MATAR MANYA

5

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

KANSA'U BELLO

(OUM FATIMA)

GAJEREN LABARI

PAGE 5

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Kamar yanda muka shirya da Alhaji Murtala dala washe gari bayan sallar magrib sai gashi yazo gidanmu Mota cike da kayan abinci, babu irin kayan daÉ—in da bai sayo ba don har alawar yara sai da ya sako a cikin siyayyar. Muna zaune a tsakar gida sai gani muka yi ana shigowa da buhun shinkafa, taliya, makaroni, indomee, jarkar mai da sauran tarkacen kayan abinci.

Ina gani na san daga Alhaji ne don tare muka shirya komai, amma nima sai na nuna mamaki irin ban san komai ba kamar yanda naga mutanen gidan sun yi. Sai da aka kammala shigowa da komai sannan akace ana sallama da Baba.

Ba musu kuwa ya fita don dama jira yake a gama ya tambayi daga ina wannan kayan ke shigowa. Da sauri direba ya buÉ—e masa Mota ya fito ganin Baba ya fito yana waige-waige "Barka da fitowa Baba." Alhaji Murtala dala ya faÉ—a yana sunkuyar da kai. Da mamaki Baba ya É—ago yana kallon mutumin da zasu iya yin sa'a da shi amma yana kiransa Baba har da sunkuyar da kai.

Mamakinsa ya shanye yace masa "Barka dai." Shiru ba wanda ya ƙara magna sai Baba da yaga shirun yayi yawa yace "Ko kaine ka aika kaya gida."

"Eh nine Baba." Ya bashi amsa.

"To madallah, amma ko zan iya sanin dalili?." Baba ya tambaya yana tsare shi da ido don yasan ruwa baya tsami banza.

"Kyautatawa ce kawai Ba." Shiru Baba yayi yana nazarin mutumin, shi dai mamakin dalilin daya sa zai kawo musu wannan uban kayan haka kawai ya tsallake kowa a unguwar ya kawo gidanshi alhalin bashi kaɗaine mabuƙaci ba a unguwar. Yana cikin wannan tunanin ne ya tsinci muryar Alhaji yana faɗa "Baba wata magance mai muhimmanci ke tafe dani nake son mu tattauna idan babu damuwa."

"To bari nasa ayi shimfiɗa a zaure." Baba ya faɗa yana raya cewar 'nidai na san ruwa baya tsami banza.' Sagir ya ƙwalawa kira yace ya kawo masa tabarma zaure yayi baƙo, ba'a jima ba Sagir yazo ya shimfiɗa tabarmar ya leƙo ya sanar da Baba.

"Bismillah." Baba ya faɗa yana nunawa Alhaji hanya. Bayan sun shiga sun zauna Alhaji Murtala dala ya yiwa Baba bayanin abinda ke tafe da shi. Sai da ya gama bayanin sa gaba ɗaya kafin Baba ya sauke ajiyar zuciya ya fara magana. "Alhaji naji bayaninka duka amma sai dai ita yarinyar da kake magana a kanta an tsaida ranar aurenta ina mai baka haƙuri." Baba ya ƙare maganar yana kallon fuskar Alhaji ba tare da wata shakka ba.

"Eh na san da wannan maganar Baba amma sai dai ta sanar dani bata son shi wanda aka tsayar musu da ranar, shi yasa nace zan zo in sameka ko za'a duba lamarin ayi wani abu a kai."

"To na fahimta, amma gaskiya ba abinda zan duba na riga na bada aurenta sannan kuma maganar bata son sa daga baya ne don ita ta kawo shi, saboda haka ga kayanka zansa a fito maka da su." Yana gama faɗa ya miƙe zai shige ciki.

Da sauri Alhaji Murtala dala yace "A'a Baba baza ayi haka ba, ni kyauta na kawo bana buƙatar a dawo min dasu." Bai jira abinda Baba zai kuma faɗa ba ya fice a gidan, da sauri direbansa ya buɗe masa suka wuce zuciyarsa ba daɗi.

Bayan tafiyar Alhaji Baba ya shigo gida yana ƙwala min kira ransa a matuƙar ɓace "Salamatu wai ba dake nake ba!." Fitowa nayi kaina a ƙasa ina tura baki nazo na tsuguna.

"Kece kika turo mutumin can yazo neman aurenki bayan kin san kina da ranarki akai ko?."

"To ai Baba bana sonsa n..." Marin dana ji saman fuskata ne ya hana ni ƙarasa maganar dana fara.

"Zaki rufe min bakinki anan ko sai na taka ki a wurin nan, sha-sha-shar yarinya, in kin san bakya son sa wa yace ki kawo shi." Ƙoƙarin sake magana nayi Baba ya kai min hauri da ƙafa. Ganin in na tsaya dakuwa zanyi a hannun Baba yasa na ruga na shige ɗaki ina jinsa yana rantsuwar akan na sake sai ya min dukan tsiya, sannan kuma nayi kaɗan in mayar dashi ƙaramin mutum, na barshi ma yaji da maganar dasu Yaya Habu ke ɗauko masa.

"A'a Malam kada ka sanyo min yara a maganarka, can ku ƙarata da fanɗararriyar ƴarka da taƙi jin maganarka." Baba Mari ta faɗa tana ci gaba da sakin masarta da take soyawa. Daga haka rikicin ya koma tsakanin Baba da Baba Mari suke ta musayar magana tana ta faɗar munanan magan-ganu a kaina. Mama dai na ɗaki tana kukan zuci sabo da sanin da tayi duk Salama ta jawo wannan rikicin kuma duk wannan abin dake faruwa ba zai sa ta canza daga kafewar da tayi ba sabo da ita ta haife ta tafi kowa saninta.

Kamar ta san abinda nake saƙawar kuwa don ina zuwa ɗakin nace "Wallahi aka kuskura aka ɗaura min aure da wanda bana so sai an yi nadamar abi..." Ban ƙarasa ba Mama ta taso ta rufe ni da duka tana kuka take faɗin "Kiyi duk abinda kikaga dama Salma, ba dai so kike sai kin kasheni ba? To ki kasheni ki huta, nace kin daɗe baki sa munyi nadama Ba!."

Sai da ta gaji ta ƙyale ni sannan ta fice a ɗakin. Sagir dake zaune kamar zai yi kuka yace "Don Allah Yaya Salma ki daina abinda kike yi, kinga fa kin saka Mama kuka."

"Zanci Ubanka Sagir, Sa'arkace ni?." Na faɗa ina zaro masa ido, tashi yayi ya fice yana ƙunƙuni na bishi da gudu zan kamo shi.

★★★

Bai fi saura sati biyu ba bikina da Suhail amma har yanzu naƙi amincewa da shi kullum rikici muke yi ba kalar wulaƙancin da bana masa amma yaƙi zuciya ya rabu da ni, har yanzu bamu rabu da Alhaj Murtala dala ba kuma maƙudan kuɗi yake kashe min yana ƙara tunzura ni. Idan na kalli Alhaji na hasaso irin rayuwar jin daɗin da zan yi a gidansa, in ci mai kyau in sha mai kyau in saka mai kyau in hau mota mai kyau. Idan kuma na kalli Suhail na ɗora su a mizani shi da Alhaji sai inga kwata-kwata babau haɗi, tamkar a kejin dabbobi zan kasance a gidansa. A ɓangaren kyau da zubin hallita da kuma ƙuruciya bama zan haɗa Suhail da Alhaji ba domin ya fishi komai ta wannan fannin, duk da shima Alhajin ba za'a kira shi mummuna ba ko tsoho sosai.

A waɗannan watannin da suka wuce babu irin boren da banyi ba amma Baba yayi rantsuwar ba fashi, duka kuwa na sha shi a wurin Baba ba sau ɗaya ba akan rashin zuwa idan Suhail ya kira ni. Mama kuwa ba irin rarrashi da nasihar da bata min ba amma na shafawa idona toka, duk tabi ta rame sabo da damuwa ga Baba kullum laifinta yake gani akan taƙi tanƙwara ni.

Sajida da Karima da aka haÉ—a bikinmu za'a É—aura rana É—aya tuni suka fara shirye-shiryensu, sun fitar da anko da duk wani abu da za'a yi sunyi. Baba Mari kullum suka je siyyayya suka dawo haka za'a baje kaya a tsakar gida ana nunawa Mama ana mata habaici.

Ko a fuska Mama bata nuna mata komai domin ta san duk abinda akewa ƴa Mace zata yi bakin ƙoƙarinta, ta sha zaunar da Salma tayi mata nasiha ta daina kashe-kashen kuɗin da take yi a banza a wofi, garama ta rinƙa sayen abu mai amfani wanda zata mora a gidanta. Buɗar bakina sai cewa nayi "Ni ba abinda zan saya saboda Alhaji yace baya buƙatar komai ni kaɗai yake so.

Tsabar takaici bata ƙaramin magana ba ta bani wuri taci gaba da shirye-shirynta ita kaɗai ba tare data ƙara bi ta kaina ba. Kairiyya ita kaɗai ke shirin bikin ita da angon komai ita yake nema yabawa har anko ita ta fitar da sauran ƙawaye na har rabon invitation sun raba, duk abinda suke yi naƙi shiga don haushinsu nake ji cewa nake wahalar banza suke sha don ba zama zanyi ba.

Yau saura kwana biyu a fara biki Alhaji ya kirani a waya yace inzo muyi bankwana, ban wani damu ba na shirya na fito zan wuce Mama ta kira ni. "Ina zakije haka kike sauri?." Ta tambaye ni.

"Saƙo zan amso can bakin titi." Na bata amsa ina addu'ar Allah yasa kar ta ƙara min wata tambayar.

"Kar ki daɗe to kinga bai kamata ki riƙa fita ba."

Kai kawai na ɗaga mata na fice da gaggawa ina jin Aunty Zaliha ƙanwar Mama da suka zo tana tambayarta ina zanje, ban tsaya jin amsar da Mama ta bata ba nayi gaba ina amsa wayar Kairiyya dake tambaya ta ina ina?.

"Na ɗan fita yanzu zan dawo." Ina faɗa na kashe wayar na nufi inda Alhaji ya faka Motarsa, ina zuwa ya buɗe min na shiga na zauna. Gani nayi yana ƙoƙarin tada Motar nace masa "Ina zamu je?." Don zuciyata raya min tayi ɗauke ni zai yi mu gudu ganinsa shi kadai ko direba babu, shi yasa na ɗanji tsoro ya kamani don duk rashin jina ban taɓa tunanin guduwa ba.

"Saƙonki zamuje kinamso."

"Ok." Na faɗa ina shiga tunanin inda zamu je kuma wane saƙo zai bani. Ganin mun bar unguwarmu mun nufi wata yasa na ƙara kallon Alhaji sai dai ban ce komai ba har muka tsaya bakin wani haɗaɗɗen gida, horn yayi mai gadi ya leƙo yaga waye sannan ya buɗe da sauri yana gaishe da uban gidan nasa.

Sai da ya gama dai-daita parking sannan ya juyo ya kalle ni "Feel free mana, ba wani abu fa." Ya faɗa yana jifana da wani irin murmushi ganin kamar a ɗarare nake. Zuciyata cike da wasi-wasin dalilin da yasa ya kawo ni nan na bishi har dai-dai wata kyakykyawar ƙofa da naga ya ciro key ya buɗe "Bismillah." Ya faɗa yana matsa min alamar in shiga. Sai da na haɗiye wani miyau kafin nayi shahadar shiga cikin ƙaton living room ɗin da aka ƙawata shi da kalar green wacce tayi matuƙar kyau ba kaɗan ba.

Abinka da abinda rai keso tuni na manta da wani tsoro dana fara ji na shiga ƙarewa living room ɗin kallo ina faɗin "Wow You have a beautiful house Alhaji."

"Thanks, amma in kina so zai iya zama naki." Ya faÉ—a yana jifana da wani irin kallo da yake yawan min shi a kwanakin nan.

"I love it so much." Na kuma faÉ—a ina zazzagawa har wurin wata irin matakala da zata kaika sama wacce aka yiwa wani irin shape mai kyau.

"Ki aure ni kawai sai in saka ki a ciki kiyi zamanki, sannan zan mallaka maki shi kyauta." Ya kuma faÉ—a. Tuni idona ya cika da hawaye tunawa da nayi yau saura baifi kwana huÉ—u a É—aura min aure da wancan matsiyacin da bashi da komai sai shegen naci da son kansa.

"To ya zanyi Alhaji? Kana ganin ba irin abinda ban yiba don ganin an fasa wannan auren amma kamar ƙara zuga Baba da Suhail nake yi!." Na ƙare maganar ina fashewa da kukan tsananin baƙin cikin asarar da zan tafka matuƙar na bari aka aura min Suhail. Kama kafaɗuna Alhaji yayi ya zaunar sani saman cushion ɗin da aka ƙawata living room ɗin dasu.

Damuwar da nake ciki tasa ban kawo komai ba akan taɓanin da Alhaji yayi ba don mafita kawai nake nema ido rufe. "Kwantar da hankalinki ki nutsu, akwai mafita ɗaya da zata sa ko an ɗaura auren ba zai iya zama da keba sai ya sake ki." Ya faɗa min yana min murmushi. Cikin zaƙuwa na tambaye shi "Mecece wannan mafitar."

Bai amsa min ba sai Fredge da ya nufa ya ɗauko lemu ya nufi kiching ya ɗauko cup ya zuba ya bani yana faɗin "Sha zuciyarki tayi sanyi sai muyi maganar." Ba musu kuwa na shanye lemun duka na aje kofin ina sauke ajiyar zuciya. Ɗaki ya shiga ya ɗauko wani ɗan ƙaramin boxs da aka naɗe shi yayi kyau sosai ya miƙo min yace "Ga gifts ɗinki na aure nan."

Karɓa nayi ina jin yanayina na canzawa, lokaci ɗaya naji kamar ana min tafiyar tsutsa a cikin jikina. Ƙoƙarin buɗe gifts ɗin nake amma na kasa sabo da abinda nake ji ƙara yawa yake. Cikin abinda bai fi minti biyar ba yanayina gaɓa ɗaya ya gama sauyawa na rikice da wani azababben feeling da ban taɓa tsintar kaina a ciki ba.

Kallonta yake yana irga mintuna har sai da yaga ta kai matakin da bata isa taja da buƙatarsa ba sanna ya taso ya jata suka haura sama yana mata abubuwan da suka ƙarasa rikita yanayinta da abinda yasa mata a lemu.

Ban tashi dawowa hayyacina ba sai bayan da mai afkuwa ya gama afkuwa sannan hankalina yayi matuƙar tashi na fara kuka ina faɗin "Me yasa a aikata min haka?."

"Kinga ki kwantar da hankalinki, wannan itace mafitar da nake nufi Kin ga ko an É—aura auren ba zai zauna dake ba idan ya gane abinda ya faru, zai sako min ke ni kuma

Sai na aure bata." Da irin waɗannan mayaudaran kalaman Alhaji ya samu ya shawo kaina na bashi haɗin kai ya taimaka min cike da nuna min ƙauna.

Hankalina bai ƙara tashi ba sai da na duba agogo naga ƙarfe 10 00:pm sannan na ɗaga masa hankali ya maida ni gida sabo da na san ana can ana nemana, daga can bayan layinmu nasa shi ya sauke ni na lallaɓa gida ina takawa a hankali zuciyata cike da tsoron kar a gano abinda na aikata, sai dai in na tuno kalaman Alhaji sai in samu nutsuwa sanin cewa ba zan daɗe a gidan Suhail ba zai sake ni inje inyi irin rayuwar da nake so a gidan Alhaji....

Akwai complete document a Naira 300

08238665227

Oum Fatima