Chapter 02
JANNATAN WA HARIRAH
Daga Alƙalamin Asral G....✍️
WhatsApp number
***
Only WhatsApp.
رَبِّ ٱشْرَحْ لِى صَـــــدْرِى ﴿٢٥﴾
وَيَسِّـــرْ لِــىٓ أَمْــــــــــرِى ﴿٢٦﴾
وَٱحْلُلْ عُقْدَةًۭ مِّن لِّسَانِى ﴿٢٧﴾
يَفْقَـــهُوا۟ قَـــــــــــــــوْلِى ﴿٢٨﴾
𝐏𝐀𝐆𝐄 02
Yaro Allah ya maka Albarka, yayiwa iyayanka albarka, ni godiyace ta kawoni domin a jiyane yarinya ta a hanyar zuwa makaranta aka saceta, mun shiga tashin hankali ba kadan ba, yau tunda Asubah sai ga yarinyar mu ta dawo, na tambayeta miyafaru tace bayan sun dauketa suka kaita wani guri suka daureta, suna cewa, itace amaryar ogah a daran yau, da rana sun kwamceta sun bata abinci takasa ci, suka cilasta mata bayan taci, suka sake daureta, zuwa dare taga sun dawo a gigice tare da ogan nasu, taji suna cewa aminu dawa ne yadawo, cikin daran nan sun ganshi ma, haka yasa suka kwanceta, ogan yace Idan anyi sallah asubah sukaita gida, sannan karta fadawa kowa, sune suka ɗauke ta, to ammah kasan halin mutanan unguwa, shine suka fara tsegumin, taje dakin saurayi dai acen ta kwana, sau yau ta dawo, maganar ta daki zuciyata sosaiii, ina godiya ga Allah da ya dawo muna da kai a wannan gari.
Dan Allah ka taimaka man, a gane ko suwaye, dan a wanke, yarinya daga wannan zargin.
Ya gama magana, yana mai haɗa hannayansa, alamon roqo.
Gyaɗa mashi kai kawai Aminu yayi, yacewa jazuli, katai abincika suwaye, idan kasamu labarin su da inda suke, ka kirani a Waya, kasanar dani, sai mu Diran masu a Daren yau.
Sannan wani dattijo ya tashi yace, ni sunana malam musa ba a garin nan Nike ba, mu makwabtanku ne, jin ka dawo a daren jiya, na kamo hanya nazo, akan hanya na kwana, dan haduwa dakai, ni manomi ne, nayi noma sosaiii, dan a kakan wannan shekarar zan aurar da ƴarta, na kwashe hatsin nasakashi a cikin runbun cikin gona dan idan ya bushe abuge nakawoshi akawoshi gida, to ammah wasu azzalumai, sun hanani daukar ko kara wai yazama nasu, koma wallahi ga Allah nadugara ga wannan noman na dogara dan Allah ka taimaka man.
Aminu yace to, yanzu naji korafi biyu ayau, kuma insha Allah, zan magance su dan haka, kutaso muje yanzu, muraka wannan Bawan Allah, ya kwaso hatsin sa.
Suna tashi suka hau mashonan su, nan take suka shiga garin, bayan kwashe awa ɗaya, suna gudu a mashin ɗin, suna shiga garin, suka wucee gonar, malam Musa, anan suka tarar da wasu miyagon mutane, duka jikin su lulube yake da fatar damisa, babu gashi akansu anyi wani Zane akansu, zannan kamar wani tambarine sannan ga wasu yan kunne akunnan su, yan kunnan na haukorin wata dabbace.
Da qasusuwan giwa a hannunsu, ga alamu sune maka man nasu.
Nan take aminu ya ja kwakiyarsa, ya nufacesu, muda kuma ya rufamashi baya, da hanwanginsa sannan sauran yaransa suka bi bayanshi, kowa da makaminshi, hannu ɗaya hannun, makamin kai sarane kamar ada, takobi, gario, barandami, mayan yaran kuwa ƙwakiya ce ko hanwagi, waƴanda ke qarshe acikin yaran Aminu, suke da gatari mai shegen tsini da kaifine a hannunsu dashi suke faɗan, shikuma ɗaya hannun kokarace ta kare dukan amatsayin garkuwa, nan suka nufacesu sai da Aminu yakaiwa dab dasu, muda yajefa mashi kokararsa yacafe,.
KUDA KACENI INA DAWOWA BARI MULEQA SABON BIRNI.
Wata matashiyar yarince, siririya baƙace, sai dai baƙinta mai kyau ne, dan fatarta kamar jikin maciji, harwani daukar ido fatarta jikinta keyi, tanada tsayi dai dai misali, hakan ya bayyanar da rashin qibarta.
Saukowa takeyi saman matattakala, harta qaraso cikin parloun, da gudun tanufi wajen wata mata dake cikin parlourn, ta rongume matar tana cewa ina kwana mom.
Ɗaga kanta kadan matar tayi tace ni sa'ankice da zaki faɗoman haka to a haka addini ko al'adar mu ta hausawa suka ake gaishe da iyaye ?.
Jannat ki dai na wannan shirme na yara dan yanzu kin girma shekara 17 ba wasa bane.
Kai mom zaki fara wa'azin nan naki shekara 17 ai ba wasu bane ni gaskiya har yanzu yarinyace.
Hmmmn Allah ya shiryeki jannat ameeeen momeena dama fita zanyi.
Fita kuma zuwa ina kinsan dadynki baya son yawan fitar nan dakikeyi.
Haba mom nasani ammah ba jimawa zanyi ba yanzu zan dawo shopping nakeso nayi dan chocolate ɗina sun kusa qarewa.
Hmmmn sai mugun shan zaki ai gashinan kinki yin qiba.
Haba mom wake son qiba kuma nidai yanzu sai na dawo.
Har takai kofar parlourn momee takirata da qarfi.
Ke a haka zaki fita babu mayafi ?
Mom kin manta a motafa zan tafi miye kuma na saka mayafi kamar wata matar liman.
Cikin dakewa momeey tace ko bata matar liman kike ba ai diyar musulmai kike dan haka kije ki saka mayafi kafin ki fita idan ba haka ba Dad dinki zan fadawa kin fita.
Da sauri ta dawo cikin parlourn tace to momeey bani wannan mayafin dan bazan koma dakina ba gaskiya.
Mayafin momeeyn ta karba ta fita.
Mom dai da addu'ar Allah ya shirya da Allah kiyaye ta bita ta wuce dakinta.
GONAR MALAM MUSA.
AMINU.
Yana qarasawa garesu ya kaiwa mutane biyar duka da kokara a qafafunsu gaba daya suka zube qasa yasaka kwakiyarsa yakai masu sara a qirji mai makon jini ya fito said wasu ruwa masu wari kuma ruwan baqaqe qirin kamar ruwan gawaye suka fito suka wanke mashi fuska nan take su biyar din suka tashi tsaye suna dariya.
Suna nunashi sai ganin yayi wanda yasara ya tufa yawunsa a hannu ya shafa qirjinsa kawai wajen ya kowa daidai kamar ba'a taba saransu ba.
Aminu da yaransa gaba daya hankalinsu ya tashi.
Aminu yayi kabbara gaba daya yaran nasa sukayi yace kowa ya karanta ayatul kursiyu ya shafawa makamin sa.
Aiko kawayayi yadda aminu yace.
Yaqara kaiwa wayannan biyar din sara aiko sai ga jini yato tsar kawai sai yaga duka biyar din sun fadi yaqara kabbara ya danna cikin su yaransa ma haka kan minti biyar sun kusa qarar da rabun mutanan da ke cikin gonar hakan yasa organ su yazo dan an kaimai labarin ana kashe mai runduna Yana zuwa yayi tozali da Aminu gaban sa ya fadi nan yayi wata razananniyar qara ai kowa ya tsaya harda su aminu.
Nan ya durkusa yayiwa yaransa alamun su durqusa haka kowa yazube gaban su aminu shugaban nasu yace.
Muntuba kayi muna rai ina rantsuwa da abun bautata har aljanu mun yaqa kuma munci galaba akansu ammah kai mutun gashi sai kashe man mutane kakeyi wane irin asiri ne dakai ?
Aminu murmushi yayi yace babu asiri kawai na karanta ayar alkur'anice koma mafi girma acikin ayoyin alqur'ani shiyasa idan nasaresu nake kashesu wannan aya duk girman aljani ko ƙarfinsa idan mutun yakaranta wannan ayar to da zai riƙe wannan aljani wallah bazai iya kubcewa ba.
Miye Alkur'ani shugaban su ya tambayi aminu.
Aminu yace littafin da Allah yasaukarwa annabinsa Annabi Muhammad s a w.
Wanda babu littafin da ya kaishi tsarki da girma a duniyar nan kuma dukanshi maganar Allah ce.
Wannan wane littafi ne kuma na yan wace addini ne ?
Littafin addinin musulunci ne Addinin gaskiya kuma zaɓaɓɓen addini agurin Allah.
Kai muyi sunanka.
Sunana Aminunllah ana kirana aminu.
Aminu ina son shiga wannan addinin naka nida mutanena dama ni a duk lokacin da naga wanda yafini karfin koya fini ƙarfin tsafi nakan karbi addininsa.
Murmushi aminu yayi yace mu addinin mu ba haka yake ba ba'a shigarshi dan a fita kuma ba'a shigarshi dan wata manufa kashigeshi dan Allah kawai.
Nan take yace na amince zan shiga dan Allah to idan ka amince karka tilastawa ma biyanka sai sun shiga duk wanda bayason shiga ka umurceshi da ya tashi ya tafi karya sake dawowa.
Sai lokacin shugaban yatashi tsaye yace duk wanda baya sun shiga addinan wannan mutuman ta shi ya tafi yatai ya fadi hakan sai ukku babu wanda ya tashi.
Hakan tasa Aminu yayi farin ciki sosaiii yace yanzu duk Abunda na fadi ku fadi.
Ash hadu.
Suka amsa da
Ash hadu
An la'ilaha
Suka sukace
An la'ilaha.
Illallah
Sukace
Illallah.
Wa'ash hadu
Sukace
Wa'ash hadu
Anna Muhammadu.
Suka amsa da.
Anna Muhammadu.
Rasullullahi.
Sukace
Rasullullahi
S a w.
Yanzu kuma kun zama musulmai abunda kukace kunce nashada babu abubu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma annabi Muhammadu mazon sane.
Juyawa yayi yakalli malam musa yace Alhamdullillah.
Yanzu malam musa zan barka dasu ka kuyar dasu abunda ya wajaba a kansu da sauran karatu akan addinin musulunci yanzu sun zama yan uwa mu suma.
Haka ya juya yace su tashi kowa yazo agaisa dashi babu fada yaqare haka aka gama gaisawa yayi masu sallama suka hau mashunansu suka baron garin.
Sun jero mashin din aminu shene gaba mashuna goma sha hudu ne kowa ya goyo mutun biyu haka suka hau babban titi suna gudu sun kawawo wajen fitilar bada hannu anan suka tsaya sai ga wata mota tazu da mugun gudu Aiko kade mashunan biyu mutane hudu suka fadi kan titi.
Aminu Yana juyowa yaga yarasa hudu kan titi nan yace da wasu sukai su asibiti sukuma suka bi motar da mugun gudu yake ba hannun ta bane haka yasa aminu yayi saurin shan gabanta da mashin din shi haka yasa motar ta tsaya.
Aminu Yana zuwa kawai gilashin motar duka da hannunshi ta gefen driver Aiko nan take ya tarwatse batsaya dubawa ya tura hannu dan yajanyo kowaye a ciki.
Kawai yaji ya kamo hannun mace ji yayi kamar ya riqa tiyo na ruwa dan har motsin jinin jikinta da bugawar zuciyata sai da yaji da sauri ya jaye hannunsa saboda tuna da yayi da wani Abu.
Cen yaji tace dan Allah kayi haquri tana hada hanuwanta biyu alamun roko nan fuskarta ta bayyana da sauri yace harira.
Cikin tsoro tace suna jannat dan Allah kayi haquri hankali ta a tashe dan ganin jinin da ke kan fuskarshi da jikinshi ta dauka na wayanda ta kadene yanzu.
Ai suman tsaye yayi jinshi ya dauke ganin yaqame kamar gunki yasa ta juya motar ta fece duka sun ganta kowa sai kiran harira yakeyi ammah aminu sai da suka daukeshi suka dorashi kan mashi.
Har suka qaraso gida baice komi ba kawai wucewa yayi yanufi gida.
Muda yace mai gida tsaya munwake maka jinin nan kar hankalin yan gida ya tashi.
Tsaye yayi suka zuba mashi ruwa suka yi wanke jinin duk da bai fitaba sai da sanyi ruwa ya tashi sannan ya dawo hayyacinsa yana tunano abubuwa a baya.
Nan yace ka barshi zan shiga ciki na sauya waya nayi wanka kuje kuyi sallar azahar idan anyi sallar la'asar kudawo.
Aminu yana shiga gida ya cire rigarsa ya saka aciki wani bokiti dake baki toilat yacire dogon wandonsa ya jefa aciki yawuce cikin gidan kanshi a sunkuye yawuce dakinsa ya sauya kaya kwance yayi yana tuna nan jannat dake kama da harirar sa.
Ita kuma jannat tana komawa gida ko parking batayi ba ta fito shiga ciki tawuce parlourn nata momeeey na magana ammah ina batajin momeeyn nata.
Haka ta shiga cikin dakinta ta wuce toilat ta sakarwa kanta ruwa.
Sai da sanyin ruwan yashigeta sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta kai dubanta ga hannun ta wanda aminu ya riqa nan taga jini takama wanke wajen har saida yayi ja.
Cikin zuciyarta take tambayar kanta waye wannan wanda ya riqa hannuna inba aljani bane wane mutun ne zai riqa hannuna haka Ammah har bugun zuciyarsa sai da naji a nawa hannun nifa har gudun jininsa inaji a lokacin bugun zuciyata da tashi bugu daya sukeyi haka jinmu tamakar wata gaba ta jikina haka naji jikina haka nakejin hannunsa.
Jin shigowar mama ta katse mata tunanan ta dan tashiga tana kiran sunanta.
AMINU.
Mama zulaice ta shigo dakin tace.
Ina wuni aminu nakawo maka abinci ?
Jin bai amsa mata ba yasa ta kai kallonta gareshi taga yana ta murmushi gashi kwance yana kallon silin.
Juyawa tayi ta fita dakin mama larai tashiga da sallama.
Mama na zaune ta amsa sallamarta.
Shiru mama zulai tayi sai da larai tace ina fatan dai lafiya naga kin shigo kinyi tsaye bakice komi ba.
Zulai tace wallahi lafiya qalau yayan su aminu ne ya dawo to nashiga nace mashi na kawo mashi abince baice komi ba ammah kuma naganshi yanata murmushi.
٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭٭