Page 36
Page 36
....."Bawan Allah, idan ba damuwa in tambaye ka ma na na ga mutanen sun taru cirko-cirko a wurinnan wani abun ke faruwa ne?",cewar Nurain da ya k'araso gurin yanzu.
Wani kallon banza mutumin da ke tsaye a wurin yai ma sa kana ya ce,"Kar ka raina min hankali ya za ai ka ce ba ka san abinda ya ke faruwa a fad'in Garinnan ba sai ka ce ba a ciki ka kwana ba alhalin labari duk ya karad'e kowanne lungu da sak'on".
"Da gaske na ke ban san abinda ya faru ba, yanzu na shigo cikin Garin".
"Ohwo Halan kai bak'o ne a cikin wannan Garin?".
"Eh ni d'an kasuwa ne shigowata cikin Garin kenan na ga mutanen sai gungu-gungu su ke".
"Wani mutum ne ya gudo daga cikin kurkuku tamkar mahaukaci haka ya ke ya yi muguwar 'barna a cikin Masarauta,ya,kashe mutane da yawa hakanan nan ya zo wannan mashayar ya haddasa ma su Gobara".
"Kaico labari bai yi dad'i ba Allah ya kyauta gaba,in ce dai sun kama shi ko?",Nurain ya sa ke tambayarsa don neman k'arin bayani.
"Ina fa ai wannan da k'yar zai kamu a wajen su domin yanda kasan Hawainiya ko Aljani haka ya ke saurin rikid'a ya ke,tamkar ba mutum ba haka ya ke ", yai k'asa da muryarsa ya na mai k'arewa da cewa," In fad'i ma ka wani sirri tsakar daren jiya na gan sa sai faman rangwad'a ya ke ya na tafiyar mata har wani lanlank'washewa ya ke".
Da wani irin sauri Nurain ya d'ago ya na kallonsa,kafin ya ce da shi komi sai da zuciyarsa ta raya masa kenan HARZAN,NARSHAD, AZEELA da AZLA sun bayyana a cikin garinnan tabbas akwai babban rikici da zai fara faruwa nan ba da jimawa ba, muryarsa har rawa ta ke wajen cewa,",Ka bari dan Allah yanzu ina ya nufa ?".
"Ban sa ni ba gaskiya amma na ji wai ance ,wai fa amma ya ga wasu mata ya bi bayansu har tsakiyar kasuwa da bisani Dakaru su ka far masu ya tarwatsa su daganan ban san me kuma ya sa ke faruwa da shi ba".
"Dan Allah za ka iya taimaka min ka nuna min hanyar da kasuwar ta ke".......
Da sauri mutumin ya katse shi da cewa ,"Lafiya na ga duk ka wani rikice sai ka ce kasan shi ko kuma dai d'an Uwanka ne,irin wannan rud'u da tashin hankali har ina?".
"Eh nasan shi farin sa ni ma yanzu haka a Garin mu neman sa a ke ruwa a jallo,Dan Allah ka fad'a min wanne 'bangare ne a cikin kasuwar in nufi can domin in samu tabbacin shine ko ba shine ba shin 'bangare dabbobi ko 'bangarem ma su saida hatsi ne ko kuma wani na daban ne".
"To me za kai idan ka tabbar da shi d'inne na san dai ba ka da jarumtar ko k'arfin damtsen da za ka tunkare shi".
"Hmmmm kai dai ai sha'ani wai an cuci bak'auye,kuma a bar kaza cikin gashinta ba tare da an figeta ba,amma bayan haka,ina mai tabbatar ma ka da sai na cizge kansa madamar zan yi Ido hud'u da shi".
Sakarce wannan mutumin yai da Idonsa ya na kallon Nurain irin Anya kuwa kasan me ka ke fad'a kuwa,da sauri Nurain ya d'ora da cewa duk dan gudun kar ya zargi wani abu,har da fara matso hawayen k'aryar ,"Kar ka so ka ga irin kisan gillan da ya yi ma 'yan'uwa da ahalina yai mu su munmunan kisan gilla ba tare da na samu damar ko kwarzanar fatar jikinsa ba,dan Allah ka taimaka min ko da bazan iya kashe sa ba,in na zubda ma sa da jini zan samu kwanciyar hankali da salama a raina".......
Dakatar da shi yai da cewa,"Ka ga bar kuka hakanan nasan irin haka akwai ciwo da rad'ad'i mai zafi in har ba ka rama ba ba za ka samu salama da kwanciyar hankali da ta ruhi ba,ma za tafi ya na 'bangaren kasuwar hatsi a can abun ya faru,ma za tafi can ".
Nurain ko tsayawa yai masa godiya bai ba, ya nufi Gurin a guje sai dai me sanda zai je duk mutanen Gurin sun watse ,sai fanga-fanga ya ke gami da guje-gujen nemansa ya ke amma bai ga kome kala-kalarsa ba da k'yar ya samu wata tsohuwa ya tambayeta ta nuna ma sa hanyar da su ka bi.
~~~~~~
"Tabbas abun dubana nan ya nuna min a matsayin wuri na k'arshe da su Gimbiya Junainah su ka tsaya ",Cewar Boka Dürsäås ya na mai samun wuri ya tsaya.
" Kamar ya Boka Dürsäås me ka ke nufi da wannan zancen na ka in har nan ne Gurin da su ka tsaya na k'arshe ina su ke to,Ina Jikata guda d'aya da na ke da ita ta ke, ina Gimbiya Junainah ta nufa,",Malikat Juwairiyya ta tambaye shi cikin marairaicewa da son sanin wanne irin hali Gimbiya Junainah ta ke a ciki.
" Ya Shugabata ba na iya cewa komi a yanzu ba sai dai in ce zamu iya k'arasawa Ga'bar kogin can domin mu bincika ko ta na can ko Jirgin ruwan da ta hau bai kai ga ta shi ba domin ina da tabbacin ba su yi ni sa da wannan Gurin ba ".
Tun kafi ya ida sa zance da ya ke Sarauniya Junayyah ta umarci wasu daga cikin Dakarun da su ka zo da su ,da su bazama zuwa Ga'bar kogin Nizla domin su duba su gani sauran kuma su warwatsu lungu da sak'on da ke wajen ko su nanan sun 'buya ba tare da an gansu ba, amma ina har su ka k'araci zagayen su ba abun da su ka samu haka su ka juyo su ka dawo sai lokaci mai tsawo da su ka 'bata amma ba biyan buk'ata.
A rikice Sarauniya Junayyah tai kam Malikat Juwairiyya ta na cewa," Yau ni na bani na lalace na d'aid'aice na shiga uku ina wannan Yarinyar ta nufa ,wanne waje ta je ta 'buya kaddai ace ta jefa kanta cikin wani tashin hankali da musiba ba tare da ta lura ko ta sa ni ba".......
Malikat Juwairiyya ce ta rufe ma ta ba ki ta ce da ita cikin muryar da ke nuna zallar tashin hankalin da ta ke a ciki,"A kul kar in sa ke jin kinyi irin wannan furcin ke fa uwace komi ki ka fad'a a kanta zai iya tabbata a gare ta, ya kuma zama gaske don haka kar ki sa ke fad'in wata kalma in har ba alkairi za ki fad'a akanta ba".
"To Malikat ya zan yi ina cikin musiba da tashin hankali rashin 'yata guda d'aya da na ke da ita,wanne irin zantuttuka ne ba za su fito daga baki na ba,ta na ina yanzu a ina zan mu sa me ta ,me ta ke aikatawa a wanne irin hali ta ke a ciki,ta ci abinci ko ba ta ci ba,ta na buk'atar wani abu ko ko?,duk ba mu sani ba,a cikin mu ba wanda ya ke da wannan amsar hatta ta inda za mu cigaba da nemanta ba mu sani ba".
"Ki kwantar da hankalin ki ba ga su Bokanya Azizah da Boka Dürsäås nan ba kuma ga tarin Dakaru nan mu na da su,ban ga amfaninsu ba in har ba su yi amfani da k'arfin damtsen,na gwanji har da na tsafi ko asirin su ba, su gano ma na inda su ke, a duk inda su ke sai mun gano su in har su na da ran su kuma su na taka doran duniya gami da shak'ar iskar da,ke k'adawa a cikin ta,sannan za mu huta".
Sarauniya Junayyah sai da ta share hawayen da su ka zubo ma ta kana ta ce,"Tabbas duk wanda a cikin su yai nasarar gano inda su ke ko ya kawo min su gabana zan ba shi kyautar wani yanki a cikin k'asar BAIBAH ina nufin zan ba shi kyautar wani 'bangare da ga cikinta ya je ya mulketa ta za ma tasa halak malak".
Ba k'aramin zaburar da Dakaru da bokayan da su ke tare da su Sarauniya Junayyah tai ba,da wannan furcin na ta ba.
Sai dai tun ba aje ko ina ba Bokanya Azizah ta da'bawa zancen wuk'a ta hanyar cewa,"Ki gafar ce ni ya ke wannan Sarauniya mai d'unbin dara da girma domin a hasashen da nai Gimbiyarmu Gimbiyar Masarautar BAIBAH ta na cikin wannan jejin na Irsaba tunda har an duba ko ina na fad'in wurinnan ba a ganta ba kenan ba makawa cikin dajinnan su ka shiga"......
"Ba ta da hankali ne ita Gimbiyar da za ta shiga cikin wannan Dajin ,ko ba ta san shi ba ne ba, Dajin Mutuwa shine lak'abin sa ta ya za tai kuskuren shigarsa ",cewar Malikat Juwairiyya a cikin matsanancin rud'u da tashin hankali.
Ita kuwa Sarauniya Junayyah ka sa iya cewa komi tai sai jikin ta da ya tsanan ta rawa," Allah ya huci zuciyarki ya sanya ya mi ki ita amma wannan lamari a bud'e ya ke in ma ba ki yarda ba sai in nuna miki tabbacin",ta k'are batun ta na mai fito da wani kullin maganin ta barbaza shi a ko ina na wurin nan ta ke sai ga sahun k'afafun su Yarima Haisam na bayyana har zuwa dai-dai saitin inda su ka fara takawa a cikin Jejin.
Ba tare da Malikat Juwairiyya ta jira komi ba ta umarci Dakarun su shirya su afka cikin Jejin domin su fiddo da su Gimbiya Junainah ta kowanne irin hali.
Da sauri Sarauniya Junayyah ta dakatar da su,"Kar wanda ya kuskura ya shiga cikin wannan Dajin domin aikata hakan babban zunubi ne da ka iya sake tak'alo yak'in da ba asan har yaushe zai tsaya ba".
"Ban gane me ki ke son cewa ba ko dai har yanzu kina kan bakan ki na nuna ma ta k'iyayya da rashin so da ki ke ma ta shin har yanzu ba ki hankalta ba,'bacewarta ba ta zama ishara a gare ki ba ?".
"Haba Malikat me ya kawo irin wannan maganar a irin wannan lokacin kin sa ni wannan Dajin ya na d'aya daga cikin dalilan da su ka assasa gami da ha'b'baka wutar gaba da ta k'iyayya tsakani k'asar BAIBAH da kuma k'asar BIHINAR, kuma abubuwa marasa dad'i duk sun faru a d'an wannan tsakin wanda sukan iya zama silar fara Yak'i tsakanin mu da su amma ba su biye ma na ba a wasu lokutan,a wannan karon kuma Babu tantama ba shakka muddin mu ka ratsa wannan Dajin ba tare da izinin ba jai tsaye za su d'auki hakan a matsayin hanyar takalar yak'i a tsaninmu da su".......
" Kin ga ki dakatar da wannan dogon sharhin da ki ke ,domin ba ganewa zan yi ,ba abinda na ke ganewa face in ji cewa in zo ga Gimbiya Junainah an ganota ban damu da ko ma me ka iya biyo bayan haka ba kawai dai ni batun Jikata kawi na sa kuma shi ne abinda zan tsaya sauraranka".
"Gimbiya Junainah za ta dawo amma fa sai kun bi komi a hankali,in ba haka ba wata sabuwar matsala sai ta sake kunno kai,domin dole sai da yarda ko sahalewa Sarikn BIHINAR kafin hakan ta yiwu ",....
" A taya kuma a ta wacce hanya hakan za ta faru ko ta kasance ,kun san dai ba yanda za ai mu tunkari k'asar BIHINAR da irin wannan batun,da wanne irin harshe ko baki za mu yi ma su bayani shin za mu ce Gimbiyarmu ta shiga cikin jejen bisa tsautsayi ko kuskure ne,ko-ko za za mu ce da su fursunan da mu ke da su sun tsere a hanyar su ta tserewa sun ci karo da Dajin su ka afka cikin sa bayan sun san mu na tsare da mutanen su a matsayin fursunoni, kuma har da d'an Sarkin su a ciki suma ba makawa za su fito farautarta su kamata su tsare kamar yanda mu ka tsare ma su nasu Yariman",Cewar Malikat Juwairiyya.
Sai da Sarauniya Junayyah ta nisa ka na ta matso kusa da Malikat Juwairiyya ta na mai sassauta murya da kwantar da ita ta ce, "Ya ke Mahaifiyata ki natsu ki kwantar da hankalin ki gabad'ayan mu nan mu na damuwa da halin da Gimbiya Junainah ta fad'a a ciki ba wanda bai son a samu mafita ko hanyar da za a ceto ta,sai dai hakan ba ya na nufin za mu cilla kanmu ko k'asar mu da mutanen cikin ta cikin wata musiba da tashin hankali ba,dole mu nemi hanyar da zamu bi domin mu ceto ta amma ba ta hanyar gaiyato ma kan mu Yak'i tsakanin mu da mutanen k'asar BIHINAR ba",........
Da sauri ta katseta da cewa," To miye abun tsoro a ciki ba muna da hazik'ai kuma jajurtattun jarumai da Sadaukai ba, a kira Yak'in ,Yak'in ya zo mun shirya in har hakan ne kad'ai hanyar da mu ke da ita wajen dawo da Gimbiyarmu zuwa Gida".
"A'a ba ran wanda zai salwanta in dai a kan ta ne domin su ma d'in mutane ne rayuwar su na da matuk'ar amfani da muhimanci, mai yiwuwa ma rayuwar su ta fi ta ta amfani,don haka a barta ta yi yanda ta so ina ji a jikina gami da tabbacin ba lalle ne ma ta fito da rai a cikin wannan Dajin ba ".
Wani irin bugawa k'irji Malikat Juwairiyya yai har sai da ta sa hannunta ta dafe saitin wurin ta ke nan zufa ta fara tsatstsafo ma ta, ta kowacce kafa ta jikin ta komi na ta ya dakata,tamkar wacce a ka buga ma guduma a saman kai.
" Junayyah kin ko san me ki ke cewa kuwa,anya kuwa kunne na ya jiye min abinda ki ka ce dai-dai, a bar 'yar ki ta cikin ki kwaya d'aya da ki ka haifa a cikin ki a cikin wannan Dajin ,'Yar ki ce fa kuma magajiyar KARAGAR MULKIN K'ASAR BAIBAH, Kuma Sarauniyar gobe,ita ce fa a cukin Dajin Irsaba,har ki na had'a ranta da na Dakaru hadimai ma su yi mata hidima wad'anda a an haife su ne kawai dan suyi ma ta hidima ,Wai me hakan ke nufi na ka sa gane manufar ki a cikin wannan zance?".ta k'are zance ta na faman waige-waige tamkar za ta ga amsoshin tambayar da ta yi ma ta a fuskokinku mutanen da ke wurin.
Cikin Isa da tak'ama Sarauniya Junayyah ta matso kusa da ita sosai da sosai ta ce da ita,"Da gaske na ke ma ki ba wani rai ko kwaya d'aya da za a salwantar in har a wajen neman ta ne, ko a tashin hankali mutanen k'asarnan da hana su neman abincinsu, ko a jefa su cikin firgici da rud'u in dai a kan ta ne, ta je can ta k'ara ta a can, Allah ya sa ma wasu namun dajin su cinye ta kowa ma sai ya huta da rashin kunya da fitsararta".
"Anya kuwa abun da na ke ji da gani gaskiya ne,ina mamaki wai yau 'yar cikina ce ke musayar yawu da ni kamar ma ta na shirya ko yunk'urin yin fito na fito da ni,ko don kina ganin ke ce a matsayin Sarauniyar da ke mulki a yanzu, ko don kin ga yanzun ke ce a kan KARAGAR MULKIN K'ASAR BAIBAH ne shiyasa har ki ke k'ok'arin aikata abinda ki ka ga dama to bari ki ji har yau har gobe ruwa na maganin daud'a,kuma jiya ba yau ba ce ba,kuma a dad'e a nayi sai gaskiya ina da hanyoyin da da dama da zan yi amfani da su in kai ki k'asa ba tare da kin sa ni ko kin farga ba,tun wuri ki mai da hankalin ki a jikin ki,ki san me ya kamata ki aikata da wanda bai kamata ki aikata ba,ko da yarda ko ba yarda ki ni zan shiga in fiddo da ita ni na rasa wacce irin gaba da tsana ce a tsakanin ku?, in kuwa ba haka ba za ki yi mutuwar kasko k'asa wanda ba zai ta'ba faruwa ba ko kuma ki yi fargar jaji".........
"Fargar jaji kuma ai wannan ke ce ki ka yi ta tun ranar da ki ka nad'a 'yarki a matsayin Sarauniyar ko magajiyar KARAGAR MULKIN K'ASAR BAIBAH to a tun ranar kuskure tare da tarin nadama su ka kawo ma ki ziyara".......
Wata irin cakuma Malikat Juwairiyya ta kai ma Sarauniya Junayyah cikin k'araji ta ke cewa,"Me ki ke son ki ce da ni,wace ce ke Ina 'yata ta ke me ki ka aikata ma ta?".
da k'arfi Sarauniya ta 'ban'bare hannayen ta a jikin ta ce da ita ,"Ai kin ma karo domin yanzu lokaci ya k'ure ma ki, don haka sai ki tara hannayen ki hannu bibiyu ki kar'bi abinda k'addara ta zo ma ki da shi,don nan ba da jimawa ba za ki tsinci kan ki a jerin ko layin mabaratan k'asarnan,k'asarnan da ki ke tunk'aho gami da nuna girman kai da d'agawa a kanta za ta dawo mallakin ahalin ko tsatson k'asar KALISTA ba tare da kin fargaba "duk ta na wannan maganar ne a hankali yanda ba wani da ke wurin zai iya jin abinda ta ke cewa.......
Wani uban ihu Malikat Juwairiyya ta kwarma gami da zaburowa ta yo kan Sarauniya Junayyah da sauri Boka Dürsäås ya nuna ta da 'yar sandar da ke hannunsa sai ga wata iska ta fito da ga ciki ta fara katantanwa da Malikat Juwairiyya da ga k'arshe kuma ta bugata da wata bishiya da ke kusa da su,ko motsin ba ta sa ke yi ba.
" Ka yi min dai-dai ya kai Kawuna ma za ku kuma ku nannad'eta a cikin wani abun yanda mutanen Gari ba za su gane kome a ciki ba,sannan ku nufi Masarauta da ita",ta k'are zancen ta na mai fuskantar Dakarun tare da d'orawa da cewa ,"Ita kuma waccan Allah ya sa tagamu da Zaki ko Kura su cinye ta mu huta da k'aya gaba ki d'aya "......