2
by @pherty001
Shiru yayi yana qara saurare daga harabar gidan tamkar hayaniya yake jiyowa, ya maida idanunsa ya lumshe tare da kai yatsun hannuwan sa biyu ya toshe kunnuwan sa saboda wani xafi da xuciyar sa dake masa baya son hayaniya ko kad'an.
Ya xiro fararen qafafuwansa qasa bayan ya sauka daga saman gadon, kai tsaye window ya nufa tare da yaye curtains d'in yana kallon qasa ta harabar gidan, mutane ya hango birjik harda iyayen sa, ya ja qaramin tsaki yana fad'in koma menene damuwar ku ce, ganin wani bafade yana qoqarin xuwa sashen sa da alama qofa xai buga masa ransa ya qara baci tunawa da gargadin da yayi wa jakadiya akan kada wani ya kuskura qara xuwa sashen sa domin a dame sa.
Sakin curtains d'in yayi tare da sauka stairs ya nufi babban falon sa dai dai lokacin da yaji ana buga qofar a hankali cikin nutsuwa, cikin tsananin bacin rai ya bud'e qofar amma ga mamakin sa Mahaifin Afiya ne tsaye tare da bafaden, ya yatsina fuska yana qare masu kallo batare da yayi magana ba dai dai lokacin umma ta qaraso da sauri tana fad'in yarima ka tabbata Afiya bata tare da kai.
Qara kallon su yayi ransa na qara baci kamar baxai yi magana ba sai kuma ya motsa labbansa a hankali wanda da kyar ne kajiyo abinda yake fad'a,
Yace nace bata nan menene?
Abba yace an neme ta an rasa a gidan nan baa ganta ba hassalima kayanta dana baby kad'an ne aka samu a sashen ta.
Aiman ya tabe bakin sa cikin halin ko in kula kafin ya juya xai rufe qofar falon sa, Abba yayi saurin tsaida sa yana fad'in,
Aiman baka ji abinda nake gayama bane an nemi Afiya an rasa a gidan nan.
And so.... Aiman ya katse sa cikin bacin rai, bayan sharrin zina da ake min kuma shine aka biyo ni a qaramin wani sharrin d'auke Afiya ko me? ya fad'a yana kallon iyayen nasa idanunsa jawur.
Umma tace are you shouting at him yarima? Shi abban mahaifin Afiya, meke damun kane, family issue kana nuna halin ko in kula akai sai kace ba matar ka da d'an ka ba.
Bai yi magana ba, ganin surutun nasu na qara sa masa ciwon kai juyawa yayi tare da maida qofar ya rufe, kallon juna suka yi lokaci daya kafin su girgixa kai su bar gurin.
Idan ta bata miye nashi, shi xaije neman tane or what, what makes her to run away? Mts yaja qaramin tsaki batare da ya damu ba.
Neman duniya anyi qasa da sama an nemi Afiya an rasa, sosai yan uwan nata suka shiga tashin hankali, meyasa Afiya xata yanke hukunci guduwa saboda laifin da yarima ya aikata, ina taje?duk basu sani ba.
Nan take aka soma sanarwa akan batan ta ga duk wanda ya ganta tabbas yana da tukwici mai tsoka a gurin president da sarki.
Duk wannan bidirin da ake aiman na kwance d'akin sa ya rasa yanda xaiyi da rayuwarsa game da nabila, bai taba sanin tashin hankali ko shiga damuwa ba sai dalilin Afiya da nabila, matan nan biyu baxai taba yafe masu ba baxai taba barin su ba, yanda suka sa xuciyar sa ta kasa samun nutsuwa suma sai sun rasa tasu nutsuwar xai hukunta su dai dai da laifin su, ana so dole ne, menene so kuma meyasa ake so, meyasa mutane suke ganin basa iya rayuwa sai da so? I will not love and I don't want to be loved, to hell with the both of you mtsew.
Washe gari ya gama shirin sa tsab na barin qasar dan baiga amfanin xaman sa anan ba.
Mai martaba na tare da waziri a fada lokacin da suka ji ana sanarwa shigowar yarima, fuskar nan tasa a daure tamkar bai taba dariya ba, ba da son ransa ba ya xauna ba walwala a fuskar sa yana gaida sarki.
Sarki ya amsa yana kallon sa cikin mamaki tun daga yanayin kayan dake jikinsa ya san aiman na son barin qasar ne, yace har yanxu banji kayi wata magana akan batan iyalin ka ba ni naga tamkar abin bai dame ka ba yarima.
Aiman ya yatsina fuska yana kallon sa tare da fad'in ni xan koma Phoenix yanxu.
Baka isa ba... ya xubawa mahaifin nasa idanu tamkar ya rusa ihu a wurin, waziri na ganin haka ya tashi sum sum ya fice daga fada.
Meyasa? Aiman ya tambaya yana kallon sa?
Ina ma maganar iyalan ka kana min mgnr barin qasar baka da hankali ne.
Yace amma ni miye nawa a batan nasu, da xata bar gidan ta nemi ixini na?
Cikin mamaki sarki ke kallon sa yace baka da ruwa a batan matar ka da jinjirin ka kenan, kai wane irin mutum ne yarima, kana so ka gayamin baka taba son Afiya ba tun xaman da kayi da ita.
Yarima ya gyad'a kansa cikin tabbatarwa, ni ban taba son wata mace ba, ban kuma taba jin xan so wata mace ba har yanxu, ka sanni ka san ko waye ni, kasan abinda xan iya da akasin sa amma meyasa ka yarda da wannan dabbar da abinda taxo maku dashi, meyasa ka yarda da ita fiye dani, guduwar Afiya ba laifina bane laifin kune ni ba wani laifi dana aikata da xaa nemi hukunta ni akan sa kuma xata je ta dawo ta same ni sai ta gayamin dalilinta na gudu na ni ban guje ta ba sai ita, me take dashi me take taqama dashi, ya tashi a fusace cikin bacin rai xai fice sarki yace na gayama ba inda xaka je, ya juyo yana kallon sa.
Gaskiya dad ni sai naje bana son xama a gidan nan bana son qasar gabaki d'aya.
Sarki ya bada umarni kada a kuskura abar aiman ya fita daga gidan hakan ba qaramin qona xuciyar sa yayi ba, ya juyo xai yi magana sarki ya nuna sa yana fad'in idan ya kuskura yayi magana anan fadar ku kama shi ku d'aure shi.
Yarima ya had'iye wasu yawu da kyar yana kallon mahaifin nasa ganin bacin rai sosai a tare dashi banda haka mai martaba bai taba cewa a kama shi balle a daure shi ba tabbas ba qaramin wulaqanci da xubar masa da girma yayi ba a gurin wad'annan qartin bayi dake tsare da shi, ya juya ya fice a fusace ya bar fada.
Yana xuwa sashen sa ya bada umarni duk wanda yaxo ko waye shi kada a barshi ya shigo.