KARAGAR MULKI

Page 33

by @cwtsumiey19988

Page 33

....."Zo mu bar wurinnan tun kafin su dawo,za su illata ka,ba sa da imani ko tausayi ko kad'an",jan shi ta ke tamkar rak'umi da akala shi kuma sai faman bin ta ya ke zaro-zaro ba tare da ya dakatar da ita ba,hakin da ta fara yi ne ya sa ta sare gami da samun wuri ta tsaya ta na cewa.
     "Ka ga bazan iya ba,na sare ka bi wannan hanyar ka yi ta tafiya,kar ka tsaya ko ka waiwaya,ka yi duk iya yanda za kai ka tseratar da rayuwarka, kar ka damu da ni ,ba za su iya cutar da ni ba,ko su yi min abinda Allah bai nufa a gare ni ba",duk ta na wannan maganar ne ta na fidda haki alamun ta gajiya.
     Sai da ta kai k'arshen maganarta ta ta kula hankalinsa da tunaninsa ba ya kanta,duk'e ya ke gwuiwowinsa a k'asa ya kama gefan rigarsa ya na share ma ta k'urar da ta ke a saman k'afarta,sai da ya tabbatar da da babu sauran k'asar a jikin k'afar sannan ya d'ago ya na fuskantar ta ya ce da ita,"Ba zan iya ba,ba zan iya ko da k'ara taku d'aya ba matuk'ar ki na a cikin matsala ko kuma wani yanayi mara dad'i, ba zan huta ko in samu salamar ruhi ba,har sai na ga kin fita daga cikin k'angin da ki ke a ciki,Ni d'in tamkar bawa haka na ke a gare ki,zan rayu ko in mutu a saboda ke, ke ko da a kusa da Inuwar ki na ga wani a cikinsu sai na zama silar dakatar da Shak'ar numfashinsa,idan ba damuwa in tambaye ki ma na?".
Ba tare da ya tsaya ya ji wani abu daga bakinta ba ya ce,"Me ya sa za ki rik'a zuwa irin wannan wajen,shin ba ki san wani abun zai iya samun ki a wurin ba,ko ba ki tunanin muhimanci da rayuwar ki da ta ke da shi ne?,Rayuwar ki na d'anfare kuma lik'e a jikin ta wani,da zaran wani abu ya same ki shi kuma zai cutu,har ya kai ga ya rasa ta shi Rayuwar ki daure ki rik'a kulawa da kan ki domin in har wani abu ya same ki ba zan ta'ba iya yafewa Kai na ba,ke d'in "..........
Da sauri ta dakatar da shi da cewa," Waye kai,a ina ka sanni,wacce irin alak'ace tsakanina da kai,ko dai wani abun ka ke nema a guna?".
Marayan murmushin ya yi ka na ya ce,"Kar ki damu da wannan domin ba wani babban dalili ba ne ba".....ta katse shi.
"A'a a gare ka ne ba babban dalili ba amma ni ya na da muhimanci in san dalilin da ya sa ka ke k'ok'arin ko yunk'urin sarayantar da rayuwar ka a saboda ni,bayan ban sanka ba,ba ka sanni ba,babu wata alak'a ta kusa ko ta  nesa a tsakanin mu ".
Gwuiwowinsa ya zube a k'asa gami da had'a hannayensa wuri guda ya ce...." Ni bawan ki ne,hadimin ki,kuma mai ba ki kariya dakaren da zai iya ba ki kariya a koda yaushe komi runtsi da tsanani ke har d'an aiken ki za ki iya kira na da shi,wannan shine matsayina a fare ki,bayan haka kar ki kawo wani dalili da zai sa in bibiyi har zuwa nan".
"A'a ni ba haka na ke son ji daga gare ka ba,kai waye d'an wanne gari ne kai,kuma me ka zo yi a wannan Garin,me ya sa kasa rayuwarka a cikin hatsarin saboda ni?!!!! ,ta k'are zancen cikin k'araji
Cikin tausasa lafazi ya ce da ita,"Da gaske na ke mi ki ni ba kowa ba ne face sunayen da na lissafo ko na ambata ma ki, ki yarda da ni bayan haka ba ni da wata manufa a kan ki".
"To na ji kai ba kowa ba ne amma me ye ya sa ka shiga cikin wannan lamarin da ni kad'ai ya shafa ba ka tsoran ka cutu a saboda haka ?".
"To me ye abun damuwa in na rasa rai da rayuwata a sanadinki,ni ba kowan kowa ba ne ba don haka kar ki wani damu da hakan".
"Duk tarin tambayoyin da na ke ma ka har yanzu ba ka bani gamsasshiyar amsa ko d'aya ba,ka ba ni amsar wannan tambayar da zan yi ma ka ta k'arshe,wani abun zai d'arsu a zuciyata in har ba ka amsa min ita ba,Me ye ya kawo ka cikin k'asar BAIBAH domin kwata-kwata ba kai kama da d'an wannan k'asar ba,me ka zo yi a cikin ta ?".
"Zan amsa ma ki wannan tambayar amma sai in kin ba ni amsar tambayar da zan ma ki yanzu,Mene ne dalilin da ya sa wad'ancan mutanen su ke bin ki?,to a sannan zan ba ki amsar tambayar da ki kai min wannan shine kawai".....
Da wani irin sauri Kuyanga Jazila ta iso inda Gimbiya Junainah ta ke ta ja ta baya kad'an gami da fara yi ma ta rad'a a kunne,"Kar ki yarda ki amsa ma sa wannan tambayar domin aikata hakan babban kuskure ne, don haka ki san abinda za ki ce da shi amma ba gaskiya za ki fad'a ma sa ba,domin ni dai har yanzu ban yarda da shi ba".
Sai da Gimbiya Junainah ta d'an saita kanta sannan ta fuskance shi ta ce dashi,"Ba zan fad'a ma ka ba har sai ka fara amsa min tambayar da na yi ma ka,tunda ni ce na fara tambayarka ai".
"A'a kin tambaye ni abubuwa da dama kuma na amsa ma ki kamata yai ki sanar da ni abinda na tambaye ki a wannan lokacin".
"A'a ni ba zan iya sanar da kai ba domin ni kad'ai hakan ta shafa in kuma ba za ka iya sanar da ni ba sai ka je da tambayar ka nima in tafi da tawa".
"Hmmmm shikenan yanda ki ka ce haka za ai da zaran kin bani amsar tambayar da nai ma ki to na yi maki alk'awari sanar da ke abinda ki ka buk'ata a wurina".
Sai da Gimbiya Junainah ta nisa kana tace da shi,"Ka ga ba damuwa na gode da taimakon da ka yi min ba zan ta'ba iya mantawa da kai ba,zan sa ka a cikin kudun tarihin rayuwata na gode sosai da sosai"...."Am ki yi hak'uri na katse ki domin ban fahimci abinda ki ke nufi ba ?".
"Ina nufin ga hanyanan ka yi tafiyar ka kar ka sake ko da wasa ka zo cikin wannan k'asar, kai ko da a mafarki ka ga hakan ta kasance da ka farka ka yi gaggawa ka nemi yafiya sannan ka yi sadaka domin hakan ba alkairi ne a gare ka ba,kai da ma duk wani wanda ya shafe ka kuma ya ke da alak'a da kai".
"A'a dan Allah kar ki kore ni da gefe ko bigiren da ki ke rayuwa,ki bar ni in rayu da ke ko da a matsayi mafi k'ask'anci ne,amma dan Allah kar ki kore ni ina son ganin ga ni ga ke,ina son na kasance tare da ke a ko da yaushe,in k'are sauran rayuwata tare da ke".
"To fa me ka ke nufi da wannan dogon zance?, ina ce anyi ma ka godiya ko,to me yai saura ba sai ka kama gabanka ba ka yi tafiyar ka",cewar Kuyanga Jazila.
Tamkar zai zubda hawaye haka ya sake marairaice fuska da muryarsa ya na cewa,"A'a dan Allah kar ki d'auki shawara ko maganar da ta ke fad'a, zan cutu in zauce,wata k'ila in rasa hankalina ko in rasa rayuta in har ki ka ce da ni a'a, ko kin manta a ranar da mu ka yi had'uwata ta k'arshe da ke kin min alk'awarin za mu rayu da ke har sauran tsayin rayuwar da na ke da ita,har ki ka ce za ki biya bashin da ki ka d'auka a shekarun baya na tafiya da ki kai ki ka barni,ko duk kin manta da hakan ne ?".
"Alk'awari kuma ni d'in ataya,a yaushe kuma ?,da alama dai da akwai wani abu da ya ke damun ka a cikin kwakwalwarka, da ya ke hassasa ma ka tunaninnika daban-daban amma tabbas ni ban san ka ba ban kuma ta'ba ji ko ganin ka ba".
Tamkar zai fad'a jikin ta haka ya matso ku sa da ita ya na cewa,"Na ji na yarda ba ki sanni ba amma dan Allah ki ba ni damar da zan bi ki in tafi tare da ke ko da na wani lokaci ne ,idan ki ka k'i amincewa tabbas d'ayan abubuwan da zan lissafo zai sa me ni ko dai in haukace in d'imauce,in rasa tunani da hankalina k'arshe ma in je munmunar mutu wacce ba za tai kyan gani ba ta riske ni"......
"Ka ga ya isa ban sanka ba ba ka sanni ba don haka ba yanda tafiyarmu za ta zama d'aya ,ka je abinka na gode da taimakon a ka gare ni".
"Allah ya k'ara zama gatanki kar kiyi saurin yanke wannan hukuncin",cewar Kuyanga Jazila.
"Kamar ya kan in yanke wannan hukuncin, kin fa san girman bala'in da ya jefa kansa, ba sai na fad'a miki ba ke me bawa wani labari akan haka ne ma ,me ye zai sa ba zan ba shi damar da zai kaucewa waccan guguwar bala'in da ke tun karo mu gabad'aya ba".
"Saboda mu na buk'atar taimakon sa"ta ba ta amsa a tak'aice......"da sauri ta dakatar da ita ta hanyar d'aga ma ta hannu tare da cewa.
"Kar ki soma iya haka ma ya isa bana son rayuwar wa ni ta shiga cikin hatsari a saboda rayuwata",
Matsowa kusa da ita yai ya na cewa "Ba ni da wata rayuwa wacce ta fi in baki kariya a duk sanda wani abu  mai rikitarwa ko hatsari ya tunkaro ki"..."Kaima ka dakata min domin ba ka cikin hankali da natsuwar ba dan haka ba da tunin ka kai ga Ankara da abinda ke shirin tunkaroka,ke kuma Jazila mu tafi mu barnan idan kinna da ra'ayin hakan".
"Zan biki amma sai in zamu tafi tare da shi,domin ina da tabbacin ba inda zamu iya zuwa in har ba tare da taimakon sa ba".
A d'an zafafe Gimbiya Junainah ta fuskanceta ta na cewa,"Baki da hankali ne saboda son cikar burin ki sai kisa rayuwar wani a had'ari alhalin kuma kina sa ne".
"Ba mu da wani za'bi ne face amincewa da hakan shi ya na buk'atar ya taimaka ma na,mu kuma mu na buk'atar taimakon sa har zuwa sanda za mu bar k'asar BAIBAH, in kuma ba haka ba mu koma asalin inda mu ka baro kina da tabbacin su Malikat Juwairiyya ba za su ta'ba barin mu ba har sai sunga sun kamo mu,mun shiga hannunsu".
"Amma Kuyanga Jazila "......." Amma me ?,ba abinda za ki ce da ni wanda zan yarda ko in amince da ke,za'bi biyu ne mu ke da shi ko dai ki yarda mu tafi tare da shi lami lafiya ko kuma ki juya mu koma cikin Masarautar BAIBAH ba tare da mun sa ke wahalar da kawunan mu ba".
Ka sa cewa komi Gimbiya Junainah ta yi sai tsura ma ta Ido da tai hakan ne kuma ya ankarar da ita kuskuren da ta tafka tun fara zancen su cikin hanzari ta zube a gabanta ta na mai cewa,"Ki gafarce ni tsananin tashin hankali da tunanin abinda ka iya riskar mu ne ya sa na manta ko ni wace ce da matsayina, ki yafe min dan Allah ",sai da Gimbiya Junainah ta d'auki wani dogon lokaci ba wai tunani ta ke na mafita ba a'a rasa abinda ya kamata ta yi ne a yanzu, shin komawar za su yi zuwa Masarautar BAIBAH ko kuma amincewa za tai su tafi tare da wannan mutumin me kama da mahaukaci,da ga k'arshe ta ce da su," Na yarda na amince mu tafi tare amma kuma a koda yaushe zan iya sauya ra'ayina matuk'ar na ga wani abu na shirin faruwa wanda bai can-canta ko ya kamata ba".
Wani tsalle Kuyanga Jazila ta buga ta na mai ruk'unk'ume Gimbiya Junainah gami da nuna farincikin amincewar da tai,ba jira Kuyanga Jazila ta kwashe kayan da su ka taho da su a cikin sanho,wanda za su rik'a amfani da su,in buk'atar hakan ta ta so, nan fa su ka cigaba da tafiya ba tare da sun sa ke tsayawa ba.
     Ba k'aramin farinciki Yarima Haisam ya shiga ciki ba lokacin da ya ji Gimbiya Junainah ta amince da su tafi tare,wannan shine burinsa ko ba kome ya na da yak'inin zai sa ta farinciki wanda hakan shine buri da fatan shi ko da kuwa zai zama silar datsewar numfashin sa, Sai da su kai tafiya mai nisan gaske sannan su ka ci karo da wani mai amalanke ya rage ma su hanya.







Da sauri ta sa hannunta ta kange bakin sa tare da cewa,"A'a kar ka sa ke cewa haka kuma kar ka k'ara bari wannan tunanin ya zo cikin rai da zuciyar ka",ta sharce hawayen da su ka fara zubo ma ta.
"Tabbas kai ma d'a ne tamkar kowanne d'a a doran duniya da ya can-canci sadaukarwa kulawa da kuma soyayya Uwa, Alk'awarin da nai ma ka ba zai ta'ba sauyawa ba sai na sa ka yi MULKI wannan doran duniyar sai na mai da ka SARKIN SARAKAI na wannan k'arnin tabbas sai na cika ma ka wannan alk'awari madamar ina Shak'ar numfashi,Kai ko mutuwa ba ta Isa ta d'auki raina ba har sai na cika wannan mafarkin nawa a kan ka, sai na mai da Kai wanda ya fi kowa girman matsayi a wannan duniyar"....
"Har sai yaushe hakan za ta faru,na ga ji da jin irin wad'annan zantuttukan na ki ma su kama da k'anzan kurege".
"A'a a'a da gaske na ke yanzu haka ma ina kan k'adamin na na aikata hakan ka ba ni tsowon makonni shidda za ka tabbar da hakan".
"Shikenan na baki tsawon mako sha biyu in har ki ka k'asa aiwatar da hakan zan had'iye zuciya na mutu kowa ma ya huta".
A rikice,d'imauce tare da tarin damuwa ta sa ke fuskantar shi gami da fara lallashin sa amma ko kusa ya k'i ya saurare ta har ta da nonon rak'uma da ya kasance a matsayin abincin ci da shan sa a ranar kin sha ya yi,wani irin ihu ta sa ki daga k'arshe ta na mai cewa na ,"Na rantse da furfurar da ke kai na,na rantse da kai ya ya d'ana sai na d'auki ran koma waye in har ya shigar min gaba a k'ok'arin sama ma ka lafiya da na ke,kuma ina mai sanyaya ma ka zuciya da cewa madamar mun Isa tsibirin zimbar an d'aura ma ka Aure da Gimbiya Junainah to duk wata lalura da cuta da ta dame ka zata ya ye ta koma akanta, daganan sai mu komo ka fara MULKAR K'ASAR BAIBAH har zuwa ka kai matsayin da za ka zama SARKIN SARAKAI ".
Wata irin dariya ya fashe da ita a nan nannad'ad'd'en da ya ke mara dad'in ji ka na ya d'ora da cewa," Da ko na yi alfahari da ke fiye da yanda kowanne d'a ya ke yi da Mahaifiyar sa,zan yi farinciki in yi annashuwa gami MULKAR K'ASASARNAN yanda na ga dama ,in ta ka kowa yanda na ke so".
Ita ma Bokanya Azizah dariya ta sa ki ta na mai share hawayen dad'in da  su ka zubo ma ta ta ceda shi ,"Ko iya wannan farincikin da ka nuna ya ya isar min kuma ya k'ara min k'aimi wajen jajurcewa a kan wannan lamarin,Zan yi duk me yiwuwa wajen ganin na aikata fiye ma sa abinda na ce ma ka zan hi".
"Na san za ki yi nasara za ki aikata kamar yanda ki ka ce  don haka bani abincinci na in ci ", da sauri ta sake matsowa kusa da shi ta na mai bashi abincin sai faman fara'a da dariya ta ke.
Bayan ta  tabbatar da ya gama ci ta koma wajen Alon tsafinta ta tsaya ta na mai cewa gani gare ki Gimbiya Junainah, domin yanzu zan yi amfani da cutar da ki ke da ita in sa ki kai kan ki mayanka da kan ki  ba tare da kin wani wahalar da ni ba ,zan sa ki ki ki fad'a cikin dajin da ke gaban ki duk da na dan akwai abinda zai iya cutar da ke amma ba matsala na san ba za ki mutu ba har sai na cika burina a kan ki,don haka ki shirya ganinnan saman kan ki yanzu za'a fara wasan.
      Ta duk'ufa akan alon tsafin nata da sauri ta d'ago ta na mai cewa," A'aha me ye ke shirin faruwa ya na ga ba na ganinta sai duhu da na ke gani meye ke shirin gani ,ko dai ta samu wata kariya ne,ban sa ni ba ? "......