Page 40
~Page 40
Tunda ya shigo ,harabar wurin ya ke ta faman sallama amma shiru ka ke ji tamkar ba alamun mutum a cikin Lambun, kasa hak'ura yayi ya cigaba da yin sallamar amma shiru ka ke ji Malam ya ci shirwa daga k'arshe ne ya yanke hukuncin idasa sa kan shi cikin 'bangaren da ta ke zaune kai tsaye, ya duba ko lafiya,tunda yanayin wurin ya nuna da akwai mutum a cikinsa,ko da ya shiga a kishingid'e ya iske ta saman kilisa da alama ta lula duniyar tunani ne shiyasa bata san da zuwan sa ba,har ya samu wuri kusa da ita ya zauna bata kula da shi ba,sai jin tafin hannunsa da tai ya na d'auke mata kwalar da take zubowa daga idaniyarta.
A dan firgice ta ja baya,sakamakon tsoran da ya kawo ma zuciyarta ziyara,ganinsa da tayi ne yasa tai ajiyar zuciya tana mai cewa," Yaya Zafar kai ne,yaushe ka shigo har nan ban sani ba ?".
Tsuru yai ma ta da idanu ba tare da ya ce da ita komi ba,har ta sa ke maimaita ma sa abinda ta ce a kara na biyu amma duk da hakan bai ce da ita komi ba,cikin yanayin shagwa'ba da ta mai da fuskarta da muryarta ta ce da shi,"Haba Yaya Zafar magana fa na ke ma ka tun d'azu,amma ka yi shiru sai faman kallona kawai ka ke,ko na yi ma ka wani laifin ne?",
Murmushin shi mai tsaya ma ta arai ya sakar ma ta kana ya ce da ita,"Ina mamaki ne wai dagaske wannan da take a gabana Gimbiya Hafsat ce,Kai in wani ne ya ce zata zama haka kai tsaye zan karyata shi,balle kuma in ga hakan a mafarki tuni zan farka ince soki burutsin mafarki ne,har sadaka zan iya yi don tsoran kar hakan ta tabbata zuciyata ta kasa amincewa da hakan,Ina jin zafi da k'unar ganin ki a cikin wannan yanayin".
Sai da ta fiddo da idanunta waje don mamakin zancen da ke fita daga bakinsa kana tace da shi," Bana son tsokana,kuma ma ni mai ya same ni da naji kana danganta ni da irin wannan zancen".
"Bazan 'boye ma ki ba duk kin fita daga kamanninki har ma da natsuwar ki kallo d'aya za ai miki a fahimci hakan daga gare ki,ko ma meye ya faru a baya ya riga da ya wuce kar ki bari ya rusa maki y'ar sauran rayuwar da ta yi maki ragowa a gaba,ki manta da komi ki zo ki yi rayuwar ki kamar kowa a cikin Gidannan ".
" Yaya ai na riga da na manta da duk abinda ya faru tun ba yanzu ba kuma ma ai".......Kasa k'arasawa tayi sakamakon kafeta da idanun da yayi.
"Kuma ma ai me?,Ki idasa mana ai shiyasa da na shigo naga kin rabka uban tagumi gami da zurfafa cikin duniyar tunani ko".
Kasa cewa da shi komi tayi,sai duk'ar da kanta k'asa da tai tana mai sake k'arfafa kukanta da ya kwace mata yanzu,tare da cewa,"Taya ka ke kallon sauk'in wannan lamarin, mahaifina fa wanda ya kawo ni duniya shine fa ya bada ni Aure ga d'an'uwanka na jini wanda ku ke Uba d'aya da shi,kuma har ka ce in manta da komi inyi rayuwa kamar yanda na saba abaya, natsuwa da kwanciyar hankalina ka ke so a wurina,a taya hakan zata kasance ba ma zai yiwu ba ?,kuma dad'in gushi ka ce da ni mahaifin ku ya fi karkata ga 'bangaren d'an'uwanka ai dole in shiga cikin tarin damuwa",
"To shine me,sai aka ce ki yi amfani da wannan damar ki jefa kan ki cikin wata sabuwar damuwa ko me,mutane nawa ne su ka fi ki shiga cikin matsin rayuwa ,wahala da kuma k'uncin ta,amma kuma duk da haka su ka d'aure su ka cije su na rayuwa a haka ba tare da mutane sun san halin da su ke ba, ki dubi wasu da ga cikin mutanen k'asarnan ma na wasu abincin da za su ci wahala ya ke mu,wasu wurin kwana wasu kuma lafiyar su gabad'aya a ka jarabce su akanta shin za ki yi duba da su ne ki d'auki k'addarar ki ne ko za ki d'auki hanyar da za ki illata kan ki ko ki kashe kanki ?",.
Duk jikinta ne yai sanyi kuma tai shiru,to ai in dai zata danganta kanta da wad'nnan da ya lissafo,dumuwar da take a ciki ba komi bace.
" Kiyi min magana Gimbiya Hafsat, domin na rasa ko na kasa gane asalin abinda ke a ranki da zuciyar ki,ya kamata ki manta da komi izuwa yanzu ,kije kiyi rayuwar ki kamar yanda kika saba,matuk'ar in ba so kike ki butulce ma Allah akan sauran ni'imomin da yayi maki ba, ki d'auki k'addara kamar yanda kowa ya d'auka kinji dan Allah, badan halinah ba".
Yanayin yanda ya kai k'arshen maganartasa ne gabad'aya ya k'arasa kashe mata dan sauran kuzarin da take dashi,ko motsin kirki ta kasa sai binsa da idanu kawai da take.
"Dan Allah mana kice dani wani abu ko yaya ne kinsan bana son shirunki,yace da ita yana mai langa'bar da kansa gami da yin fuskar tausayi tamkar yaron goye.
Murmushi k'arfin hali ne ya su'buce mata wanda hakan shi kuma ya dad'ad'a masa rai gami da sanya shi farinciki ko ba komi yai nasarar sauya mata yanayin da take a ciki koda na yanzu ne kawai,bai bar ta haka ba sai da ya sa hannunsa ya d'auko Ayaba guda d'aya daga cikin kayan marmarin da su ke jibge a gabanta ya 'bare ma ta ya mik'a ma ta ta kar'ba ba tare da tai masa musu ba kamar yanda suka saba ,saboda tana da tabbacin ba zai kyaleta ba,kusan gabad'aya yammacinsa anan ya k'arar da shi,kuma Alhmdllh domin an samu canji ,sosai Gimbiya Hafsat ta saki jiki da shi suka sha hirarsu,har sun mik'e zai tafi yaja ya tsaya yana mai sake zuba mata idanu ba tare da ya iya cewa da ita komi ba.
"Lafiya,wannan kallon kuma fa na mene ne?,ko tare zamu tafi ne?",ta ce da shi.
" Ina ma da za'a ce min hakan ai dana fi kowa farin ciki ,da hakan",ya ce da ita,fad'ar hakan ke da wuya da yai fuskarta tai saurin sauyawa sai ga hawaye sun fara kwaranyowa ma ta ta na cewa
"Na kasa jurewa da irin yanayin da nake rayuwa a yanzu,Zuciyata sai sak'a min abubuwa masu yawa kuma duk akanka ta ke".....
Katse ta yai da sauri," Ni kuma,ba dai maganar da mu ka gama yanzu ba ce ta dawo ba ko ?",kasa cewa dashi komi ta yi duk kuwa iya lallashin da ya ke ma ta ba ta iya tace da shi komi ba,har sai da ya fara nuna ma ta 'bacin ransa.
Da k'yar ta iya rik'e kukanta ta ce da shi,"Tsoro na ke ji ,ji na ke kamar idan ka ta fi ba za ka sa ke dawowa ba tamkar ba zan sa ke ganin ka ba,ina jin kamar iyayenmu za su yi nasara a kanmu,su raba mu rabuwa ta har abada".
"A'a Gimbiya Hafsat kar kisa iyayenmu a matsayin wani dalili da zai sa ko hana Aurena dake ,ina da yak'inin baza su ta'ba kasancewa kamar yarda kike tunani ba da so samu ne a gare ni kuma za ki ji ki yarda da duk abinda zan fad'a ma ki da mun bar wannan maganar na wani d'an lokaci,mu yi ta addu'ah mu ga abinda Allah zai yi,idan har mu kai hakan mu ka k'ara da yi ma iyayenmu biyayya tabbas za mu ci riba ko da ko ba mu kasance a tare da juna ba".
Da sauri ta d'ago ta na kallonsa muryarta na rawa ta ce da shi,"Mu rabu fa ka ce,mai ya kawo wannan kalmar kuma,ko dai ka hak'ura da ni ne ban sani ba? ".
" A'a wallahi ba haka na ke nufi ba,ina so ne dai mu bi komi a hankali"...."Banyarda da kai ba",ta fad'a ta na mai ja da baya,"Da abinda ka ke 'boye min tabbas dole da akwai wani sirri da ka ke k'ok'arin 'boye min".
"Subahanallah wanne irin tunani ne wannan ta ya za ki rik'a fad'in wannan maganar,wallahi ina son ki ,ina k'aunar ki ina son in rayu da ke in k'are ragowar rayuwata da ke".
Da matsanancin fushi ta tari numfashi sa ta da cewa,"Ya Isa haka kalaman yaudarar ta ka sun fara gundurata,ka dakatar da su,in ka na da wani sabbin ka fito jai amfani da su bismillah ina sauraren ka,zan daure kuma in jure in cigaba da sauraranka har zuwa sanda za ka gama,na lura da kai tunda wannan matsalar ta kunno kai tsakanin mu kullum sai k'ara ja baya ka ke da ni,ban sa ni ba ko dama ka yi maraba da hakan ne ko mene ne ban fuskarta ba".
Ba ki sa ke Zafar ke binta da kallo, sai ka ce,ba Gimbiya Hafsat d'in da ya sani ba,zuciyarsa rawa ta fara ,abubuwa da dama su ka fara kai kawo a cikin kwakwalwarsa, sosai ta zage sai faman fad'a ma sa duk maganar da ta zo kan ba kin ta ta ke,kuma har lokacin hawaye ne ke zubowa daga kan fuskarta,duk iya yanda ya so ta bashi dama ya lallashe ta hanawa tai,sai faman tutturjewa ta ke daga k'arshe ma cewa tai,Kar ya sa ke nuna ma ta fuskarsa,tunda dama zai iya rabuwa da ita ,ba tayi zato da tsammani haka daga gare shi ba,sosai ya ke lallashin ta tunda ya san ya yi mata laifi wanda zai iya ba ta dama ko ya bud'e k'ofar zargi a tsakaninsu,sau wajen uku ta na aika amintaciyar baiwarta akan ya zo ta na son ganin sa amma bai zo ba sai yau,kuma ga yanayin yanda yau d'in ta kasance a gare su.
Duk zancen da yake yi mata kasa cewa komi tayi ji take ina ma da zata iya dakatar da shi,Ina ma da tana da kalami ko zancen da zata fad'a masa da tayi hakan domin ta dakatar da shi ,ko ba komi a had'uwarsu da shi ya bata gudunmuwa mai tarin yawa a cikin rayuwarta,kasancewarsa mutum mai hankali da hangen nesa.
" Ko dai zuciyarki na kan d'an'uwana Zahir ne?",ya jefo mata da tambayar da ta rikita ta kuma ta sa ke jefata cikin wani sabon yanayin..
"Idan har haka ne ya kamata ki fito fili ki yimin bayani ta hanyar da zan gane ba wai kiyi ta yimin yawo da hankali ba".Ya jeho ma ta tambayar da sai da yai danasanin fitarta daga cikin bakinsa.
Jikin ta ne yai sanyi komi na ta ya dakata,hatta da bugun numfashin ta sai da ya dakata na wasu 'yan dak'ik'ai,miyan bakinta ta ne ma ta rasa,sakamakon bushewa da mak'okwaronta da yai,da k'yar ta iya samun damar fusgo numfashi da harshenta ta ce da shi"Babu daga kai har shi ba wanda zan aura tun da abun ya zo da haka,na fasa kowa ya je ya nemi wata fak'at,kuma wannan shine matsayata ta k'arshe ka na iya tafiya in ka gama",tana Kai wa nan tai juyawarta tai tafiyar ta.
Tana shiga ciki ta fashe da wani sabon kukan "wannan wacce irin musiba ce,take bibiyar rayuwata daga wannan sai wannan ba a gama magance matsalar Yarima Haisam ba sai maganar Aure ta biyo baya, bayan kuma tarin k'alubalen da kowa ke fuskanta a cikin Gidan,har sai zuwa yaushe komi zai zama dai-dai?".
Shi kuwa Zafar rasa me ma zai yi yayi hatta da hanyar fita sai da ya manta da ita bayan ya gama tsayuwar da zai yi ,ji yake ina ma da yana da damar da zai kamota ya rik'eta har sai ya fad'a ma ta asalin gaskiyar da ke binne a acikin ransa ya sanar mata ba abinda ta ji bisa saman harshensa ba,tuntu'ben harshe ne,wanda ba kowa ke iya tsallake shi ba,ina ma da ya iya yin tafiyar baya ya goge lafazin da ya yi,ya koma tamkar ma be fad'e shi ba, to da ba makawa sai ya yayi hakan ko kuma idan da da hali zai shiga cikin zuciyarta ko ya tsagata domin ya samu tabbacin matsayin da yake da shi a wajen ta sai da Ina hakan bazai yiwu ba,hasalima yasan ko damar ganinta bai zai sake samu ba dan yanzu.