Page 42
~Page 42
Motse-motse ta ke ta faman yi hannayen ta dafe da saitin cikinta,har wata 'yar kwalla ce ke d'ogowa daga idaniyarta,Kuyanga Jazila ce ta k'araso kusa da ita ta na cewa,"Ranki ya dad'e lafiya naga sai faman juya kan ki gefe da gefe ki ke,ko wani abun ne ke damunki? ".
Sai da ta runtse idanuwanta ta sake bud'ewa kanan tace "Cikina ke min zafi da ciwo Kuyanga Jazila, har wani k'ara ya ke min".
" Yunwa ce Gimbiya Junainah,wannan k'arar da ki ka ji k'ugin yunwa kenan ki k'ara hak'uri in sha Allah yanzu zai dawo".
"Anya Jazila wannan yunwa ce,kin ji yanda na ke ji kuwa zai wahala in yarda haka yunwa ta ke",Ba ta kai ga rufe bakinta ba sai ga shi ya nufo su,hannayensa d'auke da mabanbanta 'ya'yan itatuwa,ko da ya iso hannu ba ka hannu kwarya haka ta rik'a kai duk abinda ta samu bakinta ,da sauri Yarima Sadauki ya rik'a d'aukar duk abinda yasan na 'barewa ne ya na 'bare ma ta.
Sosai ta ci kayan itatuwan tamkar ba za ta daina ci ba,sai shine ma ya dakatar da ita da cewa,"Ki bar shi hakanan kar ki hare kan ki in ya so zuwa anjima sai ki sa ke ci".
Tsura mi shi idanuwanta tai tare da ce mi shi, "Ban k'oshi ba fa"," Eh na sa ni,amshi ruwa ki sha,zuwa anjima sai ki sa ke ci",Tana ji ta na gani,ba dan ta so ba haka ta hak'ura,sai da su ci su ka k'oshi sannan ya samu ya d'an ci wani abu daga cikin kayan marmarin da ya zo da shi.
Sun kwashe wajen sa'a guda bayan gama cin abinci kafin ya ce da su,"Ku shirya mu cigaba da tafiya domin ina tunanin in sha Allah nan da mako biyu ko uku za mu isa cikin k'asar BIHINAR ".
Kwa'be fuska Gimbiya Junainah ta yi tare da cewa," Dan Allah ka bari sai gobe sai mu cigaba da tafiya domin k'afafuwana sai faman zugi da rad'ad'i su ke min ".
" Yanayin wurinnan ba shi da tsaro saboda surk'uk'i da tarin dogayen bishiyu da ya ke da shi,Mai yiwuwa akwai wani mugun abun a wurin,don haka bai kamata mu cigaba da zama a wurin ba mu cigaba da tafiyar mu kawai zai fi".
Da sauri ta mik'e tsaye ta na mai cewa ,"Na shirya mu ta shi mu tafi ",Gimbiya Junainah ta fad'a cikin saurin murya,murmushin gefan baki ya sa ki a ranshi ya na cewa," Matsoraciya kawai in ba haka nai mi ki ba ban sar ranar da za mu isa inda mu ke so ba,domin wancan lokacin haka tai mu su da su ka fara yada zango ,sai da su kai kwana uku a wurin da ance su tashi su tafi sai tace a'a ita ta gaji ba huta ba.
"Kawo kayan in d'aukar mi ki",ya ce da Kuyanga Jazila, "A'a kabar mi ni kayana wannan nauyin nawa ne,hak'ina ne in d'auke su,in kai su duk inda za mu,ko ka manta ni baiwa ce aikina ne in yi mata hidima ko kuma in d'auki duk wasu kaya na ta,Komi nauyi ko yawansu".
Be sa ke cewa da ita Komi ba tunda ya riga da ya fahimci har cikin zuciyar ta ta fad'i abinda ta ce.
Tun ba su yi wani nisa ta kwalla wata uwar k'ara,wacce sai da ta karad'e ilahirin wurin da su ke,da wani irin sauri tare da azama ya juyo baya kasancewar shine a gaba su na biye da shi,"Lafiya me ya faru da ke,me ya same ki,garin yaya haka ta faru?".
"K'afata,waiyo Allah k'afata ciwo za ta cire zafi azaba ta ke min",Da sauri ya kai hannunsa ya kama k'afar ya na dudduba abinda ya same ta,Jini ne ke zuba daga k'afar sosai kamar wacce a ka yanka da wuk'a.
"Mene ne ya same ki garinya haka ta faru ?".
"Ban sa ni ba,nima kawai dai ina tafiya ne na ji wani abu ya karce ni ba tare da na sa ni ba".
Ka sa ce ma ta komi yai sai zuru da yai ma ta da idanu,wani abu sai kai kawo ya ke ma sa a mak'oshinsa,"Me yasa ba ki da kula tun d'azu fa na ke cewa da ke ki kula da hanya akwai abubuwa da yawa da za su iya cutar da ke Amma kalli ki gani jibi abinda ki ka jawo ".
" Ni dai ka dakatar da wannan zancen na ka ka taimaka min da wani abun kar jinina ya kai ga k'arewa".
Gefan rigarsa ya kama ya yaga ya fara goge ma ta jinin da ke zubar amma ina yak'i tsayawa sai sa ke 'bul'bulowa ya ke,da sauri ya aje k'afar ya shiga cikin yayin da ya ke gaban shi da alama wani abun ya ke nema,Kuyanga Jazila ce ta nufo inda ya ke tace,"Me ka ke nema in taya ka",Kai tsaye ya ce da ita,"K'aduwa na ke nema ciyawa ce da ke tsayar da zubar jini kin San ta ne".
"Eh na santa bari in taya ka dubawa",Cikin k'ank'anin lokaci sai gashi sun samota da sauri ya samo dutse ya d'an dandak'ata ya zuba akan inda ta ji ciwon zuwa wani lokaci jinin ya tsaya,ita kuwa sai faman raki ta ke.
Duk yanda Kuyanga Jazila ta so ta taka k'afar k'i tai,Ganin da gaske ba za ta taka k'afar ba,ya sa'ba ta a baya ya goye sannan su ka cigaba da tafiya,haka su ka cigaba da tafiya har su ka Isa wajen wani dutse su ka yada zango a wurin ,ba su da matsalar kumi domin suna da sauran kayan marmarin da su ka yi ma su saura har ma ruwa su na da shi,a cikin gorar fata,itatuwa kawai ya samo su ka had'a wuta a gefe su ka zauna,da niyar sai zuwa da safe za su cigaba da tafiya tunda dare ya yi.
Yarima Sadauki rabi da rabi yai barcin sa,su ne dai su ka sha barcin su sai bayan da su ka yi Sallah da safe kana shi kuma ya kishingid'a barci ya sace shi duk da ba wai me nisa ne ya kwashe shi ba.
Tun su Gimbiya Junainah na tunanin yanzu zai farka har su ka fara tunanin Anya wannan barcin da ya ke na lafiya ne kuwa,domin ya kusa kwashe sa'a hud'u ya na yin sa,shida ko barcin rabin sa'a ma ba ya yi,ko d'an motsi akai sai ya farka,wani lokacin ko magana mai k'arfi su kai sai ya farka amma yanzu ko cikakken motsi ba ya yi,sai ka yi da gaske za ka gane ya na da rai in ka kula da yanda numfashinsa ya ke fita a sannan ne za ka gane cewa ya na raye,sau kusan biyu Gimbiya Junainah na k'ok'arin tadashi amma Kuyanga Jazila na hana ta.
"Gani na ke kamar bai kyautu ki tada shi ba wata k'ila ya gaji da yawa ne shiyasa wannan nannauyen barcin ya kwashe shi",Kuyanga Jazila ta ce da ita.
"A'a Jazila wannan ba barcin lafiya ba ne ba,dube shi fa ki gani baya ko motsi numfashinsa ne kawai ke fita zo ki ga wani abu da ya sa na fad'i hakan".
Kusa da shi ta matsa ta sa hannunta ta bud'e idon shi,sai ga farin idon shi ya bayyana babu bak'in ciki,farin cikin idon kuma yai wani irin haske,hasken gabad'aya ba irin wanda su ka saba ji da gani ba ne ba.
Da sauri Kuyanga Jazila ta ja baya dafe da k'irjin ta ta na cewa, "Mun shiga uku,me ye ke shirin faruwa da mu ko dai rauhanan jikin sa ne su ka dawo ?".
" Ban sa ni ba Jazila,amma dai ina zuwa bari ki ga abinda zan yi",Da sauri Jazila ta shiga gabanta ta na cewa,"Me za ki yi,kar ki je ki aikata wani abun da zamu je mu yi danasanin anan gaba ".
" Me ki ke nufi ne,ki na so ne mu zuba mi shi Ido a haka, mu cigaba da zama a haka,har yaushe zai farka,tsawon wanne lokaci zai d'auka a haka?".
"Duk ba ni da amsoshin wad'annan tarin tambayoyin da ki kai min,kawai dai ina tsoran me zai iya faruwa idan ya farka".
"To idan kuma rashin tayar da shi ne zai haifar da matsalar da ki ke gudu kuma fa ?",Kasa cewa Komi Kuyanga Jazila tai domin anan ba ta da abinda za ta ce,haka ta na ji tana gani Gimbiya Junainah ta d'auki sauran ruwan shan su a cikin gorar fata ta watsa mishi da k'arfi.
Da wani irin zafin nama, tamkar wanda aka janyo shi da mayen k'arfe,ko giftawar walk'iya haka ya taso ya na mai kai ma Gimbiya Junainah shak'a saitin wuyanta,Kasa kai hannunsa a wuyanta yai ya na mai tsura ma ta Ido tamkar yau ya fara ganin ta.
Ita kam Gimbiya Junainah duk ta tsorata ta shiga cikin firgici ta takure kanta gami da rufe idauwanta gam ta na mai jiran tsanmanin abinda zai faru ko ya afku a gare ta.
"Wace ce ke me ki ke yi anan,nima me na ke yi anan,meye dalilin da ya sa na ganmu a wuri guda ?", shine furcin farko da ya fara fita daga bakin sa.
Wanda jin wannan zancen ba k'aramin hargitsa tunanin su Gimbiya Junainah yai ba da sauri ta bud'e idanunta ta na mai sauke ganin ta akan shi,ita kuwa Kuyanga Jazila na can gefe ta yi mutuwar tsaye,jin batun da ya fita a bakinsa kuwa kusan sakin fitsari tai.
" Nnnn ni ce fa,ba ka gane ni ba?",matsowa yai kusa da ita sosai har jikinsa ya na gogar jikinta,ya kai hannunsa saitin bakinta ya na zagaye shi kana ya ce da ita,"Ban san ki ba,ban ta'ba ganin ki ba,hasalima a yau na fara ganin ki a rayuwata,sai dai kin san me?".
Ba tare da ya bari ta ce komi ba duk da dama ita ba niyar cewa komi ta ke ba sakamakon d'aukewar wutan kanta da ta yi na wani lokaci dalilin abinda ke faruwa a tsakanin ta da shi.
"A kallon farko da nai ma ki na ji wani tsam a cikin jiki da jijiyoyina,na ji bugun zuciyata ya canja kuma a sanda na bud'e idanuna na d'ora su a kan ki na ji kin samu wani guri mai girma da muhimanci a cikin zuciyata na ji zan iya ba da komi nawa indai akan ki ne,na tunkari komi, na fuskanci duk wani abu akan ki,firgicin da na ga ni a tare da ke ya birge ni,ya kuma tsaya min a zuciyata,kai tsaye dai kin min za ki Aure ni?".
Saukar wannan kalmar a cikin kunnen Gimbiya Junainah dai-dai ta ke da saukar guduma a tsakar kanta,jikinta ko ina rawa ya ke bakinta ya yi ma ta nauyi,ta kasa sarrafa Zuciyarta da ma komi na jikinta.
"Oh yi hak'uri ba tare da kin san ko ni waye ba kawai na zo mi ki da maganar Aure ba tare da kin san ko da suna na ba ko,suna na Harzan, zan ba ki soyayya fiye da wacce ki ke zato da tsammani, zan ba ki kulawa jin dad'i da mace ke son samu a wurin d'a Namiji da duk wani abu da ba ki ta'ba tunanin samunsa ba ko da a mafarki".
Da wani irin gudu Kuyanga Jazila ta rugo ta shiga tsakiyar su ta na mai sa hannunta ta kare Gimbiya Junainah ta ce,"Ba ta son ka ,ba zata Aure ka ba domin ita d'in ba irin ka ba ce ba, ka je can ka nemi dai-dai da Kai".
Da hannu d'aya ya sa ya ture Jazila ya zama ba shamaki a tsakaninsu ka na ya ce cikin yanayin mara dad'i,"Wacce bera ce wannan, wanne sakarci ne ta ke yi da har za ta shiga tsakanina da ke,ba tasan ba zan lamunci ganin wani na uku a tsakaninmu ba,zan iya cutar da duk wanda yai niyar aikata hakan, ba zan lamunci ganin wani a tare da ke ba,zuciyata ba zata iya jura ko d'aukar hakan ba,da gaske ina son ki irin so mai tsananinnan,so mai tsayawa a zuci,so irin mai yankar shakkunan,mai zafi da rad'ad'i, inajin zafi a kowanne 'bangare na jikina".....
"Ya Isa haka",Gimbiya ta dakatar da shi,ba wai don ta na da k'arfin zuciyar da za ta aikata hakan ba,a'a kawai ta aro jarumta ne ta sanya wa kanta ba asalin ta ta d'in ba ce ba.
"Ka dakatar da wannan shirmen banzar da ka ke aikatawa, domin ka san na riga da na san ko kai waye,Kai ba kowa ba ne ba face wata halitta mai amfana da gangar jikin wani a haka zan so ka ko bare har mu kai ga maganar Aure ?".
Yanayin sa ya canja gabad'aya, hakama bugun numfashin sa ya k'aru,sai da ya furzar da iskar bakin sa ka na ya ce da ita,"Kin kuwa san me ki ka aikata Soyayyar tawa ta farko ita ce ki ke kira da shirmen banza?"......