Chapter 4
by @zainab221
NI DA GIDANA
By
Zainab Ilyas mazawaje
Best brilliant intelligent writer..... 🖋️
page 4
A tsukin kuma wanda nake kira da d'an fodiyo wato (usman), ya matsa lamba.
Sai ya nuna ala tilas sai na barshi ya turo manyan sa shi ya gaji da jirana. Ga a binda yace da nak'i yarda.
"Sumayya, don Allah ki rufamin a siri nasan Matsayina. A farga ba nake tsindim na zaki iya kub'cemin. A komai kin canza kin samu haskakar da za'a k'yalla idanu a kan'ki a kawo miki hari. Babban a binda nafi kwad'ayi a kan'ki shine kamun kan'ki da nutsuwa da tarbiyya. A ina kike tunanin zan lalubo irin'ki idan na rasa ki?
Tabbas zan shiga tasku idan na rasa ki. Ina sonki Sumayya fiye da tunaninki, don Allah kar kiyi min wasa da hankali. Ni dai na fito a San dani nasa rai ma. Aure zan jiraki zuwa lokacin da kika shirya."
Sam aure baya raina a lokacin, ko fidda ma gwani. Tausayin Usman shi yayi rinjaye a raina, bawai son'sa ko son auren'sa ba. Saboda nacin sa da magiya na a mince amma nace ya bani kwana ki biyu nayi magana da Kawu na.
Yayi ta murna kuwa.
Ranar da mukayi zan fad'awa Kawu Sulaiman, Usman zai zo yaji inda a ka kwana, ranar Kawu na ya tashi da gyare gyaren d'akin'sa, saboda ranar lahadice baya fita Sai yamma, ni kuma bani da lacture. Na shiga taya shi, saboda gyaran da yawa. Kusan yayi d'ai d'ai da komai na cikin d'akin. gyare gyare da goge gogen da yawa.
Na kafe Sai ya barmin nayi ni kad'ai. Ya saduda ya tafi ya barmin.
Da yake Ina da saurin aiki, sai gashi na gama, ina mai da komai muhallin'sa naci karo da wata farar ambulan 'yar babba.
Ko Ancle Sulaiman ya sanni da lafiyar bincIke. kamar nawa na Shiga k'ok'arin bud'ewa, domin naga menene a ciki. Amma a tsorace nake kar ya shigo ya ganni, yace mai hali kin soma ko? Domin na saba da wannan kalma tun Ina yarinya.
Tuni na fahimci hotuna ne, da sauri na shiga zaro su, duk zatona hotunan budurwar sace da ban tab'aji da gani ba.
A bin takaici a gareni, hotunan maza na gani, saye da kayan 'yan boll har dashi. Wani Mutum uku wani mutum biyu wani shida. A Kwai kuma wanda suka had'u su duka suka sa boll d'in a tsakiya shida 'yan club d'in nasu.
Amma menene yaja hankalina na kasa a jiye hotunan kamar yarda naso da fari, da naga ba hoton mace bane?
Mutumin da na yanke zaton zan sake gani a rayuwata, Mutumin da nasan babu wani dalili na sake had'uwata da shi, shine a cikin hotunan 'yan club d'in su Kawu
Sulaiman.wanene?
Faiz Bukar.
Na sake kai ganina ga hoton, amma bisa ga wanda ya d'au hankalina da ganin'sa wato Fa'iz.
Gaba d'aya ya haske hotunan. Kowanne da ka kalla, shi zai fara janye kallonka. Muryar Kawu Sulaiman naji a tsakar kaina.
"Me hali baya fasa hali dai. Bincike kike min ko gyara sumayya?" .
Nace. "Yi hak'uri my Ancle. Wani malamin mu na secondry na gani shi yasa na tsaya dubawa ma, dama kasan shi kawu?".
Na nuna masa shi.
Ya duba yace.
"Au, Yarima kike nufi?".
Na sake nuna masa shi, ga zatona bai kulaba.
"Ka ganshi fa, wannan farin na cikin ku, malam Fa'izu fa."
Yace. "Shi d'in nima nake nufi ai , sunan'sa Fa'izu, amma mu a bokan'sa Yarima muke ce masa. Mu kance masa kuma Gimba, wato d'an sarki, a hausance kenan. Amma mun fi Kiran'sa, da Yarima, a yaren barbarci ne, saboda usulin mahaifin'sa babarbare ne, mahaifiyarsa kuma k'abilar shuwa a rab ce.
Na dubi Kawu saroro.
"Me yasa kuke ce masa
Yarima Ancle.?".
Murmushi yayi ya karb'i hoton."Abokai suka sa masa kuma ya bishi. Baki ga takunsa yayi kama da na masu wannan sunan ba kema?".
Nayi gajeriyar dariya.
"Tabbas na harbo jirgin Kam, sunan ya dace da shi sosai, kun iya sa sunan a muhallin'sa. Ai ya yiwa dalibai horo sosai a school d'in mu. Bana zaton a kwai d'alibar da zata mance dashi. Sunayen ma da za'a kirashi da shi suna da yawa. Dama d'an club d'inku ne Ancle?".
"Sosai, a harkar boll kuma muka had'u muka saba. Shekara shida Kenan da ya shigo club d'in mu na Kaduna united. Ya iya boll fiye da zaton mai zato, da shi muke ji a club. Ko jiya na had"u da shi da yamma a club, mun Sha hira a kan gasar wata boll da muka je. A Kwai mutunci tsakani na dashi, duk da babu wata a bota dai sosai tsakanin mu, Sai mutunci sanadin club tare da buga k'wallo.
Hirar ta datse ne saboda baba Talatu da ta kirani.
Usman dan fodiyo da yazo hak'uri na bashi, nace ya k'ara min kwana biyu dai. Mantawa nayi ban yi Maganar da kawuna bama.
Kwana biyu tsakani da yamma Lis, ina zaune tsakar gida, Kawu sulaiman ya shigo, nayi masa sannu da zuwa, haka ma baba Talatu. Yayi mata sannu da gida.
Ya dubeni yace.
"Sumayya yau ina tare da Yarima, yace a gaisheki."
Nace"Ina amsawa."
Ya wuce yana yin wani murmushi da bansan musabbabin'sa ba. Ni dai nasan babu yarda za'ayi wallahi Fa'izu yace a gaisheni. Mutumin dake bala'in jida kan,sa. Ta ina ma ya tuna da sumayya, a rayuwa? Shekaru biyu fa Kenan rabona da gama makaranta. Kawai bazan iya k'aryata kawuna bane. Washe garima da Kawu zai fita sai yace min.
"Sumayya yau ma zamu had'u da Yarima da k'arfe uku na rana a club, me zance wa Yarima?".
Nace"Bani da a binda zance masa Kawu."
Yace. "K ika yi haka baki kyauta ba, amma shi yace a gaisheki? amma zan ari bakinki na cimiki albasa kawai. Ni dai ban tofa ba. A yar tambaya ce ta soma tsayamin a rai name kawuna yake nufi da son had'a a lak'ata da malam Fa'izu? anya babu wani b'oyayyan al'amari a zuciyar'sa?.
Ture komai gefe kawai nayi na shiga dakon jiran'sa ma na ya dawo nayi masa zancen d'an fodiyo, domin ya matsamin da sai ya turo iyayen'sa
Usman yazo zance wurina, gaisawa Kawai mu kayi, kafin ma muyi nisa da magana, Sai ga Kawu Sulaiman ya dawo. Yana shigowa farfajiyar gidan, Usman ya rusuna ya gaisheshi, cikin tsantsar ladabi. Ni kuma nayi masa sannu da zuwa. Yace.
"Sumayya zo na ganki na 'yan mintina".
Nace"To, gami da Mik'ewa. Ya kuma waiwayi Usman yace.
"Usman, kad'anyi hak'uri na katse muku hira, yanzu zata dawo."
Ya nuna har a fuska babu komai. Hanyar fita waje yayi, na bishi. Kafin mu isa ga k'ofar fita yace."Sumayya, Yarima na kawo miki Ku gaisa. Daga meeting muke na wasan k'wallo da zamu buga da k'ungiyar 'yan boll ta Dolfin, very soon. Shi ya kawoni gida ma a babur dinsa, kinsan
nawa ya samu matsala. Sai nace to why not bazaku gaisa ba, ko kuwa?"
Murmushi nayi nace "To, Ancle."
Kawai Samun kaina nayi da fargabar had'uwata da Fa'izu. Gabana ya rink'a fad'uwa ma, Yayin da na tuno d'abiun'sa na cin zarafi da fushi ko yaya aka kuskuroshi. Ban manta komai ba. Shi yasa nake ganin komai ma kamar lokacin da yana koyar damu, kamar zan yi masa kuskure yaci zarafina.
A k'ofar gidan Mak'ocin mu Alhaji Bilyanu muka sameshi ya jingina jikin sabon Jan babur daya kasance nasa. Hasken fitilar k'erarren gidan mai haske komai ya haskemin shi sosai. Saye yake da Kayan 'yan boll koraye, Amma wandon dogone mai taushi. Ban tab'a ganin Mutumin da kayan 'yan boll suka yi masifar yi masa kyau ba, irin Fa'izu. Domin sun k'ara haskaka shi ma. Wani kyau naga ya k'ara da haske da 'yar k'iba ma kad'an, da ta k'ara yi masa kyau fiye da da. Ko har yanzu yana koyarwar?. Kaina na tambaya. Na yarda lallai ya samu dan cigaba na rayuwa, don ada bashi da babur sanda yake koyar da mu a makaranta.
Na rusuna na gaisheshi.
Ya k'ara d'aga idanu ya dubeni sosai bayan ya janye daga jingina jikin'sa da yayi jikin babur. ya dubi kuma Kawu sulaiman. Kawu Sulaiman kuwa tsare mu yayi da kallo ni da fa'izu ya kalleni ya kalleshi hak'oran sa waje cike da nishad'i da bansan dalili ba. Fa'iz ya dubi Kawu na.
"Kasan Sai yanzu na ganeta Sulaiman? ai da ban fahimci wacce kake ta kwatantamin ba, saboda d'aliban da yawa ,ko na santa, ko sunan'ta iyanzu mantawa zan yi, an fa jima da yawa. Na manta sunan ta dai, amma na ganeta a ido. Sanin monita nayi mata na Class 6 B ko?.fitinan nun school ai dole na rike wannan class, duk da na gyara musu tsari".
Tabbas baka da mantuwa Malam Fa'izu. Zuciya ta ta kimsamin.
Na gyad'a kai, Sannan na kai dubana ga Kawu Sulaiman, na kuma dire kan Yariman nasa .
Carab Sai muka had'a idanu kuwa. Sai yayi dan murmushi kafin ya maida kallon'sa ga Kawu Sulaiman ganin mun hada idanu.
Zan iya cewa shine farko da nata b'a ganin murmushin Fa'izu gareni, a iya sanin da nayi masa. Cikin tausasa murya yace.
"Sumayya, ai ban tab'a sanin ke Jinin Sulaiman bace. Da nasan hakan, Atleast ai da kinsamu kulawa irin wacce ta dace. A Kwai a minci da girmamawa tsakanina da kawun naki, he mean so much to me. Ina ganin k'imar'sa da shi kan'sa baisan iya ganin kimarsa ba da nake ji game ni. Nima yanzu Ancle d'inki ne Sumayya kinji ko?".
Na sunne kai k'as cikin murmushi nace"To".
Ya maida hankalin'sa kan Kawu Sulaiman kuma.
"My man, Ina cikin mamaki fa yarda k'addara take ta had'ani da wannan Daughter taka, bayan mun rabu.
Sau uku Kenan fa. Three times Sulaiman. Ya nuna yatsun'sa uku yana nuni da shi.
Ni Kam sak'e sak'ena nake, Ina ganin kamar a majigi komai ke faruwa. Malam Fa'iz ke tausasa harshe yana fad'amin wad'annan kalaman? Dama ya iya tausasan kalamai a she?
Kawu Sulaiman ya duba yana mai cewa.
"Farko ta yarda wayar'ta na tsinta, ta kira layin mu kayi magana ta kwatan'ta min gidan nan na kawo mata. Kasan ban tab'a zuwa gidan nan ba Sai yau ai da tun a ranar na d'au haske, domin Sai yanzu komai ya dawo min,nan gidan nazo na kawo mata waya. Bayan watanni mun sake had'uwa da Sumayya a makaranta nayi teaching d'inta, Kenan a malamin ta nazo. Yanzu kuma Bayan shekaru biyu mun sake had'uwa da ita ta dalilin ka. Me hakan ke nufi Sulaiman, da sanadi ke ta had'ani da 'yarka?".
Murmushi Ancle d'ina yayi yace.
"Da walakin goro a miya. Kuma ruwa baya tsami banza. Idan kaji gudu kuma to da magana.
Fa'izu baice wa kawuna komai ba, game da furucin da yayi, don wasa ma naga ya dau zancen. Ya sake dubana cikin dan jin kan nan nasa kamar bazaice komai ba ya dan juyar da kai sannan ya dawo da shi kaina yace.
" Karatu kike yi ne Sumayya?".
Nace"Eh".
"Da kyau, kin birgeni. Ki daure ki zurfafa karatu, kici moriyar sa tun da kIna da k'wak'walwar fahimta. Ina yi miki fatan alkhairi da nasara."
"Na gode Ancle."
Na fad'a cikin wani nishad'i da naji ya bak'unci zuciya tashi guda. Gani nake tamkar ba Fa'izun da na Sani bane. Wannan yafi wancan kyawun Siffa ma da ake ta kwaroroto, da dan jiki kadan da ya kara, duk sanadin dan hutu da na fahimci ya samu, kuma sai naga yafi kyau a hakan, kuma halinsa ya canza wurin sanyi da sauk'in kai, amma nasan da dalili.
Amma dai tabbas shine, tun da gashi mun tuna baya ma. Sai dai nasan komai yanayine sanadin kawu Sulaiman ne wanda ya nuna yana da muhimmanci a gareshi.
Ku biyo ni dai labari ba a soma ba ma tukun.
Taku Zainab ilyas mazawaje