馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
page 64
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION馃摎
BOOK 1:CHAPTER 127-128
___________________________Bayan tafiyar Hajiya Mama ta zaunar da Hauwa ta ce"ina san ki bani labarin zaman auren ki tun daga farko har karshe,ban yarda ki boye min komi ba,kin ji na gaya miki",ta fada tare da jan kunnen ta.
Zaro ido Hauwa ta yi tana tunanin abinda za ta ce.
Murya a kausashe Mama ta ce"wlh zan ci mutuncin ki,ina wasa da ke ne?,ba magana nake miki ba?".
Girgiza mata kai ta yi hawaye na zuba daga idan ta,bayan hannun ta tasa ta share hawayen sannan ta fara bata labari tun daga ranar da aka kai ta gidan har zuwa dukan da ya mata na karshe.
Duk iya juriyar Mama na ganin ta tsayar da hawayen idan ta sai da abin ya citura,sosai ta yi kuka domin abin ya taba ta,bata taba tunanin abin ya kai har haka ba,murya na rawa Mama ta ce"mai yasa kika rufe ni Hawa'u?,mai yasa baki gaya min ba tun far"..........kuka ne ya kufcewa Mama.
Tashi Ummi ta yi ta bar dakin,dan idan ta cigaba da zama Allah dai ya san abin da zai faru.
Da rarrafe Hauwa ta karaso gaban Mama ta hade hannayen ta tana kuka ta ce"ki yi hakuri Mama,na san na yi laifi,ban yi hakan dan na rufe ki ba,na ki gaya miki ne kawai sabida ban san hankalin ki ya tashi,kuma na yi hakuri ne dan a tunani na wata rana sai labari,kuma ke kika hore ni da yin hakuri,ke kika ce nayi hakuri a gidan mijina,na rike sirrin shi duk rint"..............kuka ne ya ci karfin ta.
Dago ta Mama ta yi ta rungume ta tana lallashin ta,sun dau tsawon lokaci a haka,da kyar Mama ta samu ta tsayar da hawayen idan ta sannan ta dago Hauwa ta ce"shikenan Allah yasa hakan shi ya fi zama Allhairi,Allah kuma ya saka miki chutar daya miki,ki yi hakuri,Allah na tare da masu hakuri,tashi muje ki watsa ruwa".
Mikewa Hauwa ta yi ta fara cire rigar ta,rintse ido Mama ta yi sakamakon ganin shaidan duka duk a jikin ta,shanye hawayen dake kokarin zubo mata ta yi ta fice daga dakin.
Bayan kwana biyu da dawowar ta gida ta kira Maman Fauzan,ba karamin farin ciki Maman Fauzan ta yi ba jin Hauwa ce,har kuka sai da ta yi,murya na rawa ta ce"ina kika shige Hauwa?,mai ke faruwa?,mai yasa kika bar gidan ki?".
Murmushi Hauwa ta yi ta ce"abinda aka saba ne Anty,ke kin san komai i,kar ki damu zan baki labari da zaran na dawo".
Girgiza kai kawai ta yi ta kasa amsawa,da haka su kayi sallama.
Ummi dake tsaye a bayan ta ta ce"ina za ki koma?".
Juyowa Hauwa ta yi a tsorace dan bata yi tunanin da mutun a dakin ba,a dan daburce ta ce"gidan mijina mana",ta karasa tana turo baki.
Dariyar shakiyanci Ummi ta yi tana tafa hannu ta ce"wani mijin,ko kin kuma aure ne ban sani ba".
Gyra zama Hauwa ta yi tana kallan ta da alamun mamaki,chan kuma ta ce"ban gane mai kike nufi ba?,Abban Ameen ne baki sani bahh?,ko kuma kin manta shi ne".
Gyra tsayuwa Ummi ta yi ta ce"au na manta fahhh!ashe ban gaya miki ba,yanzun ba ki da aure".
A rikice Ummi ta mike ta ce"whatttttt!",dafe bango ta yi sakamakon jirin dake kokarin kwashe ta.
Dariya Ummi ta yi ta ce"kina tantama ne,gaskiyar magana kenan,tun wuri idan kin san da burbushin son shi a zuciyar ki gwara ki yi saurin cire shi,dan wlh idan har ina raye baza ki taba komawa gidan shi ba,kin dai ji na rantse,sabida haka zabi ya rage ga mai shiga rijiya",ta karasa maganar ta tare da ficewa daga dakin,tana jin kukan Hauwa amman ta yi biris da ita.
Tayi kuka har ta gode Allah,idan ta ya kumbura ya yi sintim kamar wacce ta yi kwana biyu tana kuka.
Lalabo wayar ta ta yi ta shiga kiran number Sani.
Zaune Sani yake a Shago hannun shi rike da waya yana game kiran ta ya shigo,har kiran ya kaste bai daga ba,yana katsewa ta kuma Kira,zubawa wayar ido ya yi har ya karaci ringing din shi,wayar na hannun shi ta mai miss call goma amman bai daga ba,ganin ba ta da niyyar daina kiran shi yasa shi saka number ta a black list.
Kuka Hauwa ta fashe da shi ganin ya ki daga kiran ta,tana kuka ta ce"na hakura da kai har abada ko da ace hakan zai zama ajalina,ka chutar da ni Abban Ameeen,na so ka kaman raina amman da haka za ka saka min,nagode nagode ubangiji Allah ya saka min",haka ta yi ta kuka har barci ya kwashe ta a kasa.
Tun daga wannan ranar Hauwa ta maiyar da kuka abincin ta,ba ta da walwala,ko fita bata yi,idan ka ganta a waje toh fitsari za ta yi ko alwala da wanka.
Da farko Mama ta zuba mata ido taga iya gudun ruwan ta,ganin da gaske take ba bari za ta yi ba yasa ta jawo ta jikin ta ta kwatar mata da hankali tare da bata labari da dama,sannan a karshe ta ce"ko ta halin kaka ne sai auren nan ya rabu,aure rai ne da shi,iya adadin shekarun da Allah ya dibar miki kenan,ko da ace baku rabu ba toh tabbas sai daya ya tafi ya bar daya,sabida haka ina san ki kwantar da hankalin ki dan Allah,damuwar ki na saka ni cikin damuwa,dan Allah ki bari,baki san abinda Allah ya shirya miki ba,na tabbata da kin sani da ke da kanki za ki naimi saki".
Tana share hawayen dake ta anbaliya a fuskar ta ta ce"Mama ina san shi,ban san yanda zan cire shi a zuciya ta ba".
Murmushi Mama ta yi ta ce"babu abinda zai gagari Allah,ki fauwalawa Allah komi,ina mai tabbatar miki da cewa za kiga chanji,Allah ya miki Albarka ya musanya miki shi da mafificin Alkairi".
Da Ameen ta amsa tana kuka.
Rungume ta Mama ta yi tana lallashin ta.
Bayan kwana biyu Hauwa ta kira Maman Fauzan ta sanar da ita, Maman Fauzan na hawaye ta ce"Allah yasa hakan shi ya fi zama Allhairi,dauke hawayen dake idan ta ta yi ta ce"zanyi missing din ki Hauwa",kukan da take kokarin danewa ne ya kufce mata.
Sai da suka dan taba kuka sannan suka yi shiru.
Hauwa na jan hanci ta ce"zan dinga kawo miki ziyara Anty insha Allah".
Murmushi Maman Fauzan ta yi ta ce"babu komi,ki ba ni address,zanzo jibi insha Allah".
Kaman yanda ta fada hakan ta kasance,tun karfe goma na safe ta zo,ba ita ta bar gidan ba sai biyar na yamma,suna kuka suka rabu.
Bayan tafiyar ta Mama ta ce"da alamu halin ku daya,shi yasa taku ta zo daya,shegen kuka a cikin ku kaman dan shi aka aiko ku duniya".
Dariya Hauwa ta fashe da shi har tana kokarin tsarkewa.
Zaune su ke a parlor bayan sallar Isha'i suna hira yaro ya shigo ya ce"wai ana sallama da Ummi inji wani a waje",yana gama magana ya fice ba tare da ya jira amsar su ba.
Hade rai Ummi ta yi ta turo baki ta ce"ni fa ban gayyaci kowa ba,sabida haka ba inda zani".
Wani mugun kallo Mama ta aika mata da shi ta ce"idan kin isa kar ki tashi".
Turo baki ta yi ta ce"Mama kin ga fa na rike Ameen kuma barci yake ban san ya tashi,Hauwa ta je".
Juyawa Mama ta fara yi tana naiman abinda za ta dauka ta kwada mata.
Da sauri Ummi ta mike har tana naiman faduwa ta fice daga dakin.
Da kunkuni ta fice daga gidan,jingina ta yi da bango ta gaishe shi ciki-ciki,jin muryar da ya amsa mata ne yasa ta dagowa da sauri da alamun mamaki.
Daga mata gira ya yi ya ce"kina mamaki ne?".
Shiru ta yi ba tare data amsa mishi ba.
Murmushi ya yi ya ce"ya Mamana da Hajiya ta da mai jiki?,fatan duk na same ku lafiya",da Alhamdulillah kawai ta amsa mishi.
Murmushi ya yi ya ce"dama nazo gaishe ku ne,ki gaishe min da kowa"ya fada tare da bude motar shi ya kwaso laidodin dake ciki yana mika mata.
Kin amsa ta yi ta ce"a'a ka barshi mun gode".
Dariya ya yi ya ce"baki isa ba,dole ki amsa ko kuma ki matsa na shiga da shi ciki".
Tsayawa ta yi a bakin kofa ta tare bakin kofar ta ce"sai naga inda za ka bi i".
Dariya ya yi har da kyakyatawa ya ce"abu mai sauki,tsaf zan dauke ki na ajiye ki gefe wlh".
Jin abin da ya ce"yasa ta saurin matsawa gefe tana turo baki ta ce"Mama fa ba ta so,zata min fada".
Babu wani fa蓷a,kice mata dan ta ne,baza ta miki fada ba.
Girgiza kai kawai ta yi ta amsa su kayi sallama,har ta juya zata tafi ta ji ya ce"Ummiiiiiii".
Tsayawa ta yi chak sannan ta juyo a hankali ta zuba mishi lulu eyes din ta.
Murya a tausahe ya ce"dan Allah idan kin shiga ciki ki kira ni kin jiiii!".
Girgiza kai kawai ta yi ba tare data amsa mai ba.
Ki yi hakuri na san kin gaji da ni,sannu kin ji gimbiya ta.
Dukar da kanta ta yi tana murmushi ta ce"zan kira insha Allah".
"Toh nagode,was the for last digit".
Fada mishi ta yi kanta a kasa.
Murmushi ya yi ya ce"mu kwana lafiya,ki gaishe min da Mamana".
Sakanni sun shude,mintina sun shude,awanni sun shude,ranaku sun sude,watani sun shude.
Shakuwa mai karfi ya shiga tsakanin Ummi da Dr.
Zaune su ke a parlor suna hira Mama ta ce"ba kida mutunci Kulu,yanzu baza kije ki duba Mamin ki ba".
Tagumi Hauwa ta yi ta ce"wlh Mama zanje,bari mu shirya gobe mu tafi".
Toh shikenan Allah ya kaimu rai da lafiya.
Washe gari goman safe ta yi musu a gidan Mami,sosai Mama ta yi farin ciki da zuwan su,tunda Affan ya ga Hauwa ya makale mata,duk inda ta saka kafa shima sai ya sa,haka suka zame mata bindi shi da Ameeen.
Suna cikin hira Mami ta ce"daughter kin manta da ni,ko kira na baki yi,toh ya mai gidan na ki?".
Tun kafin ta bude baki Ummi ta yi karaf ta ce"wani mai gidan Mami?".
Bige mata baki Hauwa ta yi ta ce"ban san munafurci,sunan ki ne Hauwa".
Dariya Ummi ta yi ta bar wurin ta koma bayan kujera ta ce"wlh auren ta ya mutu Mami,wata biyar kenan".
Mikewa Hauwa ta yi ta fara bin ta suna zagaye parlor idan ta cike da hawaye,ganin ta kasa kamata yasa ta durkusawa a wurin tana rusar kuka.
Dai-dai nan Jalal ya shigo hannun shi rike da jaka,turus ya ja ya tsaya yana kallan ta da mamaki,murya kasa-kasa ya ce"har yanzun bata girma ba Allah ya shirya",saurin kawar da tunanin yayi da ya tuna cewa matar aure ce".
Hade rai yayi ya karasa cikin parlor ya gaida Mami.
Hauwa na jin muryar shi ta yi dif kaman an dauke wuta.
Ba tare daya jira gaisuwar ta ba ya nufi dakin shi yaran na biye da shi suna ihun oyoyo Daddy...............................................
By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.