KARAGAR MULKI

Page 38

by @cwtsumiey19988

Page 38

" Nnnn....Nnnn.....ni kuma me ya same ni in ce dai ban cutar da ke ba ko?",ya na maganar ya na dudduba jikin sa ko zai ga sauyin yanayi a jikinsa wata k'ara ya sa ki a razane sakamakon kai hannunsa saman wuyan sa da yai ya ji abun wuya a jiki,ba tare da ya ce komi ba ya fara ja da baya ya na k'ok'arin barin inda su ke ....rufa mi shi baya tai cikin wani sabon firgicin "Ka dakata,ina za ka kar ka je ko'ina,ka dawo".
" Ba ni ne zan dakata ba ke ce za ki dakata kar ki kuskura ki k'ara matsowa kusa da inda na ke, domin ni ba ni da hankali,macuci ne,zan iya cutar da ke harma in illatar da ke".
"A'a wannan ba gaskiya ba ne kai ne ka ke jin hakan a cikin rai da zuciyarka,ko ka manta tun farkon had'uwata da kai taimakona ka fara yi ta ya yanzu kuma daga baya ka ce za ka cutar da ni,rayuwar ka gabad'aya ka sa ka a cikin halin k'ak'anikayi a saboda ni ko ka manta hakan ne?".
Har yanzu bai dakata da k'ok'arin barin wurin ba cikin zafin naman da Allah ya halicce shi da shi,Gimbiya Junayyah har da Kuyanga Jazila sai faman binsa su ke.
"Wannan a da kenan amma a yanzu kuma a halin da ake ciki ,ba abinda zan iya amfana ma ki da shi face in cutar da ke ni d'in tamkar dabba haka na ke,ke in tak'aice mi ki dabba ta fi ni hankali da muhimanci da kuma amfani,domin ita ba ta cutar da d'an'uwanta"......
Da sauri ta dakatar da shi da cewa,"Dan Allah ka dakata ka bar fad'in irin wannan mugayen maganganun a saman bakinka saboda me za ka rik'a had'a kan ka da dabbobi, Alhalin Allah da ya halicce mu ya ce ba wata halitta a doran duniya da tafi muhimanci da daraja Sama sa mutum,ko ka manta a cikin mu a ka halicce Annabin rahama,Annabin ceto Annabin da babu kamarsa kuma mafifici akan kowacce halitta da kuma sauran komi da komi na duniya Gabad'ayanta ?",ta k'are zancen muryarta na raunana,tamkar wacce ke san tsaga zuciyarta ta nuna ma sa halin da ta ke a ciki.
Jikin sa ne yai wani irin sanyi sakamakon sauraronta da yai lokaci guda kuma sai sa ke birkicewa yai,ya na mai girgiza ma ta kansa gami da cigaba da ja da baya,ya na mai nuni da hannunsa d'aya alamun ta dakata ta daina biyo sa,"Ba ki san koni waye ba shiyasa ki ke fad'in duk abinda ya zo mi ki a bakinki to ni tamkar shed'ani haka na ke,ko in ce annoba mai fasa taro ko gungun mutane,ni wofintacce d'a ne abun korewa da gudu GA iyayensa,wanda ba a maraba da haihuwarsa ko kasancewarsa a cikin Ahali, Ko acikin dabbobi ba kowacce dabba ce ke cutarwa ko kashe 'yar'uwarta ba ,bare harta shirya ko k'ok'arin yin fito na fito da Mahaifiyar ta ba".
Ya dakata sakamakon bugun zuciyarsa da ya tsananta numfashin sa ya sark'e,take ya fara tari gami da yunk'urin fad'uwa k'asa,kusan rige-rigen tarbe shi Gimbiya Junainah da Kuyanga Jazila su kai amma ina hakan ya gagara domin nauyinsa da kuma k'arfi ba d'aya ba ya sa ya rinjaye su sai gashi su duka sun fad'i k'asa .
Gimbiya ce a k'asa shi kuma ya na sama sai Kuyanga Jazila da a kai watsi da ita can gefe, da k'yar suka iya d'aga shi su ka tashi zaune,duk da hakan son cewa wani abu ya ke amma halin da ya ke a ciki ya hana shi ,shi kuma ya kasa iya hak'ura da abinda ya ke son cewa ba.
"Dddd....Dddd.....Da kaina,n....ni dai kuma da wa'innan hannayen nawa na kashe su,na kashe su har lahira na yanke ma su jin dad'in rayuwar su na basu mutuwa mafi tsanani da azaba"....
"Ka kashe su waye kuma a inane ?",Kuyanga Jazila ta tambaye shi a d'imauce,Kasa iya cewa da ita komi yai sai tsurawa fuskar Gimbiya Junainah idanu da yai har na wani lokaci,har Kuyanga Jazila ta kasa hak'uri ta sa ke tambayarsa.
Sai da ya tashi zaune sannan ya ba ta amsa da cewa,"Ummata Mahaifiyata,wacce tai silar zuwana duniya ta sha wahalal rainon cikina rauni akan rauni ta zo haihuwata taci bak'ar azaba tamkar za a zare ranta ya bar gangar jikinta, amma a haka ta daure ta cije har sai da ta haife ni, ba tare da ta tayi la'akari da wannan wahalal da ta sha ba,ta nunan soyayya,kuma ta fifita ni a kan karanta ,ba ta ci sai na ci ba ta barci har sai in ni na yi barci,ba ta walwala ko farinciki sai ni ma in ina walwala,idan ba na da lafiya ta kan zauce ta d'imauce ta ji tamkar ta mai do da ciwon a jikina ,ta ji ina ma da za a bata damar da za ta maido da ciwon a jikinta da ta aikata hakan da gaggawa, idan ka ga tayi dariya to ni ne nai dariya,idan kuma nai kuka duk sai ta firgice da diririce ta ma rasa me za tai ,ta lallasheni ta riritani,ta shayar da ni,ta tufatar da nii "......ya fashe da wani irin kuka wanda ya ke fitowa jai tsaye daga can cikin k'asan zuciyarsa, kuma ya ke fallasa duk sirrin da ke binne a  cikin ta,".....
"Amma duk da haka ba tare da na duba wad'annan tarin alkairin nata a gare ni ba na sa wad'annan banzayen hannayen nawa na kashe ta da kai na,na kashe ta ita da k'anwata",..... Kuka ya ci k'arfin sa, da wani irin sauri Gimbiya Junainah da Kuyanga Jazila su ka mik'e tsaye suna mai zuba ma sa idanu,da sauri tamkar wacce wani ke shirin rigan yin magana haka Gimbiya Junainah ta fara magana.
" Ban yarda ba,ban yarda ba,ban yarda ba Kuyanga Jazila,ta ya d'a zai kashe Mahaifiyar sa,wacce ta sadaukar da Komi na ta domin shi ya ya rayu, ta ya hakan za ta kasance? ".
" Nima dai shakku ya d'arsu a cikin rai da zuciyata,ko a tarihi ban ta'ba jin makamancin wannan labarin ba,ko da d'an shege ne d'an gaba da fatiha ban ta'ba jin ya kashe Mahaifiyar da ta kawo shi duniya ba balle wannan har da k'anwarsa,anya shugabata ba d'aya daga cikin makaran da ke jikinsa ba ne ke k'ok'arin raina mana hankali ba ?"....
"Ku yarda da ni gaskiya na fad'a ma ku,shiyasa na ce ku yi nesa da ni,a kowanne hali a kowanne lokaci zan iya cutar da d'aya daga cikin ku,Mahaifina ma ya wofintar da ni ya kore ni daga inda ya ke saboda jin tsoran zan sa ke cutar ma sa da wani,to me zai sa ku ba za ku ja baya daga gare ni ba?".
"Har da hakan ya jefa min sakku a kanka waye mahaifin na ka ,Anya ya na da Nagarta da jamala kuwa ?,don me zai wofintar da d'an shi saboda wani dalili ai hannunka bai ta'ba ru'bewa ka ce za ka yanke ka yar,Mahaifine fa shi,bai kamata ya aikata hakan ba,duk da akwai abinda addini ya sharrand'a ka zare hannunka akan d'anka in har ya na aikata su amma ban da lalura ban ciwo ".
Wata irin dariya yai wacce tafi kuka ciwo kafin yace,"Mahaifina mutum ne d'aya da d'aya,kuma ko a haka ina alfahari da shi domin ina da tabbacin Mahaifiyata sai da natsu sannan ta tantance kafin ta za'be shi a matsayin wanda zai zama uba a gare ni,tabbas ya amsa sunan sa uba na gari kuma na kirki,kuma jajurtaccen Namiji fiye da yanda zan iya yi ma ku bayani Mahaifina ya Kai kuma ya wuce haka,domin har yanzu har gobe,ke har ma goben-goben inaji da shi kuma ina alfahari da shi har can cikin k'asan zuciyata".
"Na kasa gasgata zancenka,in haka ne ya akai ya bar ka,a haka ya bar rayuwar sakaka ba tare da kulawa ko damuwa da ko da da lalurar da ke damun ka ba?Ina so in yarda da duk abinda ka ke ce amma zuciyata ta kasa gasgata ko aminta da  hakan",Cewar Gimbiya Junainah.
"Za ki yarda har ma ki amince da ni matuk'ar nai ma ki cikkaken bayanin yanda Komi ya faru"," Zan so haka matuk'ar za ka iya ba ni la barin komi yanda ya faru ",ta  ce da shi ta na mai matsowa kusa da shi.
Da wayau da dabara ya ja baya,sannan ya kwashe labarin yanda komi ya kasance,tun kafin ya k'arasa su duka biyun ke faman zubar da hawaye ,amma bai yarda ya ce da su shi d'an Sarauta ne ba,bai nuna na su ko shi waye ba,ya dai ba su kabarin kawai.
Har ya kai k'arshe sannan Gimbiya Junainah ta ce"Wannan ai rashin fahimta ce da kuma tsatsan rashin tausayi da me mutum zai ji da lalurar da ya ke fama da ita ko-ko da zafin abinda ya aikata ko kuma da juya ma sa baya da akai, ciki har da mahaifin da ya haife ka kuma to a ta ya mutum zai iya samun k'warin gwuiwar da zai d'auki k'addara ko jarabawar da aka d'ora masa".
" Ni ma dai haka na gani duk wani mutum mai hankali in har yai duba na tsanaki a wannan labarin ba zai d'ora laifin akan sa ba tunda kowa ya sa ni kama tunda ga kan tsintsaye, k'warin,dabbobin gida da na daji ba wata halitta da ba ta san girma ko darajar Uwa mahaifiya ba, haka ma kuma soyayyarta da sadaukarwarta ga abinda ta haifa,ta ya wanna abun da ta haifa zai iya cutarwa ko ya illata ta balle har ya kai ga kasheta har lahira?".
"Gane min hanya Wai makawo ya so gulma,jikina na ba ni dole akwai lauje cikin nad'i a wannan labarin domin dai na san ruwa ba ya tsami hakanan banza".
"Kar ku yi k'ok'arin sauyawa labarin suna ko ku sauya ma sa ma'ana ku barshi a yanda ya ke, ku nemi hanyar da za ku tsira daga gare ni ko kwa samu damar da za ku cigaba ba da rayuwa domin ni d'in tamkar dabbar dawa haka na ke, ko kusa ko da wasa ban san na Gida ba,bare in daga ma sa k'afar,ni kaina ma cutarwa na ke balle wani wanda na ke tare da shi,Na fi hawainiya saurin rikid'a ya zuwa mabanbanta kaloli launi-launi".
Ya kasa k'arasowa sakamakon rufe ma sa baki da Gimbiya Junainah tai da hanunta ta na mai cewa,"Ba dabbar dawa ba, ba saurin rikid'a kamar hawainiya ba,Kai ko da zan ga k'aho ya tsiro a tsakiyar kwakwalwar kanka ba zan gudu in ba ka wuri ba zan kasance da kai a cikin kowanne irin hali na dad'i ko akasin haka,zan sadaukar da tawa rayuwar kamar yanda kaima ka tashi sadaukar da ta ka rayuwar a kaina"......
Tureta yai da k'arfin gaske har sai da ta kai ga fad'uwa k'asa,ba tare da ya jinkirta ba ya d'ora da cewa, "Ba ki da hankali ne,ya ina gaya ma ki ga yak'i ke kuma ki na cemin ga k'ura,ba burina in sa ke kashe ki da hannu na ne ba,a karo na biyu bs, a'a burina in sa ki cikin farinciki, in k'are ki,in ba ki kariya a duk sanda buk'atar hakan ta taso,babban burina in ga kin rayu har zuwa tsufan ki ,inga 'ya'yan ki tunda ban samu damar ganin na Mahaifiyata ba ,amma ke da alama so ki ke ki kashe ni,ko ki binne ni da raina".
A razane Gimbiya Junainah ta d'ago da niyar ta ce wani abu sakamakon jin abinda ya fad'a, amma ya dakatar da ita ya hanata damar hakan,Zarya ya fara ya na mai kai kawo" A saboda ke kwakwalwata sai karo ta ke ,Komi sai sa ke rikice min ya ke,ba na iya gane komi,ji na ke kamar in yi hauka".
Da wani irin gudu Gimbiya Junainah ta Isa wurin da ya ke,ta rungumesa ta baya ta ce da shi,"Me ka ke aikatawa haka,ko dagaske so ka ke ka haukace d'in,idan har dan ni ne ka kwantar da hankalin ka ba abinda zai same ni kai ma kuma ba abinda zai same ka,zamu rayu kuna mu kasance a tare lafiya lau".....
Ya sa ke katseta a karo na biyu da cewa,"Ba shine burina ba a yanzu na fi son ki rayu fiye da in kasance da ke,Idan ki na cikin matsala kawai ki kira suna na ,zan zo a duk inda ki ke in share ma ki hawayen ki kuma in ma ki maganin matsalar ki".
"Ni ma a yanzu ba haka na ke buk'ata ba da fari kai ka fara magiya har kana fad'uwa k'asa a kan in yarda in amince in taho tare da kai sai a yanzu da na ke son bin ka sai ka ce a'a to ba zai yiwu ba,idan kuwa ka ga hakan ya yiwu to sai in ka kalli fuskata cikin tsakiyar idanuna ka fad'a min matsayina a wurin ka ka gaya min wace ce ni a gare ka,da wanne irin Ido ka ke kallo na,domin gabad'aya na ka sa gane shin kai ne ka ke rikita ni ko ni ce ke rikata kai na da kai na".
"A'a kar ki ce haka dan Allah domin ni ba na da k'arfin zuciyar da zan iya cigaba da tafiya da ke alhalin ba na da ikon hana hai na shiga cikin duk wani yanayin da ya zo min ,kuma ba na da juriya ko zarafin da zan iya sanar da ke ko wace ce a wurina saboda ina tsoran za ki tsane k'arshe ma har ki hanani damar da zan sa je ganin ki"......
"Idan kai ba ka da k'arfin zuciyar d'aukar haka to ni ina da ita ka ba ni damar da zan nuna ma ka hakan a zahiri".......