba za ka illata kanka wannan giyar ta na da mugun k`arfi kuma ba ka ga mutanen wurin sai kallon ka su ke ba ?",ya ce da shi,.
" A'a kar ka hanani domin wannan ita ce damata ba a kowanne lokaci na ke samunta ba don haka bar ni in sha sharafina yanda na ke so,su kuwa mutane ba ruwana da su bar su yi duk abinda su ke so",duk ya na wannan maganar ne cikin muryar maye da tangad`i.
"Ka ga zo mu tafi ka bar nan wajen wanne gari ka ke ?, fad`a min in d`ora ka a saman hanyar da za ta kai ka har gida",hannunsa ya kwace a cikin nasa ya koma can cikin k`uryar Shagon Giyar ya ce da shi,"Ni ba ni da Gari kuma ba ni da Gida, a iska ko saman bola na ke rayuwata nan shine Gidana ,Burkutu kuma ita ce rayuwata".
"Kaico ji mahaukacin yaro,ya sha har tafi k`arfin sa ya fara soki burutsu ina ka ga mutum ya ta`ba rayuwa a saman iska sai ka ce Aljani ma za taho in d`ora ka a hanya",ya k`are zancen ya na mai janyo hannunsa da niyar ya fidda shi da k`arfi amma ko da wasa ya kasa janyo sa kai ko motsin kirki bai yi ba,
"Kar ka hawalal da kan ka domin babu inda zanje nan d`in ya za ma Gidana don haka ba inda za ni har sai in"........ya kasa k`arasawa sakamakon hango gefan fuskarta da ya yi ta na tafe ta na magana Kuyanga Jazila ce ta kare fuskar yanda ba zai samu ganinta yanda ya so ba, kamar dai tsiwa ta ke yi ,kamar wanda a ka buga ma wani abu a saman kai haka ya fara waige-waige, da iyakacin k`arfin Zuciyar da na jikinsa ya fara k`ok`arin bin bayanta,sai dai ina ya Kasa ko da iya d`aga k`afarsa guda d`aya sakamakon nauyin da tai masa,idanuwansa sun mi shi nauyi k`ok`arin rufewa su ke ,Burkutun da ya sha tafi k`arfin sa ta dakatar da komi na jikinsa hatta ji da ganinsa ta d`auke ,Zuciyarsa ce kawai ke da zarrar da kuma sauran d`an k`arfi iya sarrafata wani abu,laluben hanyar da zai bi ya fara da nufin ya bi bayanta amma ina ko kusa ko da wasa ba ya gani daga k`arshe ma fad`uwa yai,sai ya koma da rarrafe ya ke neman hanyar fita,amma duk da haka bai samu nasarar fitan ba.
"Ka dakatar da ita kar ta tafi dan Allah Ummata ce nemanta na ke kar ta tafi ta bar ni dan Allah Um..Umma Ummata",ya k`are maganar a hankali ,daga k`arshe Giyar da ya sha ce ta ci k`arfin sa sai tuntsirewa yai a bakin k`ofar shiga ko fita na Shagon barci ya kwashe shi ba tare da ya shirya ma hakan ba.
"Haba Ranki ya dad`e Gimbiya Junainah mene ne amfanin zuwanmu cikin madaddalar mashaya,me hakan zai amfana ma na ?,ina laifin mu samu hanyar da za mu bar cikin wannan k`asar cikin sauk`i kamar da ya fi ma na"
   "Kin ga Kuyanga Jazila ki bar ganin kin girme ni nima ina da basira da hankali irin nawa, nasan duk inda ya kamata mu je ba tare da mun ci karo da Dakarun da su Sarauniya Junayyah su ka baza domin su gano mu ba".
     "To ban musa ma ki ba amma har a mashayar a na samun Dakarun Masarauta a ciki sai dai kawai mu yi fatan fita lafiya ".
" Da tun farko haka ki ka ce da abun ya fi zuwarmana da sauk`i,Ina mai tabbatar miki hankalin Dakarun su Malikat Juwairiyya ba zai ta`ba kawowa muna cikin mashaya ba za su yi tunanin mun bi hanyar da za ta fidda mu daga cikin Garin BAIBAH ne,don haka kai tsaye can za su,kin ga kenan munyi fargar haji kenan".
"Uhm tabbas na yarda da batun ki to amma dai banan za mu cigaba da za ma ba ko ?".
"Eh to nima ban sa ni ba amma dai haka zamu yi ta guje-guje har sai sun hak`ura da neman mu daganan sai mu samu hanyar da zamu bar cikin Garin BAIBAH ".
" To amma ai da so samu ne mu bar cikin mashayarnan mu samu wani wurin da yafi nan tsaro da mutumci nan gun fa har `yan iska na zuwa".
"Da alama dai hankalin ki bai kwanta da nan ba to zo muje wani wurin",da haka suka fito daga ma`boyar da su ka shige a cikin rumfunan da ke wurin kusan duk wajen sai da Giya ne.
Mutum biyu ne ke k`ok`arin shiga shagon Giyar ya ci karo da Yarima Haisam kwance lama-lama fuskarsa na kallon sama"Wai waye wannan ya sha tafi k`arfin sa ya zo yai ma na kwance a bakin k`ofa sai ka ce wani lusari shiyasa masu iya magana ke cewa ka bi duniya a hankali ka da zancen cikinta ya rud`e ka in ba dan haka ba me zai sa ya sha Giya har ta fi k`arfin kwakwalwarsa".
    `Dayan da su ka shigo tare ne ya ce da shi,"Yaran zamani kenan da yanzu za ka ce da shi ya aikata ba dai-dai ba sai yai niyar yi maka fitsara,gami da nuna maka idanunsa sun fi na ka bud`ewa kamata yai ace Idi mai shago ka zo ka janye shi ko ma samu damar shiga cikin lumana".
   "Barshi anan ya k`araci zamansa ko sa'a nawa zai,ya yi ya farka dan kanshi domin ni ba ni da lokacin sa ka ga yanda aka sha fartu da shi akan ya bar sha hakanan kar ta fi k`arfin sa amma ya k`i ni yanzu jira na ke ya farka ya biya ni kud`in Giyar da ya sha in ba haka ba ya ga yanda ake tujara",cewar Idi mai shagon Burkutu.
Wata dariya duka sauran mutanen mashayar su saki domin sun san sa sarai ba kirki ne da shi ba ba abinda bai iya aikatawa indai akan kud`in ne,ko kai waye ba zai d`aga ma ka k`afa ba,mutum na biyu da su ka shigo yanzu ne ya sa k`afarsa ya mirginar da Yarima Haisam can gefe yai rub da ciki,sannan suma su ka fara kwal`bewa da irin ta su Burkutun.
   Shigowar wasu Dakaru guda hud`u ya sa duk suka dakata da dariyar da su ke gami da mai da hankali akan su,domin su ji abinda ya ke tafe da su,"Da akwai wani fursuna da ya gudo daga Kurkuku, mahaukaci ne ,sannan ya na da k`arfi tamkar ingarman doki,don haka ana sanar da ku duk wanda ya ga bak`uwar fuska a cikin ku,yai saurin sanar da Dakarun da su ke mafi kusa da shi kada wanda yai yunk`urin ta`ba shi ko yayi motsin da zai gane,domin tamkar Aljani ya ke,sai kun bi a hankali da shi zai iya illata sama da mutun Goma a cikin d`an k`ank`anin lokaci".
        Da sauri mai shagon Giyar ya ce da su "Da zaran mun gan sa za mu sanar da ku amma ina so ku sa ni mu ma d`in jarumai ne za mu iya bada tamu gudunmuwar ko ya kuka ce abokai ?", Gabad`aya su ka had`a baki wurin cewa ," Haka ne, haka ne".
     "Tir a haka ku ke tunanin za ku iya aikata wani abun kirki alhalin duk Giya ta gama rarike duk wani abu da ku ka mallaka ta barku da wari da kuma tarin cuttuka,dan haka ba mu aiki fara shan miya ba balle ta zo mana da yauk`in baki",da wannan batun duk dakarun su ka juya su ka tafi ba tare da sun sa ke bi ta kan mashayan ba.
Sai da Yarima Sadauki ya kwashe tsawon wani lokaci ya na shar`bar barcin ba tare da ya sa ni ba ko ya shirya ma haka,shima sai da Mai shagon Giyar ya watsa ma sa ruwa sannan ya farka a gigice,da k`yar ya samu ya dawo cikin hankali da natsuwar sa ya sauke idanunsa a kan tarin mutanen da su ka zagaye shi duk `yan san ganin yanda za ta kaya a tsakaninsa da Mai Shagon Giyar ne domin su na da yak`inin ba shi da kud`in da zai iya biyansa Giyar da ya sha"Kai ashole tashi ka biya ni kud`ina tun kafin aji mu da kai ",yace da shi," Kud`i kuma, kud`in me ?",Yarima Sadauki ya tambaye sa.
"Kai yaro na fi ka zama cikakken d`an tasha,kud`in Giyar da ka sha za ka biya","Kud`in Giya ni d`in ?",ya sa ke tambaya a karo na biyu.
 Sai da Mai shagon Giyar ya kai ma sa shak`a sannan ya ce da shi,"Bud`e idon ka da kyau ka ga a ina ka ke,idan kuma ba ka gane ba nan mashaya ce,mashayar Giya Burkutu,ka sha ta kai tulu dan haka sai ka cake min kud`ina cas sannan za ka bar gun",ya k`are zancen ya na mai sakar ma sa wuya
Kamar yanda ya ce ya bud`e idon sa da kyau haka ya bud`e ya na ta faman rabasu akan duk abinda ya samu,kan tsohon da su ka zo tare ya fara sauke ganin sa da yai sai ya ji kamar ya gane sa ko ya ta`ba ganinsa a wani wurin amma ba zai iya tuna ina ya san shi ko me ye dalilin da ya za ma silar had`uwar su ba zai iya tunawa ba,har zuwa bakin fita daga shagon Giyar ya rink`a bin su da ido da sauri tamkar wanda aka tsikara ya zabura ya na mik`e tsaye ya nufi wurin da ya ga giftawarta a d`azu.
Cikin azama Mai shagon Giyar ya kama ma sa riga ya rik`e ta tamau ya na cewa,"Ina za ka ba tare da ka biyani kud`in Giyar da ka sha ba,to bari ka ji ko motsin kirki ba zan barka ka yi ba madamar ba ka biya su ba".
Cikin wata irin murya mai cike da amo ya ce da shi,"Ta na ina,Ina ta tafi mai ya sa ku ka bar ta ta tafi!!! ?".
"Kai d`an wahala wace ce ka ke tambaya,ko ma wace ce ban damu da ita ba,ban san ta kuma ba ita ce a gabana ba ,abun da na sani kawai ka bani kud`ina ato",ya k`arasa zancen ya na mai tofar da goron da ke bakinsa.
"Hmmmmm ba ka ji me na ce da kai ba kenan, Ta na ina,Ina Ummata ta ke,wanne waje ka ga ta nufa?",yai ma sa tambayar ya na mai k`ara kusanto da fuskarsa ku sa da tashi.
 Tamkar wanda ya huro ma sa iska da bakin sa haka ya ja baya da sauri ko kuma tamkar an sa k`ugiya an ja shi ta baya,ya tsorata sosai gani yai kamar wuta ce ke ci daga cikin idanunsa,cikin k`arfin hali ya ce,"B...bbbb....ban san wa ka ke nufi ba ni hasali banga kowa ba ma".
Wani ihu ya sa ki ya mai d`auke da k`araji gami da fallasa asalin sirrin da ke a cikin zuciyarsa ya na mai cewa,"Na ganta fa anan nan wurin Na ga giftawarta ,dan Allah ka nuna min ita Ummata ce ,ita na fito nema a duk halin da na ke a ciki in har zan ganta sai na gane ta ita d`in rayuwata ce,numfashinta da kuma bugun zuciyata".
Kamar wanda ya sha wani abun haka ya firgice ma su kafin ka ce me tuni ya fara yi ma su fashe-fashen tulunan Giya a wurin,duk wani abu mai amfani sai da ya lalata shi dagaske dai ya zama tamkar mahaukaci,bin su ya ke d`aya da d`aya ya na rok`on su da su fad`a ma sa ina ta ke ko kuma ina zai je ya sameta,amma ba ma wanda ya gane wa ya ke nufi balle har ya bashi amsa.
Cikin tsautsayi da kuma rashin sa'a d`aya daga cikin su ya zame bakin sa d`auke da tabar ganye,nan ta ke wuta ta fara kamawa a cikin Mashayar da sauri su ka fara k`ok`arin kashe ta amma ina ta riga da tafi k`arfin su, dole sai k`ok`arin ceton rayukan su su ka fara,suna fitowa daga cikin Shagon kamar walk`iya haka ya sa ke hango gefan fuskarta d`azu da farko `bangaren hagu ya gani yanzu kuma `bangaren dama ya gani ba tare da ya bi takan ihun gobara da mutanen wurin su ke ba ya bi bayanta.....