7
07
*Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*
*Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa*
*Malaysianfabricsng*
07020695644.
Kwanaki k'alilan na manta komai na durfafi karatuna. Bana biye wa rashin karatun Abida domin na riga da na san ba kwanyarmu d'aya ba.
Kwanci tashi muka dawo gida rubuta jamb.
Kwanaki biyu muka yi, muka sake juyawa dan rubuta jarabawar karshe.
Ranar 9 ga watan 9 muka kammala jarabawar karshe wanda ta zama ranar murna da doki hadi kuma da zullumin rabuwa da junanmu.
Ni da Basma sai kuka muke yi, Abida kuwa sai hidimarta take yi wanda Babu alamun kuka ko wata damuwa mai yawa.
Da ta gaji da ganin kukanmu sai kawai ta ce "To ku koma s.s.1 mana."
Basma ta zabura ta ce "To mu koma tare y'ar sarkin BAK'AR TA'ADAR cabawa mutane magana."
A banzance Abida ta ce "To na gaji da kukan munanfincinku. Haba da munsan junanmu? Allah ya had'amu, dukkanmu kuma munsan adadin zaman da zamu yi mu koma inda muka fito. Da lokacin ya yi muna da ranmu da lafiyarmu mai ya kamata mu yi?"
Ba wacce ta tanka mata. Ta numfasa ta ce "Sai mu yi fatan duk inda rayuwa zata kaimu mu kasance cikin aminci, ya kuma bamu sa'ar samun sakamako mai kyau. Mu da muka yi sa'a ma daga jaha d'aya muke, duk runtsi zamu dinga haduwa."
Jikinmu ya yi sanyi domin bamu yi zaton Abida zata sauko ta yi magana cikin kwanciyar hankali haka ba.
Basma aka fara zuwa d'auka. Har jikin motar na bita tamkar ba zamu rabu ba. Da k'yar muka bari direban ya ja suka tafi.
Abida tana daga kan akwatin kayanta ta ce "Ni fa Bilki na gaji da wannan kusancin naku da Basma. Ban son na ga mutane sun cika dagewa k'awance irin haka. Wallahi da bamu yi kandi ba sai na saka an bibiyeku haba wannan makalewar da kuke yiwa juna ta yi yawa "
Duk yadda na ji haushin kalamanta haka na daure na guntse baki ban tanka mata ba.
Domin na sani nice a ruwa, saboda ta fini harshen zaro magana.
Ilai kuwa ta kaikace ta ce "Da ni ce ke, murna zan yi, zan bar wajen da ake ce mini sola. Ke gabad'aya wata iri ce Bilki, har rasa ajin da zan saki ki nake yi."
Na sake matsewa ban ce komai ba.
Ita kuma ta kasa hak'uri ta sake fad'in "Wannan shiru shirun naki da kuttu yake sola."
Ko motsi mai k'arfi na ƙi yi, balle na biye ta. Kan dole itama ta kame bakinta domin tasan ba kulata zan yi ba.
Tsawon lokaci muna zaune jugum jugum sai na ji ta ce "Wato Bilki kina da hak'uri, kina da gudun mu yi faɗa. Albarkacin baƙin cikin da nake ta nausa miki idan na haihu zan ba ki abin da na haifa dan ki ta tunawa da ƙuruciyarmu da yadda nake miki sababi amma ki jure, kina sona na shaida, nima kuma ina sonki fiye da Yaya Munira da Yaya Faruƙu ".
Hawaye ya zubo mini na ce "Na gode sosai Abida, idan kuma Allah yasa kika ba ni ɗin wani a duniya ba zai ji ba ni na haifa a bakina ba, ba zan taɓa nuna banbanci da wadanda na haifa ba."
Ta matso kusa da ni tana share mini hawayen da yaƙi tsayawa ba tare da na shirya faruwar hakan ba.
Da ƙyar na yi jarumtar shanyen kukan na ƙaƙalo murmushi na ce "Amma so nake ki soni fiye da Yaya Asad".
Ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Ban iya ƙarya ba, ban iya yaudara ba, ban so wani cikin yan'uwana sama da shi ba. Dan haka ki yi haƙuri kawai Bilki".
Na dara kaɗan na ce "Na yi hak'uri Abidan Baba".
Ba jimawa Yaya Faruku ya zo, shi ya zuba kayan a but bayan mun je ya karbo mana pass din tafiya.
Na kasa sakewa na nuna masa farincikina na kammala sakandire, bare na bashi labarin abubuwan da suka faru.
Gabaɗaya alhinin rabuwa da class mate ya taɓa ni. Sannan Abida ta yi matuƙar sanyaya mini zuciyata da gangar jikina gabadaya. Haka nan sai nake ganin tamkar akwai wata ƙaddara da take ɗamfare a tsakaninmu. Tunanina ya tsananta, da na ga lallai ba fahimtar komai zan yi ba,sai kawai na hau yin istigifari.
Kan dole Yaya Faruku ya haƙura da rashin kuzarina, haka Abidan ma bata da karsashi kamar yadda ya santa da guntsi fesa. Da tuni ta ishe shi ya sayi jaridarta. Shi kuma da hanzari yake siya domin yasan mafi yawa labaran jaridarta nawa ne.
Baba ƙarami muka tarar a harabar gidan yana dakon isowarmu
a dalilin Baba babba ya je Lagos taron da gwamnatin tarayya ta shiryawa masu samar da Madara a ƙasa.
Ya karbemu da murna.
Muka tsugunna a gabansa muna gaishe shi domin shi din ba shi da haba haba irin baba Babba.
Ya amsa cikin sakin fuska tare da yi mana fatan alheri a cikin kammala karatun da muka yi.
Ya kuma ce "Yanzu ne zaku fara gwagwamarya da rayuwa, na roki kada ƙalubalen rashin samun abin da ake so ya sanya ku canja kyawawan ɗab'iunku, sannan duk inda rayuwa zata kai ku to ku zama wakilan addini musulunci da Hausa Fulani na gari abin koyi".
Murya babu amo muka ce "In Sha Allah Baba!
Kaitsaye sashenmu muka dosa domin kuwa mun riga mun san Baba babba baya tab'a yarda ya yi tafiyar da yasan zai wuce kwana biyu ba tare da rakiyar Momi ba.
Gabadaya Baba babba bature ne. Ma'ana a bayyane yake nuna soyayya ga ahalinsa. Baya yarda da al'adun bahaushe akan sha'anin aurensa. Duk inda zashi momi na gefensa. Amma Baba k'arami kuwa shine asalin d'an gargajiya gabadaya irin wannan rayuwar bata dame shi ba. Ga shi har digirin digir gir ya yi.
**
A wannan shekarar muka samu gurbin karatu.
Dukkanmu a A.B.U Zaria. Abida ta samu nasarar samun MBBS din ma'ana burinta na zama likata zai tabbata.
Yayin da ni na samu Nutrition and dietetics. A wanccan lokacin ban so kwas din ba, domin ba shine zabina ba, amma na hak'ura tare da fatan ya zame mini alheri, tunda ba zai yiwu na ce zan sake neman wani kwas ba.
Basma ma ta samu nasarar shiga jami'ar sai dai ita jami'ar Bayero ta samu, inda zata karanci lab science.
Baba k'arami tare da Baba Babba suka kaimu har cikin makaranta, bayan nasiha da jan kunne iri iri.
Ba abin da ya tsaya mini irin yadda Baba k'arami ya fito da al'amarin da yake ciwa iyayen yau tuwo a kwarya.
Da kakkauran murya ya ce "Tunda kuka iso duniya bamu huta da hidimarku ta kowanne bigire ba, har zuwa yau dinnan bamu huta da dawainiyarku ba, ba kuma mu tab'a gazawa ba. Bayan hidimar da muke yi muku da aljihunmu da k'arfinmu haka nan bamu tab'a gajiyawa wajen yi muku addu'ar shirya da samun nasarar rayuwa ba.
A yau da zamu kai ku jami'a wajen ka zo na zo, wajen da babu kwaba. Abun da zamu fad'a muku d'aya ne tal. Ubangiji ne wakilinmu akan tarbiyar da muka wanzu muna yi muku, idan kun taimaki kanku kun k'are mana mutunci kun kare naku, to kun tsallake kalubalen rayuwa mai yawa, idan kuwa kun ha'incemu kun watsar da tarbiyar da muka d'oraku a kai, kun jefa rayuwarku cikin garari da tashin hankali hadi da bak'in ciki marar yankewa. Ubangiji kuma zai mana sakayya. Ku kiyaye, ku kiyaye, kada ku kusancin zina bare ta baku sha'awa ku afka mata, masifarta yawa ne da ita, naso take yi.
Kun isa aure duk wacce ta had'u da namijin da ya yi mata, ya nuna zai aure ta ta turo mana shi, zamu aurar da ita babu jinkiri."
Gabaɗaya mun yi laƙwas kunya ta dabaibaye mu domin Baba ƙarami cire kunya ya yi sosai ya ding faɗin "Mun san sha'awa halitta ce, kuma kun kai shekarun da zaku buƙaci namiji amma kuma bata gurbatacciyar hanya ba, kada ku yi sanadin da zamu kunyata mu mutu da baƙin ciki dan Allah."
Nasihar ta yi matukar ratsamu, gabaɗaya kuka muke yi, har Abida da ta fini taurin zuciya.
Sun jima tare da mu a makarantar tare da Yaya Munira da a lokacin ta shiga ajin ƙarshe inda take karantar (Law) shari'a kevnan.
Haka suka barmu cikin jan kunne da nasiha iri iri.
Ba bangarenmu ɗakunan kwananmu ɗaya da yaya Munira ba.
Amma muna haduwa akai akai, yayin da muke ɗaki ɗaya da Abida haka abincinmu a haɗe tamkar muna F.G.C Bakori.
Sannu a hankali muke karatun har muka cinye shekarar farko. Yaya Munira ta kammala cikin nasara. Mun yi kewar rashinta a kusa da mu, domin sosai take yi mana alheri da saka ido a kanmu.
Cikin sa'a a wannan shekarar jamiar zata yi bikin yaye dubban ɗalibai(convacation).
Sosai muke ɗoki da murnar yaya Munira na cikin waɗanɗa suka yi sa'a baza su yi dogon zama kafin a yi bikin ba.
Kusan kowa ahalin gidanmu ya halarci bikin inka dauke Yaya Asad da bai samu sukunin zuwa ba. Domin bai ɗaɗe da komawa jihar Anambara ba, tare da ƙarin girma.
Amma hatta dukkan yayunmu mata da suke da aure sun zo.
Kwalliya muka yi ni da Abida sosai tamkar mune graduate ɗin. Hakanan mune mu ke kai komon hidima da ahalinmu a wajen. Su Baba sai farinciki suke yi, suna mana addu'a muma Allah yasa su ga namu bikin gamawar.
Gabaɗaya aka amsa da "Ameen".
Ɗiyar Yaya Zainab Anisa ta ce zata yi fitsari.
Sanin da na yi Abida bata yarda ta yiwa yara tsarki ya sanya na ruƙo hannunta na yi can gefe inda babu jama'a da ita, bayan na dauki ledar pure watee guda ɗaya.
Na ɗago daga sunkuyen mayar mata da pant idanuwana suka sarƙe a cikin na tsalelen saurayin da nake kwana nake tashi da tunaninsa.
Sanye yake cikin graduation gown wanda hakan ya tabbatar mini shima ɗalibi ne a makarantar.
Da murmushi ya ce "Duk yadda aka yi ke ce alherin da nake ta roƙa babu gajiyawa."
Bugun zuciyata ya tsananta domin ban taɓa zaton zamu sake haɗuwa ba. Ya tausasa harshe ya ce "Fara faɗa mini sunanki dana garinki. Dan kada ki sake ɓace mini".
Na yi ƙasa da kaina harshena ya yi mini nauyin da ban yi zaton zai yi a wannan saɗarar ba.
Ya kalli Anisa ya ce "ya sunan antinki?"
Ta ce "Anti Bilkisu."
Ya murmusa ya kalle ni ya ce "sunan ya dace da zubin hallitar da ubangiji ya yi miki, tabbas ke ɗin sarauniyar mata ce, kuma sarauniyar zuciyar Sahal."
Na kasa tanka masa, na kuma kasa tafiya na bar shi.
Kamar jifa Abida ta iso, na zuba mata ido ina kallon yadda take masa wani iron kallo.
Jikina ya hau ɓarin kada ta mini sanadin tsiya domin har zuciyarta na shaida bata ƙaunarsa tun hadɗuwarmu ta farko.
A sanyaye ta nuna shi da yatsa ta ce "S.S.Mashi again?
Da walwala ya ce "Tabbacin haɗuwarmu haɗin Allah ce. "
Ta rausayar da kai ta ce "Ubangiji ya yi zaɓin alheri."
Da karsashi ya ce "Ameen ƙanwar rijalu".
Dukkanmu muka yi dariya domin mun gane tsokanarta ya yi da nufin raha.
"Ya mayar da hankalinsa kanta ya ce baki tambayi naki masoyin ba?"
Taɓe baki ya yi tare da faɗin "Na mance ma yadda yake, ban sake tuna shi ba sai yanzu daka yi maganarsa."
Ya rausayar da kai ya ce "Da kinsan yadda Musawa ya rikice a kanki da kin ji kunyar wai kin manta da shi".
Kaitsaye ta ce "Ina abin jin kunya tunda ba dama zan bashi ba!
A sanyaye ya kalle ni ya ce "ina fatan dai Bilkisu zata ba ni dama."
Ban amsa masa ba, ya juya ga ABIDA ya ce "ki taimake ni kada ki hana a bani dama".
Ta maƙe kafada tare da ce wa "Matuƙar tana sonka ai fatan alheri ne nawa, abu da ba ni zan tayata ɗaukar jidalin ba"
A matuƙar sanyaye ya ce "Wanne irin jidali kuma?"
Ba fargabar komai ta ce "Tiritiri da matsalolin da ake shiga a dalilin auren yaro kuma mai bayanannen kyau, artabun da ake yi ai ba kaɗan ba ne".
Mamaki ya sanya ya kasa magana. Da ƙyar ya ce "da alamu idanuwanki sun haska miki ni a baibai".
Yana rufe baki ta ce "Ina da yaƙinin shekarar da shugaban ƙasa Fashola ya sauƙa daga mulki ka iso duniyar."
Ya kaɗu da furucinta domin kuwa hasashenta gaskiya ne, tabbas a wannan shekarar aka haife shi a ƙarshen shekarar ma.
Ganin ya yi turus ta ce "Ni nasan ba zaka wuce warin yaya Munira ba"
Ya haɗiye bacin ransa ya ce "Amma ina ganin ke zan baki shekaru shida zuwa bakwai."
Ta ƙyalkyale da dariya ta ce"Ka girme ni tabbas amma da shekaru uku da watanni, ita kuwa Bilki babu watanin ma".
Daga haka kuma ta silale ta yi tafiyarta.
Takaicinta ya shaƙe shi a dalilin ya gano bata maraba da soyayyarsa da ƴar'uwarta shiyasa ta shigo da wannan rainin hankalin.
Ni kuwa gabaɗaya na kasa magana domin ina tsoron jidalin Abida idan mun koma hostel.
Amma gabaɗaya na ji babu daɗi yadda take yi masa iyashege mai cin rai. Gefe guda ina cikin zullumin kada ta kore mini shi, ni kam ko na girme masa ina sonsa a haka bare sarkin kankanba ta ce ya ba ni shekaru uku.
A matuƙar sanyaye ya ce "Dan Allah saka mini lambarki"
Tare da miƙo mini wayar hannunsa.
Na karba na sanya masa.
Na fara tafiya ya biyo ni yana faɗin "Yayanki ne ya kammala ko Yayarki?"
Cikin nutsuwa na ce Yayata ce"
"Wanne course ta karanta?"
Ya tambaya a gajarce.
"Law". Da matuƙar mamaki ya ce "Ya sunanta?"
"Munirah Musa Funtua".
Na furta cike da alfahari, domin sunanta ya yi fice a department din art and social secience gabaɗaya.
Da mamaki yake girgiza kansa yana faɗin "Munee sister ɗinki ce?"
Na ɗaga masa kai tabbacin eh.
Ya ce "Munee gifted ce ƙwarai da gaske."
Kafin na amsa masa sai gata, sanye cikin irin rigarsa. Ta ce S. Mashi kai kaɗai anan?"
Tare nake da Bilki ƙanwarki, nifa na ga mata Munee".
Ta yi dariya tare da ce wa "Idan tana sonka ai shikenan".
"Idan bata sona ba zaki taya ni kamfen ba Munirah?"
Kai tsaye ta ce "Ni da ba ni zan zauna mata ba, kaga bai kamata kuma na tirsasa mata ba".
Ya ce "Hakane". Tare da sakin ajiyar zuciya.
Tare da yaya munirah suka shige cikin taron da alamu wani abu zasu yi.
Yayin da ni da Anisa muka koma cikin ahalinmu.
Sai yamma lis suka ɗauki hanyar komawa gida Funtua.
Yayin da Abida ta kaikaice take faɗin yau zuciyar sola sai Allah ta ga masoyinta.
Ban yarda na buɗe baki na tanka mata ba.
Amma matuƙar zamu zauna daga ni sai ita, zata kaikaice ta ce "Bilki yanzu sai ki amince da yaron nan? Na rantse miki fa da kad'an zai girmi yaya Munirah. Ya miki yaro da yawa, ga shi sololayi zubin makirai, kin ga Bilki ina raba ki da kisan mummuƙen namiji".
Ranar da ta fara faɗa mini wannan maganar na yi dariya ƙwarai da aniya domin yadda ta yi maganar tamkar wacce tasan kuttun ya'ya maza. Shiyasa a kullum ina tuna Abida sama da sau goma a rana. Domin komai ta faɗa mini a hankali nake ganinsu a cikin rayuwata, suna tabbata. Na numfasa na fashe da kuka ainun, sosai na yi kuka. Kukan da na tabbatar ba zan daina yinsa ba ila yau mil ƙiyamati sannan na cigaba da hakaito rayuwarmu tamkar a majigi.