MATAR MANYA

2

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 2

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Tafiya nake cikin yanga da taku ɗay-ɗaya wanda na san yana jan hankalin duk wani wanda yayi tozali dani, tasowarmu kenan daga Makaranta wacce nake ajin ƙarshe a Secondary. Sanye nake cikin Uniform ɗina kalar blue da fari wanda yayi matuƙar haska farar fata ta dake ta sheƙi sabo da tana samun isasshen gyara. Kai in ka ganni kai tsaye bazaka ce shekaruna duka basu wuce goma sha takwas ba sabo da yanda nake da cika ido, sai ka ɗauka ƴar jami'a ce ba ƴar secondary ba.

Tarkon dana ɗana kuwa ya kama kurciya domin wata zuƙeƙiyar Mota ce data zo wucewa ta dawo da baya tana min horn, yi nayi tamkar ban san dani ake ba nayi gaba ina jan ajina. Direban dake tuƙa Motar ne ya fito ya tare ni da sallama yace "Madame yallaɓai ne yake son magana dake, Bismillah." Ya faɗa yana nuna min Motar daya buɗe mun gidan baya inda mai gidan nasa yake hakimce a ciki.

Juyawa nayi zanci gaba da tafiya duk don jan zarena yanda ya kamata, amma a ƙasan zuciyata fata nake kar ya ƙyaleni yaci gaba da naci. Kamar yanda nayi fatan kuwa bina yayi yana cewa "Madame kin san waye kuwa yake son ganinki kike ƙoƙarin yiwa kanki baƙin ciki?." Jin abinda ya faɗa yasa zuciyata yin tsallen murna tana ayyana cewar ba ƙaramin kamu nayi ba.

Amma a zahiri sai na haÉ—e rai na fuskance shi nace "Ko waye shi ai bai kamata ya tare yarinyar mutane a titi ba ko?."

"Ke ba irin su yallaɓai ake yiwa musu b..." Sallamar da muka ji a bayanmu da wata dattijuwar murya yasa direban bai ƙarasa maganar ba ya juya da rawar jiki yana yiwa uban gidan nasa magana. Ni kuma da wutsiyar ido nake ƙare masa kallo ba tare da kowa ya lura ba. Babban mutum ne da a ƙalla zai kai shekara hamsin koma fiye da hakan, amma kallo ɗaya zaka masa ka san cewa naira ta zauna masa. Sai dai fa baƙine sosai irin mai shaining ɗin nan, ba za'a kira shi mummuna ba kai tsaye sabo da gyara da hutu sun ɓoye hakan.

Duka a cikin ƴan seconds ɗin da basu wuce goma ba na ƙare masa wannan kallon, "Wa'alaikumussalam." Na amsa masa sallamar kafin na ɗora da gaishe sa "Am kiyi haƙuri an tsayar dake a titi kuma hakan ba girmanki bane, ga katina idan kin koma gida ki kirani sai muyi magana." Ya faɗa yana miƙa min katinsa daya fito da shi. Hannu nasa na amshi katin na masa godiya nayi gaba abina.

Suna wucewa naji kamar in kwaso shoki tsabar jin daɗi amma na maze, ban san daga ina ya taho ba sai gani nayi kawai ya sha gabana ya miƙamin hannu "Bani katin nan." ya faɗa fuska a ɗaure ba alamar wasa.

"Wai Suhail meye haka kawai zaka sha gabana ba ko sallama kace in baka kati, ajiyarsa ka bani da zakace in baka." Na faɗa nima fuska a haɗe don ko mai zai yi ba zan bashi ba ya jawo min asara naga samu in ga rashi, don haka na ƙara damƙe katin a hannuna.

"Salma ki bani katin nan nace ko?."

"Bafa zan baka ba Suhail, gara ma ka haƙura."

"Wai me yasa kike irin haka ne, shike nan ke ba damar kiga Mutum da ƙatuwar Mota sai kibi ki tada hankalinki, kin manta cewar Allah shine mai azurta bawa a lokacin da yaso, Salma kin san ina sonki tsakani da Allah kuma aurenki zanyi amma kin ki tsaida hankalinki wuri ɗaya, haba Salma me kike nema ne a duniya ina sana'a ta dai-dai gwargwado kuma sannan ina karatuna, in sha Allah kafin lokacin daza muyi aure zan kammala karatuna kuma in sami aikin yi muyi aurenmu muyi zaman mu cikin rufin Asiri."

Yana maganar cikin rarrashi amma wani irin ɓacin rai take sa min, ji nake kamar in make shi wai wani yana sana'a yana karatu sannan in ya gama zai samu aiki, ni kuma ina zaune sabo da ga Salmar mahaukata in yi ta zaman jiransa sai ya samu aiki bayan ga manyan Alhazawa masu Naira a hannu ina gani.

"Kaga Suhail sai an jima, daga Makaranta na dawo ko hutawa banyi ba ka tare ni da Waɗannan magan-ganun naka." Na ƙare maganar ina yin gaba abina. Bin bayanta yayi da kallo yana jin rashin daɗi a ransa na abinda take masa, Allah ne ya jarabceshi da soyayyar Salma so mai tsananin da baya ganin laifinta akan abubuwan da take masa, duk irin tarin ƴammatan dake haukar son sa ciki harda ya'yan masu kuɗi amma bai ga wacce tayi masa ba sai ita, gashi ita kuma kuɗi kawai take ganin daraja da ƙimarsu shi kuma baya dasu shi yasa yake matuƙar shan wahalar ta.

A kullum bashi da burin daya wuce yaga ya faranta mata shi yasa duk abinda ya samu yake ƙoƙarin ganin ya kyautata mata, amma sai dai kyauta ɗaya wani saurayin mai kuɗi zai yi mata ta manta da duk tarin kyautatawarsa a gare ta. Hakan da take masa bai taɓa sawa sonta ya ragu ko kaɗan a zuciyarsa ba, shi yasa ya dage yake karatu tuƙuru yake kuma taɓa sana'ar sayar da katin waya, ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya nufi inda za shi.

*****Sallama nayi lokacin dana shiga zauren gidanmu wanda koda yaushe baya rasa mutane masu shige da fice wurin Baba Mari don sayen abincin da take sayarwa. Da Karima da Aliya na haɗu a zauren ɗauke da kwanikan abincin da suke sayarwa yayinda ƙannensu Maza ke ɗauke da manyan kulolin abincin sayarwar tasu.

Ido muka haɗa suka kalli juna suka bushe da dariya "Kaga ƴar Malam Shehu matar manya, da girman kujerarki." Karima ta faɗa cike da shaƙiyanci. Tsaki naja na tsartar da miyau nace "Ƴan wahala kanku ake ji, ku dai kuje kuyi ta fama da kayan talla kuna zaune wani hamshaƙin zai aureni, ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu." Ina gama faɗa nayi gaba na barsu suna cewa "Idan hamshaƙin bai aureki ba an ba wani almajirin sadakarki duk randa Baba ya gaji da iskancin da kike wa mutane ƴar mai da dogon burin tsiya." Aliya ta faɗa cikin jin haushin maganar dana faɗa musu.

"Oho dai kanku ake ji ƴan baƙinciki." Na faɗa ina ɗaga murya don nayi nisa.

"To sababbiya yau kuma keda waye kike faman yiwa mutane tijara daga shigowarki." Baba Mari ta faÉ—a daga bakin murhun da take sallamar masu sayen abincinta.

"Nida wanda ya shiga gonata." Na faÉ—a ina murguÉ—a baki na shige É—akinmu ina jin Baba Mari na faÉ—in "Uwarki Hadiza kika yiwa ba ni ba, fitsararriya mara kunya."

Zan ɗaga baki in maida mata Mama ta wurgo min wani mugun kallon daya sa naja bakina nayi shiru ina turo shi gaba. "Kin kyauta Salamatu, nace kin kyauta, ko me tayi min bake kika jawo ba, ai dama hausawa sunce ɗan kuka shike jawa uwarsa jifa. Ace baki da aiki kullum sai janyo min magana a gidan nan kullum ke Salamatu ko ƙannenki gasunan basa abinda kike yi, mai kike son zama ne wai ni kam?." Ta ƙare maganar tana kafe ni da ido.

"Allah ya baki haƙuri Mama, ni kam na matsu in gama wannan makarantar in samu wani Alhajin in aure in bar wannan azababben gidan in huta da ciwon kan Mutanen cikinsa." Ma ƙare maganar a hankali sosai yanda Mama baza taji abinda na faɗa ba.

"Allah ya shirya." Kawai ta faÉ—a ta kabbarta sallarta ni kuma na aje jakar Makararanta ta na shiga cire kayan jikina don yin wanka in yi sallar nima....

Oum Fatima