KARAGAR MULKI

Page 37

by @cwtsumiey19988

Page 37

"Na rantse ma ki, ki zo ki kwance ni tun kafin in samu damar da zan kwance kaina,domin ina mai tabbatar mi ki da sai na lahira ya fi ki jin dad'i".
" Ka yi ka gama domin ba abinda zai sa in kwance ka har sai sanda ta dawo kamar yanda ta ba ni umarni".......
"Kai!!! Ni ki ke kirada Namiji ba wai na ce kar ki sa ke danganta ni da jinsin Maza ba ?,na rasa gane wanne irin kai ko kwakwalwa ce da ke da ba ta rik'e abu ko jin magana ba kya yi oho?".
"To mene ne laifina dan na kira ka da namiji ba,ko ba Namijn ba ne Kai ba,Kalli fa ji bi k'irjinka silin ko ince shafe ko d'an tudunnan babu irin na mata, kalli damtsen hannunka yanda ka tara kwanji ga gemu ka tara, sai kuma ka ce in kira ka da sunan Mata aiko abun da kamar wuya gurguwa da Auren nesa".
"Au da abinda ki ka fake kenan to bari in d'auke k'irjin ki in maido shi a nawa sai in maido damtse da gemun da kike fad'a a jikin ki,kin ga kenan ni sai in koma ni ne Macen ke kuma ke ceNamiji".
Da sauri  Kuyanga Jazila ta kai hannayen ta dafe k'irjinta alamun ta tsorata da abinda ya fad'a daga k'arshe ma fara ja da baya tai idanuwanta duk sun fito waje ,motsin da ta ji ne ya sa tai saurin waigawa har ajiyar zuciya sai da ta fara sa ki sakamakon ganin Gimbiya Junainah da tai.
Da d'an gudun ta ta k'arasa ku sa da ita ta ce,"Na ji dad'in dawowar ki yanzu domin wannan mutumin nema ya ke yai min tsintsilar tsiya",duk ta na wannan maganar ne hannayenta nannad'e a saman k'irjinta.
"Kamar ya ban ga ne ba,me ki ke nufi","Nema ya ke ya raba ni da wad'annan kayan".
"Kaya kuma wad'anne kayan ?",ta sake tambayarta ba tare da ta fahimci me ta ke son cewa ba.
"Ki gane mana wannan kayan arzik'in na ke nufi",ta k'ara zancen ta na mai d'an d'aga k'irjinta yanda za ta gane,Azla ce ta shiga tsakiyar maganar da su ke da cewa.
"Kin ga k'awata 'yar gayu manta da ita,tunda daman nasan ita ce ta zuga ki har ki ka d'aure ni, ki zo ki kwance ni ina da inda na ke son zuwa wani taro ne na masu kyawun duk duniya ina son in kalla don wata Rana in za a sake  wannan gasar da ni za ai,yanzun ma wani dalili ne ya hanani shiga".
"Ba damuwa ki ji ra ni kad'an ga ninan zuwa,yanzu zan zo in kwance ki",ta ba ta amsa ta na mai maida hankalinta a kan Kuyanga Jazila,Ita Gimbiya Junainah duk a tunaninta kayan da ita Kuyanga Jazila ta ke jigila da su tun farkon fitowar su daga Masarauta dan haka ta ce da ita,"Idan dan kaya ne ki barshi ya d'auka daga ya rage ma ki wani nauyi da ya addabe ki tun da dad'ewa ai ke hutu ne ya same ki ki barsa kawai ya d'auke ma ki su".
Sosai Kuyanga Jazila ta kad'u da jin zancen da ya ke fita daga bakin Gimbiya Junainah, su'bul ta sa'bule ma ta duk wani d'an sauran karsashi ko k'anfin jiki da na zuciya da ta ke da shi, wata duniyar tunani can ta tafi ta na hango kanta ba k'irji ga gemu da kwanji duk sun fito ma ta na Maza, ba tare da ta sa ni ba ta kwalla k'ara wacce har sai da Gimbiya Junainah ta tsorata,ta waigo ta na mai tambayar ta,"Lafiyar ki k'alau kuwa ko wani abun ya same ki ne?".
Cikin rev in'ina ta ce da ita,"Bbbbb.....Ba ba komi wani abu ne ya ta'ba ni na zaci ko maciji ne".
Girgiza kai kawai ta girgiza ba tare da ta ce da ita komi ba,ta cigaba da k'ok'arin samo busassun itatuwa kana ta ce da ita,"Zo ki tai maka min in kunna wannan wutar in har dai abinda na ke zato da zargi ne yanzu zan yi maganinsa".
Jiki ba kwari haka Kuyanga Jazila ta nufo inda ta ke ta amshi dutsan k'ank'ara ta fara k'yastawa,har Allah ya ba su sa'a ta kunnuwa iccen wuta ya kama har ya cinye ya bar garwashin kad'ai,sannan ta d'auki Gadon Maciji yad'o ne da Buruku ta zuba a jikin don ta yi ma Yarima Haisam ko Azla turare da su,ta nufesa gadan-gadan.
Wata irin dariya mai cike da shak'iyanci ta sa ki tare da cewa,"Wai me ki ke nufi turare za ki yi min in tafi in bar jikin Yarima Haisam ko me ?to aiko kin makaro ko ince kinyi  kuskure,domi wannan shirmen na ki ba abinda zai yi,zan tafi ne kawai idan na so ,ba wai dan wannan k'aurin da ki ka kunnashi ba,to ki sa ni ba wai mun shiga cikin jikinsa don mu fita ba ne ba,ki san wani abu tun had'uwata da ke na ji kin burge ni ina jin kina da wani matsayi babba a wurina shiyasa na biye maki duk abinda ki ka ga yana faruwa ina sane k'yake ki kawai nai,zan tafi yanzu ba wai dan wani abu ba a'a don lokacin da na ke da shi ya k'are ,ina mai yi mi ki addu'a da kar Allah ya sa Azeela ce ke shirin kawo ma ku ziyara a yanzu don ba za ki ta'ba iya ji da ita ba, sannan in har Masoyina Nurain ya k'araso ki ce ma sa ina kewar sa da zaran ya zo zan bayyana mu sha firar masoya tare  da shi".
Ta na kai wa anan komi na jikin sa ya ya sa ki zufa ta fara zubo ma sa ta kowacce kafa ta jikinsa,bugun numfashinsa da gudanar jininsa ya k'ara k'arfi gudanarwa,k'ullin da ke hannu da k'afarsa wanda Gimbiya Junainah ta yi ma ya kwance, gashin kansa isaka ta fara kad'a shi tamkar za ta tafi da shi,kafin daganan komi na sa ya tsaya.
Jiki ba kwari Gimbiya Junainah ta fuskanci Kuyanga Jazila da cewa ,"Me hakan ke nufi ,ko dai wani abun ne ke shirin sa ke faruwa da shi?".
"Nima ban sani ba",Kuyanga Jazila ta ba ta amsa,motsin da ta ga ya fara yi ne ya sa tai saurin dakatar da tunanin da ta ke,ta yi kansa ta na mai kamo kansa ta d'ora a saman cinyarta,"Shugabata ba kya jin tsoransa ki ka tunkare shi har haka, kar ya illata ki fa,domin ba mu san a wanne irin hali zai farka ba shin shi d'in ne ko kuma wata sabuwar fuskarce za ta bayyana a garemu ?".
"Koma da wacce irin fuska ce zai bayyana ba zan guje shi ba zan tunkare shi a kowanne irin hali ya ke".....motsin da ya fara yi da idanunsa ya sa tai saurin dakatawa ta na mai cewa.
"Ka farka kenan ko ka na da buk'atar wani abun ne, ko da akwai wani abun da ya ke damunka ?",sake lumshe idanunsa yai sakamakon d'umin jikinta da ya fara ratsa dukkanin sassan jikinsa,hannayenta da ke cikin nasa ya sa ke k'ank'amewa ya na magana can k'asan mak'oshin sa sai wanda ya ke kusa da shi ya yi da gaske sannan zai ji me ya ke cewa,"Dan Allah kar ki tafi ki bar ni ki tsaya a tare da ni,a baya na rayu cikin k'uncin rayuwa,wahala,damuwa da rashin gata tamkar mara Uwa da Uba ".
'Dan dakatawa yai alamun abun da ya ke fad'a ya na matuk'ar ci ma sa rai gami da tsaya ma a zuciya,"Ina kewan ki,ina son in rayu da ke ,in kyautata ma ki,in zama tamkar Inuwar gajimare a gare ki,kuma in ba ki kariya a kowanne irin yanayi walau na dad'i ko akasin haka", ire-iren wannan zantuttukan yai ta fad'a har barcin wahala ya d'auke sa.
" Uwar Gijiyata lafiya me ya ke faruwa na ga idaniyar ki na zubar da hawaye,ko wani abun ke damun ki?".
Cikin sheshshekar kuka ta ce da ita,"Ban san me ya ke damuna ba,kawai dai na san ina jin tausan shi wanne irin So ya ke min wanda ban ta'ba gani ba,wacce irin alak'ace a tsakanin mu da ban zato ba,waye shi me ya ke so a wurina kuma daga ina ya fito wacce irin rayuwa ya fuskanta kafin ya zo nan ,kuma wace ce ni a garesa,wanne matsayi ne da shi a gare ni ?",......kuka ya ci k'arfin ta ta kasa idasa maganarta.
"Na bani na shiga uku ni Jazila kar ki je ki cutar da kan ki a kan lamarin wannan mutumin da ba ki san ko shi waye ba kuma ni ba ni da amsoshin wad'annan tarin tambayoyin na ki "......
Da sauri ta dakatar da ita da cewa,"Ban san ko shi waye ba,amma shi ya min farin sa ni,kalaman sa kai tsaye  suna nuna muna da wata naunauyar alak'a mai girma a tsakaninmu,wanda shi kad'ai ya santa dole akwai wani 'boyayyen sirri a tsakaninmu,akwai wani zaren k'addara da ke nannad'e a cikin rayuwarsa da kuma rayuwata".
      "'Boyayyen sirri kuma a tsakanin ku to a taya haka za ta kasance bayan ba ki san shi ba,bai san ki ba hasalima a jiya ki ka fara ganinsa,idan ma sirrin ne a ta ya za ki iya tono shi har ki jai ga bayyanar da shi?".
      "Ban sa ni ba Kuyanga Jazila,Ban sa ni ba,amma da gaske lamarin wannan mutumin da ko sunan sa ban sa ni ba ya na rud'ar min da kwakwalwa ina jin kai na kamar zai tsage gida biyu na rasa a wanne bigire zan aje shi hatta da lalurar da ya ke fama da ita na kasa iya sama ma ta wani muhalli guda d'aya a cikin zuciya ta ko kuma in rad'a mata sunan da zan kirata da shi,tunanina ya tsaya ba na iya fahimta ko gane komi karma yanzu da na saurari zantuttukan da su ke binne a cikin zuciyar sa,ya wahala ya cutu ,ya kuma shiga cikin k'angin rayuwa"....ta kasa k'arasowa sakamakon motsin da ta ga ya fara yi.
       Tamkar wanda a ka fad'a ma sa halin da ta ke a cikin yai zunbur ya mik'e ya na mai sauke idanunsa akanta ,"Me ya sa me ki na ga kina zubar da kwalla, ko wani ne yai ma ki wani abu, waye shi mai kiran tsautsayi kuma me ya aikata ma ki ?".
     Da sauri ta tari numfashi sa da cewa,"Ba kowa,ba wanda yai min komi".
"Ta ya haka za ta faru, kuka fa na ga kina yi ta ya zan amince da hakan ko dai so ki ke ki 'boye min halin da ki ke a ciki ne ?".
"Ba haka ba ne ba fa"......"In ba haka ba ne ya ne,ki fad'a min dumin ba zan ta'ba samun natsuwa ba har sai kin sanar da ni abinda ya ke faruwa da ke har ya zama silar ko sanadiyar zubar hawaye a saman fuskar ki",ya tari numfashinta.
Sai da ta kai hannayen ta ta share hawayen da su ke zubowa kafin ta ba shi amsa da cewa,"Kai ne sillar kuka na,tausayin ka daganin irin yanda ka ke rayuwa su ne su ka sa ni na ke zubar da hawaye ".
Da wani irin zafin nama ya ja baya daga kusa da ita jikinsa da muryarsa duk sun fara rawa ya ce da ita" Nnnn....Nnnn.....ni kuma me ya same ni in ce dai ban cutar da ke ba ko,ban aikata komi a gare ki ba?",ya na maganar ya dudduba jikin sa ko zai ga sauyin yanayi a jikinsa wata k'ara ya sa ki a razane sakamakon kai hannunsa saman wuyan sa da yai ya ji abun wuya a jiki,ba tare da ya ce komi ba ya fara ja da baya ya na k'ok'arin barin inda su ke .....

"Tabbas kin aikata babban kuskure Sarauniya Junayyah,ko dai ba ki san halina ba ne shiyasa ki ka aikata hakan, to amma ai Boka Dürsäås ya sanni farin sa ni ,dalilin wannan kuskuren da ki ka aikata na yi alk'awari sai kin zama abar tausayi ko darajar zama a saman kan layi da ki ke ma wani fata ke ba za ki samu ba,burin d'ana shine kwanciyar hankali kowa da kowa na cikin wannan Masarautar kai ba ma na Masarautarnan kad'ai ba duk wani wanda ya ke rayuwa a cikin K'asar BAIBAH ba zai samu kwanciyar hankali da natsuwar zuciya ba har sai Yarona kuma d'ana Irzam ya taka k'afafunsa bisa doran k'asa kamar yanda kowanne cikkaken mutum ya ke sannan za ku zauna lafiya,kuma ni da kaina zan shiga har cikin Dajin Irsaba in fiddo da Gimbiya Junainah domin ita ce mahad'in sirrin magani na, don haka ku shirya ma tarar abinda ba ku yi zato da tsammani ba", Bokanya Azizah na kai wa nan a zancen ta ta fad'in wasu d'alamisai marasa dad'i ji kafin k'iftawar Ido sai ga Malikat Juwairiyya kwance a gabanta a bisa gadon ta na alfarma, alhalin da a d'akin ta ta ke kwance bayi da hadimai na yi ma ta hidima,sannan kuma da akwai tarin Dakaru da su ke gadin k'ofar shigar ba wanda ya ke da dama ko izinin shiga sai an yarda da shi ko antantance shi tun da su ka dawo daga neman Gimbiya Junainah, Sarauniya Junayyah ta sa mata takunkumi gami da tsaro mai tsauri,ko da wasa ba a barin wani ya ganta ko ya je in da ta ke sai wasu amintattun bayin da Sarauniya Junayyah ta aminta da su ta sa su ke kula da ita ,ba tare da Bokanya Azizah ta tsaya ko ta daina fad'ar kalaman da su ke a saman bakin ta ba,tamkar an yi Ruwa an d'auke haka komi da ke cikin d'akin wanda ya ke mallakin ta ya 'bace har da Malikat Juwairiyya da take faman jinya azabarwa da Boka Dürsäås yai mata da kuma Irzam da ya ke cikin kwandonsa na ko da yaushe.