NI DA GIDANA

Chapter 3

by @zainab221

NI DA GIDANA

NA

Zainab Ilyas mazawaje

Best brilliant intrlligent writer..... 🖋️

page 3

Malam Abba, ya gyara tsayuwa, ya fuskanto mu yace.

"Ko da yake yanzu kuna birgeni, naga ma ai duk kun canza kunyi laushi.

Da idan an shigo a jin nan kamar kasuwar trade fair, amma yanzu kamar gidan makoki. Ko babu malami zanga Kowacce ta d'auko littafi tana bitar karatu. Wai yaya a bin yakene.? Ko walwalar ku ma bana gani."

Ya karashe furucin cikin wani murmushi mai nunin da wata manufa a cikin maganganun sa.

Fati d'alha tace "Sir, gaskiya ya kamata kayiwa aminin ka nasiha, ya fiye tsanani. laifi da k'arami da babba duk hukunci d'aya. Zagin da yake mana, ko iyayenmu basa yi mana. Wallahi matar'sa ta Shiga uku."

Intisar tace. "Addu'a zaku yi masa kawai, domin ya gyara halin sa, amma mutum ko aljani ba za su iya sauya malam fa'izu ba wallahi".

Kowa Sai da ya dubeta na Mamaki. Shi kuwa malam Abba murmushi yayi.

"Yauwa 'yar gari, Kunji in da ake kalamai na nutsatstsu. Kuma idan b'era da Sata ai daddawa ma da wari. Kuma k'iriniyarku tayi yawa, dole Sai irin malam Fa'izu ne zai yi dai dai daku. Malam Fa'izu idan ba'ace Sam barka ba, baza'a kushe ba. Gyaran da ya kawo cikin makarantar nan ai ya yawaita. Ko prince pal da vice sun Sara masa. Ai addu'a ya dace Kuyi masa ta alkhairi.

Ya dan yi shiru kafin ya numfasa yace.

Bayan tarbiyyar da ya kimsa muku ya gyara muku harkar karatu sosai. Kuma ku zakuci amfanin sa a gaba. Shi ba ma mazauni bane jiddin. A Kwai a binda yasa a gaba, da ya samu zai bar harkar koyarwa, Kawai ya Shiga harkar da ba itace burin'sa ba, sabod kishin kasarsa.

Zan iya rantse muku albashi ma shi baya gaban'sa. Burin sa a samu sauyi da ci gaba. Saboda haka kuskure ne d'alibi ya zauna yana aibata malami ko da dalili, tun da kullum cikin cin amfanin sa yake. Kuma ba'a iya biyan malami kun sani sai ubangiji ne kawai zai iya biyansa".

Jikin kowa yayi sanyi. A ka rasa me iya cewa komai. Ni kuwa dama nasan kuka suka kawo gidan mutuwa. Malam Abba na hannun Daman malam Fa'izu ne, bazai tab'a yarda a ai bata shi ba ya k'yale, duk da dai gaskiya ya fad'I.

Alkhairan da malam Fa'izu ya kawo, a makaranta, bai kamata a aibatashi ba, koda yayi laifin. Kowa ma yaji ba domin kud'i yake koyarwa ba, Sai domin kishin k'asar'sa. Wannan kad'ai ya isa yasa ya karb'i lambar yabo.

Tunani na kenan da na wasu d'alibai da muka zanta daga baya.

Daga baya ga mamakin mu, malam Fa'iz ya sassauta tsananin nan da tsaurara hukunci garemu. Kuma na lura canzawar da yaga munyi ne, Shima yayi d'an laushi. Sannan ya fito da wata hanya ta taimakon mu, don mu haye a

jarrabawar mu ta gama makaranta ta gaba to.

Lesson ya tsara duk yamma cikin makaranta ga duk wacce ke ra'ayi amma. Shi ya d'auki nauyin komai.hud'u da rabi an Shiga a tashi k'arfe shida na yamma. Duk d'alibai kuwa a ka yi ta tururuwar zuwa, saboda kowa so take taci jarrabawa.

Ba kuma iya darasin turanci yake koyawa ba, har ma da sauran darussa. Kuma yawancin a binda yake koya mana wanda yake tunanin zai fito mana ne a jarrabawa.

Baki d'aya muka ga ya canza ma. Ya rage zagi da fad'an nan da tsare gida. Amma duk da haka fa babu fuskar da za'a kawo masa raini ko wasa. Har hira ma yake damu amma fa a kan karatu, da bamu shawarwari masu kyau, duk a kan harkar karatu, saboda jarrabawar dake dosomu.

Da jarrabawar tazo kuwa mun taki babbar sa'a. Domin kuwa yawancin a bubuwan da malam Fa'iz ya koyar damu shi ya fito. Har zargi ma muka rink'ayi anya bai samu tambayoyin jarrabawar ba a boye, domin komai ya fito da ya koyar damu.

Ai sai yayi kuma farin jini wurin mu. Domin yayi mana k'ok'arin da babu malamin da yayi mana irin sa. Mun kammala jarrabawar cikin sa'a da kyauta ta zato, domin duk wacce ta sare, sai dakikiyar da kwakwalwarta ba ta aiki.

Ranar da muka kammala jarrabawa da yamma, aka sha hotuna, har da malamai a kayi hotuna. Amma fa banda malam Fa'izu. Kuma anfi kwad'ayin ayi hoton da shi, saboda tarihi. Kuma abin alfaharine ga d'alibai, amma mirsisi yak'i.

Ko da yake tsoron tun karar'sa ma a ke yi, malam Abba a ka tura. Ya dawo yace.

"Kuyi hak'uri fa. Abokina yak'i yace yana da mata, kuma zatayi kishin haka.

Duk d'alibai sun yarda, nice dai kunne na bai karb'a ba. Lambobin waya ma na malamai da ake karb'a malam Fa'izu hanawa yayi. A ka koma takan malam Abba ya bada lambar wayar malam fa'iz yace shi bashi da ita. Ta yiyu shi ya hana shi ya bayar, nafi kyautata zaton hakan.

Intisar tafi kowa damuwa da lambar Fa'iz, saboda son da take yi masa ma ya fito fili. Amma ko giyar wake tasha bazata iya tambayar sa ba. Tun daga Sanda tayi masa rashin kunyar nan suke takun sak'a da shi. Ta gasu a hannun'sa.

Tsakanin sa da ita hararace. Duk Sanda ya shigo class Sai ya tasheta yayi mata tambayoyin abinda ya koyar. Ta fad'i wanda ta d'an fahimta, tana yi yana jefa mata kallon wulakanci, da ta kakare kuwa zai ta gasa mata maganganun tozarci da gwara dukan ma dasu gaban dalili bai, to ya fuskanci tafi jin ciwon bakaken kalmomi, shi yasa baya dukanta ma sai dai ya tozarta ta gaban jamaa, ta hanyar cin zarafi da furuci.

Gaskiya Ancle Fa'iz yasan takan iya tsiya, da ka fada tarkon sa, gwara a jefa ka gidan yari iya na waadin laifin ka. A cewar zuciyata .

Tsawon wata guda, tun da na gama secondry, babu in da nake zuwa bayan islamiyya. Sam kuma fitar bata dameni ba ma saboda ni dama ba ma'abociyar son yawo bace. Sannan soyayya da tarairayar da nake sha wurin kawuna sulaiman ta isar min daga damuwa da wani a bu a rayuwa da zai sa na rinka yin tunane tunane.

Kulawa gata, sangarta so da k'auna duk Kawu sulaiman ya tattare su a kaina. Haka ma kakana Laminu mai turare. Sai 'yar korar su mai taya su, matar kakana Baba Talatu da ya auro bayan rasuwar Inna Hajara kakata. Duk da baza'a had'ata da kakata ba inna Hajara, amma tana kamantawa sosai.

Ni d'in marainiyace ta sosai, tun da ban bud'i idanu da iyaye na ba duk sun rasu Ina yarinya sosai. Bayan nan kuma nazo na rasa kakata Hajara ita ma data rungumi maraicina da kyau, take nunamin k'auna muraran. Sai da ta shekara da rasuwa kakana yayi aure, kuma saboda ni. Saboda babu yarda za'ayi ya zauna dani babu mace.

Naga mutuwa a rayuwa ta Kam. Amma Sai a tara masu iyaye Sama da d'ari ba'a samu mai Samun kulawa da tattalin k'auna iri naba.

Shi yasa bayan rasuwar kakata Soyayyar ta dawo kaina. Haka ma kawuna Sulaiman Soyayyar dake tsakanin sa da yayarsa mamana Khadija da bazata fad'uba, kaina ya tattarota bayan rasuwarta. Su biyu ne tal wurin iyayen su, kuma a Kwai k'auna da fahimta mai zurfi tsakanin su. Wannan dalili yasa Kawu yake mugun Sona da tausayina. Motsi kad'an yana bibiyar me nake ciki. Kome ya samu ni zai kawowa. Tun da ya gama digree babu aiki ya Shiga buge bugen aikin Samun k'ud'i na k'arfi, daga wannan zuwa wannan, duk saboda ni. Ma'abocin son K'wallon k'afa ne sosai. Suna da Club babba ma na matasa irin sa. Suna buga mach kurfa kurfa na state state bayan na garin su idan an gayyace su. Yama fi Samun kud'i tanan babu laifi. Amma lokacin daya ke bawa boll dabam, lokacin buge bugen sana'oin sa ma na kafi zuru da bam. Yayi rini, yayi Aikin gini, yayi aikin electric, har aikin fenti ya iya, idan an kirashi zai b'adda bami yasa Kayan aikin yaje yayi ya karb'i kud'in'sa.

Mai k'wazon neman na kaine Kawu Sulaiman, bashi da girman kai Sam. Kuma duk sana'ar da yaji ana Samun kud'i zai koya, ba tare da raina taba. Shi yasa baya rabo da'yan kud'ad'e. Bamu da shi sai dai na rufin a sirin rayuwa, kakana ma a zaune yake ba kullum yake fita ba, da harkar Sai da turare ta karye masa. Da kanti ne da shi guda na saida turarurruka, yanayin rayuwa komai yaja baya. Kawu sulaiman ne ke k'ok'arin a bubuwa da yawa. kuma rayuwar mu babu fallasa, komai a Siri a rufe ruf.'Yan kayan k'walam na motsa baki ma Kawu na kan sayo lokaci lokaci. Ban rasa kuma 'yan Kayan ado irin na 'yammata ba, Kawu sulaiman yana fito dani kunya, ko ban furta ba zai sayo dai dai ikon sa. Ya kuma ban k'ud'i ko zan buk'aci wani a bu.

Wani lokaci zaice na samo takarda da biro na rubuta duk abinda nake bukata na 'yan mata, nakan rubuta na bashi, shi kuma duk sanda ya samu iko ya kan sayo su a hankali a hankali. Kuma da an dauki lokaci zai sake cewa na rubuta abinda nake bukata, sannan ya kan bani 'yan kudi na kashewa ma jifa jifa, kuma ya danganta da nauyin aljihunsa na daga a binda zai bani.

Ya wanke min duk wani hawayen maraici, saboda ubana talaka ne sosai, bai barmin komai na gado bama. Ko gidan da suke zaune da mahaifiyata ma na hayane, kuma biya masa ake yi. Tun mahaifiyata tana raye Kawu na yake nunamin Wata irin kulawa da soyayya, da Ina yarinya naji daga kakata, bawai

sai data rasu ba. Domin da ta rasun ninkawa kuma yayi.

Ya kusa zautuwa ma kawu da mamana ta rasu saboda kusancin sa da ita da k'auna. Kakana ma da matar sa kulawa da k'auna suna bani iyayin'su, saboda maraici hawan hawa da na samu kaina a ciki.

Ina da ra'ayin son ci gaba da karatu, shi yasa ma aure baya gabana, ko kula kula da shaannin samari ba nayi, kuma kawu ya goyamin baya.

Ina da samari, tun kafin na kammala secondry. Duk da haka dai i

na da samari biyu da nake sauraren su sama sama.

A Kwai Alhaji Rabi'u magidanci mai mata da yara. Yana da sukunin sa kuma yanayi min 'yan hidindimu. Yana da mota da yake zuwa wurina ma. Sai usman shi kuma saurayi ne, tela ne na aikin surfani.

Hankalina ya d'an fi kwanciya da Usman saboda shi saurayi ne dai dai dani. Ina tsoron fad'awa tsakiyar ma'aurata. A nawa ra'ayin gwara tazo ta sameni.

Amma shi Alhaji Rabi'u kullum zancen'sa na bashi dama ya fito, amma bana bashi had'in kai. Shima Usman ya damu da azo a yi wani a bu, Shima d'in ma ni nake bashi matsala. Ina son na samu ilimi sosai nayi aiki na rink'a tallafawa Kawu da kakannina. Wannan shine burin sumayya a b'oye.

Kwanci tashi jarrabawar mu ta fito na samu sakamako mai kyau k'warai. Shi yasa direct jami'a,suka amsheni.

Kawu yayi ta samin albarka. Sosai yayi farin ciki, har kyauta yace zai min. K'awaye nama duk sunci da kan mu yake a had'e. Saboda halayyar mu guda ce ta son karatu. Amma nafi su kyawun sakamako dai.

Kawu sulaiman yayi min nasiha sosai da shawarwari, wurin tafiyar da rayuwata ta jami'a. Yaja kunne na sosai a kan kar nayi mu' a mala da k'awayen banza da samari. K'arshe yace.

"Na baki dama, don Allah kar ki bani kunya Sumayya, kija mutuncin ki, kiyi a binda ya kai ki Kawai, wato karatu."

Nace" Kar kaji komai, Ancle, zan kiyaye, ka ta yani da addu'a."

To ban bashi kunyar ba kuwa. A shekarata ta biyu a jami'a ya dad'a sakin ransa sosai saboda yarda yaga komai nawa yana tafiya dai dai, Sai ma k'arin ci gaba. Na k'ara nutsuwa wurin kula da tattalin kaina. Na k'ara sanin darajar kaina sanadin k'yamatar wasu a bubuwa da nake gani. Na k'ara kyau na gogewa da wayewa kuma, amma wayewa ta sanin mutuncin kai da darajar kai, da iya muamala da mutane, da kiyaye abinda zai rusamin rayuwa.

Ba fara bace ni, amma za'a iya sani a layin farare idan sunyi k'aranci. Saboda kulawa da kaina da nake sosai, fatata Sai ta k'ara gogewa ta haskaka sanadin gyara. Kawu lokacin Samun'sa ya k'aru, ya kuma Saki Samun'sa sosai a kaina ma a lokacin. Burin sa Kawai Sumayya ta zama a bar kwatance da alfahari.

Alkalamin...... 🖋️

Zainab Ilyas mazawaje