4
by @pherty001
Dreams that you think are coming true turn into nightmares, ta gyara kwanciyar ta tare da rungumo sultan sosai a jikinta tana shaqar qamshin jikin sa. Ko da mafarki bata taba tunanin akwai ranar da xata rabu da aiman ba, kulawa da soyayyar da ya soma nuna mata kenan ba gaskiya bane, kenan mafarkin ta baxai taba cika ba na xama cikakkiyar matar yarima mai yanci, kenan aiman baxai taba son ta ba kamar yanda ya fada a baya, ni meyasa nake son sa, meyasa na damu da shi yaushe soyayyar sa tayi Mani wannan mugun kamun da har na kasa mantawa dashi a rayuwa ta har yanxu? I didn't know how to stop loving someone as dangerous, tainted and flawed as him, ya Allah ka taimake ni ka bani haquri da juriya na rashin wannan bawan na ka, ta rumtse idanuwan ta yayin da hawaye masu xafi suka soma xarya a fuskar ta. Tun da ya fito daga sashen yake tafiya da sauri da sauri sakamakon wani abu da yake ji a xuciyar sa da ya kasa gane ko menene, bacin rai ne ko baqin ciki bai sani ba, d'akin sa ya nufa ya soma cire kayan jikin sa, ya rage daga shi sai dogon wando na kayan sarauta dake jikin sa sai farar shimi, kallon kansa yake ta mirror fuskar sa tayi jawur, yana son sanin abinda yake da wanda maxa basu da shi da har mata suke rububinsa haka, shi suke so ko kud'in sa ko kuma sarauta har yau ya kasa gane hakan. Idanu ne basu da, ko baki, eyes or ears, mouth? Yake tambayar kansa yana kai qaramin yatsa akan lips d'in sa or pink lips, yayi shiru sakamakon jin motsi da yayi kamar a falon sa, cikin kakkausar murya ya soma magana yana fad'in waye ya shigo kuma da ixinin wa? Allah ya huci xuciyar d'an sarki, yallabai Bilal ne yake neman iso, yaji muryar bafaden sa ya fad'a. Mts yaja qaramin tsaki kamar baxai yi magana ba yace shikenan, da kyar mutumin yaji abinda ya fada kafin ya tashi jiki na rawa kamar yana ganin sa ya fice da sauri yana fad'in godiya nake ranka shi dad'e. Sallama bilal yayi ya shiga har cikin d'akin nasa, kallo daya yayi masa ya san akwai damuwa tare dashi, da kyar yace meke damun ka prince. Shiru aiman yayi yana kallon sa, batare da yayi magana ba ya juya ya xauna yana qara tsurawa fararen yatsun qafafuwan sa ido, meke damun shi, shi kansa bai sani ba ya dai san xuciyar sa ba dad'i. Sanin hali da miskilanci irin na aiman ya saka bilal ko kad'an bai damu da rashin kula sa da bai yi ba, shima ya xauna kusa da shi fans qara kallon kyakkyawar fuskar da tayi matuqar ja sosai kamar wanda aka daka, to waye xai daki Prince?ya tambayi kansa, ya kai hannun sa kan shoulder d'in aiman yana fad'in daga fada nake sarki yasa aka yi kirana... Wani kallo aiman yayi masa kafin da kyar ya bud'e baki yana tambayar meya faru kuma? Bilal yace sarki yayi min bayanin komai da ya faru kuma ya tambayeni gaskiya tsakanin ka da nabila, sanin kanka ne baxan iya masa qarya ba and I told him. Aiman ya tabe bakin sa tare da d'auke kansa gefe yana kallon wani gu, bilal ya cigaba da fad'in amma meyasa nabila xata yi haka, a tunanin ta wannan hanyar da tabi shi xai saka ta same ka kamar yanda take so, tayi kuskure ta batawa kanta lokaci da rayuwar ta dan matuqar sarki ya gane gaskiyar qarya take Ma baxai bar ta ba. Wait.... Aiman ya katse sa yana kallon sa wace gaskiya kake magana kana nufin kai ba gaskiya ka gayawa sarki ba da har bai yarda da kai ba? Bilal yace ina ji wannan case naku yau ya kai sati biyu da akayi shi har batan Afiya ka taba gayamin halin da kake ciki, wai ace matar ka ta bata amma ka kasa gayamin ina babban aminin ka...... Aiman ya sake katse sa a Karo na biyu yana yatsina fuska, just look ga abinda na tambaye ka ga abinda kake gayamin. Bilal ya tashi yana fad'in har akwai wani abu da kake son ji sama da wannan, gayamin akwai abinda ya kai Afiya muhimmanci a rayuwar ka? Aiman yayi masa wani kallo yana fad'in ashe kaima baka da hankali tunda kake tunanin Afiya tana da muhimmanci a rayuwa ta, akwai abu mai muhimmanci a rayuwa ta bayan wanda ka sani a baya? Kowa ya bud'e baki Afiya Afiya me Afiya take dashi wanda ni bani da, menene a gurin Afiya wanda ni babu a gurina, kyau, ilimi, kud'i, MULKI KO SARAUTA? Menene bani da aciki? Bilal yayi shiru yana kallon sa, kafin yace meyasa kowa baxai ce Afiya ba bayan ita d'in daban ce da kai, Afiya tana son ka tana son kasancewa da kai, Afiya tayi iya bakin qoqarin ta na ganin ta cusa soyayyar ta a xuciyar ka, ka gayamin abu guda da yarinyar ta kuskure ka dashi, ka gayamin aibun ta da baka son ta, idan baka so ta dan tana qanwar ka yar uwar ka ba ai xaka sota ko dan yaron da ta haifa ma, da gaske Prince baka taba son yaron ka ba baka taba jin son wannan jinin na ka ba, idan haka ne banga laifin ka dan kaqi son wani ba, banga laifin ka dan kaqi son Afiya ba tun da ka kasa son tsatson ka, ka kasa tunanin sa ko sau d'aya balle kayi tunanin sa, baka san soyayya d'a da mahaifi ba shine dalili. Aiman yayi shiru yana tunani, yes yaron sa tsatson sa idan bai so shi ya nuna masa gata ba waye xai so shi, idan bai bawa jinin sa soyayya da kulawa ba waye xai bashi, Karo na farko daya soma jin wani abu ya taba xuciyar sa game da yaron sa, ya dubi bilal a raunane yana fad'in, Ina xan sami yaron? Cikin takaici bilal ke kallon sa, sanin aiman baya son a nuna jin haushi kansa yasa ya sauya fuska yana fad'in hanyar da kabi ka sami yaron shi xaka bi ka neme shi, baka son yarinyar mutane taya kayi mata abinda ta haifa ma yaro, sha'awa tana xuwa ne a inda ake so... Enough... Aiman ya katse sa, bilal yaqi shiru bayan ya matsa kad'an daga kusa da shi yana fad'in I pray Allah ya d'ora Ma son Afiya fiye da yanda take son ka ko xaka san xafi da rad'ad'in so, ko xaka san ciwo da quncin so, ko xaka san love is strange but sometimes it can make you go crazy and it can burn or break you. Aiman yace amin, Allah ya karbi addu'ar ya samin son yarinyar ko kad'an ne domin na huta da fada da mita dana ke sha akan wannan yarinya, kayi min addu'a I want to love her small. Shiru kawai bilal yayi yana kallon sa, al'amarin aiman ya soma fin qarfin sa. Ya tashi yana fad'in muje naga waccan shegiyar.... *****