CHAPTER 5
ALLURA TA TONO GARMA 5
Malam Hassan ya ɗago kansa ya kalli Asabe cike da mamakin ƙaryar da ta ƙera yanzu a kansa. Ya jinjina kai ya ce, "Asabe Allah Ya shirye ki, ban taɓa tunanin za ki iya jifana da irin wannan mummunan ƙazafin ba, amma ba komai Allah yana nan."
Nan ya dubi abokinsa Malam Nura ya yi masa duk bayanin yadda aka yi ya samo jaririyar, ya ƙare da cewa, "Wallahi ko a yanzu sai na kira maka DPO a waya domin ka ji gaskiyar lamarin. Tun da nake a rayuwata ban taɓa aikata zina ba, hasalima babu abin da na fi tsana kamar ta, amma yanzu Asabe ni ta ke jifa da wannan mummunan ƙazafin?" Ya ƙarashe maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka..
Cikin ɓacin rai Malam Nura ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Ka yi haƙuri abokina." Ya dubi Asabe ya ɗaure fuska ya ce, "Yanzu abin da ki ka yi kin kyauta? Na tabbata duk abin da ki ka faɗa min ƙarya ki ke yi. Asabe ki ji tsoron Allah ki daina wannan abin da ki ke yi wallahi sam bai dace ba.."
Ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe tana magana ƙasa-ƙasa, tana cewa "Wallahi ko sama da ƙasa za su haɗe wannan jaririyar ba ta isa ta kwana a cikin gidan nan ba, ba a isa a yi min daɗin baki a cuce ni ba. Ko ka ɗauke ta ka san yadda ka yi da ita, ko kuma na kashe ta cikin daren nan.." Tana faɗin haka ta tashi da sauri ta shige cikin ɗakinta.
Malam Hassan da Malam Nura suka bi ta da kallon mamaki, cikin tsantsar ɓacin rai Malam Hassan ya ce, "Don Allah kar ki fasa kashe ta, kuma sai ta kwana a gidan nan. Ban ga uban da ya isa ya hana ta kwana ba, ni da ke mu zuba mu gani..." Da sauri Malam Nura ya kwaɓe shi ya ce, "Haba Malam Hassan bai kamata ka rinƙaa biye mata ba, ka rabu da ita idan ta kashe ta, ita ma babu abin da zai hana a kashe ta, tun da dai rai bai fi rai ba.."
Bai gama rufe bakinsa ba sai ga Hauwa'u ta yi sallama cikin gidan, da sauri Malam Hassan ya ɗago ya kalle ta. Sai a wannan lokacin ma ya lura ba ta gidan, saboda kansa ya riga ya kulle gaba ɗaya, da kyar ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ya ce "Sannu da zuwa," ta amsa cikin kulawa.
Ta durƙusa har ƙasa ta gai da Malam Nura sannan ta ƙurawa jaririyar da take bacci a kan cinyar Malam Hassan ido fuskarta ɗauke da alamun mamaki. Da Malam Nura ya lura da ita sai ya ce da ita ta zauna ya yi mata bayani. Bayan ta zauna Malam Nura ya yi mata bayanin komai, har masifar da Asabe ta tayar da zargin da take yi wa Malam Hassan sai da ya faɗa mata.
Cikin tausayawa Hauwa'u ta karɓi jaririyar daga hannun Malam Hassan ta ƙura mata ido tana murmushi. Nan take Malam Hassan ya ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarsa, kafin ya yi magana Hauwa'u ta riga shi da faɗin, "Malam ka yi haƙuri saboda na daɗe, na tarar da jikin yayar ne babu daɗi sam, sai da muka koma asibiti muka yini a can sai bayan sallar Isha muka dawo gida. Amma yanzu Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi.."
Malam Hassan ya ce, "Ayya! Allah ya ƙara sauƙi, in sha Allahu gobe idan na fita zan biya gidan na yi mata sannu." Hauwa'u ta ce da Malam Hassan za ta riƙe jaririyar a hannunta ta kula da ita, har zuwa lokacin da za a ga mahaifiyarta, idan ma ba a gan ta ba, za ta riƙe ta tsakani da Allah tamkar ƴar da ta tsugunna ta haifa.." Nan fa Malam Hassan da Malam Nura suka rinƙa zuba mata addu'a da godiya.
A cikin daren sai da Malam Hassan ya je ya nemo madarar da ake bai wa jarirai kafin safiya su je asibiti a ba su shawarwari...
Washe gari da sassafe Malam Hassan ya ɗauki Hauwa'u suka nufi asibiti domin a duba lafiyar jaririyar. Suna fita Asabe ita ma ta fita daga gidan ta nufi gidan maƙwabtansu, inda wata ƙawarta take mai suna Rabi.
A zaune ta tarar da ita tana dama koko, sai da ta jira ta ta gama ta rabawa yara, sannan suka shiga ɗaki, nan fa Asabe ta faɗawa Rabi duk abin da ya faru a daren jiya. Nan take ran Rabi ya ɓaci sosai saboda an taɓo ƙawarta, Asabe ta ce, "Rabi zuwa wajenki na yi ki taimaka min da shawara me yakamata na yi a kan wannaan al'amarin wallahi kaina ya kulle, yanzu haka ma ya ɗauke ta sun tafi asibiti a dubo lafiyar jaririyar. Ni babban tashin hankalina ma ko yaran da muka haifa tare da shi, bai taɓa ba su kulawa kamar yadda yake bai wa wannan tsintacciyar shegiyar jaririyar ba.."
Rabi ta ɗan jima tana tunani cikin shiru, daga bisani ta dubi Asabe ta yi mata raɗa a kunne, suka fashe da dariya suka tafa. Asabe ta ce, "In sun san wata ai ba su san wata ba".
Asabe ta yi wa Rabi godiya ta fito ta wuce cikin gidanta da sauri, saboda tana tsoron Malam Hassan zai iya dawowa a kowane lokaci don ba ta son ya san ta fita..
HUSSAIN YUSUF✍️