𝐂𝐡𝐚𝐩𝐭𝐞𝐫 03
JANNATAN WA HARIRAH
Daga Alƙalamin Asral G....✍️
بِـــــــــسۡم اللَّـــهِ الرَّحـۡمــٰنِ الرَّحــِـيمۡ.
رَبِّ ٱشْرَحْ لِى صَـــــدْرِى ﴿٢٥﴾
وَيَسِّـــرْ لِــىٓ أَمْــــــــــرِى ﴿٢٦﴾
وَٱحْلُلْ عُقْدَةًۭ مِّن لِّسَانِى ﴿٢٧﴾
يَفْقَـــهُوا۟ قَـــــــــــــــوْلِى ﴿٢٨﴾
𝐏𝐀𝐆𝐄 03
AMINU.
Mama zulaice ta shigo dakin tace.
Ina wuni aminu nakawo maka abinci ?
Jin bai amsa mata ba yasa ta kai kallonta gareshi taga yana ta murmushi gashi kwance yana kallon silin.
Juyawa tayi ta fita dakin mama larai tashiga da sallama.
Mama na zaune ta amsa sallamarta.
Shiru mama zulai tayi sai da larai tace ina fatan dai lafiya naga kin shigo kinyi tsaye bakice komi ba.
Zulai tace wallahi lafiya qalau yayan su aminu ne ya dawo to nashiga nace mashi na kawo mashi abince baice komi ba ammah kuma naganshi yanata murmushi.
Dariya mama larai tayi tace Allah yasa dai lafiya.
A'a lafiya qalau fa inaga fa ya fara soyayya.
Soyayya kuma wace mai sa'ace haka Allah yabata nasarar fasa wannan dutsin ?
Dariya zulai tayi tace aiko ansamu wace keda gudumar fasa wannan dutsen wai Aminu ya fara soyayya aiko da nafi kowa murna muddun aka samu yar sa'ar da tayi nasara shiga zuciyar shi.
Tashi larai tayi zulai na biye a bayanta suka shiga dakin da sallama bai amsa ba kawai sai murmushi yake tayi shika dai abun Dariya ma ya basu.
Dariyarsu tasa ya dawo hayyacinsa yace mamana kece da mama zulai ?
Mikukewa dariya ?
Mama zulai tace yaya Aminu wacece wannan dan Allah ka fada man sunan yar sa'ar nan.
Cikin jin kunya yace bari nayi sallah idan na dawo zan fada maku.
Mama larai tace tofa zancen ki da qamshin gaskiya zulai wata ta kwamashe zuciyar dan nan naki.
Zulai dariya tayi ta fito cikin ɗakin ta zuba mashi ruwa a buta kafin ya fito sai gashi sanye da irin kayanda yacire ta miqa mashi butar harda dan duqawa murmushi yayi yace.
Mama zulai kenan nace ki daina duqa man ammah kinqi ko ?
Dariya tayi tace yaya Aminu kenan nariga nasaba shiyasa.
Alwala yayi zai fita yaga kayanshi cikin bokiti kamar yadda yabarsu yace mama zulai ina mashkur ?
Inaga baya gidan nan wani Abu kake so ?
Dama kayan nan da suka ɓaci nake son ya sawo omo ya wanke man.
Ayya to bari nasa akirashi sai ya wanke maka.
To nagode yace ya fita cikin sauri ta dauki bokitin ta fara wanke kayan ita dai tana son farin cikin Aminu haka take mashi aiki kamar shine mijinta ba malam ba.
𝐉𝐀𝐍𝐍𝐀𝐓
Zaune take gaban mama ta Kasa cewa komi gomi na tsatsafo mata duk da (A/C) dake kunne.
Mama tace kinga fada man mike damunki baki da lafiya ne ?
Girgizata mata kai jannat tayi, alamun a'a.
Taɓa jikinta mama tayi, taji yayi sanyi sosaiii tace cikin qawayanki wata ta rasu ?
Shima girgizata kai tayi alamun a'a.
To miya faru, gashi kina zufa, kuma jikinki najishi da sanyi ?
Fashewa da kuka jannat tayi.
Mama tace banson iskanci, miye na kuka, ki buda baki kiyi magana inata tambayarki kinyi man shiru sai girgiza man kai kikeyi kamar wata qadangaruwa, ko wadda aka yankewa harshe.
Daqar jannat tace, mama kiyi haquri wannan fitar da nayi nabuge wasu da mota.
Mama tace inalillahi wa ina ilaihi raji'un, sun mutu ne ?
Aa mama inaga basu mutu ba ankaisu asibiti naji wani yace akaisu asibiti wallahi mama naji tsoro sosaiii rungumeta mama tayi, tana bubbuga bayanta, alamar rarrashi.
Kwashe komi tayi ta faɗawa mama.
Mama ajiyar zuciya ta sauke tace mungowa Allah.
Jannat tace mom wallahi har yanzu inajin motsin hannunsa akan fatar jikina mom wallahi da ya kama hanuna sai da naji hannunshi Kamar hannun nasa yanitse cikin jikina, ba a iya fatar jikina najishi ba har atsokar jikina da qashina naji mom, har bugun zuciyarsa naji a tawa zuciyar, mom inajin gudun jinin jikinsa a hannuna, a lokacin da yake riqe da hannuna, da yacere hannunsa a nawa jinayi kamar an zare wata gaɓa ajikina.
Mom bansan ya akayi ba nidai nagan ni a gida kawai.
Mom mi ke faruwa danine mom idanuwansa da nakallah ba tsana, ko rashin sani nagani ba, na ga mamaki a shinfiɗe akan fuskarshi, mom wallahi duk yadda nake kama da dady wannan yafini, da dady na wallahi da kuntaɓa haihuwa wani kamin Ni ko bayan ni da nace tabbas wannan ɗan uwana ne, kawai dai naji ya kirani da wani suna wai harirah, gaban mom ne ya fadi.
Tace tsohone ?
Aa matashi ne ammah ga alama baya da aure ma ammah zai kai shekaru 35 haka ko zai kusa kaiwa.
Momeeey tace.
kin tambayi sunansa?
Ko kinji ankira sunansa ?
A'a mom jannat ta faɗa.
Momeeey ban ji ankira sunansa ba kuma a halinda nake ciki bansamu damar tambayar sunansa ba inaga kamar yasani ko yasan wata mai kama dani shiyasa yakirani da sunanta harira hakan kaɗai naji ya faɗa mom.
Cikin tashin hankali mom ta tashi, ta fito ɗakin jannat, ta nufi ɗakinta, ta shiga tana neman wayarta, cikin tashi hankali.
ƁANGAREN AMINU KUWA.
Shigowa yayi bayan ya dawo sallar azahar ya tarar da mama zulai na shanya kayanshi yace mama zulai ba nace kidaina man aiki ba ?
Kinsan idan baba yagani zai man faɗa.
Aminu kenan ba abunda mallam zaiyi dan nayi maka wanki ai rashin uwa kesa ayi uwar daki dan bana da aiki yaune yasa nayi maka wanki dan naga mushkur bayanan.
Murmushi mai sanyi yayi yace nagode sosaiii.
Hajarace tafito ɗakinta tace kawuce ciki qannanka habibu da matarsa suzo jin kadawo sukazo ganinka.
Cikin farin ciki yace Ɗan uwa mai daɗi kenan ina surukar tawa ?
mama hajara tace tana ɗakin ashibilo ƙannanka mata ma sunzo da yaransu suna Baban ɗaki.
Takawa yayi yashiga baban ɗaki anan yatarar da ƙananan nasa mata da yaransu.
Nan Amina da khadeeja da Fatima suka tashi suna ga YAYA ga yaya samu da zuwa yayan mu da fatan kadawo lafiya.
Yaran nasu ne kowa ya gaisheshi nan yace ina uwar surutu ko maku zo da ita bane ?
Dariya AMINA tayi tace yaya kenan da ita muka zo ammah sun fita da habibu.
Tare da matarshi yazo shima ta dakin mama ashibilo taje yin sallah.
Nan ya zauna suka dan taba fira.
Sai ga habibu tare da wata kyakywar yarinya mai kyau irin kyanta mai sanyi ne.
tana ganin Aminu ta rugu da gudu tayi tsaye ta rungumeshi tana cewa.
Kawo Babba wallahi tun da safe naso Nazo mama tace sai na dawo makaranta shine natafi Ashe abun baqin ciki zan gani a makarantar.
Wallah abokiyata kuma babbar qawata masoyita jinin jikina malam qa'a'qa'u ya zagwaɗe mata kamar wanda Allah ya aiko haka Yakama jibgarta har sai da tayi fitsari wallah kawo ni kaina sai da nakusan suma tsabar tsoron dukan da yake mata.
Cikin jimami Aminu yace kai na tausayawa wannan yarinyar.
Kai dai bari kawo abun babu kyau sai ma wanda yagani yauwa kawo ina da magana dakai wai kai haka zaka tabbata bazakayi aure ba wallahi kawon qawata yayi aure har sai da ta kawo man cincin da diɓilan ammah kai Dana tambayi mama yaushe zakayi aure shine tace bata sani ba idan naganka na tambayeka.
Dariya yayi har da rufe fuska dan yaji kunya saboda malam ma yashigo yana jin firarsu dariya yayi irin tasu ta manta yace to kadaiji abunda fauziyya tace.
Kabata amsa.
Fauziyya saukowa tayi tana cewa la tsohon mijina mai furfura.
Yace babban matata sannunki da zuwa gidana.
Nikam ba matar ka bace ni matar masu sabon jinice yanzu, ada dai nake matar ka yanzu kam mama saki ukku dan likkafa taci gaba kai ya fito cikin kwali ga Matan kanan su hudu kaji dasu nikam nayi nan.
Wucewa tayi tana cewa kawo baba zan dawo idan tsohon nan yafita na karbi tsarabata.
Mamanta amina tace zan maki dukan tsiya Baban namu ne tsoho.
Dariya sukayi mallam yace to yanzu dai ka dawo ya kamata kayi aure dan Allah.
Ka duba habibu gashi nan yayi aure.
Baba zanyi shine ma yanzu ya dawo dani.
Ashibilo ta fito tare da matar habibu gaishe dashi matar habibu tayi ya amsa cikin fara'a yana sawa auren su albarka.
Cewa yayi kowa yazauna nan take kowa ya zauna dan kowa yaqaqu ya jin maganar auren Aminu,
mama zulai tasake tambayarsa yar ina ce miye sunanta ?
Bayan sun zauna cikin natsuwa yace sunanta harira Ammah yau ahanyata ta dawowa naga wata mai kama da ita sak sai dai ita inaga yar mai kudi ce dan a cikin mota take tace sunanta jannat nan ya kwashe komi ya fada masu har musuluntar wayannan azzaluman.
Malam yace ammah kasan ba ayaqi a wannan watan mai alfarma ko ?
Yace baba ba yaqi bane wannan fadane ai, saboda yaqi tsakanin gari da gari ko qasa da qasa ko qabila da qabila ammah wannan tsakanin mutanan daji ne da manoma kuma anyi nasara tunda fiye da mutun ɗari 200 sun musulunta.
Allahu Akbar kowa yace.
Sannan yace to zance harira kuma acen dajin illela akwai wani daji dake mararar bar Nigeria da Niger to a cikin dajin muka shiga muna farauta munfara kama dabbobin ciki sai muka fada hannun wasu mutane.
Ashe dajin nasune suna nada wata sarauniyace mai tsananin karfi da tsafi.
Shigar mu dajin Ashe an daure dajin sai dai a shiga ammah ba'a fita ciki munyi farauta mun gama kama dabobin mun ɗibi kayan marmarin da zamuci kawai muka kasa fita muna ta kewayan dajin anan wasu macizai suka kewaye mu sai ga mutane sun fito sun kewaye mu kowa da kibiyarsa dawasu kalar tufafi ruwan ganye dawani tsanwan Abu agoshin su mai sufar maciji sai haske yakeyi.
Haka suka tasamu gaba har gaban sarauniyar su, hada idanuwa da nayi da ita sai naga kamar Gwaggo tace huraira tsaye a gabana sai dai ita wannan bata da jiki kuma baqace mai kyaun gaske sannan budurwa ce iyakarta shekaru shabakwai.
Umurni ta bayar da cewa a rufemu a cikin kurkunta haka aka sakamu cikin kurkukun tsawon kwana ukku sannan aka fito damu anan akace waye Babba a cikin mu nace nine aka fiddo dani sauran aka mayar dasu a cikin kurkukun aka bani ƙwakiyata nan take aka fitar da jarumai waƴanda duka kamosu akayi kamar yadda aka kamomu.
Akace duk wanda yayi nasarar kashe abokin karawarsa yatsira idan yana son ya tsiratar da mutanensa to zai sake karawa da wani jarumin aciki idan yakashe shi to ya tsiratar da yan uwansa.
Anan kowa yaja abokin karawarsa muka fara bugawa na lura da wanda nake faɗa dashi yana da sihiri a jikinsa hakan yasa na karanta ayatul kursiyu abayyane nan take har sarauniyar sai da jikinta ya kama rawa suka toshe kunnunwansu.
Hakan yasa bayan na gama karantun makami mashi sara a wuya nan take kansa ya yaɗi a ƙasa baqara karawa da wani shima ya tabarshi biyu hakan yasa aka kamani aka kaini gaban sarauniya nan ta fara tambayata.
Miye Sunanka ?
Nace Aminu tace waƴanne kalmomin tsafi ne makaranta yanzu ?
Nace ba kalmomin tsafi bane ayar alqur'ani ce.
Nan tace aje dani a wani gurin dan ta tabbata duk wanda yashiga baya fitowa ba taɓa saka wani bil adama ba komi tsafinsa ya fita.
Wata babbar rijiyace aka jefani acikin rijiyar akwai wata babbar zakanyace wadda ban ta6a ganin zakanyar da tayi girmanta ba.
Bayan an jefani a cikin rijiyar nan na fara neman kare kaina ita kuma tana qoqarin sai ta rauratani kamin ta cinyeni na lura bata jin yunwa hakan yasa take son raunatani.
Bayan najima ina kare kaina naji na fara gajiya hakan yasa na fara kaimata nawa martanin nafara kai mata sara tana gocewa tsalle nayi na taka turkenda take daure ajiki nayi sama sosaiii nace bismillahi rahmanin rahim na sauke mata ƙwakiyata a tsakiyar kanta kawai ta rabe biyu.
Anan naga kowa hankalinshi ya tashi nan suka zuɓe makaman su suka durkusa kan guiwuyin su.
Budewa akayi nafito daga cikin rijiyar ashe komi dake faruwa suna gani a allun tsarin su nan aka akaini wani guri ni da abokaina aka kawo muna abinci makaci mukayi wanka bayan mugama hutawa mun gabatar da sallolin da ke kan mu mukayi sallar isha duka atare muka kwanta.
Cikin dare aka shigo inda muke akace nazo sarauniya na nema na nan na tashi nabi bayan ɗan aiken har muka isa fadarta.
Tabbas fadarta babbar fadace tasha ado, ga macizai nan ta ko ina, suna sunkuyar da kai agareni alamar jin jina.
Na tarar da ita cikin fararen kaya komi na fada kuma farine macizan ne kawai baqaqe Amman na kusa da ita fararen macizaine.
Anan tanuna man kujera tace na zauna .
Bayan na zauna tace ni sunana harira nice sarauniyar wannan gari baki daya wannan dan uwana ne hari tanuna man wani qatun maciji baƙi shine ɗan uwanta tanuna man wata macijiya fara tace itace matar ɗan uwanta.
Macijin zuwa yayi yakewayeni yana kallon idanuwa nima haka gama kallonta yakoma kusa da ita yatsaya tace dan uwana ya aminta da kai.
Tasowa tayi ta qaraso wajena ta zauna takamo hannuna nan naji irin abunda naji Dana riqa hannun jannat ayau.
Cikin sanyi murya tace man tabbas tana sona kuma nine wanda zata aura.
Nace mata Ni bazan aureta ba saboda ba addinin mu ɗaya da itaba sannan ita mai tsafice
Cewa tayi zata iya shiga addina dan ta aureni yanzu dai itama ta musulunta kuma yanzu haka tana jiran dawowata dan naji aɗaura aure muna aure.
٭٭٭