DINGISHIN KWADO

,9

by @surayyaibrahim

09

Bojuwa herbs*

*Oder your kayan mata for women of class*

*Our products are healthy and original*.

*Tested and trusted*.

*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*.

*Dan Allah Ki zo Ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi Ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai ita zuba kudi ya sarosu ba*.

*Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*

*Just DM for your order @****.

*09*

Da mamaki ya ce "Maigado wannan kike nufi?"

Da kazangi ta ce "Bilkin da take gefenka dai".

Ya numfasa ya rasa abin fad'i. Can ya sake numfasawa ya ce "Wonder shall never end! To kuma ta fasa da Faruku ne?"

Abida ta ce "Ai tunda ya yi aure ta ce "Ta fasa fas dama kuruciya ce".

Ya kallo ni kad'an ya mayar da fuskarsa a kallon gabansa.

Ya ce "Maigado wai kin fasa da Faruku da gaske?"

Da yake ni ban iya karya ba, ko zagaye zagaye ba.

Sai kawai na daga kai tabbacin eh.

Ya ce "Ikon Allah ban yi zaton akwai lokacin da zaki ce soyayyar da kika wanzu kina yi masa zata zama ta kuruciya ce ba. Lallai yau na sake fahimtar al'amarin mata da kuma kuruciya babban al'amari ne da ba zaka ganesu ta dad'in rai ba."

Abida ta sake ce wa "Kasan tun akan auren da Yaya Faruku ya yi na karaya da lamarin Bilki. Domin ranar da muka dawo ta samu labarin ya yi aure kukan da ta yi ba kad'an ba ne. Sannan sai wanccan term din fa ta yarda suka shirya take kula shi. Gabadaya boye masa take yi. Shima sai da sharadin ita ba budurwasa ba ce"

Yaya Asad ya saki gauron numfashi ya ce "Allah ya kyauta. Amma dai ki dage da karatu, kar ki yarda ki jefa kanki a cikin had'arin soyayya. Idan kika yi Ilimi maza da yawa zasu so ki kala kala. Sai ki ga har da manyan mutane masu rik'e da mukamai daban daban ko manyan Alhazai y'an kasuwa".

Abida ta sake ce wa "God forbid auren d'an kasuwa, basu iya komai ba sai ra'ayin ruk'au, da dunkufe cigaban mace".

Cikin kaduwa ya ce "Autar Momi gaskiya kin kerewa tunanina, wato saboda kun girma ba'a gabana ba ya sanya giggiwar ki ta yi yawa ko?

Ki tabbatar a gidana zaki yi karatun ki na jami'a, na ga alama sai na sake sanya ido akan ki k'warai da gaske."

Yana rufe baki ta yi maza ta ce "Haba Yaya ai idan sallar daren da nake yi akan Baba ta karbu ai abroad zan wuce na yi karatuna. Sola zaka dauka ka saka mata ido tun bata daukowa kanta mijin kara da kiyashi ba".

Kan dole ya yi shiru yana mamakin yadda k'ananun yara suka girma tashi guda. Ya numfasa yana tuna shekarar haihuwarsu ya kammala karamar sakandire.

Har suka k'arasa garin Bakori bai bar mamakin wayewar da ya gani tare da Abida ba. Haka nan shiru shirun Bilki da yake ganin ya yi mata yawa tun tana k'arama ya fahimci ya bita har kan girmanta da alamun rashin wayo a tare da ita, amma kuma ya fahimci tana cikin mata masu tsananta soyayya masu tsananin kishi. Wanda hakan alamun mace na cikin kalubalen fad'awar gararin rayuwa. Domin abubuwane guda biyu da mace ba zata iya tsallakewa ba. Na farko soyayya ta zama mahadi ne na rayuwar kowanne bil-adama har ma da wasu halittun irinsu jinnu da dabbobi.

Sannan kuma kishi shima wani gini ne da ba zai yiwu mace ta rushe shi daga jikinta ba.

Shi a yanzu da yake da shekaru bakwai da aure matarsa bata huta da saka masa ido ba, bata hutar da zuciyarta zullumin kada ya so wata ko ya kula wata macen ba. Duk da babu wata k'ofar da ta gani na ce wa yana soyayya da wata macen. Shi a karan kansa ya k'yamaci polygamy domin yana kallon artabun da ake yi a tsakanin yan'uwan da suka fito daga mabanbanta iyaye mata. Mahaifi kuwa kullum a cikin zargin yafi karkata a wani bangare yake, mafi yawa iyaye mazan da suke da mabanbanta iyalai sun fi saurin tsufa da gajiyawa sabida tsananin zullumi da fargabar yadda ahalinsu suke a wargaje.

Bayan hakan y'aya'n kullum a cikin artabu suke da matan uban, haka matan uba a cikin dauki ba dad'i ake da su akan y'aya'n da ba nasu ba. Wadannan dalilan ya sanya ya k'i polygamy ya k'udire mace guda ta ishe shi rayuwa kamar yadda ya taso ya ga iyayensa maza da mata guda guda. Shiyasa zumunci da soyayyar gidansu ta sha banban da ta kowanne ahali.

Amma matarsa bata gane hakan ba, kullum cikin tsanantawa kanta take, har fad'i take yi, jikinta na fad'a mata kamar watarana zai samo yarinya sa'ar Nauwara d'iyarta ta farko ya aura. Da haka gara ya yi yanzu ba sai ta tsufa ya dauko mata yarinyar da zata zo ta rainata ta hanata sakat a gidanta, saboda tak'amar tana gamsar da miji da kuruciyarta ba. A duk sadda take irin wadannan kalaman dariya yake yi tare da ce wa "K'arin aure ai zuwa yake yi, idan an k'addara mini zan k'ara da kaina ne zan fad'a miki. Ki daina tayar da hankalinki akan abin da yake gaibu ne".

Amma a k'asan ransa baya da ko sha'awar ya k'ara din, amma baisan me yasa tsayin Bilki ya yi masa ba, yadda take a tsaye cak, mai fadadden k'ugu zata dace da matar jarumin d'ansanda irinsa.

Sai dai kuma yana ganin yarinyace k'ankanuwa da bai kamata ya bijiro da wannan maganar a tsakaninsu ba, mussaman da yake ganin Faruku yafi shi cancantar ya yi amarya da ita.

Daidai lokacin ya isa cikin harabar babbar makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori.

Ya tayamu sauke kayanmu, ya damkawa kowacce sabbin y'an d'ari guda goma, dubu d'aya kenan, wanda a wanccan lokacin dubu guda kudi ne mai nauyi ainun.

Ya mana nasihar mu kame daga k'awayen banza, mu kuma dage mu fito da result mai kyau ta yadda zamu samu gurbin shiga makarantar gaba.

Muka yi masa godiya, ya ja motar ya tafi.

Yana fita, motar gidansu Basma ta shigo. Muka rungume juna da ihun murna. Tare muka biya leburori suka kwashe mana kayanmu zuwa hostel.

Daren ranar bana mantawa da shi domin da k'yar barci ya sure ni. Ba komai ya hana ni sukuni ba, illah yadda na ga mutanen gidanmu sun gasgata soyayya muke yi ta gaske da Yaya Faruku. A farkon kam lokacin da ba ni da wayo ina sonsa, da na shiga sakandire na gane soyayya tabbas ina jin sonsa har raina duk da shi zolayarsa ba zata bari a gane gaskiyar alqiblarsa ba. Haka dai muke tafiya a shine saurayina, domin duk sadda zan hakaito saurayina a duniya to Yaya Faruku ke zuwa mini, komai da komai nasa yana burge ni. Amma daga lokacin da ya yi aure na ji a duniya na tsani ko kallonsa na yi. A yanzu da nake yin hankali sai na fahimci ba sonsa nake yi da aure ba, kawai shakuwa ce, da kuma yadda yake girmama lamarina, shiyasa zuciyata ta bashi wani babban matsayi da ya zarce kowa a gidanmu har yan'uwana da muke ciki guda kuwa.

Amma tsakanina da Allah an jarrabe ni da ƙin auren zumunci. Ba dan komai ba ni dai a tsarina ne bana so, ban ga kuma wadda zan iya aura ba cikin ƴaƴan Baba Babba. Ko Yaya Usman da na ga take taken cewa zai yi yana sona tunda Faruku ya yi aure, nan da nan na canja masa fuska ko gaishe shi na daina yi, dan kada ma ya samu fuskar tunkarata ko bayyana maganar. Da ya fahimci bana ra'ayinsa ko kadan sai ya haƙura cikin salin alin, wata uku da aurensa yana zaune a katsina tunda a can yake aikinsa.

Baki da baki Baba ƙarami ya nuna mini yana son ya bawa Yaya Usman aurena da zarar na kammala sakandire, bayan auren na cigaba da karatuna a dakina.

*Bojuwa herbs ****

*Na ce kin taba shan sanyin flusher Dinmu?*

*Ko kinsan takanas ake kawo mini saiwowin da suke dagargaza dukkan sharrin sanyin da yake yiwa mara har ma da jijiya?*

*Ko kinsan sanyi flusher na kan gaba wajen garantin aikinsa a dukkan kayan da nake siyarwa?*

Ban ji nauyi ko shakku ba na ce "Baba bana sonsa, na ro'ke ka kada ka furta wannan kudirin naka wani ya ji".

A sanyaye ya ce "Ba zan miki auren dole ba, Allah ya had'aku da abokan arzikinku daga ke har shi. Na rufe magana tunda dama shi bai fad'a mini ba, amma nasan tabbas yana sonki, duk da yana iyakacin k'ok'arinsa wajen dannewa tunda bai ga fuska a wajen ki ba."

Na bata rai na ce "Na rufe k'ofar da zai furta, Yaya Faruku kad'ai zan iya karba, shima kuwa tunda ya yi aure magana ta k'are da ikon Allah ba zan yi auren zumunci ba. Ina jin tsoron kada zumuntarku mai k'arfi ta shiga tasgado".

Ya yi dariya sosai ya ce "Bilkisu babu yadda za'a yi akan dana na bata da d'an-uwana. Kinsan kuwa yadda muke son juna da Baba babba? Mu kad'ai iyayenmu suka haifa, kuma bamu tab'a rayuwa ba waje d'aya ba, ban da aikin da nake zuwa katsina na yi kwanaki bamu tab'a rabuwa ba, domin ko makarantar kwana tare muka yi a Barewa duk da ya zarta ni aji sosai.

Har yau ban haifi d'an da zai shiga tsakaninmu ba, tunda dai ba kya so, to na bar maganar domin Annabi ya ce "Kada mu aurar da ku sai kuna so, sannan yayunki da aka aurar babu wacce muka yiwa tilas, kema kuwa ba za'a yi miki ba."

Dad'i ya ratsa ni domin kuwa a da ina cikin zullumin kada a mini tilas din amincewa da Yaya Usman. Yanzu da ya yi aure kuwa hankalina a kwance tamkar ruwa a cikin randa.

Ni dai bansan ya aka yi na yi barci ba, tsabar tunani da kuma haushin da na ga ni a tare da Yaya Asad akan lamarina. Na tabe baki a zuciyata kuwa na ce me ma zaisa na yi tunanin zai iya cewa yana sona don na fasa yi da Yaya Faruku?

Me zan yi da mutumin da ya ba ni shekaru sha takwas kusan ashirin.

Da kaina na yiwa kaina dariyar hasashena.

*MalaysianFabrics*

*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*

*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba suda nauyi.*

*7020695644.*