ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA

SHAFI NA GOMA

by @ummishatu

©️Love story 2025

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA.....!

NA

*UMMI A'ISHA*

Last free page

10

***Gaba ɗaya Imaan bata cikin farin ciki bare a samu nutsuwa a tattare da ita, radadin mutuwar mommy yaƙi barin zuciyar ta haka kuma tunaninta yaki barin cikin kwakwalwarta, ko a mafarki bata taba kawowa mommy mutuwa yanzu ba, yau dai da yake Baba Mari ta sakata a gaba dan dole take tura abincin da aka ajiye mata ba wai dan tana jin dadinsa ba sai dan babu yadda ta iya haka kuma bata da yadda zata yi tana ci tana kukan zuci a haka har ta dan ci kwata daga cikin wanda aka kawo mata.

Tun bayan da aka kai Anaam asibiti bai san inda hankalinsa yake ba bare yasan a inda yake kwance, Najla ce ke tare dashi tana zaman jinyarsa har akayi kwana bakwai kuma sai lokacin ya iya gane abinda yake faruwa da kuma halin da yake ciki sannan take mutuwar mommy ta dawo masa wadda yake jinta kamar cikin mafarki, wani kuka ya fashe dashi tare da tashi zaune ya sauka daga kan gadon da yake domin shi kadai ne yanzu cikin dakin ita Najla ta fita zuwa pharmacy, yana tafe yana share hawaye sai gata ganinsa yasa ta cikin sauri nufarsa tare da riko hannunsa,

"Babe ina zaka je?"

Ba tare da ya kalleta ba yace "zan je gida....."

"A'a babe kayi hakuri, ai ba a riga anyi discharging dinka ba, kayi hakuri har zuwa time din da Dr zai sallameka please...."

Har lokacin tana rike da hannunsa, girgiza mata kai yayi kafin yace "Ba zan iya ba babe..... Bazan iya zama anan ba...." daga haka ya fara tafiya, duk yadda ta so ta hana shi bai hakura ba dole ta bishi suka tafi bayan ta tattaro komai nasu dake cikin dakin da aka basu, fata ya rinka yi acikin ransa Allah yasa suna zuwa gida ya ga mommy sai dai amma kaddara ta riga fata dan lokacin da suka je gidan tun daga bakin gate zaka gane akwai abinda ya faru, cikin gidan ya shiga hawaye na bin kumatunsa part dinsa ya shiga kawai ya rufe kofa ya zauna yana kuka kamar karamin yaro, kuka yake sosai kamar ransa zai fita, ganin shuru shuru bai fito ba yasa Najla tashi ta nufi part din nasa saboda ada tana can sashen mommy sai nuna ta ake yi ana cewa itace wadda Anaam zai aura ita dai Imaan tana zaune tana kallonta saboda dama ta santa ba wai yau ne ta fara ganin ta ba. Bugun duniya Najla tayi amma Anaam yaƙi bude kofar har tayi ta gaji ta koma part din mommy tana sanarwa da mutane amma duk wanda yaje haka yake dawowa saboda yaƙi ya bude kofar yana zaune yana ta gunjin kuka cikin budewar murya, sai zuwa yamma sannan aka samu ya bude kofar, saka shi a gaba Najla tayi yayi wanka yaci abinci sannan ya fita bakin gate wurin masu karbar gaisuwa dan har lokacin mutane basu daina tururuwar zuwa gaisuwar ta'aziyya ba. A haka a haka a kwana a tashi asarar mai rai har aka share zaman makoki nan kuma ma'aikata da sauran jama'ar gidan kowa ya fara tunanin inda zai nufa dan cigaba da gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum, itama Imaan tana cikin masu wannan tunanin saboda dama zaman mommy take yi to ita kuma mommy gashi yanzu babu dan haka zamanta a gidan bai da wani amfani, kusan kowa na gidan ya watse dan haka itama ta shirya jakarta dan tafiya gobe duk da bata san inda zata je ba kuma bata da wani wurin zuwa amma ya zama dole ta bar gidan saboda yanzu gida ya zama na Anaam komai ya zama mallakinsa ita kuma dama jininta da nashi bai zo daya ba kai baima hadu ba sam sam, washe gari ta tashi da niyyar tafiya saboda komai na gidan ya tsaya haka kuma kowa ya kama gabansa bai fi su uku suka rage ba daga mai gadi sai malam bala driver, wanka tayi ta shirya ta saka kayanta ta dauki jakarta ta fito, shigowar wata babbar mota jeep ya dakatar da ita daga fitar da take kokarin yi, Alhaji Nura bature taga ya fito daga cikin motar wanda yake shine makocin mommy kuma kowa ya san shi a unguwar saboda yana daga cikin manyan mutanen dake rayuwa cikin unguwar,kada kai tayi ta wuce abinta tayi gaba saboda tun bayan da akayi rasuwar nan kusan kullum sai anyi manyan baki yan gaisuwa, muryar mai gadi ta dakatar da ita daga kokarin fitar da take yi,

"Imaan..... Zo ana neman ki"

Dawowa tayi har lokacin tana rike da jakarta, durkusawa tayi ta gaida Alhaji Nura ya amsa fuskar sa cike da alhini da damuwa kafin taji yace, "kece Imaan ko?"

"ehh nice....."

"Anaam yana nan ne?"

"ehh kamar yana nan bai fita ba gaskiya"

"ok muje ciki ki kirawo min shi...."

Wucewa tayi yana biye da ita har cikin gidan, a babban falon baki ya zauna ita kuma ta wuce part din Anaam inda ta san yana can tare da Najla amma koda taje sai ta samu Najla din bata nan watakila ta tafi sai shi kadai yana kwance yana bacci amma yayi rama ta fitar hankali,

"Ana sallama da kai a falon baki..."

Daga haka ta juya ta fita shikuma ya tashi ya saka rigar shi jallabiya ya fita, iya Alhaji nura kadai ya samu sai Imaan dake zaune amma ganin ya shigo yasa ta mike zata fita nan Alhaji nura ya dakatar da ita ta hanyar ce mata,

" A'a dawo ki zauna mana ai wannan zaman kema ya shafe ki....." mamaki abin ya bata saboda ta yaya za ace itama zaman ya shafe ta alhali bata daga cikin ƴaƴa ko kuma ahalin gidan, amma sai ta koma kawai ta zauna din zuciyar ta cike da tarin tambayoyi kala kala tana ta faman tambayar kanta to me kuma ya faru da zama ya hado har da ita? Ko dai wani abunne kuma ya sake faruwa aka ce harda ita? Zuciyar ta cike da wasi wasi har Alhaji Nura ya gama gaisawa da Anaam sannan cikin jimami da kuma Alhini ya zaro wata envelope daga cikin aljihunsa yace,

"Ubangiji Allah ya jikan Hajiya Batool yayi mata rahama, halin ta na gari ya bita, Allah ya yafe mata ya bata aljanna madaukakiya, hakika ita din ta kasance mace ta kwarai kuma ta gari mai son mutane da kuma son zumunci, wannan takardar ta bani ita watannin baya lokacin da zata yi wata tafiya zuwa Kasar chairo domin duba lafiyarta sannan kuma ta umarceni da duk lokacin da ta Allah ya kasance idan har ta rigani rasuwa to inzo in tara ku kai Anaam da kuma ke Imaan domin in isar muku da wani saƙo ko kuma ince wasiyya kamar yadda ta rubuta gashi da hannunta sannan kuma taje har gidana ƙafa da ƙafa ta bani ta kuma barmin wasinci na in daure in isar da wannan sako zuwa gareku tun kafin ta cika kwana 40 da komawa ga Mahaliccinta...... "

Daga Imaan din har Anaam kowannensu ya ƙosa yaji kowanne irin wasiyya mommy ta bari kuma, sannan me yasa ta zabi sai iya su biyu za a sanarwa da wasiyyar bayan ita Imaan matsayin hadima take gareta, duka tunaninsu ne ya katse saboda jin Alhaji nura yaci gaba da kora jawabinsa kamar haka,

"kamar yadda muka sani ita wasiyya wajibi ne a cika ta matsawar mamaci ya rubuta ko kuma ya fada da bakinsa, to ita dinma ta fada da baki ta sanar min sannan kuma saboda gudun samun zargi ko kuma kaucewa jita jita shiyasa ta rubuta ta da hannunta kamar yadda kuke gani, kafin hajiya ta rasu ta taba samuna da wata magana wacce ta sakani cikin fargaba da kuma rudani domin tace min idan har Allah yasa ta rigani rasuwa to inzo in isar da wannan sako kamar haka, duka dukiyar da ta ta bari a duniya wadda ta mallaka kama tun daga kan gidaje, filaye, company, motoci da duk wani abu wanda yake mallakinta ta mallaka muku ku biyu wato kai Anaam da kuma ke Imaan amma kuma bisa wani sharadi guda daya....... "

Daga Imaan har Anaam kowanne maganar ta bashi mamaki to ita kuma Imaan a gayyar wa da har mommy zata bata rabin dukiyarta?

" Sharadin shine..... Za a daura muku aure cikin nan da sati biyu sai a baku dukiyarku gaba daya sannan babu saki duk rintsi zaku rayu tare....."

Wadannan kalaman nasa sune suka sake jefa su cikin mamaki da al'ajabi, "aure kuma?" Anaam ya bukata batare da yasan ma lokacin da yayi tambayar ba,

"tabbas.... Kwarai da gaske aure ta bada wasiyyar a daura muku koda kuwa bakwa son juna........"

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun......." shine kawai abinda Imaan ke maimaitawa cikin ranta saboda ita dai duk duniya idan akwai mutumin da bata kauna to Anaam ne amma kuma sai gashi ana maganar mommy tabar wasiyyar su rayu tare har karshen rayuwarsu ita kuwa mommy saboda me? Me yayi zafi da har zata bar wannan wasiyyar mai mutukar wahala bayan ta san yana da wacce yake son zai aura itama take sonshi sannan banda wannan ma ita sam baiyi mata ba a matsayin mijin da zata aura saboda ba irin shi take so ba sam bai yi ko kama da irin namijin da take so ba domin ita nagartaccen namiji take so ba sangartacce ba sannan hali take nema ba kyale kyalen duniya ba haka kuma kamili take nema komai muninsa ba wanda yayi kyan dan maciji ba, tafi son miji na gari ɗan gaske wanda zata ƙaru dashi ta kowanne fanni wanda zai so ta ya nuna mata ƙauna ako ina, wanda yasan farillai da sunnonin aure wanda zai kare mata mutuncinta ya tsare mata kansa wanda zai sauke duk wani nauyi nata wanda ya rataya a wuyan sa, shi dai Anaam shuru yayi yana nazari dan gaba daya ya rasa me ma zai ce aure? Kuma auren ma da wannan kidahumar marar wayewa, yar aiki wadda ba kowan kowa ba kuma ba yar kowa ba, inaah ai ba zata taba sabuwa ba wai bindiga a ruwa, idan sama da kasa zata hade ba zai taba auren wannan kaskantacciyar yarinyar ba,

"haba mommy..... Why?? Why? Why??" shine abinda yake ta sakawa yana fada a cikin ransa amma a fili yarasa da wacce kalma ko da wanne yare zai yi amfani wurin nunawa Alhaji nura sam wannan maganar da ya zo da ita bazai amince da ita ba,

"Dan haka idan Allah ya nuna mana sati mai zuwa za a daura muku aure amma kuma ku tuna babu maganar saki ko rabuwa bayan anyi muku aure domin wannan shine wasiyyar mahaifiyarka....."

Dafe kansa yayi da dukkanin hannayensa guda biyu wanda ke barazanar fashewa, wannan wacce irin masifa ce kuma? Wannan wanne irin bala'i ne yake shirin faruwa dashi yanzu duk duniya mommy ta rasa wadda zata bar wasiyyar a daura masa aure da ita sai ƴar aikin gidan su? Boyi boyi marar gata yarinyar da ko asalin ta basu sani ba, yanzu shi da wanne idon zai kalli duniya ya nuna musu wannan bagidajiyar yarinyar da har yanzu babu alamar wayewa a tare da ita? Yar aiki?,

"am... Am.... Am nace dama..... Idan ban amince da maganar auren ba akwai wata matsala ne?" ya tambayi Alhaji Nura zuciyarsa na bugawa tara tara tamkar zata fashe dan fargaba da tashin hankali,

"ehh gaskiya akwai dan hajiya tace idan har baka amince ba to a raba dukiyarta gida biyu daya akai gidan marayu daya kuma a zuba cikin gidauniyar da ta bude ta marayu da gajiyayyu.... Gashi dai karanta da kanka ka gani..... Have it..."

Karɓa yayi hannunsa yana rawa ya soma karanta wasiyyar mommy wadda gashi nan da hannunta ta rubuta ba wai wani ne ya rubuta mata ba saboda ga rubutun ta nan rangadadau kamar yanzu ne tayi shi da kuma sa hannunta, ɗago kan shi yayi idanuwansa jajur bayan ya gama karanta wasiyyar mommy........

Tirƙashi wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa, shin ya zata kasance? Anaam zai yarda da wannan auren? Idan har anyi auren wacce waina za a toya a gidan auren nasa? Shin Najla zata bari auren nasa ya tabbata? Ƙiyayya da Ƙiyayya basa taɓa haduwa har su zauna inuwa ɗaya, Amsoshin wadannan tambayoyi da ma wadanda ba a san su ba suna cikin cigaban labarin wanda zaku sameshi kan naira dari shida 600 kacal, kar ku bari ayi babu ku sannan kar ku bari a baku labari,Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,

FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA

Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shida shida, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no *** ko kuma recharge card na mtn ta wannan no *** da shaidar biya.

Ummi Shatu👌🏻