Page 45
~Page 45
"Na shiga uku Kuyanga Jazila, kalli abinda ya kuma sa ke riska ta ,wallahi ba zan iya Soyayya ko tarayya da Aljani ba,ba zan iya ba,lamarin ya yi min girma zuciyata tarwatsewa za tai idan har nai yunk'urin amincewa da wannan zancen".
Sosai Kuyanga Jazila ta rik'e Gimbiya Junainah wacce ta k'ara 'barkewa da wani sabon kukan.
" A'a kar ki ce haka ,inki ka aikata hakan ba mu san kuma me ye zai biyo baya ba,idan har ya fahimci duk maganganun da ki ka fad'a ma sa duk zancen baka ne".
Rabuwa tai daga jikin ta ta na mai cewa da ita"Jazila ba ki ji irin zantuttukan da su ke fita daga bakin sa ba,kamar fa ya nufin ba zai ta'ba iya rayuwa in babu ni ba,ba zai rabu da ni ba,ya na nufin in k'are Rayuwata a tare da shi fa ,ya ki ke ganin zan iya rayuwa da Aljani a matsayin mijin Aure na,me zan haifa anan gaba Aljani zan haifa ko mutum ko kuma rabi mutum rabi aljan zan haifa,akan wannan lamarin ji na na ke kamar inyi hauka,in na ce mugudu saurin gano mu zai yi,kuma ba zan iya tafiya in bar shi a jikin wannan bawan Allah ba domin ban san wacce irin cutarwa zai yi masa ba ina jin tsoro,wallahi ina jin tsoro Kuyanga Jazila"wani sabon kuka ya sa ke zuwar mata.
Duk yanda Kuyanga Jazila ta so ta lallasheta ta k'i bata damar hakan," Dan Allah ki natsu mu bi komi a hankali har zuwa sanda za mu samu damar da zamu kawo k'arshen lamarin".
"Baza ki gane ba Jazila, ni kad'ai nasan me na ke ji akan wannan lamarin, Zuciyata zafi ta ke kwakwalwar kaina a cunkushe ta ke ,gefe guda kuma bana da wani k'arfin da zan iya tunkarar gobar da ke nufo ni ta na ci gadan-gadan, ba na da kwarin gwuiwa ko wani mataimakin da zai dafa min shi wanda zai taimaka min,wanda na ke ganinsa a matsayin bangon jinginata,kafad'ar da na ke d'ora kaina in yi kuka a samanta ita ce a wannan karon da wata bak'uwar zuciya ta ke son ta cutar da ni ,gangar jiki d'aya,fuska d'aya murya d'aya amma sai dai da mabanbanciyar zuciya ya ke tafe".
"Ki taimaka min ya ke Uwargijiyata kar ki bari wannan lamarin ya firgita ki har ya kai ga jefa ki cikin wani halin in haka ta kasance ban zan yafewa kaina ba,ina tur gami da Allah wadai da ya kasance bani da wata hanya da zan iya fidda ki daga cikin wannan lamarin, amma na miki alk'awari zan tsaya a tare da ke a duk wani hali walau na dad'i ko akasin haka, bazan ta'ba iya yin wata rayuwa ba tare da ke ba".
"Na sani Jazila ki na tare da ni a koda yaushe hakan ne ma yasa nai dabarar da zai tafi ya bamu wuri ko ma samu mu 'bullo da wata dabarar da za ta amfane mu,domin mu ceci Haisam da mu kan mu a wurin wannan k'anin shed'anun".
"Ba mu da wata mafita ko dabara da ya wuce mu hanzarta isa k'asar BIHINAR to anan ne fa zamu yi tunanin me ya kamata mu yi".
"Kina nufin mu bar komi har zuwa nan da wajen makonni biyu in mun isa, ba kya tunanin wani abun ka iya faruwa kafin cikar wannan wa'adin?".
"Sai dai muyi fatan kar wani abun ya faru amma ba mu da tabbacin za mu isa yanda mu ka so ko muka tsara",Kuyanga Jazila tai k'asa da muryarta sakamakon hango shi ya taho da tai,kafad'arsa rataye da manya-mayan kifaye, sai hanunsa d'aya rungume da k'irare.
Da wani irin razanannen kallo su ka dubi junansu har Gimbiya Junainah na cewa,"Garin ya akai ya samo wad'annan mayan kifayen baya tun da dad'ewa mu ka wuto inda su ke ya a kai ya samo su da wuri haka ?".
"Shugabata kar ki wahalal da kan ki wajen tsaurara ma kan ki dogon tunani domin kin san wannan aikin Aljani ne kawai zai iya aikata shi cikin k'ank'anin lokaci irin wannan",Kuyanga Jazila ta ce da ita tana mai yin k'asa da muryarta don kar ya ji.
"Matana ya na gan ki a inda na barki tsaye,duk kunyi cirko-cirko ko da akwai wata matsala ne,ko kuma kuna shirya wani abun ne ?".
Sai da Gimbiya Junainah ta gyara tsayuwarta gami da saita kanta, duk da kalmar Mata na da ya kirata ta bugi Zuciya da ruhinta ta ce da shi,"A'a ba komi, kawai dai muna sa ke duba girman lamarin da ya tunkare mu ne".
Har yai niyar ya ce da ita wani abu kuma sai ya fasa ya fara k'ok'arin had'a wutar da zai gasa ma su kifin domin shi kan shi yasan ya zo da lamari mai girman gaske,wanda ka iya jefa su cikin firgici da kuma rud'ani.Soyayya tsakanin mutum da Aljani ai ba k'aramar magana ce ba ga duk wanda ya ji balle shi da jai tsaye ya ke maganar Aure har su tara zuri'ah.
Cikin k'ank'anin lokaci sai ga shi ya gama gasa kifin ya samo manyan ganye ya zuba duka kifin ya kai shi gaban Gimbiya Junainah sannan ya ce,"Ma za ki ci kiyi maganin yunwar da ta ke addabar ki".
"To....to... Zanci amma ina na Kuyanga Jazila? ","Ban samo kifayennan da sunanta ba,amma za ta ci sai in kin k'oshi tukunna,sai ta ci ba baiwar ki ba ce ba",
Tura mi shi gaban shi tai tare cewa da,"Na k'oshi in dai ba za ta ci ba", ganye d'aya ya samu ya d'ibar mata "Ke Bera zo ki amsa".
Jiki d'ar-d'ar haka ta matso ta d'auka amma ko da wasa sun kasa kai shi bakin su," Lafiya ya na ga kin kasa ci,alhalin kuma kin ce da ni yunwa ki ke ji ?".
"Am...Am..to zan ci yanzu",ganin shi ya maida kan Kuyanga Jazila itama ya ga ta kasa kai kifin cikin ko kad'an.
"Ke ma Bera ba za ki ci kifin ba?".
" Ni dai ba suna na Bera ba ,kuma wannan kifin na ka ba zan iya cin sa ba domin ban san da ga ina ka samo shi ba,tsoran shi ma na ke ji,inda za ka d'auke abinka da ma so haka".
"Tsoro kuma a saboda me, ko kin ga wani abu a jikin sa? ".
Cikin d'ar-d'ar da murya ta ce da shi," A kaf zagayen nan ba wata k'orama ko rafi da har za ka samo irin wannan kifin har da zan sa ki jiki in ci sa,salan ina gama ci in yanke jiki in fad'i ,shikenan k'arshe na ya zo?".
"Ruwan ki ci ko kar ki ci,in ya so ma daga yau kar ki k'ara cin komi a rayuwar ki,dama ba dan ke na samo ba,ba ni da matsala da hakan".
Da kan shi ya matsa kusa da kifin ya fara mik'a shi saitin bakin Gimbiya Junainah ba yanda ta so haka ta bud'e bakin ya sa mata kifin tamkar wacce ta ke cin magani haka ta rik'a taunarsa.
"Kar ki damu lafiyayyen kifi ne,da kaina na yi su d'in shi a cikin rafi,ai kin san ba zan cutar da ke ba ko?".
Da ka ta ba shi amsa ta na mai had'iye wanda ke a cikin bakinta
Kukan tsuntsuwar da su ka ji ya karad'e yankin inda su ke ne ya sa duk suka dakata da abinda su ke,da wani irin gudu Nurain ya k'araso inda su ke,bai tsaya ko ina ba sai da ya dangana jikinsa da na Yarima Haisam,yana kuwa gami da murnar ganinsa.
"Na yi farinciki ganin ka d'an'uwana, na yi kewar ka sosai ,Ashe da rabon mu gana".
"Eh da rabon mu gana d'an'uwana kwana da yawa mun dad'e ba mu had'u ba".
Da sauri Nurain ya raba jikinsa da na sa ya na binsa da kallo gefa da gefe,sakamakon jin yanayin yanda sautin muryarsa ke fita cije da iko da izza ba kamar yanda Yarima Haisam ya saba magana ba.
Saitin kan sa ya duba ya ga yanayin yanda ya d'aure gashin kansa ya ce,"Tabbas kwana da yawa mun dad'e ba mu had'u ba,ashe kai ne,na sha mamaki da ban ga Ara ta iso inda ka ke ba,tun a lokacin nasan da akwai matsala ".
" Hmmmm ka ce ita ce ta kawo ka nan,ta yi k'ok'ari ta can-canci a jinjina ma ta".
"Ka zo ka bar wurinnan domin ka san in har ina nan bana buk'atar ji ko ganin wani ba d'an'uwana Yarima Haisam ba ".
Wata dariyar mara sauti Harzan ya sa ki tare da cewa," Indai wuri ne zan bar ma ka ,saboda nasan in d'ayanmu ya na wuri ba ba za a kwashe lafiya ba, ka sa ni ni ne zan tafi da shi da kuma mai d'akina", ya k'are zancen ya na mai duban saitin inda Gimbiya Junainah ta ke.
"Ka ci k'arya ka bi da ruwa ai ba a halacci gangar jikinsa domin kai ka amfana da ita ba,shi d'in mutum ne mai daraja wanda ya fito daga Gidan karamci ka bar rayuwarsa ya huta haka, ka cutar da shi cutarwa mafi tsanani don Allah ka bar shi haka,ka yi tafiyar ka can duniyar ku kowa ma ya hutu".
"Kar ka wahalar da kanka wajen bani baki domin ba zan saurare ka ba don a yanzu haka na gane muhimancin rayuwa da kuma amfanin da gangar jikinan ta ke min,da ita ne kawai zan samu damar da zan yi rayuwa da abar k'aunata,zai fi kyau ka hak'ura, ka bar ni salin alin inyi wucewa ta".
"Ka yi wucewar ka zuwa ina,ni ban gane abinda ka ke nufi ba ?".
Da sauri Kuyanga Jazila ta ce da shi,"Wai Son ta ya ke kuma ma Aurenta zaiyi har su haifi 'ya'ya a tare,shiyasa ya ke ce ma ka zai tafi ,ya na nufin zai tafi tare da ita".
"Ba ka da hankali ina ka ta'ba ji ko ganin anyi Aure tsakanin mutum da Aljani, in ba dan shafewar basira da tunanin irin ta ka ba".
"Za a fara a wannan karon,idan kuma ka Isa ka dakatar da ni domin a gabanka zan d'auketa mu tafi zuwa inda na ga dama,yau ce rana ta k'arshe da za ka sa ke sa d'an'uwanka a Ido,tunda dama ba wani so da k'auna ce a tsakanin ku ba,shi kad'ai dama ya ke rayuwa ba tare da kulawar kowa a cikin ku ba,shi kan shi bai san daraja da amfanin kan sa ba,to me zai sa ni ba zan amfana da shi ba tunda ba shi",......da wani irin zafin zuciya Nurain ya cakumi shi su ka fara danbe,danbe ba ni da danbe ba haka su ka rik'a yin sa.
Dama can kusan haka ta ke faruwa,In har Nurain zai had'u da Harzan to ba za su ta'ba kwashewa làfiya ba,Nurain ya na da zafin zuciya hakan ya sa abu kad'an ya ke tunzurasa su fara fad'a, duk da dai Harzan ya fi k'arfinsa ne sa ba kusa ba amma haka ya ke haik'e ma sa.
Kuma a haka wani lokacin Allah ke ba sa dama a kansa ya ci nasara akan shi,Zafi ya had'u da zafi hakan ya sa kowa ya ke jin jiki a cikinsu,kafin ka ce me ne tunin sun raunata kansu kowa a cikinsu sai zubda jini ya ke a mabanbanta wurare.
Gimbiya Junainah da Kuyanga Jazila ba k'aramin tashi hankalinsu yai ba,ba su ta'ba ganin irin wannan tashin hankali ba,kowa a cikin su neman makasar d'an'uwansa ya ke,cikin sa'a Nurain yai ma Harzan wani kaye wanda ya bashi damar d'aure hannayen sa ta baya,d'aurin da ba zai iya ko kyakyawan motsi ba balle ya samu ya kwance,ko da ya d'auresa bai daina dukan sa ba.
Ganin haka ne ya sa Gimbiya Junainah ta k'araso wurin da wani irin gudu ta shiga tsakanin su ta na mai ruk'unk'ume Harzan, ta hana Nurain cigaba da bugunsa duk inda yai sai ta tare.
Cikin hargagi ta ce da shi,"Na rok'e ka da ka dakata ka dai na cutar da d'an'uwanka da kan ka haka duk wannan abun da ya ke faruwa a jikin d'an'uwanka ya ke k'arewa shi ba shi da asara dai-dai da kwarzanen farce ba zai samu a jikinsa ba ,ba shi da asara ya mutu ko yai rai kai ke da asarar in har wani abu ya same shi".
"Ki matsa ki ba ni wuri in kashe shi kowa ma ya huta,don ba kin san ko waye ki ke tare da shi ba da kin san kowa ye da ko kusa da shi ba za ki je ba,shi d'in maciji ne ko bai sare ka ba in har ya ta'ba fatar jikinka sai ya shafa ma ka dafi,shi d'in annobace mai tarwatsa taro ko ahali,mutumin da zai iya sa d'a ya kashe Mahaifiyarsa me ye yai saura a duniya da ba zai iya aikatawa ba,don haka tun muna mu biyu ki matsa ki ba ni wuri in isa gare sa".
"Idan har ka ga ka k'ara d'ora hannunka a saman jikinsa to ka tabbata ba na motsi ko numfashi ne anan wurin,narasa ga ne me ya ke damun ka shi d'in fa d'an"uwan ka ne me zai sa ka rink'a cutar da shi da kan ka",juyawa tai inda Harzan ya ke tafara kakka'be mi shi jikin sa da goge duk inda ya ji ciwo.
K'afarshi ta hagu ce ta fi buguwa dan haka sai da ta taimaka masa sannan su ka Isa zuwa k'asan wata bishiya ta zaunar da shi.
Sosai Gimbiya Junainah ke hawaye a sanda ta ke goge masa jikinsa sosai Nurain ya ji masa ciwo,ganin yanda ta ke kukan ne ya sa Harzan ya ce da ita,"Na rok'e ki ki dakatar da wannan kukan da ki ke in ba haka ba zai iya zama sanadin da zan aikata kisa ,in har ba ki dakatar da shi ba".
Da sauri ta had'eye kukan gami da share hawayen da su ke a saman fuskarta amma duk da haka wasu ne ke sa ke zubowa,"Na yi shiru ka ga ni,na ma daina kukan gaba ki d'aya,yanzu ma haka dariya na ke ka gani",ta bud'e ma sa ba ki gaba ki d'aya da nufin Wai ita dariya ta ke anan.
"Ba na son kukan ki ko kad'an ya kan sa ka Zuciyata tai rawa da jin rauni,inji tamkar na gaza a wani fanni mai girma a rayuwata da bai kamata in nuna gazawata ba a kan shi".
" Na fa ce ma ka na daina kukan tun d'azu ".
" Ba ki daina ba domin har yanzu ga hawayenan suna k'ok'arin zubowa daga cikin idanun ki,ko na aikata ma ki wani laifin ne,ki fad'a kai tsaye ko mi girmansa na yi maki alk'awarin zan daina ko in aikata shi,matuk'ar hakan zai sa ki cikin farinciki ".
Tsura ma shi idanu tai na wani lokaci kafin daga bisani tace da shi,"Komi na ce Ina so daga gare ka zan samu?".
" Za ki sa mu ko da kuwa rayuwata ce","Ka tafi ka bar wannan gangar jikin ba zan iya jure ganin ka a cikin irin wannan yanayin ba,shi ba zai fasa ba kuma kaima ba za ka iya hak'ura ba har sai kun nuna asalin ku su waye,zuciyata ba ta da wani kwari ko k'arfin da za ta iya cigaba da ganin wannan fitina da tashin hankali da ke gudana a tsakanin ku".
Run the idanunsa yai da iya kacin k'arfin sa kafin ya ce da ita" Me yasa za ki tambaye ni irin wannan buk'atar bayan kin san hakan ba mai yiwuwa ba ne ba a gare ni,idan ma har zan tafi to sai dai na tafi tare da ke,Idan kuwa har zan tafi da ke sai na kashe ko illata wani ran a yanzu",.....
Da sauri ta katse shi da cewa,"A'a a'a ba na so ka ji abinda bazan ta'ba iya yafewa kaina akan shi ba indai har na zama silar da za ka kashe wata rai ko da kuwa dabba ce,don haka na rok'e ka in har da gaske Son da ka ke min na gaskiya ne,inhar da gaske za ka iya sadaukar da komi na ka a kaina to kai min wannan alfarma ka tafi ka koma inda ka fito salin alin ba tare da wani tashin hankali ya sa ke afkuwa ba".
"Tabbas Soyayyata a gare ki gaskiya ce,hasalima ita ce Soyayyata ta farko a rayuwata,ba rayuwar wani ki ke so in ba ki ba,to na baki kin Cece shi,ke ko da rayuwata ki ka nuna kina so sai na mallaka mi ki ita kiyi yanda ki ka so da ita ba ta wani ba,don haka na hak'ura a wannan lokacin amma ki sani muddin na dawo babu wata halitta ko wani dalili da zai hana ni tafiya da ke,don haka ki shirya kuma ki sa wannan a can cikin k'asan Zuciyar ki inda ba za ki manta ba".
Yana kaiwa nan ya mik'e tsaye tare da fusgar igiyar da Nurain ya d'aure masa hannu ta tsinke har ya na jima Yarima Sadauki ciwo a wurin .
Kai tsaye kusa da Nurain ya nufa ya na mai cewa da shi,''Kai d'an wahala ka yi nasara a kaina a wannan lokacin ta dalilin Matana zan tafi amma ina so ka sa ni zan dawo kuma a shirye zan dawo, ka kuka da irin shirin da zan dawo da shi ko dai in tura Uba ya had'u da matarsa da 'yarsa ko kuma in tura d'a ya had'u da Mahaifiyarsa ko kuma in had'e ahalin wuri guda su rayu a tare sai ka za'bi wanne ya fi a ciki".
da wani irin zafin Zuciya Nurain ya nufo in da Harzan ya ke sai dai tun kafin ya k'araso tuni Harzan ya bar gangar jikin Yarima Haisam, daganan tsaye ya tafi luluuuuu zuwa k'asa zai yi munmunan fad'uwa wacce Allah kad'ai yasan me ka iya faruwa in har haka ta kasance da shi, duka su ukun Nurain, Gimbiya Junainah da kuma Kuyanga Jazila su ka nufe shi da niyar tare shi......