CHAPTER 2
ALLURA TA TONO GARMA 2
Da Malam Hassan ya ga kawai so take ta tayar musu da fitina da safiyar nan, sai ya cewa Hauwa'u, "Ni na yi gaba sai kin taho." Ya fita daga ɗakin da sauri, Asabe ta watsawa Hauwa'u wani irin kallo ta ja dogon tsaki ta ce, "Ai indai ina raye a gidan nan, ba ki isa ki samu wannan tagomashin daga wajen Malam ba." Ta fice daga ɗakin ta bar Hauwa'u a tsaye riƙe da hijabi.
Zama ta yi a gefen gado tana tunanin irin wannan rayuwar da take yi a gidan Malam Hassan, ba ta isa ta keɓe da mijinta ba, sai Asabe ta yi musu laɓe. Ta rasa me ta tsare mata a rayuwa. Ta daɗe a zaune ita kaɗai tana tunanin wannan rayuwar da take, zaman haƙuri kawai take yi, don sai abin da Asabe ta faɗa shi ake yi a gidan, duk wanda ya bijirewa umarninta to ranar ba zai yi wunin daɗi a gidan ba. Bayan ta gama tunaninta sai ta tashi ta ɗauki hijabinta ta saka ta fice daga gidan zuciyarta cike da tunani kala-kala a kan irin zaman da take yi a gidan Malam Hassan.
Rana tana daf da faɗuwa. Ta rine nahiyar sararin samaniya na yamma da launin ja, a wannan lokacin idan ka kalli motoci da adai-daita-sahu da suke kan titin Zaria Road kowa burinsa ya isa gida. Ba a bar Malam Hassan a baya ba, shi ma cikin sauri yake tuƙa napep ɗinsa domin ya isa gida da wuri, don ba ya so magriba ta riske shi a hanya. Yana tsaka da tafiya, ya ga wata mata a tsaye ita kaɗai a gefen titi, fuskarta rufe da baƙin niƙab ta rungume wata jaririya da take ta faman kuka sai faman jijjiga ta take yi amma ta ƙi shiru.
Yayin da Malam Hassan ya ƙaraso kusa da ita sai ya ja burki ya tsaya, ya leƙo ya kalle ta ya ce, "Hajiya ina za ki je?"
Muryarta tana rawa kamar za ta yi kuka ta ce, "Malam don Allah ka taimaka min, Darmanawa zan je."
Malam Hassan ya ɗan yi jim, sannan ya dube ta ya ce, "Gaskiya ba can haka na nufa ba, da a ce dai Hotoro za ki je sai na ɗauke ki, amma ba Darmanawa na nufa ba."
Kamar za ta fashe da kuka ta hau roƙonsa a kan ya daure ya taimaka mata, ta daɗe a wajen ba ta samu abin hawa ba, kuma ga jaririyarta ta gaji sai faman kuka take a ƙarshe ta ce indai zai kai ta Darmanawa za ta biya shi ko nawa ne.
Ba yadda Malam Hassan ya iya, dole ya yarda ya ɗauke ta saboda tausayinta da ya mamaye zuciyarsa lokaci guda. Suna tsaka da tafiya yayin da suka zo dai-dai wani shago da ake sayar da kayan sanyi, sai ta tsayar da shi ta ce, "Malam don Allah ka ɗan yi min haƙuri zan shiga shagon can na sayo drinks."
Malam Hassan ya ce, "Ba damuwa, amma ki yi sauri."
Ya tsaya a gefen titi, ta ajiye jaririyar da take hannunta a kan kujerar ta fita da sauri ta nufi shagon sayar da drinks ɗin. Malam Hassan ya gyara zama a cikin adaidaita sahun yana jiranta, wasa-wasa yana zaman jiranta har ya shafe fiye da minti talatin ba ta fito daga shagon ba. Nan take ransa ya fara ɓaci, ya fito ya shiga shagon ya duba ko lafiya ba ta dawo ba.
Yayin da ya shiga ya tambayi masu shagon ko wata mata ta shigo ta sayi drinks, sai suka ce masa babu matar da ta shigo ta sayi drinks. Kan Malam Hassan ya ɗaure sosai, 'Ina wannan matar ta nufa ne?' Shi kaɗai ya yi wa kansa tambayar da ya gaza samun amsarta.
Cikin sanyin jiki ya dawo cikin napep ɗin nasa ya zauna ya ci gaba da jiran matar. A hankali duhun magriba ya fara saukowa, hankalin Malam Hassan ya ƙara tashi sosai ya fito ya tsaya a jikin napep ɗin yana hangen hanƴa don ya ga ta inda matar za ta ɓullo.
Babban tashin hankalinsa ma shi ne jaririyar da ta tafi ta bari a cikin napep ɗinsa. Yana nan tsaye har aka yi kiran sallar magriba, amma ko alamun matar bai gani ba, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganta ba. Hankalin Malam Hassan bai ƙara tashi ba, sai da jaririyar ta farka daga baccin da take yi ta fashe da kuka, nan take sautin kukanta ya cika wajen da yake gaba ɗaya.
Jikinsa yana rawa ya sunkuya ya ɗauko jaririyar yana jijjiga ta a jikinsa, amma ta ƙi yin shiru. Kafin wani ɗan lokaci mutane sun fara kewaye shi suna yi masa tambayoyin da shi kansa bai san amsarsu ba, dakyar ya rarrashi jaririyar ta yi shiru. Yana niyyar shiga napep ɗinsa ya tafi, mutanen wajen suka ce babu inda zai je sai ya faɗa musu inda ya samo wannan jaririyar.
Zuciyar Malam Hassan ta hau bugawa da ƙarfi, nan take zufa ta fara kwaranyo masa yana sharewa, duk bayanin da ya yi wa mutanen wajen da rantsuwar da yake yi musu amma sun ƙi yarda da shi sun kasa fahimtarsa, har wasu fusatattu daga cikinsu sun fara surfa masa zagi suna yi masa barazanar duka idan bai faɗa musu inda ya samo wannan jaririyar ba..
Ana cikin haka sai ga motar ƴan'sanda ta iso wajen, nan take suka saka Malam Hassan a mota, wani daga cikin ƴan'sandan ya tuƙo napep ɗin suka nufi division ɗinsu da shi..
HUSSAIN YUSUF✍️