6
by @oumfatima33
💓MATAR MANYA💓
By
KANSA'U BELLO
(OUM FATIMA)
GAJEREN LABARI
PAGE 6
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
Cikin sanÉ—a na shiga zauren gidanmu ina takawa cike da taka tsan-tsan sabo da ko da wasa bana fatan wani ya gano yanayin da nake ciki, addu'a nake kar Allah ya haÉ—a ni da kowa har in shige É—akinmu duk da nasan da wahala hakan ta kasance sakamakon gidanmu daya kasance na shige da ficen mutane sabo da sana'ar Baba Mari ta abinci. Ga kuma biki da za'a yi na Æ´aÆ´a uku wanda tuni Æ´an'uwa na nesa suka fara hallara.
Addu'ata bata karɓu ba don kuwa ina gab da shigewa ɗakinmu na ƴammata naji muryar Mama tana faɗin "Zo nan Salamatu." Wani irin tsinkewa gabana yayi ya faɗi da jin kiran nata domin kuwa na san tambayoyi ne zata tsare ni dasu waɗanda zasu sa ta iya gano abinda nake ɓoyewar idan aka samu kuskure ko yaya. Gyara tafiyata nayi sosai na daure duk irin azabar da nake ji kuwa na shiga takawa cike da ƙarfin hali zuwa gaban Mama data tsare tafiyar tawa da ido tana kallo na.
"Daga ina kike? Ina kika je baki dawo ba har irin wannan lokacin." Shiru nayi na kasa bata amsa ina tunanin inda zance mata naje.
"Dake nake Salamatu, nace daga ina kike!." Ta faÉ—a a tsawace zuciyarta na dokawa da tsoron abinda ke kai kawo a cikinta. Da in-inar rashin gaskiya nace "Gidansu Kairiyya naje fa Mama." Hannuna ta warta ta jani cikin É—aki ganin wasu daga cikin Æ´an'uwan Baba Mari sun fara fitowa don ganin abinda ke faruwa.
"Ƙarya kike yi ba gidan su Kairiyya kika je ba don Kairiyyar tazo neman ki, wai me kike so ki zama ne Salamatu me kike son maida kanki ne? Zaki faɗa min ko saina taka wuyanki a wurin nan!." Mama ta faɗa ɓacin ranta na ƙara bayyana.
"Meke faruwa ne Yaya?." Aunty Zaliha da shigowarta kenan ɗakin ta tambaya. Bata bata amsa ba sai hannuna danake ta ɓoyewa cikin hijabi ta warto tana faɗin "Uban miye kike ɓoyewa?." Bata tsaya jiran amsata ba ta shiga buɗe boxs ɗin data fito dashi daga cikin hijabin nawa sai ga danƙareriyar sarƙar zinari da ƴankunnenta da awarwaraye wanda Alhaji ya bani a matsayin gift ɗin aurena.
Salati Aunty Zaliha da muke kira da Aunty Zali tayi tana dudduba sarƙar tace "Yaya gold ne fa!."
Da kallo nabi sarƙar nima don tunda ya bani ban buɗe ba sai yanzu, mamaki da daɗi suka cika ni lokaci ɗaya ina jin idan ban auri Alhaji ba na tafka asarar da ba zan taɓa mayarwa ba.
"Daga ina wannan ɗin?." Mama ta tambaya tsoro na cika mata zuciya. "Kar dai ace yarinyar nan mutuncinta ta sayar akan kwaɗayin abin duniya Zahiha na shiga uku!." Mama ta faɗa tsoronta na bayyana ƙarara. Gabana dukan tara-tara kawai yake na tsoron kar Mama ta gano ni don duk rashin jina ban taɓa sadaukar da mutuncina ba sai yau shima ba da son raina ba duk da na gamsu da dalilin Alhaji na aikata min hakan da yayi.
"Kinga Yaya mubita a hankali tayi mana bayani kar kisa mutane su fara zargin wani abu kin san ba ƙaunarki Mari da danginta suke ba, yanzu sai su samu abin faɗa suyita yayatawa." Aunty Zali ce mai maganar tana kama hannuna ta zaunar da ni.
"Salma waya ya baki wannan sarƙar?." Aunty Zali ta tambaye ni.
"Alhaji Murtala dala ne ya bani ita a matsayin kyautar aurena." Na faÉ—a cikin dakiya.
"Me kika bashi da ya iya maki wannan kyautar?." Ta kuma tambaya fuskarta ba alamun wasa.
"Ba abinda na bashi Aunty, kawai sona yake tsakani da Allah shi yasa ya bani."
"Meye ya samu ƙafarki kike tafiya da ƙyar?." Mama ta tambaya zuciyarta cike da tsoron amsar da zan bata.
"Faɗuwa nayi a ƙofar gida da zan shigo shine naji ciwo a ƙafar." Na faɗa ina fatan ta yarda kuma kar ta ƙara min wata tambayar. Ba don ta yarda ba ta ƙyale ni suka shiga yi min nasiha ita da Aunty Zali wacce take shiga ta dama tana fita ta hagu don ko kaɗan banji zan iya zama a gidan Suhail ba bare na masa biyayyar da suke faɗar don ni kaɗai na san mai na shirya masa. Ba ƙaramar dauriya nake ba don duk jikina ba daɗi so kawai nake su sallame ni in je in kwanta ko zan ji dama.
Tamkar Aunty Zali ta shiga zuciyata kuwa tace "Je ki kwanta ki huta." Kamar jira nake na miƙe ina cije bakina duƙa zan ɗauki sarƙar Mama ta wurga min wani mugun kallon da yasa na ajeta ta ba shiri ina tura baki na fice a ɗakin. Ajiyar zuciya Mama ta sauke bayan wucewar ta ta kalli Aunty Zali tace "Anya kuwa Zaliha yarinyar nan ba zuwa tayi ta sayar da mutuncinta ba? Zuciyata ta kasa samun nutsuwa da yanayin da na ganta!." Mama ta faɗa cikin damuwa.
"Ba abinda ya faru in sha Allah Yaya kici gaba da mata addu'a kairan in sha Allah."
"To Allah ya kyauta." Mama ta faɗa tana ɓoye sarƙar da niyar in Baba ya shigo zata nuna masa duk hukuncin daya yanke a kanta shike nan.
Ina samu na shige ɗakinmu na kwanta saman shimfiɗata ina sauke ajiyar zuciyar kuɓutar dana samu, har cikin zuciyata ban so na rasa martabata ba tare dana shiga gidan Mijina ba amma ba yanda zan yi mai faruwa ta riga ta faru kuma Alhaji ya tabbatar min da cewar ba wata matsala ina fitowa zai aureni. Ruwan zafi nake son shiga ko zanji daɗi kamar yanda Alhaji ya ce nayi amma ba dama sabo da ban san inda zan samu ruwan zafin ba kuma ban isa in tambaya ba don zan iya jawowa kaina abin zargi.
Ranar haka na kwana jikina na min ciwo ko isasshen bacci ban samu ba.
★ Washe gari da sassafe na tashi na ɗebi ruwan zafin da Mama ta ɗora na shiga wanka na gada jikina sosai kafin na fito, sai da na gama shirya wa naje ɗakin Mama nace ta bani maganin ciwon jiki in sha ƙafata na min ciwo. Maganin ta bani nasha na kwanta saman gadonta nan da nan bacci ya ɗauke ni.
****** Tuni an fara gudanar da biki su Sajida sun shirya bridal shower da yini sai walima, da ƙyar da rarrashi su Aunty Zali da su Kairiyya suka shawo kaina na shiga cikin amaren aka ci gaba da gudanar da bikin tare dani.
Sanin da nayi aure ba fashi dole sai an ɗaura yasa na saki jikina bisa shawarar da zuciyata ta bani na in kwantar da hankalina a gama komai tunda na san ina da shirina a ƙasa. Mamaki sosai ya kama Mama ganin yanda na sake duk da daure wa nake jikin bai gama warware wa ba, ta san dole da abinda na shirya tun da tafi kowa sanina ita ta haifeni don haka ta zaunar dani ta tambayeni "Idan da wani abu a zuciyarki tun wuri ki fitar dashi Salamatu don na san wannan shirun naki ba yana nufin kin haƙura kin amshi Suhailu ba."
"Ni ba abinda na shirya Mama, kawai gani nayi Baba bazai fasa aura min shi ba shi yasa na haƙura."
"Kin tabbata har cikin zuciyarki kike wannan maganar?."
"Eh Mama."
"Shike nan Allah ya maki albarka." Ta faɗa cikin jin daɗi. Tun daga nan Mama da Aunty Zali suka riƙa bani abubuwa ina sha na gyaran jiki, yayinda nake jin tausayinsu a kan hakan sakamakon na san ba zan kai abinda zasu yi alfahari dani ba.
Sosai Suhail yaji daÉ—in yanda na sake ake hidima dani duk da bana sake masa fuska bai damu ba yace akwai lokaci, abinda ya faru tsakanina da Alhaji kuwa na barshi sirri a cikin raina don ko Kairiyya ban sanarwa ba duk amintarmu duk kuma yanda ta bincike ni akan sauyin da taga nayi ban faÉ—a mata komai ba bayan abinda na faÉ—awa su Mama.
Anci gaba da gudanar da biki cikin kwanciyar hankali don banyi komai da zai tadawa Mama hankali ba har aka É—aura aure ranar Asabar.
**** Lokacin da aka sanar da ɗaurin auren a speaker masallacin ya kai goshinsa ƙasa yayi sujjadar godiya ga Allah, yana ɗagowa yace "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Finally Salma ta zama mallakina bani da sauran fargabar rasata har abada." Suhail ne mai wannan maganar cikin tsan-tsar farin cikin da yake ciki na mallakar wacce yake tsananin so.
Sanye yake cikin dakakkiyar farar shaddarsa da taji ɗinkin shakwara da jamfa, yayi matuƙar kyau ya fito a cikakken angonsa sai fara'a yake abokansa na masa tsiya "Daga yau dai kuka ya ƙare akanta an riga an baka." Abokinsa Jalal ya faɗa yana kai masa dukan wasa, "Yes everything has gone in sha Allah." Ya faɗa yana jin sanyi a zuciyarsa.
Raharsu suka ci gaba dayi irin ta abokan ango har aka gama watsewa suka É—unguma zuwa inda zasu yi walimar da abokansa suka shirya masa ta cin abinci.
****A can gidan su amare kuwa ƴan ɗaurin aure na dawowa suka sanar da an ɗaura gida ya cika da guɗa yayinda naji tamkar wani dutse mai nauyi ne aka ɗora min saman ƙirjina. Shike nan duk wani tanadina ya rushe, duk wani tsari da nayi na yanda zan gudanar da rayuwata a gidan aurena ya lalace.
Wani irin kuka mai ɗaci ne ya kufce min na fashe da shi ina kwanciya saman katifar da nake ta ɗakin matar ƙanin Babanmu da muke zaune a can nida ƙawaye na, su Sajida kuwa gidan wata maƙociyarmu suke nasu yinin don kowa da tawagarsa kuma babu wata kyakykyawar alaƙa tsakaninmu sai habaici da yada magana da muke wa juna. Kairiyya ce ta matso kusa dani ta dafa kafaɗata tace "Take it easy Bestie, everything will be fine in sha Allah." Ta faɗa tana daddaɓani alamar rarrashi.
"Zafi zuciyata take Bestie na tsani wannan auren ba irin wannan shagalin na shirya yi a bikina ba, ba irin wannan rayuwar na tsarawa kaina ba, ba ita nake mafarki ba Bestie, ba haka naso aurena ya kasance ba, baki ga irin gidan da Alhaji ya gina da sunana ba, ba kiga irin rayuwar jin daɗin daya tanadar min ba amma Baba yaƙi ya saursreni ya barni in huta."
"Haba Bestie ki kwantar da hankalinki mana ya kamata ki godewa Allah da irin ni'imar daya maki na samun Suhail a matsayin Miji, Suhail fa nagartaccen mutum ne yana da duk wasu qualities da ake buƙata wurin zaɓen Mijin aure. Ita rayuwar aure da kika gani zaman lafiya da kwanciyar hankali ake bukata a cikinta ba ƙyale-ƙyalen duniya ba, bako wane ƙyal-ƙyali bane kake hangowa daga nesa idan kaje kusa dashi ka same shi a yanda kake tunani ba, ni dai ina baki shawara kada ki butulcewa ni'imar da Ubangiji ya maki, ki gode masa sai ya ƙara maki."
Shiru nayi ina saurarenta ina kuma saka magan-ganunta a ma'auni, tabbas gaskiya take faÉ—a min amma sai dai banji zan iya É—auka ba sabo da zuciyata ta riga da ta bushe da wan can tunanin.
Da haka aka ƙaraci yinin bikin zuciyata ba daɗi don ko anguna da suka zo ayi hotuna ƙin fita nayi sai da su Kairiyya suka dage da ƙyar na yarda na fita.
Ana gama sallar magriba motocin ɗaukar amare suka zo, dukan mu aka shirya aka kaimu ɗakin Baba don muyi masa sallama daga nan kuma a miƙa kowacce ɗakin Mijinta kamar yanda naji ana faɗa....
Akwai complete document a Naira 300
***
Oum Fatima