CHAPTER 13
ALLURA TA TONO GARMA 13
"Shekarata ashirin da yin aure, amma ban taɓa samun haihuwa ba. Wannan matsalar tana yawan damuna, na sha zuwa wajen likita ya gwada ni, amma abu ɗaya yake faɗa min shi ne; lafiyata ƙalau kawai lokacin haihuwar ne bai yi ba, amma matana sun ƙi yarda sam a yi musu gwajin a ga lafiyarsu kuma sun hana ni ƙarin aure wai lafiyarsu ƙalau amma a cewarsu. Watarana ina zaune a office abin duniya ya ishe ni, sai na shirya na tafi wajen aminina tun na yarinta, domin na faɗa masa matsalata ko yana da shawarar zai ba ni. Ina isa shagonsa ya tarbe ni cikin girmamawa ina zama sai ga wata matashiyar budurwa ta kawo masa fura da nono a cikin ƙoƙo ta durƙusa har ƙasa ta miƙawa abokin nawa cikin girmamawa..
"Yana karɓa ya miƙo mini ya ce na sha, duk da na nuna masa na ƙoshi amma sai da ya tilasta ni na sha. Haƙiƙa na ji daɗin fura da nonon nan ba kaɗan ba, har ce masa na yi ya rinƙa saya min kullum zan rinƙa aikowa a karɓa min. Daga nan muka fara tattaunawa har na faɗa masa matsalar da ta kawo ni wajensa.
"Ba tare da wani dogon nazari ba ya ce min aure kawai zan ƙara shi ne maganin matsalata. Nan take kuwa na yarda da maganarsa, amma ban san wacce mata zan aura ba, ya kalle ni da murmushi ya ce "Ai Hafsatu yakamata ka aura Alhaji Iliyas." Cike da mamaki na ce, "Wace ce kuma Hafsatu?" Ya ce, 'Ita ce wacce ta kawo min nonon nan da ka sha, ita yakamata ka aura, saboda tana da hankali. Alhaji na tabbata idan ka auri Hafsatu sai ka zo ka yi min godiya, kuma ƴaƴanka za su samu tarbiyya mai kyau..' Na tambaye shi inda take, ya ce min mahaifinta daga ƙauye ya dawo birni yake gadi a gidan wani mai kuɗi, suna zaune a unguwar Darmanawa amma dukkansu Fulani ne.
Ban yi ƙasa a gwiwa ba, da daddare abokina ya raka ni gidan su Hafsatu muka samu mahaifinta da maganar amma sai ya nuna sam bai amince ba. Ba ya so ya yi wa ƴarsa auren dole, ko kuma ya aura mata wanda bai dace da ita ba. Duk yadda muka so ya fahimce mu a lokacin nan, amma ya gaza hakan. Tilas muka taho muka rabu da shi, a hanya abokina ya rinƙa kwantar min da hankali tare da cewa bayan kwana biyu mu koma zai amince. Amma kar mu nuna masa kuɗi, don indai muka nuna masa kuɗi to har abada ba zai bamu aurenta ba, tsatstsauran ra'ayi gare shi...
"Hafsatu matashiyar budurwa ce kyakkyawa ce sosai jinin Fulani. Tana da hankali nutsuwa da kamun kai, kuma ƴar talakawa ce sosai amma yanayin suturar jikinta ne kawai zai nuna ma hakan, amma ba fatar jikinta ba.
Bayan mun koma wajen mahaifin Hafsatu an kai ruwa rana kafin ya amince ya ba ni aurenta, sai da Hafsatun da kanta ta ce ta yarda za ta aure ni sannan ya yarda. Ya ce ya bamu ita ne don ta furta cewa tana sona, amma ta sani duk abin da ya same ta laifinta ne don shi ya fita haƙƙinta. Dalilinsa na ƙin amincewa ya ba ni aurenta shi ne ba ya son ya kai ƴarsa cikin kishiyoyi musamman ma waɗanda suka girme ta, suka fi ta sanin rayuwar aure. Ba mu baro wajensa ba, sai da na yi masa alƙawarin cewa ba zan bar Hafsatu ta sha wahala ba. Ba a ɗauki dogon lokaci ba aka ɗaura aurena da Hafsatu a kan sadaki naira dubu hamsin. Da farko dubu ɗari biyar na bayar da sadakinta, amma sai ya ce kuɗin sun yi yawa shi ba sayar da ƴarsa zai yi ba, na biya yadda ake biyan sadakin duk wata ƴar talaka.
"Ranar da aka ɗaura aure da yamma aka ɗauke ta zuwa gidana da yake Hotoro GRA, part huɗu ne a gidan matana kowace da part ɗinta shi kuma sauran part ɗin shi ne nawa. Amma tun da Hafsatu ta shigo gidan nan na tare a nata part ɗin, idan ka ga na je part ɗina to wanka zan yi, daga ƙarshe ma a part ɗin Hafsatun na tare gabaɗaya duk da hakan bai yi wa sauran matana daɗi ba. Tun da aka kawo Hafsatu gidan nan, ba ta taɓa hayaniya da kowa ba saboda tsananin haƙurinta. Tana yi wa sauran matana biyayya tamkar su suka haife ta, da farko ƙiyayya da wariya ta fara fuskanta daga wajen kishiyoyinta. Amma kyawawan halayenta ya sa suka fara sassauta mata, har suke shakkar nuna mata ƙiyayyar a bayyane.
Watan Hafsatu shida a cikin gidana Allah Ya ba ta juna biyu, na yi murna sosai da samun wannan cikin. Sai dai ba haka yake ba daga wajen matana, a gabana su ma suna nuna jin daɗinsu da samun juna biyun amma a bayan idona kullum hanyar da za su lalata cikin suke nema.
"Da wata amintacciyar ƴar aikin gidana mai suna Dije ta same ni ta faɗa mini duk irin makircin da suke shiryawa Hafsatu a kan wannan juna biyun da ta samu. Ni kuma da na ji haka sai na hana ta cin duk wani abinci da ya fito daga hannunsu, hatta abincin gidan ma gaba ɗaya wanda ƴan aiki suka girka na hana ta ci, kuma na hana ta girkawa da kanta saboda ba na so ta rinƙa shan wahala saboda juna biyun da yake jikinta. Duk abin da ta ce tana so komai wahalarsa sai na nemo mata shi.
"Yayin da ta shiga watan haihuwarta ma daina fita ko ina na yi. Da kaina nake tarairayarta, don ba na so naƙuda ta zo mata matana su zo kanta ban san abin da za su shirya mata ba. Da yake ba a yi wa Allah wayo kuma mutum ba ya gujewa ƙaddararsa sai wata ranar litinin aka kira ni daga kamfanina cewa na yi baƙi daga U.S.A suna jirana urgent. Dole sai na zo, tilas na shirya na tafi, ba don raina ya so ba, sai don ba yadda zan yi. Ina fita naƙuda ta zo wa Hafsatu, da taimakon Dije da sauran matana aka kai ta asibiti, ta haihulafiya amma ta jigata sosai ta fita daga cikin hayyacinta.
"Sai sauran matana suka haɗa kai da likitan asibitin suka ba shi maƙudan kuɗaɗe suka ɗauke jaririyar da Hafsatu ta haifa suka bai wa wata mata da ban san kowace ce ba ta je ta jefar da ita. To shi ne da ba ta samu inda za ta jefar da ita ba, sai ta bar ta a cikin adaidaita-sahunka ta gudu.."
Malam Hassan ya jinjina kai ya ce, "Haba koda na ji, ai na san babu uwar da za ta haifi ɗa kuma ta gudu ta bar shi a cikin adaidaita-sahu. Kuma wallahi Alhaji lokacin da na ɗauko matar nan, a jikina nake jin cewa ba ta da gaskiya, kawai don na ga tana buƙatar taimako ne shi ya sa na taimaka mata."
Alhaji Iliyas ya ci gaba..
"Sai da matana Suka yi wa Dije ƴar aiki barazanar kisa idan har ta tona musu asiri, sannan suka ba ta maƙudan kuɗaɗe masu yawa a kan ta yi shiru a kan lamarin. Lokacin da Hafsatu ta dawo cikin hayyacinta sai suka kira ni cewa naƙuda ta tasowa Hafsatu amma sun kai ta asibiti, sun kira ni ba su same ni ba amma har ta haihu ɗan bai zo da rai ba. Har an binne shi.
"Daga yanayin yadda suke ba ni labarin sai na ji ban yarda da su ba, kuma batun kira tabbas sun kira ni a lokacin da muke meeting. Dalilin da ya sa ban ji kiran ba na saka wayata a silent sai da na fito na ga kiran, kafin na kira sai na ga sun sake kirana. Cikin sanyin jiki na zo asibitin na tarar da Hafsatu a kan gado tana barci, yayin da ta farka aka shaida mata cewa ba ta haihu da rai ba, sai da ta sha kuka sosai ni ne na rinƙa ba ta haƙuri tare da kwantar mata da hankali duk da ni ma abin ya taɓa ni sosai sai dai na miƙa duka lamurana ga Ubangiji wataƙila hakan shi ne mafi alheri a gare mu. Bayan sati guda ta samu lafiya sosai muka dawo gida.
"Amma kullum Hafsatu a cikin damuwa take, tilas na dawo zaman gida na rinƙa kwantar mata da hankali har ta manta da batun haihuwar da ta yi ba rai.. Bayan wasu watanni ina zaune a falona da safe sai ga Dije amintacciyar ƴar aikina ta shigo cikin falona fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye.. Cikin tashin hankali na hau tambayarta abin da ya faru take kuka, nan ta durƙusa a gabana tana kuka tana faɗin na yi mata afuwa na yafe mata ta ci amanata.
"Cikin rashin fahimta nake tambayarta abin da ya faru, kuma wanne laifi ta yi mini. Sai da ta share hawayenta sannan ta fara faɗa min duk abin da ya faru tun daga lokacin da Hafsatu ta fara naƙuda har zuwa sanda ta haihu da barazanar da matana suka yi mata cewa idan har ta tona musu asiri sai sun kashe iyayenta da suke ƙauye, kuma ita ma sun hallaka ta.. Cikin kuka ta ƙarashe da faɗin 'Wallahi Alhaji babu hannuna a cikin lamarin nan, ina son iyayena ba na son na rabu da su shi ya sa na kasa sanar da kai gaskiyar abin da ya faru. Kuma wallahi duk kuɗin da suka ba ni a matsayin cin hanci suna nan a cikin ɗakina ko naira biyar ban taɓa ba.' Wani abu na ji ya zo ya tsaya mini a zuciya kamar ƙashi a maƙoshi, na ji wani irin fushi da ɓacin rai suna taso mini daga can ƙasan zuciyata..."
Hussain Yusuf✍️