KARAGAR MULKI

Page 35

by @cwtsumiey19988

Page 35

"Mun kusa rabuwa da kai da zaran mun Isa Ga'bar kogin Nizla zamu rabu,muna k'ara Godiya da taimakon ka a gare mu baki d'aya".
      Kasa ce ma ta komi yai sakamakon wani yanayi da ya ke riskarsa ko miyan bakinsa da k'yar ya ke iya had'iyesa ji ya ke kamar ya yanke jiki ya fad'i komi nasa k'ok'arin rasa sa ya ke hatta da isar numfashin da ya ke Shak'a k'ok'arin dakatawa ta ke,gudanar jinin jikinken sai k'ara hauhawa ta ke,samun wuri yai ya ja ya tsaya tare da fusgo magana daga saman harshensa ya ce,yana mai rarraba haruffan zancen" Ku .....tafi..,ku barni anan ku cigaba da tafiyar ku,ni zan tsaya wani abu".
     Sosai Gimbiya Junainah ta zuba idanuwanta a kan sa ta na mamakin halin da ya shiga ciki,"Me ya sa me ba ka da lafiya ne,ko cikin ka ne ke ma ka ciwo?".
         Ta jero ma sa wa'innan tarin tambayoyin, "A'a ba abinda ke damuna kawai ku cigaba da tafiyar ku,ku barni a baya zan biyo ku daga baya".....
         " A'a ba inda za ni alhalin ka na cikin irin wannan yanayin,ka fad'a min me ya ke damunka in akwai taimakon da zan ita ba ka in ba ka"....
            Shima katseta yai da cewa," Ba ki da wani abu da za ki iya yimin ko ki taimaka min da shi kawai ki yi tafiyar ki abin ki,ki bar ni anan".
      "Bazan tafi ba,ba inda za ni, in na aikata hakan ban cika cikakkiyar mai imani ba,na zama butulu mai sa ka alkairi da sharri,meye zai sa na kasa tsayawa da kai a lokacin da ka ke buk'atar taimakona bayan kai ka taimake ni a lokacin da ban yi zato da tsammani ba ?",Wannan shine kalamin ta na k'arshe wanda kusan ihu tai bayan hari domin wanda ta ke domin shi bai ma san tana yi ba, tuni ya dad'e da fita a cikin hankali da tunaninsa, ya juye izuwa wani daban ba Yarima Haisam ko Yarima Sadauki ba,,ya tashi daga asalin wanda su ka had'u da shi har su ke tafiya a tare,jikinsa ya saki,idanuwansa sun rufe ruf tamkar mai barci,gashin kansa da ya ke a tare wuri guda ya barbazu a saman fuskarsa, ba Gimbiya Junainah ba hatta da Kuyanga Jazila da ke gefanta a tsaye ta tsorata da sauyin yanayin da ya riske sa cikin gaggawa.
       "Allah ya k'ara zama gatan ki ki zo mu bar wurinnan mutuminnan ba shi da lafiya kar ya cutar da ke a banza a wofi"......" Ba ki da hankali ne ba ki fuskanci halin da ya ke a ciki ba ,ya na buk'atar taimakon shine sai ki ce mu tafi mu bar sa alhalin shi ya sadaukantar da tashi rayuwar domin ya kare mu".
          "Ina tsoran kar ya cutar da ke tunda ba mu san wacce irin cuta ko musiba ya ke d'auke da ita ba ?".
     "Wannan ke ta shafa amma ba ni ba zan tsaya kai da fata akan lamarisa ba tare da na guje shi ba,har yanzu k'ofa a bud'e ta ke a wurin ki kina da damar da za ki aikata duk abinda ki ke so ko zuciyar ki ta d'arsar ma ki gami da kwanciyar a cikin ran ki",ta na k'are zancen ta d'ora hannunta saman kafad'arsa ta na mai cewa, "Bawan Allah.... Bawan Allah ka na ji na.....me...me ya ke damun ka ko ba ka da lafiya ne ?", da sauri gami da hanzari ya d'ago ya tsura ma ta idanunsa ,kamar wanda aka tsikara haka yai saurin matsawa baya gami da bige hannunta da ya a saman kafad'arsa ya ce da ita cikin siririyar muryarsa irinta mata mai d'auke da sanyi tare da yauk'i da kuma yanga,"Ke wace ce da har za ki zo kusa da ni kina faman ta'ba ni kamar kin samu k'awarki ko ance mi ki ni k'awar ki ce ko kuma ina son abota da ke ne ?".
     " Innalillahi, na shiga uku Kuyanga Jazila me na ke shirin gani yanzu haka a gabana,hankali da tunanina sun kasa had'a su guri guda har su iya samun damar da za su tantance asalin abinda ke afkuwa anan",cewar Gimbiya Junainah.
           Sai da Kuyanga Jazila ta matso kusa da Gimbiya Junainah ta kama hannayen ta ta rik'e kana ta d'ora da cewa"Nima haka, na kasa gasgata ko yarda da abinda na ke ji da kuma gani,shin wannan mutumin waye mutum ne shi ko Aljani  ,in ko mutum ne to tabbas ya kasance abun tambaya da zargi,shin shi d'in a cikin wanne irin jinsi ya fito".
       Sai da AZLA ta yamutsa baki irin Kuyanga Jazila ba tai mata ba ko bata kwanta ma ta a rai ba ta ce,"Ke kuma a suwa k'are da d'aukar gara,me ya jefa bakin ki a cikin maganar mu sai ka ce an kasa da ke balle har ki haramar d'auka ".
       Wani abun wuya da ke mak'ale a wuyan Gimbiya Junainah ne ya d'an d'auki hankalinta tabar fuskantar Kuyanga Jazila ta koma babin Gimbiya Junainah, duk yana wannan maganar ne da muryar Mata," Kai!!!.... Tubarkallah Masha Allah wannan abun wuyan na ki ya yi min kyau sosai da sosai a ina ki ka siye shi,kuma a kan wanne farashi ki ka saye shi,kin sanni ni ina son kayan k'arau kayan kwalliya mutum ya sa yai ta shek'i da walwali duk in da ya gifta ai ta kallon sa,ni d'in  akwai son gayu,bari in fad'a mi ki wani abu ina da tarin sunaye da ake kirana da su ko ki ce da ni Azla 'yar kwalliya,ko Azla gayu ko kuma Azla k'amshi amma ke na fi son ki Kira mi da AZLA gayu domin na ga ke ma 'yar gayu ce kamar ni".
       Haka Azla ta ke, da shegen surutu in ta fara ba tasan ta tsaya ba, ba ruwanta da yau ta fara ganin ka ko kun saba,ita kwata-kwata ba ta ba ta da bak'unta akwai ta da sabo,Kar ma in zance ya fad'a akan kayan gyaran jiki ne da kwalliya ma su sa k'amshi da walwalin jiki.
     Hannayen ta ta kai saitin wuyan Gimbiya Junainah da nufin ta ta'ba abun wuyan da sauri,Kuyanga Jazila ta buge hannun ta,ta na mai cewa,"Ba ka da hankali ne da za ka kai hannu jikin ta da niyar ta'ba wani abu?".
     Kallon wulak'ancin dai Azla ta sa ke bin Kuyanga Jazila da shi ba tare da ta ce da ita komi ba,sai sa ke k'ok'arin kai hannu a karo na biyu da tai,da d'an sauri Gimbiya Junainah ta ja baya ta na k'ok'arin cewa da ita wani abu, amma ina ba ta bata damar hakan ba ta hanyar cewa,"Haba ke kam ya ki ke wani abu irin kamar ba ki waye ba alhalin ba haka ba ne,so kawai na ke fa in ta'ba in ji ko ta gaske ce,domin yanzu-yanzu nan kafin in zo nan mu ka had'u da wata k'awata a bangon duniya ta ce min ta samo sa da har zan bi ta in samo sai kuma na ji kira daganan shine fa na taho".
     Cikin rawar murya Gimbiya Junainah ta ce,"Ni zan iya ba ki ita kyauta in ki na so",wata irin rangwad'a Azla tai har ta na mai kai hannunta d'aya a saman bakin ta,ta rufesa alamun abun ya bata mamaki ko ya zo ma ta a bazata,gami da zaro idanunta waje tare da d'ora d'ayan hannun na ta kan k'irjinta ta ce,"Ke Haba amma dai da wasa ki ke min ko ?,nasan wannan abun wuyan fa mai tsada ne ?".
"Da gaske na ke amma sai in za ki fad'a min ko ke wace ce",ta'be fuska Azla tai gami da ja da baya ta ce da ita,"In dai haka ne to rik'e abun ki ba ni so in na so a yanzu-yanzu sai in mallaketa ba tare da na sha wata wahala ba".
"Oh dama ba da gaske ka ke son ta ba kenan, tunda ba za ka iya aikata wani abu dan ka mallake ta ba ni abun ma a wani banbarankwai ya ke zuwan min wai Namiji da suna hajara ,ko mi ya had'a Namiji da abun wuyan  Mata oho?".
Da wani irin fushi Azla ta d'ago ta na maidawa Kuyanga Jazila martani ta ce da ita,"Kashedin ki da ni kar ki k'ara sa min baki in ina magana in ko ba haka ba na lahira sai ya fiki jin dad'i kuma kar ki sa ke kirana da Namiji in kuwa ba haka ba Hmmmmm hohoho za ki  ba su labari".
Tsuru Gimbiya Junainah tai ta na kallon Azla gabad'aya tunaninta ya cunkushe komi na ta ya tsaya ta wuri guda balle har ta saran za ta samu abinyi,mai da hankalin ta tai kan Kuyanga Jazila ta ce da ita,"Sunan Azlda wanne irin jinsi ya ke ma ki kama na Mace ko na Namiji ?".
"Sai dai macen don gaskiya bai kama da na Namiji ba",ta ba ta amsa a gajarce.
"Kenan hakan na nufin wacce mu ke tare da ita Mace ce ba Namiji ba ?","Shakka babu Uwar d'akina wannan hasashe na ki haka ya ke duba da yanda ya ke rangwad'e-rangwad'e da kashe murya wannan ba asalin wand mu ka taho tare da shi ne ba".
"To in har haka ne Kuyanga Jazila da akwai matsala, dole cikin biyu da akwai d'aya ko dai tun farko Mace ce tai shigar Namiji mu ke tare da ita,ko kuma akawai wani sirri binne a tattare da wannan mutumin".
Cikin yanayin jin tsoro Kuyanga Jazila ta ce da ita,"Ina jin tsoro Ranki ya dad'e, ina jin kamar wani abu na shirin faruwa da mu ,ki zo mu bar wannan wurin tunda wuri".
"Kin ga ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da mu domin mun kusa fita daga cikin k'asar BAIBAH, kin ga kuwa da zaran mun tsallake mun fita daga cikin hatsari",ta k'are zancen ta na mai maida hankalin ta a kan Azla wace ta zurawa kunne da wuyanta Ido tun d'azu.
"Kin ga Azla ki ka ce sunan ki ko to zo ki amshi wannan abun wuyan gashi na bar mi ki har ma da d'an kunne ga su zo ki amsa".
Fuskar Azla sai da ta fad'ad'a amma kuma lokaci guda ta dakata ta ce da ita," Da gaske ki ke ko ko zolaya ta ki ke ni fa bana son wasa ko tsokana ?".
"Da gaske na ke mana ga su ba ri in ciro ma ki",ta sa hannunta ta ciro duka ta mik'a ma ta su, akwai sai murna da d'oki ta ke, ta sa hannu ta d'auki abun wuyan ta ce da ita ,"Na gode sosai amma abun wuyan kawai na ke so ",ta k'are zance ta na mai sa shi a wuyanta,sai juyi ta ke alamun abun ya kai ma ta karo.
" Mun ba ni mun lalace Gimbiya ",cewar Kuyanga Jazila, a kid'ime Gimbiya Junainah ta waigo ta na mai cewa," Lafiyar ki lau kuwa Jazila ?".
"Ga mutanen Masarautar nan da tarin Dakaru sun nufo wannan hanyar kuma ba makawa mu su ka zo nema",ba k'aramin bugawa k'irji Gimbiya Junainah yai ba nan da nan tunaninta ya hautsine ta rasa me ya kamata ta yi ga dai Kuyanga Jazila ta rud'e gami da fita cikin hankalinta ba yanda za ai ta iya bata shawarar ko neman mafitar da za su bi,ga Azla can ta na k'ok'arin tafiya ta bar inda su ke tunda ta riga da ta samu abinda ta ke so,da wani irin zafin nama da bata ta'ba tunanin ta na da shi ba tai tsalle ta kamo hannun Azla ta had'a da na Kuyanga Jazila ta d'aure gam da mayafin ta ba tare da ta saurari tarin tambayoyin da Kuyanga Jazila ta ke ma ta ba da kallon tuhumar da AZLA ta ke ma ta ba, kawai ta ja su cikin k'asurgumin dajin da su ke kusa da shi ba tare da wani dogon tunani ba.