NI DA GIDANA

Chapter 2

by @zainab221

NI DA GIDANA

BY

Zainab Ilyas mazawaje

Best brilliant intelligent writer.... 🖋️

Page 2

__Aharkar jajircewa da karatu, da rashin sakin fuskar jawo wasa a karatu, sosai Fa'iz ya burgeni, saboda malamai da dama wasa suke shigarwa cikin karatun,su .

Amma daga baya nima sai na rink'a k'yamar wasu halayan Fa'iz Bukar. Bayan rashin sakin fuska kokad'an, a Kwai kuma iya cin zarafi ainun idan an b'a ta masa, akwai shi kuma da d'agawa da jin kai, kamar d'an sarki.

Na kan had'u da shi a harabar makaran'ta, nayi niyyar gaishe shi, ko nuna sanayya, amma Sai ya wani d'auke kai ya kuma tsare gida,wato kar ma na samu kafa. Jinkai dai wurin fa'iz ya shaddade.

Wasu mata suna dagawa idan sun san sun mallaki wani abu kamar kyau ko kudi ko sarauta, amma namiji yawanci bai fiye yi ba gaskiya, ballantana malam Faiz da iya abu daya nake jin zai iya jin kai, shine kyau, don ba dan wani attajiri bane da gani, ko mulki ko wani gawurtaccen ilimi da ya kai ya kawo, don da bazai zo koyarwa secondry ba, a fahimtata. Shi yasa nake jin haushin yarda yake wani dagawa, da wulakanci. Wannan dalilai yasa naja baya. Idan na ganshi a gabas, to sai nayi yamma ni.

Washe gari, period d'in sa tana shiga, sai gashi ya shigo. Ya ninka jiya a kyau kam.

Kayan da yasa, bayan haska ka shi da suka k'ara, sun yi masa kyau sosai. Ba kuma wasu Kaya bane na musamman ba. Kayan sanyi ne. Rigar sanyi ce mai duhu ruwan k'asa mai kwala, Sai wani gida gida a gaban rigar mai launin fari fari. Jin's d'in wandon daya sa, Shima ruwan k'asa ne, amma mai haske. Sai safar hannu, ruwan k'asa, safar k'afa ma haka.

Komai dai to mach. Duk dai sanadin sanyin da a ke yi, yayi wannan shigar. Sanyin ranar yafi na kullum ma. Kayan da yasa jiya ma sun yi masa kyau, Amma na yau kam ba'a magana. ko daya ke, dole Kaya suyiwa Fa'izu kyau, ko wani iri. Amma fa ba kowa ne zai yarda ba, Sai Wanda ya ganshi.

Ya tsaya gaban a ji, ya dafa tebur d'in teacher, yana kallon d'alibai d'ai d'ai cikin jin kai da isa.

"Ina a ka kwana game da topic d'in da na karantar jiya, Kowacce ta fahimta?"

Shiru babu Wacce tayi magana.

"Wata ta tashi tayi min bayani ko in brief."

Nan ma shiru.

"A kwai tambaya? "

Nan ma babu Wacce ta d'aga hannu.

Ya gyad'a kai.

"Cab'? Lallai yau jiki zai yi tsami. Kuna nufin wahalar banza nayi Kenan?"

Ga rashin sanin Fa'iz, yawanci an gane aikin sa. Kawai shiryawa a kayi a nuna masa bai isa ba. Saboda yaci mutuncin d'alibai shalelen makaranta daga zuwa. Kuma ya nuna musu iyakar'su. Kuma intisar da ita ce zak'ak'uwa wa ta ma rasa kunya, ita ta tsara a nuna masa mun gagara, sunan da malam Abba ya Sama na. Ni dama bana cikin had'in kan. Shiru nayi naga na samu 'Yar uwa, Mu zama Mu biyu. ganin zai yi zaniya, nayi saurin d'aga hannu.

Daya ganni ya fara da yi min kallon kufula.

"Da kema kin iya kika saje da su? duk zan iya daku don k'aniyar'ku. Naku wasa ne Wallahi."

Da sauri na soma yi masa bayani cikin turanci, saboda banason a binda zai tab'a min lafiyar jiki. Ina tsoron duka sosai, tun ina k'arama.

Tambayoyi ya Shiga jeromin da turanci, uwa da 'ya'ya har da jikoki, duk domin na gaza amsa d'aya nima na fad'a tarkon'sa. Haka na fassara shi. Allah ya taimakeni na bashi amsa,saboda duk cikin class d'in babu Sama dani a kaifin basira, da haddace a bu. Ni nake d'aukar lambar farko duk jarrabawa ma.k'oK'arina ya haskakani, har na samu muk'ami.

Yace cikin watsomin kallon raini.

"Kinyi sa'a kin haye, kin tsallake hukunci na. Da kin gaza amsa tambaya d'aya da bazaki tsallake hukunci irin nasu ba. Amma zaki fad'o tarko na wataran, domin ban huce da ke ba.Saboda na kula ku duka taron tsintsiya ne babu Shara,ba kusan ma me yakawo ku makaranta ba. Shashashan Kawai, dak'ik'ai." Yau mun gamu da gamon mu.

Haka na rink'a fad'i a zuci Kowa ya k'ara fusata da raina kan'sa fa ga wannan tahaliki. Bai d'auke mu ma a bakin komai ba, face Shara, tun da aibata mun ma da yake shaida ne.

"Je ki kisamomin bulala babba a staff room, kuma ban yarda da babu ba." Yace dani. Na tashi zan fita mata ta d'aga hannu wai zata yi bayani. Yasakar mata kallon banza, Sannan yace

"Is too late"

Ta koma ta zauna ragwaf.

Nayi sa'ar samo k'atuwar bulalar malam tukur. Nasan da ban samo ba, nima tawa ta sameni.

"Ten, Ten, lashes ta tabbata ga kowace yarinya. Ku fito one by one Kowacce ta k'arb'i tata. Na baku damar da zan baku kun wofuntar, saboda baku da kirki, ban San me kuka d'auki kan, Ku ba. Ni kuma nasan kaina da darajar lokaci. Bazai yiyu na rink'a zuwa Ina aikin banza ba. Kullum Sai kun daku Wallahi, in dai baku canza ba. Zanga ni da bam bamci ku da jaki ko babu. Tun da shine kullum cikin duka, amma baya canzawa".

Wata matsoraciyar duka irina farida ta soma bashi hak'uri tana hawaye.

Ai kuwa da sauri ya d'aga mata hannu.

"Yi min shiru ko bulalarki ta k'aru. Banace muku ni bansan kalmar hak'uri ba?"

Wai yau 'yan class d'in Mu za'a daka.? Ko tsawa bamu Sani ba. Kuma Wai bulala goma goma. Na tabbata yarda a jin ke cike da 'ya'yan gata'ya'yan so, wasu ko yatsa ba a'tab'a sa musu ba da sunan hukunci.

Intisar Ina kallon'ta taunar cingam take ma a binta, tana tab'e baki, Tana kallon fa'izu k'asa k'asa, saboda gani take tafi k'arfin nan. Duk cikin a jin babu kamarta a kyau, kuma babu Wanda ya kai Uban'ta kud'I. Malaman dake son'ta da yawa, shi yasa take tsula tsiyarta. Bata da kok'ari ko kusa, Amma Sai muga taci jarrabawa.

Bata kallon kowa da gashi. Ta gasawa malami bak'ar magana kuma ta kwana lafiya.

Ita ta fara fitowa, kamar zuwa tayi a fara dukan takanta, Amma Sai ta tsaya daga d'an nesa ta dubi Malam Fa'iz tace.

"Sir, gaskiya bamu can can ci duka ba. K'aidar koyarwa, duka shine mataki na k'arshe. Kamata yayi kayi ta mai mai ta Mana karatun, ko na Sati guda ne, har Mu fahimta. Kuma fa mu senior ne kar ka manta, duka ai Sai jenior."

Ina lura da kallon mamakin da yayi mata, tare da jin jina k'arfin zuciyar'ta da ta iya fad'a masa hakan. Rashin sanin intisar yasa yake mamakin. Bata da shayi, ga isa da alfaharin dukiyar uba da kanta. Shi yasa take ganin babu namijin da bazata taka ba, ta Sha ko da yake naga ta sassauta ma rashin kunyar tata a kan'sa ga yarda takewa malamai.

Yace da ita.

"Come here ". Ta isa gareshi yarda ya umarceta. Yace"Me kika ce?" Ta sake mai maita masa kuwa, har ma da 'yar dariya.

Ya fusata yace "Why are you laughing.?

Mai makon ta bashi amsar dalilin dariyar, Sai ta sake yi ma. Wani irin mari ya kai mata, ba domin tayi saurin kaucewa ba, ranar da taga taurari.

Cikin harzuk'a yace.

"Koni bawan ubanki ne, nake yi masa bautar koyar dake, baki isa ki dubi idona ki fad'amin wad'annan kalaman ba ki tsira. Saboda kin rainamin hankali zaki fad'amin wad'an nan lafuzan? Saboda jaka ce ke ko? Kuma a Ina kika zama senior? Kan ki fanko ne fa babu komi Sai tarin rubish. Simple topic irin wannan kika sa understanding?

Ballagaza dak'ik'iya irin ki Zaman gida, shi yafi dacewa dake. Mai makon dai kizo a yi biyu babu. Ki wahalar da malami, ki kuma wahalar da kan ki, tun da k'wak'walwarki ta kifi ce

,ba fahimta za kiyi ba ma."

Intisar Kam ta muzanta a lokacin, Wai ita aka tozarta gaban wad'an da take ganin ta fisu. Za'ace ba'a tab'a ci mata mutunci ba a rayuwarta ma Sai ranar. Kuma namijin da take takawa.

Kasa cewa komai tayi, saboda yarda ta karanci zafin sa, idan ta sake tagawa, Sai a binda ta gani kuma. To bata tsaya nan ba, babban a binda ba'a tab'a yi mata ba, ranar an yi mata. Zafafan bulalai yayi mata da tafi ta kowa. A hannu yake bulalar sa, da tak'i tsayawa ne, ya k'arashe mata a jiki. Tasha kuka, Sai gata magiyar Hak'uri take bashi. Bai kuma saurara ba. Na yarda Fa'izu baisan kalmar hak'uri ba.Kowa bulala Sai da ya fito ya karb'a Kam. Amma biyar biyar, Sai dai ko Wacce d'aya Sai ka fad'awa mutan garin Ku. Yarda yake da zafi, haka ma bulalar'sa. Ni Amma na tsira, Sai d

ai na k'ara tsorata da lamarin malam Fa'izu.

Ai tun daga ranar kowa ya Shiga taitayin'sa da shi. Karatu babu wasa. Nutsuwar fahimta, kowa Sai da ya lalubo, idan ma baka da shi, to Sai ka aro. Tuni ya gyarawa marasa kunya zama da kuma dak'ik'ai , da yayi tambaya kuwa rige rigen bashi amsa ake yi.

'Yan a jin mu da malamai ke masifar ji damu, to fa'izu yafi tsanar mu shi. Yafi kuma takura mana ma. Amma yana da hujja gareshi. A Kwai ranar da yace.

"Na fahimci kun d'auki kan Ku Wata tsiya, shi yasa kuka d'auki girman kai kuka d'orawa kan Ku. To zan saukar muku da shi kuwa."

Gaba d'aya makaran ta ta d'auka da Fa'izu Bukar,ko'Ina ka zaga Zancen sa. Makaranta tuni ta soma gyaruwa, saboda matsayin displine master a ka bashi, saboda jajircewar sa wurin kawo gyara a makarantar. Ya gyara makaranta Kam, ko ga tsafta da tarwatsa Zaman da malamai suke na hira a k'i Shiga a ji koyarwa. Meeting na dole yasa a kayi harda prince pal aka kawo sauye sauye. Ko a makararru ma an samu sauk'i sosai. Domin Sai a jima ma ba'asamu wad'anda za'a tare ba da sunan makara.

Saboda malam Fa'iz ke hukuntawa. Kuma babu sauk'i ko a fuwa a lamarin sa, ko wacece ke zaneki zai yi tas kuwa. Kuma idan zaki d'ige kina bashi hak'uri bazai hak'ure ba. Bada Hak'urin ma shi fusata shi yake yi naga.

Tofa!.

watan'sa na biyar nima na fad'a komar sa. Dama yayi min baki.

Garin tsautsayi rannan Sai gani cikin makararru guda biyar. Zance tsautsayi, tun da ban tab'a makara ba.

Abinka da matsoraciya. Jiki har rawa yake Ina bashi hak'uri da yazo kaina ya rik'e baki.

"Cab' , monita kina shugabar d'alibai amma kika makara? Muk'amin ki bashi da wani amfani, tun da ke shugaba mai gyara kin gaza wazai gyaru kuma?"

"Wallahi sir ban tab'a makara ba, yau ma akasi a kasamu na tuba, bazan k'araba."

Yace"Kome zaki ce ba zaki tsira ba Wallahi. Kuma bulalarki Sai ta ninka tun da shugabanci aka baki ga 'yan baya, dole muna so ki ki yaye.

Zafafan bulalai goma yayi min da naji kamar na shid'e domin zafi. hak'uri da nake bashi naga kamar tunzurashi ma nake, shi yasa na hak'ure. Hannaye na har tara jini suka yi bayan kumbura. Na yarda Fa'iz mugu ne na k'arshe. Da gayya ma nasan yayi min irin wannan bulalar mai ratsa k'ashi. Tabbas Sai a lokacin na yarda da zafin bulalar sa da d'alibai ke fad'a suna tsoro. Tun daga ranar naji na tsaneshi. Tun da uwata ta kawoni Duniya Kam ba'a tab'ayi min bulala ba nima ballantana mai zafi irin wannan. K'udirewa nayi a raina na daina yi masa magana ko a aji.Amma daga baya dole na saddak'ar, saboda malam Fa'zu yafi gaban nan. Tambaya ma baka amsa masa ba, hukunci ne mai zafi. Domin kuwa ko zagin'sa na tsamar nama yayi maka ma bainan nasi, ya cuceka.

Ga dai intisar nan duk tayi laushi ta horu. Duk rashin kunyar nan da felek'e ta dire. Muddin ya shigo class wata nutsuwa ma take yi.

Amma a jita jita naji wai son sa take kuma. Bama ita ba ya kwashi Jama'a masoya mata jingim, amma na b'oye. Tun da dai kota Ina babu Wata alama da ta nuna Fa'zu Bukar Zai karb'I tayin k'ok'on barar Soyayyar wata mace a makarantar, face ma Sai dai yayi fatali da k'ok'on barar. Ni Kam duk Wacce zata so ma Fa'iz wahalalliya na d'auketa, Wacce kuma aka yankawa kazar wahala a kace Sai ta fige.wahala bata ishe suba ne da wulak'anci suke neman k'ari. Haka nake cewa duk Wacce aka cemin ta Mato a kan son Fa'iz.

Ban kuma yarda ta had'oni da malam Fa'izu ba, gudun inda zan ganshi ma nake yi idan ba 'ajin mu ya shigo ba. Duk domin kar ya kamani da laifin da zai ci zalina, saboda na daku, jikina bai manta ba. Kuma kumburin hannu n'a bai gama Sab'ewa ba. Amma duk guduna da shi, Sai da rannan ta sake had'oni da shi.

Rannan na Shiga staff room Kiran malam labahani saboda period d'in sa ta shiga bai zoba.

Ina Shiga staff room bisa tsautsayi idanu na da malam Fa'izu suka fara kicib'is. Suna zaune shida malam Abba da na fuskanci tasu tafi zuwa d'aya suna cin gyad'a. Malam Abba yana kan desk d'in da suka zube gad'ar, shi kuma malam Fa'izu yana kan kujera, suna hira har suna 'yar dariya ma. A raina nace. Dama malam Fa'izu yana dariya? Zatona ko murmushi bai iya ba.

Da wuya ma naje staff room na ganshi Sai Jifa Jifa idan bashi da class, saboda a Kwai himma a wurin sa wurin kula da karantar da d'alibai.

Muna had'a idanu da shi kuwa, ya wani d'aure fuska, ya kuma sakar min wani uban muzurai.

"Zonan ke monita"

Jiki ya na rawa na isa garesu. "Gidan'ku ba'a koyar da tarbiyya ne?"

Yace , bayan ya jefa gyad'ar da ya murje bakin sa. Na Shiga dawurwura saboda bansan laifin da nayi ba, Sai da malam Abba yace min.

"Tsuguna Mana Sumayya. Ya kiraki kuma kin zo kin tsaya Mana a ka.

"Nan na fahimci Laifina, amma ni shi duk ya gigitani. Ganin Fa'izu Kawai tsorata nake yi.

Malam Fa'izu batare da ya ko kalleni ba yace.

"Sintirin me kike damun Mu da shi a staff room? Kullum kina kan hanyar zuwa nan? Uban me yake kawoki matattarar malamai?"

Na sunkuyar da kai sannan nace.

"Malami nake kira idan period d'in sa ta Shiga bai shigo ba".

Ya tsaya da cin gyad'ar cikin d'aga murya da fusata yace.

"Wayace Miki aikin ki na monita yana cikin haka? Hak'k'in ki ne Kiran malami, ko Hak'k'in malami ne yazo teaching da kan'sa?"

Ba suna da time table ba ma?"

Nayi tsuru tsuru da ni nak'i magana, gudun nayi laifin da zai casani.

Tuni duk kallon malaman dake staff room yayi yo kan Mu, saboda yawancin malaman suna hallare.

Da k'arfi Fa'izu yake magana, kuma nasan domin sujine, domin babu Wanda yake shakka, Sai ma su da suke shakkarsa, har ma da prince pal, da vice prince pal.saboda bayan zafin sa,ya tab'a cewa a kunne na da suna hira da malam Abba bayan staff room da zan wuce ta window, cewa yaja kunne a meeting domin kowa yayi hattara, na yana da hanyar da zai kai k'ara ma'aikatar ilimi ga shugaban kula da matafiyar ilimi na k'asa, in dai shugaba da malamai suka ci gaba da cin albashi a b'agas babu kula da hak'k'okin aikin su.

Malam Fa'izu ya dubeni cikin fushi.

"Kar ki sake na k'ara ganin k'afarki a staff room da niyyar Kiran wani malami. Wallahi na sake ganin ki? zaki fuskanci hukunci na ban Mamaki. Ihope you get it?".

Na jinjina kai.

"Kin fahimta nace? Talk to me."

Na gyad'a kai da sauri.

"Na fahimta, sorry sir."

Yaci gaba da kallo ga malamai da suka kafa Mana idanu.

"Albashi a na biyan kowa duk month mai nauyi kowa ya lamushe cikin jin dad'i amma ace wai Mutum baisan time d'in aikin sa bama Sai an kirashi? Why? Is not fair gaskiya. Menene amfanin time table da agogo Kenan?

zamu sake zama da prince pal da teachers dole a yi gyara."

Babu wanda ya iya cewa kanzil kuwa, saboda gaskiya ya fad'i da ba kowa zai iya bugar k'irji ba ya fad'I, Sai irin sa Mara tsoro mai dakakkiyar zuciya kuma.

"Tashi Kije".Yace dani da nayi sunk'ui da kai.

Tun daga ranar, ban sake yarda naje staff room ba, saboda gargad'in malam Fa'iz. Domin nasan makomata ma idan ya kamani.

Ba'ajima ba kuwa na fahimci anyi gyara.

Domin da lokaci ya Shiga malami Zai shigo da kan'sa. Ba kuma Zai fita ba, Sai lokacin'sa ya fita. Kuma karatu ya k'ara zafi. Malamai sun daina shigo da hira da wasanni cikin karatu, Wanda nafi kyauta ta zaton malam Fa'izu ya fahimci duk matsalolin dake cikin harkar koyarwa yasa aka kawo gyararraki. Ko Mak'iyin malam Fa'izu tabbas ya yarda sanadin zuwan sa, makaranta ta gyaru.

Sauye sauyen ci gaba da ya kawo da yawa na ci gaba. K'orafin da a ke yi da shine bai kau ba wato na tsanani da cin zarafin studen't fiye da k'ima idan sun yi laifi. To ni fahimtata da hakan , Kawai na fahimci Fa'iz Mutum ne mai fushi da zafin zuciya. Shi yasa ma Sam baya d'aukar raini. A binda ya shige min duhu da shi, na yarda baya karb'an uzuri. Kuma baisan kalmar Hak'uri ba.

Watanni uku suka rage muyi jarrabawar kammala makaranta. Saboda haka rannan Bayan malam Abba ya gama yi Mana subject d'in sa na mathematic, ya zauna yana bamu shawarwari domin mu kara zage damtse da karatu mu samu sakamakon jarrabawa mai kyau.

Zainab mazawaje