Page 41
~Page 41
"Ba matsala Ciroma za mu zauna mu jira ya gama ganawa da su in ya so daga baya sai mu shiga mu duba sa d'in", Badiyya matar Waziri ce ke wannan bayanin sun zo duba jikin Me Martaba, sai su kai rashin sa'a ya fara ganawa da wasu daga cikin attajiran k'asar BIHINAR da suka zo duba jikinsa.
"Anya Umma ba za mu tafi muje mu dawo ba,ko kuma mu je sahen Sarauniya Mubina mu zauna zuwa anjima sai mu dawo,don za su iya dad'ewa fa",Cewar Zulfa.
"Ke dai ki ce min san jikin ki ya motsa ,ko kuma dama can da abinda ki ke son yi a shashen Sarauniya Mubina shiyasa ki ka biyo ni".
Murmushi ta fara sa ki gami da sa tafin hannunta ta rufe fuskarta ba tare da ta ce da ita Komi ba.
"Ja'irar yarinya mu je to,nima dama ina son ganinta domin akwai maganganun da na ke son mu tattauna da ita,kin san an ce in hagu ta k'i sai a koma dama".
Turo ba ki Zulfa tai gami da cewa,"Ummah me ki ke nufi da wannan maganar, ban gane ba,kar fa ki je ki aikata wani abun da zai jawo kwa'bar mu tai ruwa ?".
"Dad'ina da ke Zulfa shirme da shiririta ,in banda haka me ki ke tunanin zan aikata ,ki na ganin abinda ya faru jiya yanda Yaya Iyatu da Baban ki Waziri su ka ci mutuncina su ka nuna min ni ba a bakin komi na ke ba da gani har ku,ba su k'i su wayi gari su ga ba mu acikin Gidannan ba,su yi washshagare walle d'in su su kad'ai,don haka na d'aura aniyar gami da cin d'amara wajen ganin alak'ar ki da Yarima Haisam ta yi k'arfi,fiye da tunanin mai tunani".
Wani tsalle Zulfa ta daka ta na mai k'ank'ame Mahaifiyarta Badiya tare da cewa,"Kai Umma na ji dad'in wannan maganar ta ki hakan ya sa na ke k'ara son ki,ban san ma da wanne irin baki zan fara gode mi ki ko in nuna ma ki farinciki da na ke a ciki ba".
Ita kanta Badiyya murna ta ke sakamakon yanda ta ga 'yarta ta ke tsalle da jin dad'in abinda ta zo mata da shi.
"Kin ga ya Isa haka muje mu had'u da Sarauniya Mubinan kafin mu tafi,tunda ba ma cigaba da zama cikin wannan Zauren mu kad'ai ba",da to ta amsa mata sanan su ka tashi su ka fita.
Sun wuce zaure na d'aya na biyu anan su ka ci karo da Sarauniya Mufida ita da tawagarta ta ja ta tsaya ta na mai tsare hanyar da za su bi su fita,fuskarta na nuna jin dad'in had'uwar da su kai,"Hadima Sadiyya wa na ke gani haka a gabana kamar su O'o,me su ka zo yi ko dai sun zo maular ne da su ka saba zuwa a koda yaushe ?".
Sai da Hadima Sadiyya ta matso kusa da ita sosai ka na ta ce da ita,"Da alamar haka Ranki ya dad'e, kuma ina kyautata zaton abinda su ka zo nema ba su samu ba tunda gashinan sun fito da hannayensu sankalmakal".
"Ke dakata kar ki kawo min wargi ko ki yi tunanin za ki wulak'anta ni ko ki cimin mutumci,don kin san ko a da muna yara ni ba mai d'aukar raini ba ce ba ".
Wata irin dariya Sarauniya Mufida ta yi kafin tace," Hadima Sadiyya fad'a ma ta ki ce mata jiya ba yau ba ce ba hakanan kuma bayan Giwa sai barbaje,kuma komi ya kan canja in mu kai duba ko dogaro da tasirin lokaci,a yanzu na gaba ya yi gaba na baya sai tsintar hula".
Sai da Badiyya matar Waziri ta had'eye wani abu mai matuk'ar zafi da d'aci a mak'okwaronta ka na ta ce,"Da za ki burge ni,ki nuna mi ke cikakkiya ce kuma mai nuna isarta a ko ina da kin kauce kin ba ni hanya na wuce domin kwata-kwata ba ki a gabana,ba dan ke na zo wurinnan ba".
"Oh tun yanzu za ki wuce,na so ace za ki zauna mu sha fira yaushe gamo,ni da ke fa aminan juna ne tun k'uruciya,kinga bai kamata ace ki zo har cikin Gidana a ce ba ki samu wata tarba ta musanman daga gare ni ba".
"Ba na da buk'ata domin ba dan ke na zo ba,ba abinda na ke buk'ata daga gare ki,domin ban raina matsayi ko irin rayuwar da na ke a yanzu ba, tun da na dadeda da sanin k'addara ce kawai ke da zarafi ko ikon d'auke Faso ko kaushi daga k'afa ya koma zuwa kucin mutum".
"Badiyya kenan matar Wazirin k'asar BIHINAR, duk kin canza Anya ba akwai wani abu mai muhimanci da ki ka zo aiwatarwa a wurin Me Martaba ba kuwa ?",
"Hhhhh kar ki damu kan ki domin ni ba irin ki ba ce maciya amana ba,zan fi so da k'aunar in kasance a matsayin da na ke komi k'ank'antar ko wulak'antar sa,ba na sai da mutumci,matsayina ko k'imata domin in samu wata d'aukaka ko cikar wani buri nawa ba,nasan komi a kan ki nasan duk wani mataki ko k'alubalen da ki ka taka kafin ki kawo wannan matakin da ki ke a yanzu,dan haka ki bini a hankali ko kuma in fasa mugunyar kwan da ki ka dad'a kina lele da k'ok'arin binne sa a cikin k'asa".
"Hmmmmm to sai me idan kin sa ni ,ba fa abinda za ki iya a kan haka,wad'anda ma su ka fi ki sun buga da ni kuma sun gaji sun bar ni,balle ke karan kad'a miya, ni d'innan da ki ke gani kumurcin kan dutsece ban fito ba sai da na shirya".
"Nasan haka shiyasa bana buk'atar ko dawa sa in had'a hanya da ke,amma ina mai yi ma ki bushara da cewa,dai-dai da ke na nan zuwa akwai ranar da za ki girbi duk abinda ki ka shuka",.
Har Sarauniya Mufida ta bud'e baki za ta sa ke cewa da ita wani abu ta fasa ta mai da ganinta a kan Zulfa da ke tsaye tsuru ta na kallon abinda ke faruwa,ta ce da ita,"Zulfa ne sunan ki ko ?",da Kai ta bata amsa,"Na dad'e ina son ganin ki domin labarin ki na yawan zuwa inda na ke,ina so in gargad'e ki ki fita hanyar d'ana Hashim shi ba sa'an ki ba ne ba kwata-kwata ba ku dace ba domin ruwa ba tsaran kwando ba ne ba".
Cikin rashin ta Ido Zulfa ta ce da it,"Ba ni ya kamata ki yi ma wannan gargad'in ba,d'an da ki ke ikirarin ko tak'ama da shi,shi ya kamata ki dakatar da bibiyata,ba shi a gabana ko a cikin zuciyata,ba irin shi na ke da buri ko ra'ayi mijina ya kasance ba, ki dakatar da shi,in ki kai haka zan yi farinciki kuma in sake tabbatar da ke d'in mahaifiya ta gari ce".......
"Ke!! ki iya bakin ki domin gaban rijiya ba wurin wasan mahakaho ba ne ba",Hadima Sadiya ta dakatar da ita.
"Kin ga tsohuwa ba da ke na ke ba kuma ba ke ce ki ka sa ni a cikin wannan lamarin ba ita shugabar ta ki da kanta ta tsulmani a cikin ta,ko kin ji da fari na sa masu ba ki ?,don haka ki fita cikin wannan sha'anin babu ruwan ki ki bar tsuntsun da ya ja ruwa, ruwa ya do ke shi".
"Barta Hadima Sadiyya ai barewa ba ta yi gudu d'anta ya rarrafa ba idan ba ta aikata haka ba to da kai tsaye zan ce ita ba 'yar k'awata Badiyya ba ce ba".
"Hmmmmm Ranki ya dad'e ai ko a fuska ki ka kalle ni ki ka kalketa"......"Ke Zulfa ba na son rashin kunya ita ba sa'ar ki ba ce ,don haka ba ta can-canci rashin kunya da ga gare ki ba,don haka ki bata hak'uri tun kafin ki fuskanci fushi na"Badiyya ta ce.
Cikin k'unk'unai ba don ta so ba ta ba ta hak'urin,sannan Badiyya ta ce da Sarauniya Mufida, murmushi kwance a saman fuskarta"Ki yi hak'uri kin sa yaran zamani sai a hankali,sannan maganar Hashim ta bar damun ki domin bai samu nasara ko kar'buwa a wurin Zulfa ba,ta na da wanda ya fisa matsayi ,isa,kyau,asali,hankali,natsuwa da kuma nagarta,don haka ki bar tada hankalin ki,ba ta buk'atar shi a cikin rayuwarta,in ma So samu ne ma ki ka hanasa kulata za mu yi farinciki da murna akan haka".
Maganganun sun ma Sarauniya Mufida zafi matuk'a har ta kasa iya cewa da su komi,Badiyya ta kama hannun Zulfa su ka nufi hanyar fita har ta kusa wucewa ta d'an dakata tana cewa,"Idan da zan baki shawara ki ji da kin ja d'an ki a jiki ki nuna ma sa ke Uwa ce ta gari ba wai ki barshi yai ta hauragiya ba,ba tare da ya san ko shi waye ba",tana kaiwa nan su ka ida sa fita daga cikin Zauren gaba ki d'aya, tana jan hannun Zulfa wadda sai k'ok'arin dakatar da ita ta ke.
"Umma ki dakata mana dan Allah,na ga sai sauri mu ke,ko dai ba za mu je wajen Sarauniya Mubina d'in ba",a tak'aice tace da ita,"Eh ba zamu ba domin a yanzu itace za ta neme mu da kanta".
"Ban gane ba Umma ki yi min bayani yanda zan gane dallah-dallah "," Za ki gane wata rana tunda ba ki gane ba yanzu".
~~~~~
Duk iya guje-guje da yawace ya wacen da Nurain ya ke bai ga Yarima Haisam ba,Kai ko me kama da kamarsa bai gani ba,tun yana yawo cikin kasuwa har ya koma cikin Gari,daganan ya koma k'arshen Gari tafi-tafi har ya koma yawo cikin Daji,tafiya kawai ya ke ba ji ba gani ko inda ya ke sa k'afafunsa bai sa ni ba,gabad'aya kan shi ya rud'e ba ya gane komi ,gefan bishiya ya samu ya d'an kishingid'a barci 'barawo ya kwashe shi,cikin barcin na sa da bai nisa bà kamar a mafarki ya ji kukan Arah ku sa da shi,a firgice ya farka ya na waige-waige da son gano inda ta ke.
Gefen shi can ya hango ta tana ta kad'a fiffike,da gudunsa ya k'arasa kusa da ita ya sa hannunsa ya d'auke ta ya na mai zuba mata tarin tambayoyi masu yawa tamkar ya na tambayar mutum ba tsuntsuwa ba,ji ya ke Ina ma da ta na ba ki da yasan ba makawa za ta fad'a ma sa ina Yarima Haisam ya ke.
"Arah ina Uban gidan ki ya ke Ina Yarima Haisam ya ke?",bud'e fiffikenta kawai ta ke sai gyad'a kai ta ke,"Za ki iya kai ni inda ya ke in na biki,ina son ganinsa shi na ke nema ruwa a jallo,ban san inda zan ganshi ba".
K'ura masa Ido tai sai faman rufewa da bud'ewa ta ke da alama dai da akwai wani muhimmi sak'o da ta ke son isar ma sa,ganin ta fara k'ok'arin tashi ne ya mik'e tsaye da sauri ya bi bayanta da son ganin ina Arah za ta kaisa,Allah ya sa dai takai shi wurin Yarima Sadauki, ko ya samu ya huta da wahalar neman sa da ya ke ruwa a jallo.