FreeArewaPen original
ALLURA TA TONO GARMA
- 1views
- 15chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Alƙalami ya fi takobi🖊️📝
Sample · CHAPTER 1
ALLURA TA TONO GARMA 1A cikin birnin Kano akwai wani magidanci mai suna Malam Hassan. Yana zaune a unguwar Badawa, sana'arsa ita ce tuƙa adaidaita-sahu (napep) da wannan sana'ar tasa yake kula da iyalinsa ko kaɗan bai bar su cikin wahala ba. Matarsa ta farko sunanta Asabe. Asabe masifaffiyar mata ce, marar mutunci, hatta mutanen unguwarsu tsoronta suke saboda bala'inta. Ko kai waye idan ka taɓo ta sai ta ƙare maka wankin babban bargo, ba ta ragawa kowa ba a gida da waje, hatta mijinta Malam Hassan ɗin yana matuƙar shakkarta. Ƴaƴanta biyar uku mata biyu maza. A duniya babu abin da take so sama da waɗannan ƴaƴan nata, a kansu an sha yin dambe da ita a cikin unguwa, ga shi ƴaƴan nata Allah Ya yi musu shegiyar tsokana, ga rashin kunƴa. Ko a makaranta ba sa ragawa kowa, idan suka yi laifi malami ya dake su, har makarantar take zuwa ta zage malamin tatas. A kansu an sha kai ta police sta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.