JOƊA

SHAFI NA 10

by @yarmutanargungu

Rufe bakinsa ke da wuya,  wayarsa ta fara ruri, har ta tsinke  be dauka ba,  sake kira aka yi a karo na biyu, "Alhaji ka dauka mana karta tsinke,  tare da  miƙa mishi wayar.
Daukar wayar yayi,  tare da sallama.

Azabure ya miƙe tsaye jin muryar wanda ya kira sa... har ya manta da ciwon da ke  ƙafarsa. Lukman, ya faɗa cikin sanyin murya.

Zuciyar Hajiya Falmata ce ke dukan uku-uku,  "Alhaji wane Lukman ka ke magana? Tare da fashewa da kuka tana me cewa Alhaji bani nima naji murya sa karya katse. Ganin haka ya sa shi  saka Wayar yadda za taji.

Lukman Ɗana kana ina?  A jiyar zuciya ya sauke jin muryar mahaifiyar tasa "Mama ba zan ce  muku ina lafiya ba, sabo da yanzu haka muna neman ɗauki kuma idan ba sa'a muka ci ba miyagun za su  iya biyo sawunmu!

Cikin kiɗimewa Abba ya ce;  Kaga Yanzu faɗa mana kuna ina?  Abu na biyu ku hanzarta ku isa wajen Jami'an tsaro ma fi kusa  karku wangarta.:

"Abba ku kwantar da hankulanku yanzu haka maganar da na ke yi maka muna cikin gidan Mai-gari,  Ofishin jami'an tsaro mun tarar yana rufe... " karka damu ina me- gari yake ba ni shi .Cewar Abba,  Magana Abba yayi da Mai- gari, ya faɗawa Abba sunan ƙauyen. kafin ya rufe baki Abba ya ce ku tsaya a nan ina zuwa"

Lambar IG ya kira kai tsaye, bugu ɗaya biyu aka ɗauka,  nan ta ke ya kwance mishi bakin jaa-ka.
kafin ka ce kwabo ƙarar Jirage  duk sun karaɗe Lardin Zamfara. Haka aka yi ta ɗauki ba-daɗi  tsakanin Jami'an tsaro da Miyagu mutane.
Bayan ƙura ta lafa aka ɗauko  su Lukman zuwa cikin gari, domin ba su taimakon gaggawa akwai waɗanda su ka samu raunuka.
   Tun cikin daren Abba ya kamo hanya, bai ko yi dubi da rashin tsaron da  ake fama da shi ba.

Washe gari aka shiga yi musu hidima aka ɗinka musu riguna, kasancewa mafi yawansu ba su da Suturur kirki a jikinsu.
Babu abun da ke tashi sai koke-koke, wasu ba za su iya komawa ƙauyukansu ba sabo da an ƙona musu gidajensu da Dukiyoyinsu, tare da Gonakinsu.

Kiran assalatu  cikin garin Gusau ta yi wa Abba Ya tsaya ya gabatar da Sallah subahi, kana ya iso gidan gwamnati.

Cikin girmamawa Kwamishinan 'yan Sanda  ya tarbi Abba, tare da cewa, "Ai da kayi zamanka ranka ya daɗe, mu da kammu zamu kai maka Ɗanka har gida."
"A'a, ai  gani da ido ya kori ji, ka ga jiya ko runtsawa ban yi ba,  na taso driver a gaba mu ka zo, sabo da kar ace mafarki na ke yi.  Amma ka ga yanzu da nazo na gansa, ka ga sai na ɗauke sa mu juya, baki alaikum ."

"To ba zan ce na ƙi batunka ba, amma kasan har yanzu yana ƙarƙashin Shugaban Soji, ( chief of army staff); kuma yanzu haka su na kan hanya, ya ce a riƙe sa har ya iso.  Sabo da tun jiya labari ya isa kunnensa cewa akwai ma'aikacinsu a ciki.
Cewar kwamishinan 'yan Sanda na Lardin Zamfara. (CP)

"Haka ne Ni da kaina na kira shi na sanar da shi halin da ake ciki. Ka ga kuwa ai babu matsala idan na tafi da Ɗana,  su kuma su riƙe aikinsu faƙat. Cewar Abba.

Su na wannan maganar ne a cikin gidan gwamnati, Abba da Kwamishinan 'yan Sanda da kuma Lukman.

Fitowar gwamna yayi daidai da shigowar shugaban Sojoji na  Ƙasa, wato Chief of Army staff) Haka aka yi gaisuwar ban girma a tsakanin su.

Gwamna ya jinjina wa Lukman ƙwarai da gaske, akan nuna jarumtakarsa.

San nan Shugaban Sojoji na ƙasa, shi ma  yayi nasa jawabi, tare da ban haƙuri akan rashin kula da ma'aikacinsu "hakan ya faru ne sanadiyyar Rundunar Sojoji  da mu ka turo domin kawo ɗauki a wannan Lardi a wancan lokaci,  sunyi gaba da gaba su da 'yan bindiga haka su ka yi ɗauki ba daɗi a tsakanin su, mun rasa mutanen mu da yawa, waɗanda su ka komo gida kuma sun tabbatar mana cewa su kaɗai su ka rayu, sai kuma gawarwakin da su ka ɗauko su ka zo da su, sannan suka ce mana  sauran sun ƙone a cikin wuta, hakan ya sa bamu bibiye ka ba. Amma a matsayina na shugaban Sojoji na ƙasa, muna miƙa jinjina ta musamman ga Lukman Abubakar akan ƙoƙarinka da sadaukar da rayuwarka wajen hidimtawa ƙasarka, kuma in sha Allahu zamu ƙara riƙe ka da kyau  Allah ya ƙaro mana irin ku masu yawa a ƙasarmu"

Su ka amsa ameen.

Bayan Lukman ya keɓe da mahaifinsa ya kwashe duk tarihin Joɗa ya faɗawa Abba, be rage komai ba, tare da roƙon mahaifi nasa akan su taimaka mata su tafi da ita gidansu.

Cikin tausayawa Abba ya ce " babu komai Lukman, amma ka  bari zanyi magana da gwamna sabo da a ƙarƙashinsa ta ke, zan roƙe sa ya bamu ita mu tafi da ita"

Rungume mahaifi nasa Lukman yayi tare da ɗumbin godiya a gare sa.

Abba be samu matsala ba wajen shawa kan gwamna, sabo da ya san waye Abba.

Lokacin da aka kira Joɗa aka faɗa mata abun da Abba ya ce game da ɗaukarta, ba tayi gardama ba,  to me za ta ce ita da za a taimaka wa ba ta da kowa a halin yanzu ba ta da gurin zuwa, babu wani nata wanda zata nuna,  ita da a halin yanzu take jiran mutuwarta. Hawayen dake malalowa daga kwarmin idonta ta goge a lokacin da take shiga mota.

Sauran jama'ar kuwa gwamna ya sa aka  sama musu wajen zama, wasu kuma zai sa a mayar da su gidajensu tare da alƙawarin  samar musu tsaro  da tanadar musu filayen da zasu yi Noma.

A can Maiduguri kuwa, kai da komo Hajiya Falmata ke yi, kasancewar tasan su Abba na hanya ga kuma ɗanta tilo za tayi ido biyu dashi a lokacin da ta yanke tsammanin sake haɗuwarsu a doron ƙasa, ita kuwa wace irin godiya za tayi wa Ubangiji. Abinci kala-kala su ka girka ita da ma'aikatanta.

Ƙarar buɗe get taji, Cikin sassarfa ta fita harabar cikin gidan ita da ma'aikatanta domin nuna farin - cikinsu.

Hawaye masu zafi suka zubo daga ramin idonta yayin da taji ɗumin Ɗanta a jikinta.

Shima hawayen ya share yayi kewar mahaifiyarsa ƙwarai da gaske.

Kowa yayi farin - cikin sake ganin Lukman.

Kallon Joɗa mama ke yi tun da suka shigo, amma ba ta ce komai ba. Sabo da tasan za taji ƙarin bayani daga me - gidanta.

Nunawa Joɗa ɗakin da za tayi wanka ta yi,  tare da ciro mata kayan da zata saka  bayan tayi wanka.

Ɗakin Abba mama ta shiga domin taimaka mishi wajen shiri , sabo da shima ba isashshiyar lafiya ne da shi ba, kawai ƙarfin hali ne irin na tsohon Soja.

Shi kuwa Lukman yana  ɓangarensa wanda ya sha gyara sai ƙamshin turaren wuta ke tashi. Fitowarsa kenan daga wajen wanka, ɗaure ya ke da Tawul a ƙugunsa, yana goge kansa da ƙarin tawul , jikinsa duk a mummurɗe ya ke da gani kasan ansha tirenin a wannan waje .

Zama yayi a gyafen gado yana tunano zamansa a wajen 'yan bindiga, shi da yake Soja ya azabtu iya azabtuwa ina ga waɗanda babu tirenin a jikinsu balle kuma a ce 'ya'ya  mata.

Ya kamata a ce ƙasar nan tasan halin da al'ummarta take ciki.  Numfashi ya sauke yana mai ci gaba da shiryawa, sabo da cikinsa ya fara kiran Ciroma

Dukansu sun hallara a teburin cin abinci (dinning table) Mama ta zubawa kowa abinci.
Bayan sun kammala, Abba ya dubi gefen da matarsa take, ya ce " Falmata ba ki tambaye ni akan yarinyar da nazo da ita ba?

Murmushi tayi, " Alhaji kenan, ai nasan duk-daren- daɗewa za ka yi mini bayani, sabo da nasan ruwa baya tsami banza."

Shima murmushin  ya  sakar mata, tare da ƙara son matartasa.

A hankali yayi mata bayanin komai kamar yadda Ɗansu Lukman ya sanar da shi.

Tausayin Joɗa ne ya kama Mama, tabbas ita ɗin abun a tausaya mata ne. kuma in sha Allahu za ta bada gudunmawa a rayuwar Joɗa matuƙar iyawarta.

TO! MASU SAURARE  WANE GUDUNMAWA NE KUKE GANIN MAMA ZA TA BA WA JOƊA?
YA RAYUWAR JOƊA ZA TA KASANCE A CIKIN GIDAN ALH ABUBAKAR?

KU BIYONI DOMIN JIN YA ZATA KA YA.

KARKU MANTA KU YI...

    **SHARE

    **SUBSCRIBE A YOUTUBE CHANNEL ƊI NA ME SUNA ( FATIMA ZARA AL HASSAN)

      **WATTPAD ( Ftmzara)

       **AREWABOOKS