Page 32
KARAGAR MULKI
*YOTA*
By (*Cwt-sumiey*)
Page 32
Tamkar mahaukaci sabon kamu haka Yarima Haisam ya rik`a yawo ya na bin duk wata d`iya Mace da ya ci karo da ita a hanya,idan kin rufe fuskar ki sai ya d`aga ya ga wace ce,wurare da dama ya sha mari dan wata da ya d`aga ma ta fuskarta za ta tsinke sa da Mari ,wasu su bisa da bugu har sai ya ruga amma duk da haka bai saduda ba haka ya nace ya cigaba da bin duk wad`anda ya gani a hanya,da k`yar da ji`bin goshi ya samu ya fara hango su,jikin shi ne ya bashi tabbacin su ne dan haka ya cigaba da bibiyarsu duk inda su ka shiga,ba tare da sun sa ni ba.
"Ranki ya dad`e kin lura da wani abu kuwa ?"," Wani abu kuma mene ne ?".
"Ki waiga ki ga ni mana",ta k`are maganar tamkar zata fashe da kuka,waige-waige Gimbiya Junainah ta fara yi amma ba ta ga komi ba, "Ni banga komi ba",ta bata amsa a tak`aice.
"Wani ne fa tun a mashayarnan da gobara ta kama ya ke bin bayanmu","Mutum kuma ,in ce dai ba Dakaren Masarautar BAIBAH ba ne ba ko?".
"A'a ba daga can ya ke ba,don banga alamar haka ba, sai dai naga gabad`aya ya yi zubin mahaukata tsoro na ke ji kar ya zo har inda mu ke yai niyar ya aikata mana wani abun".
"Ke dallah rabu da shi,kin cika tsoro ne shiyasa amma ba abinda zai yi mana sai ka ce mu kad`ai ne a wurin ba ki ga ga mutanenan da ke wurin su na da yawa ba,kowa sai harkokin gabansa ya ke,to ta ya ma za ai ya ce ya san ko su waye ke tafiya alhalin fuskokinmu duk a rufe su ke ".
" A'a kin manta dai d`azu sau biyu fa a cikin mashaya ki na bud`e fuskar ki ko kin man ta ne mai yiwuwa ko ya gane mu ne ta sanadiyar ki,ko kuma su Sarauniya Junayyah sun sa gwagwa`bar kyauta ga duk wanda ya ganmu shi yasa ya ke bibiyar mu ba".
"Ji wani mugun fata anya Kuyanga Jazila kina son mu tsira da rayuwar mu kuwa a cikin wannan Garin,sai mugun baki ki ke k`ok`arin yi ma na ?".
"Ba haka ba ne Gimbiya Junainah lamarin ne ya zo min a bai-bai, ba tare da nayi zato ko tsammani zai kasance a haka ba".
Sai da Gimbiya Junainah ta janyota jikinta ka na ta ce da ita"Ki yi hak`uri' in sha Allah ba abinda zai same ki zan tsaya ma ki da iyakar iyawata,Komi runtsi ina tare da ke bazan manta alkairinki gare ni ba".
Cikin sanyi jiki Kuyanga Jazila ta ce ,"To Allah ya sa amma wallahi dagaske ni duk a tsorace na ke,ban ga dalilin da zai sa mu zo irin wannan gurin ba nan d`in tamkar kasuwace ko kuma in ce madaddalar karuwai ce ko ?".
A d`an zafafe Gimbiya Junainah ta waigo ta ce da ita ,"Dan Allah in kin gaji ko kin sare ki tafi abun ki ban hana ki ba,ba dole akan ki,in dai game da wannan tafiyar ne,ba na da niyar cuta mi ki ko kad`an,"...." Ki gafarce ni ya Shugabata ba haka na ke nufi ba,Ganin wannan mutumin ne ya sa duk na sake fad`awa cikin firgici ",Kuyanga ta ce da Gimbiya Junainah ta na mai katseta.
" Indai shine matsalar ki bari in yi maganinsa yanzu ",A hankali su ka koma tafiya shima Yarima Haisam sai ya rage saurin da ya ke,in su ka cigaba da tafiya shima sai ya cigaba, in sun tsaya shima ya tsaya ,rasa MENE NE ABINYI Gimbiya Junainah tai sai ta yi yunk`urin nufo inda ya ke sai ta fasa sakamakon ganin yawa ko tarin mutanen da su ke a wurin ,gani ta ke kamar zai tona ma su asiri a gane su d`in ko su waye.
Duk da dai fuskokinsu a rufe su ke,bayanda za ka iya gane su,ko da ko kasansu zai ma ka wahala ka gane su,ka sa rik`e kanta tai har sai da ta nufe shi,da sauri Kuyanga Jazila ta rik`o hannunta ta ce," A'a kar ki je","Sabo da me ?",ta mai do mata da tambayar kai tsaye.
"Saboda ina tsoran kar da ya cutar da ke ko kuma ya gane ko ke wace ce hakan babban had`ari ne a gare mu a wannan lokacin".
"Na san da haka kuma cigaba da tafiya ya na bin bayanmu shima wani had`ari ne,idan mutane su ka fahimci hakan dole su tsaida mu mai yiwuwa ma su gane ko mu su waye".
"Oh ya Allah wannan shine ana dara ga dare ya yi,na yarda zamu tunkaresa amma ni zan yi ma sa magana ba ke ba","Ba damuwa na yarda muje".
Ba k`aramin bugawa k`irjin Yarima Sadauki yai ba da yaga sun nufo inda ya ke duk da zuciyar Kuyanga Jazila sai faman bugawa da sauri da sauri ta ke dannanewa kawai ta ke na nufar wurin,ita kawai ta san yanda ta ke ji,duk da kallon mahaukaci da ta ke ma sa bai sa ta daina tunani ko ya na da `boyayyar manufa a kan su ba da k`yar ta iya cewa da shi," Lafiya me ya ke faruwa na ga sai faman bin mu ka ke ko ka bamu ajiyar wani abu ne?".
Duru-duru Yarima Haisam ya fara yi zuciyarsa sai faman kad`uwa ta ke,gami da cewa"Wace ce wannan, ya akai haka ta kasance, me ya ke shirin faruwa haka hatta da irin tsayuwarsu iri d`aya ce",wannan zancen zuci ne da ya ke a cikin zuciyar Yarima Haisam, zuciyarsa sai kai komo ta ke bugun numfashinsa ya k`aru ji ya ke ina ma da zai iya ya ye hijabin da ya shiga tsakanin su ya samu tabbacin Umman shi ce a tsaye a gabansa,da k`yar ya iya fusgo numfashi har ya samu zarafin da ya ce da ita,"K..KKK.kkk...ki ...ki yi hak`uri Ummata na ke nema na ga giftawarta yanzu a can shine na biyo bayan ta",
" Oh Ummanka ?,to anan da akwai wacce ta yi maka kama da tsohuwa ne da za ka rik`a bin bayan mu kome ,ko dai ka na tafe da wani mugun shiri ne akan mu ?".....
Da sauri ya katseta ya na cewa"A'a a'a ba haka ba ne ,zan yi tafiya ta ma,amma dan Allah kafin lokacin ki ce da wannan `yar'uwar ta ki da ta ya ye hijabin da ta shiga tsakaninmu da ita, ta kuma zama katanga a gare ni, ,da zaran na tabbatar da ba Ummata ba ce zan yi tafiya ta,duk da dai jikina na fad`a min Ummata ce tsaye a gabana ".....
" Ka ga Dallah Malam dakata k`aton saurayin god`ai-god`ai da kai za ka kalli tsabar idonmu ka ce wai akwai Ummanka a cikinmu to a taya haka za ta kasance sai ka ce muna a Garin ga`ba-ga`ba, ko ka ta`ba ganin inda rak`uma ta haifi d`an tsako ne ko kuma ince d`an tsako ya haifi rak`uma ?"
"A'a ban ta`ba ganin haka ta faru ba,duk da dai ni ba na cikin natsuwar rai da zuciyar da zan fahimci duk wasu tarin zantuttuka na ki,yare d`aya na ke ji da gani shine yaren Mahaifiyata,da za ki yi min adalci,ki kuma tausaya min da kin yaye hijabin da ke saman fuskarkarta ko ki sa ta ya ye ,idan har ba ita ce wacce na biyo ba kai tsaye zan yi tafiyata ba tare da na sa ke bin ku ba".
"Hmmmm na gano ka yanzu to ank`i sai ka ja tsunmokaran k`afafunka ka yi gaba,sannan sai ka je ka ce da wanda ya turo ka mun ci dubu sai ceto,kuma kasanar da shi bai iya takunsa ba tunda farko da ya turo mahaukaci a matsayin wanda zai nasa Hilla ya samu abinda ya ke so kana iya tafiya amma ina mai gargad`arka da kar ka sa ke bin mu in ba haka ba sai na tara ma ka mutane ince kai `barawo ne, kuma mai satar mutanen ".
Duk wannan Batu Kuyanga Jazila na yinsa ne bisa dakiyar zuciya ba wai don ta shiryama faruwar hakan ba,sai da Yarima Sadauki ya matso dab da Kuyanga Jazila ka na ya ce da ita," Kar ki fasa a shirye na ke da in sadaukar da numfashi na na k`arshe in har zan sa ke d`ora idanuna a kanta kai ko da ko a mafarki ne na aminta kuma na shirya ma hakan,ke ban k`i kowa na cikin duniyarnan ya mutu ko ya illata ba muddin zan sa ke ganinta ko a mace ko a raye,ke ko da a matsayin mafi muni zan ganta na amince da hakan,ki tara duk iya adadin mutanen da za ki tara, madamar za ki bari na ga fuskarta".
Ba Kuyanga Jazila ba hatta da Gimbiya Junainah sai da ta firgita da jin maganganun da su ka fito daga bakinsa,da sauri Kuyanga Jazila ta kama hannunta ta na ja baya kafin ka ce me sun fara yunk`urin guduwa daga wurin sai dai ina ko taku biyu lafiyayyun ba su ba Dakarun Masarautar BAIBAH su ka fara `bullowa ta kowacce kusurwa da ke cikin kasuwar kafin k`iftawar Ido sun zagaye su,sun yi masu zobe,sun sa ka su a tsakiya Yarima Sadauki na daga can gefe su kuma su na tsakiya,k`ank`ame juna su kai a tare ,duk abinda ya zo bakin Kuyanga Jazila na addua'ah fad`i ta ke in har ta na saran zai zama sanadin da za su sami salama daga ukubar da ke tunkaro su,da sauri d`aya daga cikin Dakarun ya nufo su ya na mai sa hannu ya ya ye hijabin da su ka rufe fuskokinsu da shi.
Ba k`aramin kad`uwa gami da shiga firgici Yarima Sadauki ya shiga ba,jikinsa tuni ya fara rawa ji ya ke inama da zai iya daka tsalle ya ganshi gurfane a gabanta,ya rungumeta ya ji ta a cikin dukkanin sassan jikinsa,ina ma da hakan za ta faru,ina ma da za ta shafa kan shi kuma sannan ta ambace shi da sunan da ta ke kiran shi da shi ita kad`ai,ina ma dai,ina ma dai .......wata irin girgiza yai wacce tai saurin fargar da shi halin da a ke ciki,tuni wad`annan Dakarun sun ta fi da su Gimbiya Junainah, sai faman Waigowa ta ke ta na mik`o ma sa hannu alamun ya ce-ceta kar da ya bari a tafi da ita.
Da wani irin k`arfi da saurin da bai ta`bazato ko tunanin ya na da shi ba haka ya Isa wurin bugu d`aya yai ma wanda ya ke rik`e da ita sai ga shi a k`asa wanwar ba ko numfashi a jikinsa ,bai barsa haka ba sai da ya sake taka shi da k`afa,ya na mai sanya hannu ya mai do da Gimbiya Junainah bayansa da sauri Kuyanga Jazila ta kwace daga hannun wanda ya ke rik`e da ita ta rugo bayansa su ka `boye ita Gimbiya Junainah .
Cikin hargagi da amo mai sauti ya ce,"Kun san ita d`in wace ce da har ku ke da zarrar gami da yunk`urin d`ora hannu akanta,to ba shakka duk wanda ke son ta`bata ya shirya kwanan barzahu domin na rantse ma ku da Allahn da na ke bautawa sai dai uwarsa ta haifi fi wani".
Ya idasa zancen cikin d`aga murya ba tare da ya tsaya ko ya ba wani damar cewa wani abu ba ya cigaba da cewa,"Waye ya ke son ya maida matarsa bazawara,waye ya shirya mai she da `ya`yan sa marayu,waye a cikin ku ya ke son ya sanya gyatumarsa zubar hawayen,waye ya shirya mutuwa ba tare da ciwo ko jinya ba,waye ya shirya tarar aradu da ka,waye ya ke jin duniya ta ishe shi,waye ya ke buk`atar ya ja numfashinsa na k`arshe anan guri?,ya taho ga abokin tafiya na shirya na shirya!!!!!",ya k`are zancen ya na mai buga k`afarsa a k`asa tare da sanya hannayen sa ya tattare gashin da ya zubo ma sa a saman fuska har ya na rufe duka fuskar ta sa,a k`eyarsa ya tattare shi ya k`ulle wanda hakan ya bayyanar da fuskar shi ta asali kai tsaye
Da sauri duk Dakarun su ka ja baya.
"Kusan ko ita wace ce ,ita d`in farinciki na ce,ita d`in rayuwata ce kuma bugun numfashina a da da na gan ku na sha ni ku ka zo farmaka Ashe ku d`in tarin lusarai ne da su ke nu na kwanji da k`arfin su ga Mata,to idan har iyayen ku mata sun haife ku a matsayin maza kufuskan ce ni kafin ku tafi da su".
Wani d`ayadaga cikin Dakarun ne yanufo shi sai faman kawa ya ke da niyar ya doke shi da kashin da ke hannunsa sai dai ina kwaf d`aya yai ma sa ya fad`i k`asa a matsayin gawa.
" A baya ba na da wani buri ko fata wanda ya wuce in sa ke sa ta a Ido ko da hakan na nufin silar fitar numfarfashina na k`arshe amma a yanzu ba na da buri ko fatan da ya wuce in bata kariya har k`arshen rayuwata,daga Rana irin ta yau na zama bawanta ni d`in hadimin ta ne!!",ya d`an tsaya,wanda hakan ya ba d`aya daga cikin Dakarun damar matsowa kusa da shugaban su ya yi ma sa rad`a sai da shugaban ya bayyanar da firgita da ya yi a fili sakamakon jin abinda a ka fad`a ma sa .
"Kuje ku ce ma wanda ya turo ku ya zo da kansa ku ce da shi ya yi sa ke haka kuma ya yi kuskure da har ya bari na shiga ciki rikicin, ku sa ke zuwa da ninki adadin da ku ke da shi inanan ba inda za ni zan jira ku,ku je ku fad`a masa".
Ai ko kamar jira su ke ya ba su umarni su ka ranta a na k'are ba tare da sun tsaya jiran wani abu ba.
Duk da irin halin da su Gimbiya Junainah su ke a ciki na rud`u firgici da rashin natsuwar rai bai hana Kuyanga Jazila matsowa saitin kunnen ta ta ce da ita "Kin san shi ne , na ji ya na ta magana kamar ya san ki ko kun ta`ba had`uwa da shi a wani wurin ne?".
Ko mi ba ta ce da ita ba sai rugawa tai inda Yarima Sadauki ya ke ta kama hannunsa ta ja da iyakacin k'arfin da ta ke da shi ta na mai cewa"..........