26_27
by @kainaat1515
Episode 26_27
'''''''''''''''Wayar Aairah ce ta fara ringing, Aaimah cewa tayi "to ni sai da safe, dan nasan indai ya mus'af ne to ke kam ba yanzu ba, duba mai kiran tayi, mus'af ne picking tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "hubby barka da dare "
"barkan ki dai my love, ya gida "
"lafiya lau "cikin sauƙin soyayya suke wayar, anan mus'af yake sanar da ita next week zai wuce uk ( can ya kuma da karatun ) , Aairah kamar tayi kuka dan taso ace suna ƙasa guda da shi, bata son yayi mata nisa, ta dai yi mashi fatan alkairi sun ɗan jima suna waya daga bisani suka yi sallama.
✨SHAZIM✨
tsaye ya ke bakin window ya riƙe curtain (labule) yana waya da a hashim, fuskar shi a sake suke fira, a hashim na cewa "saboda mansoor ne kawai zan shigo gobe amma da dan kai ne bazan zo ba "
"to ko yanzun ma kakar ka shigo tun da ina nan"
"kai dai kawai saboda mansoor "
"ai da kayi zaman ka "
sun ɗan ɗauki tsawan lokaci suna fira sannan su kayi sallama,ya juya kenan zai bar bakin window ya hangi wasu manyan truck's guda ukku suna shigowa cikin estate ɗin da alama ta ƙaramin gate suka shigo,mamaki ne ya kama shi,waɗannan truck's daga ina kuma minene suka ɗauko, ya jima tsaye yana kallon truck's ɗin har suka yi parking a bakin babban store ɗin estate ɗin, mutum uku uku ne su ka fito daga cikin kowace truck, bayan truck ɗin da ke gaba suka nufa, mutum biyu ne suka buɗe truck ɗin suka shiga miƙoma sauran wasu manyan kwalaye suna shiga da shi cikin store ɗin, barin bakin window yayi ya nufi toilet ya ɗauro alwala, sallah ya gabatar ko da ya gama sallah ya jima zaune kan carpet bai ta shi ba, tunani ya shiga yi game da kwalayen da yaga masu truck ɗin na shiga da su cikin store,shin kwalin minene kuma na waye, ya jima a zaune har sai da ya fara jin bacci sannan ya ta shi ya kashe light ɗin ɗakin ya nufi bed ya kwanta, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba da shi.
washe gari kamar jiya feenah ta kawo ma shazim breakfast kamar yan da ya tsallake jiya baici ba haka ma yau baici ba ya nufi part ɗin uncle Ahmad a can yayi breakfast tare da mansoor,fita su kayi shi da mansoor.
✨KATSINA✨
......... zaune su ke kan dinning suna breakfast, kallon abie Aaimah tayi tana faɗin "abie dan Allah idan zaka je gidan dadi ka tafi da mu"
"safiya ce yanzu ku bari sai da yamma sai kuje "
Aairah tace
"dan Allah abie, muna so ne muyi mata wuni "girgiza kai mom tayi tana faɗin "ku shikenan tun aka ce ba school daga nan ƙafa fuwan ku suka dai na zama wuri ɗaya "
"ba haka bane mom mun jima ba muje gidan ba ne "
"ba ma kunjima baku je ba, ina tunanin ko ranar friday kuje gidan" Aaimah tace "dan Allah dai mom "abie ne yace
"kuyi sauri ku shirya "
haɗa baki sukayi wurin cewa "yawwa abie mungode "da sauri suka bar dinning area suka nufi bedroom ɗin su.
abie ne a parlor tsaye yana jiran su Aairah , mom ce ke sau kowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya black color, wurin abie ta nufo tana faɗin "ba su fito ba ko "
"eh kinsan su da shiririta, duk ta ƙare tafiya zanyi idan ya so daga baya mudi ya kai su"
"afuwan abie ga mu nan" cikin sauri suke taka stairs case ɗin, sanye su ke da hijab har ƙasa onion color ,ƙara so wa su kayi, kallon mom abie yayi yace "sai mun dawo "a dawo lafiya tayi masu haɗi da juyawa ta nufi kitchen, fita su kayi abie na gaba suna bin shi a baya har compound, motar su ka shiga, Aaimah na gaba kusa da abie yayin da Aairah take baya, fira suke cikin kwanciyar hankali har suka iso gidan dadi,horn abie yayi a bakin gate mai gadi ne ya leƙo ganin motar abie yasa shi komawa ciki da sauri,ya buɗe mashi gate, ya shiga ciki parking lot ya nufa, sai da ya gama dai daita parking ya kashe motar Aairah ce ta fara fitowa sannan sai Aaimah, jiran abie su ka yi har ya fito su ka shiga cikin gidan tare,cikin parlor su ka shiga suna sallama tsit parlorn yake babu kowa,wuri abie ya samu kan sofa ya zauna har zasu nufi ɗakin Aunty Rabi sai gata ta fito tana amsa masu sallamar da su kayi, gaishe da ita su Aairah su kayi da fara'a a fuskar ta amsa masu sannan ta nufi wurin abie "yaya ina kwana "
"lafiya lau, ya gidan "
"Alhmdllh"
"mama na ciki ne?" abie ya tambaya
"eh tana ciki "
"bari na shiga mu gaisa "da to Aunty Rabi ta amsa, ta shi abie yayi ya nufi bedroom ɗin dadi, zaune take kan sallaya ta gama sallar walha tana adu'a, zama abie yayi gefan gadont har sai da ta gama adu'a, waigowa tayi tana kallon abie ta ce "Muhammad kai ne tafe "
"eh mama, ina kwana "
"lafiya lau, ya su kubra "
"suna nan lafiya, tana gaishe ki "
"ina amsawa"su Aairah ne su ka shigo da gudu su ka nufi dadi suna faɗin "dadi munyi kewar ki" basu ƙarasa ba abie ya dakatar da su da faɗin "lafiyar ku lau kuwa,za ku wani nufe ta da gudu hak, salan ku danne mata ƙafafu fa bayan kun san fama take dasu, Allah yasa in ƙara ganin irin haka " ya faɗa cikin faɗa, tsaya wa su kayi suna kallon dadi kamar za su yi kuka
dadi tace "a'a da ka barsu ƙafafu ai sunyi lafiya ba abun da zasu man"
"kar kice haka mama,ji fa yanda suka nufe ki da gudu, waɗannan yaran wani lokacin jinsu su ke kamar wasu ƙananun yara"
"duk da haka dai da ka barsu, ku zo nan"dadi ta faɗa tana miƙa masu hannu, matsawa su kayi kusa da ita su ka zauna "inakwna dadi "
"lafiya lau, ya gida "
"lafiya lau"
"masha Allah" fira su ka shiga yi da dadi, abie dai na zaune yana jin su, tashi yayi yana faɗin "mama ni zan wuce "
"zauna ina son magana da kai" komawa abie yayi ya zauna yana faɗin "to Allah ya sa lafiya"
"lafiya lau" ta faɗa tana kallon su Aairah ta ce ku ɗan bamu wuri " da to suka amsa haɗi da ta shi suka fice, dadi tace " dama magana ne akan ɗana, tun ranar da nayi maku magana kai da mustafa ban sake jin wani ya ce komi ba dangane da maganar " ɗan nisawa abie yayi sannan ya ce
"haka ne mama, naje har garin na ku, amma ban samu wanda yace ya san inda ya koma ba, an dai ce man a kwai wani abokin baban sa da suke kasuwanci tare, amma yanzu baya garin, lokacin da bai da lafiya babban ɗansa yazo ya tafi da shi, sun dai faɗa man ɗanna sa yana kaduna da zama"hannu dadi ta ɗaga sama tana faɗin
" ya Allah, Allah ka bayyanar da shi, hankalina ta shi yake duk lokacin da nayi mafarkin habiba,ban riƙe amana ba " ta faɗa hawaye na sauka a fukar ta,lallashin ta abie ya shiga yi, hannu yasa ya share mata hawaye yana faɗin
"ki dai na kuka mama, insha Allah za'a gan shi, ki daina cewa ba ki riƙe amana ba Allah yaga niyyar ki"
"Muhammad dole na ce haka, amanar yaron nan ta bar man , da ace da ubansa ya nuna bazai bar man shi ba na cigaba da kula da shi ina ziyartar shi, amma sai na fita batun shi, kaga kuwa ban kyauta ba "
"kiyi haƙuri komai zai wuce da izinin ubangiji, za muyi iya bakin ƙoƙarin mu ganin mun samu inda yake "
"to Allah ya yarda "
"Ameen " abie ya ce
"Muhammad wai ya jikin abokin ka, kwana biyu ba muyi waya da safwan ba da mahaifiyar shi , ban kuma tambaye ka ba "
"jiya munyi waya da safwan, ya sanar min an ma kusa sallamar shi , ya nemi alfarmar a bar shi can wurin su"
"ai gara yayi zaman shi can, ko dan saboda azzaluman mutanen nan "
"gaskiya a gani na gara ya dawo nan, har Allah yasa memoryn shi ya dawo"
"to Allah ya ƙara sauki , amma kana ganin idan ya dawo ƙasar nan mutanen nan zasu barshi, baza su cigaba da bibiyar rayuwar shi ba "
"haka ne muddin suka san yana raye baza su ƙyale shi ba,ko da nace ya dawo nan bawai zai koma can bane, a nan zai zauna tare da mu har memoryn shi ya dawo ya tuna da iyalan shi,ta hakan ne za mu iya samun sa'a akan su, amma idan yana can ba lallai ne ya iya tuna baya ba "
"gaskiya hakan shi ya fi, dan ya ji jiki da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi, kuma yan da ya manta da abun da ya faru za su iya ƙara cutar da shi muddin ya koma " ɗan nisawa abie yayi yace
"haka ne, shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun ƙare shiyyasa suka samu galaba a kan shi har su ka kashe shi"
"insha Allah , Allah zai toni asirin su"
"Ameen, burina kwai ya dawo cikin hayyacin shi, ya tuna da baya "
" ameen, Allah ya bashi lafiya " da ameen abie ya amsa, sun ɗan jima suna tattaunawa akan abokin abie, daga baya yayi ma dadi sallama, parlor dadi ta nufa wurin su Aairah da Aunty Rabi.
✨Abuja✨
Zaune ya ke kan carpet a parlor yana aiki a laptop, sanye yake da short black color iya gwiwar sa, sai t_shirt ita ma black color, wayar sa da kan hannun sofa ce ta fara ringing , jawo ta yayi haɗi da du ba mai kiran, murmushi yayi ganin A hashim, picking yayi tun kafin yace wani abu A hashim yace " hey man gani a bakin gate ɗin estate, kasan halin securityn ku da ɓakar tambaya "
"kai kuma tambayar ce baka so?"
"ni dai ka kira su bana son surutun tsiya"
"ai kuwa sai dai kai ta tsayuwa, dama ba kace wurin mansoor ka zo ba, to mi ya hana baka kira mansoor ɗin ba, shi sai ya kira su "
"ok dan na kira ka shine zaka ɓata man lokaci, Allah ko ka kira su su barni na shigo ko na koma in da na fito "
"yo ka kuma "kashe wayar a hashim yayi ba tare da yace komai ba, number ɗaya daga cikin security ya kira yana faɗin "ɗan rainin hankalin yana iya ko mawa " picking security yayi yana faɗin "good evening sir"ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace "friend ɗi na na waje ku bar shi ya shi "
"ok sir "security ya faɗa, rejecting kiran yayi, aikin sa ya ci gaba.
security ne ya nufi motar A hashim da ke bakin main gate , baƙar mota ce ƙirar ferrari 250 ta sha tinted, security na ƙara so wa, hannu ya sa yayi nocking window motar , sauke glass a kayi a hankali, arba nayi da kyakyawar fuskar ( DR ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM , A HASHIM, BI MA'ANA YA ABDALLAH ) sanye yake da farin yadi, ya sha ɗinkin zamani, kallon security yayi yace"barka da aiki"
"alhmdllh, dama yallaɓe shazim ne yace ka shigo" ok kawai ya abdallah yace, reverse yayi ya nufi cikin estate ɗin, direct part ɗin uncle ahmad ya nufa, parking yayi a parking lot,dai daita parking yayi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi number mansoor ya lalubo haɗi da dialing, bugu ɗaya mansoor ya ɗauka yana faɗin "ka iso ne , kana bakin gate"
"gani a parking lot na shigo ciki"
"ok, ai da ka shigo "
"ka fito dai mu shiga tare"
"ka ji ka sai kace estate ɗin ba ƙon ka ne, gani nan zuwa " ok ya abdallah yace haɗi da yin rejecting,fitowa yayi daga cikin motar ya jingina da ita yana jiran isowar mansoor, bayan kamar seconds goma sai ga mansoor ya fito, parking lot ya nufo wurin shi,yana iso wa suka yi hogging ɗin juna cike da farin cikin haɗuwa da juna mansoor ya ce"barka da zuwa, ya KT"
"KT alhmdllh yasu abbah da mama "
"lafiya lau suke, kwana da yawa"
ya abdallah yace "alhmdllh "
"ka kira shazim kuwa?" mansoor ya tambaya, ɗan ya taine fuska ya abdallah yayi yana cewa "rabu da ɗan rainin wayau kawai"murmushi mansoor yayi yana cewa "ai kun fi kusa, da man can ku sababbo ne,sai in baku haɗu ba, mu shiga daga ciki ku gaisa da mama mun tsaya a waje muna ta surutu"ok ya abdallah yace, ciki suka nufa,main parlor suka shiga bakin su ɗauke da sallama, kairiyya ce da su fatima a parlor, jin sallamar su ya sa su wai gowa, ware idanu fatima tayi,tana faɗin "ya dr a abuja" da gudun gaske ta nufi ya abdallah zata yi hugging ɗin shi tana faɗin "ya dr a abuja, un believable "tare ta mansoor yayi yana faɗin "yau ina ganin ikwan Allah, hugging ɗin sa za kiyi a gaba na "duƙar da kai fatima tayi tana faɗin "a'a yaya nayi missing ɗin shi ne sosai"bin ta da wani kallon mansoor yayi yana faɗin" to sannu " ya abdallah ne yace" rabu da shi kawai fatima " ma tsowa tayi kusa da shi batare da tayi hugging ɗin shi ba tace "ya dr, nayi mamki sosai, dama kana abuja shine ko ka faɗa man zaka zo bayan ka san ina abuja "
"sorry fatima , na ƙi faɗa maki ne dan nayi surprise ɗin ki, ya kike "
"lafiya lau yaya, amma a nan zaka kwana ko? "
"a'a, anjima zan tafi "bubbuga ƙafa fatima ta shiga yi "haba dan Allah yaya, gaskiya nan zaka kwana" muryar kairiyya su kaji tana cewa "watao ya abdallah fatima kawai ka gani ko, har muke gaishe da kai ni da sa'ada baka ji ba " murmushi yayi "no ba haka bane kairiyya, ya kike ya kwana da yawa"
"lafiya lau alhmdllh, ya hanya "
"Alhmdllh "
"ya abdallah nima kenan baka ganni ba ko"sa'ada ta faɗa tana turo baki "sa'adatu sa'ar mata, ya gida"
"lafiya lau ya kt da su mom"
"suna nan lafiya "
mansoor ne ya ja hannun shi yana faɗin "mu shiga ciki ka zauna, idan ka biye masu za ku kwana ne a tsaye "bin bayan mansoor yayi har cikin parlor, zama yayi kan sofa, kusa da shi fatima ta zo ta zauna, sai sakin murmushi take kamar gonar auduga, ba ƙaramin farin ciki tayi ba da ganin abdallah ( su fatima ba zama, yau gata ga ya dr )
ya mansoor ya ce "sa'ada shiga kikira mama "da to ta amsa haɗi fa nufar bedroom ɗin mama, ta shi kairiyya tayi zuwa kitchen "ruwa da lemu ta kawo mashi " sake komawa kitchen ɗin tayi sai gata ta fito ɗauke da wani bowl ci ke da yankakun fruit ta ajiye gaban shi, tnxs yace haɗi da ɗaukar ruwa ya sha,fitowa sa'ada tayi mama na bayan ta har suka iso parlor, zama mam tayi kan sofa,"abdallah yau kai ne a garin namu "
"eh mama, ina wuni, na same ku lafiya"
"lafiya lau abdallah, ya su momyn ku da uncle ɗin ka "
"lafiya lau su ke "
" masha Allah " ta shi mama tayi ta koma ɗakin ta, kairiyya ma tashi tayi ta dalilin kiran wayar ta da a kayi, ya rage parlorn daga mansoor, abdallah, fatima da kuma sa'ada, sai zuba mashi fira fatima take wani ya bata amsa wani kuma yayi murmushi, sun ɗan jima tare da su fatima har aka fara kiran sallar magrib, sannan su ka shiga ɗakin kairiyya do min gabatar da sallah su kuma suka nufi masallaci,a can ya abdallah su ka haɗu da shazim, yi yayi kamar ma bai gansu ba, murmushi kawai mansoor yayi yana girgiza kai, ya san shazim yana wannan fushin ne saboda Abdallah , bayan an sallame sallah, suka fito daga masallacin,tsayawa su kayi har sai da uncle ahmad da uncle Ibrahim su ka fito abdallah ya gaisa da su, suna tambayar shi su mom da abie "suna nan lafiya "
uncle ahmad ya ce "masha Allah, ya uncle ɗin ka "
"yana nan lafiya "
"ina gaishe da shi "uncle ahmad yace, tafiya su ka yi shi da uncle Ibrahim, sai a lokacin abdallah suka gaisa da shazim,ta fiya suke shazim na faɗin "ai nayi tunanin tun tuni ka tsufa da komawa gidan uncle"
"ɗan rainin wayau ai ba dan kai na shigo ba"
"hmmm koma dai miye, sannun ka da zuwa, ya hanya "
"yawwa, Alhmdllh, ya kwana biyu "
"Alhmdllh" ya faɗa a dai dai time ɗin da su ke kawowa part ɗin su shazim , ciki su ka shiga ba kowa a parlor,dama shazim ne ka ɗai ke zama part ɗin,noraiz da man tun ranar da suka zo ya koma part ɗin uncle Ahmad da zama, direct sama su ka nufa part ɗin shazim, a parlor su ka ya da zango, abdallah na cewa "wai shazim yau she zaka je katsina "
"zanje insha Allah, amma saboda mom da abie zani amma ba dan kai ba "
"ya kamata dai, har yanzu fa mom bata sanka ba, gara ma abie kun taɓa haɗuwa sau ɗaya" mansoor ya ce "gaskiya baka kyauta ba, ace duk tsawan shekarun nan baka taɓa zuwa katsina ba, gaskiya nayi mamaki"
shazim ya ce "to ni dai ya isa haka kar ku cinye ni, katsina dai ce ko to zani inasha Allah " Allah ya yarda, suka faɗa, fira su ka shiga ta yaushe gamo, sai da aka kira sallar isha sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, bayan sun fito daga masallaci part ɗin uncle ahmad su ka nufa, suna tafiya shazim yace "amma zaka kwana nan ko"
"a'a komai dare sai na koma gidan uncle "
"pls ka kwana nan"
"sai ranar da kaje katsina sannan zan kwana nan"
shazim ya ce"kai ka sani kuma wannan, kar Allah yasa kwana " time ɗin da su ke shiga cikin main parlor, kamar ɗazu ma fatima da sa'ada su ka samu a parlor suna kallo,sallama su kayi, amsa masu sallamar su kayi , sama mansoor ya wuce ya bar su a parlor "ya dr har na yi tuna nin ka tafi" fatima ta faɗa
"ina nan ban tafi ba"
"zaka kwana nan ɗin"
"a'a yanzu zan tafi "
"dan Allah ya dr ba dan ni ba " sa'ada ma tace "pls yaya,mi yasa ba zaka kwana ba "
"ba komi sa'ada " fatima tace "pls ya shazim kasa baki dan Allah ya kwana"
" idan ya kwana wani abun zai maki ne? "
girgiza kai fatima tayi tana faɗin "a'a kawai dai naga mun daɗe ba mu haɗu ba "
" to tun da babu abun da zai maki karki damu mutane" kwal kwal fatima tayi da idanu alamar kuka, kallon shazim abdallah yayi yana ta ɓe baki yana faɗin
"kar ki damu zan dawo gobe insha Allah "
"pls ka kwana dai dan Allah"
"shikenan fatima zan kwana saboda ke " taɓe baki shazim yayi yana faɗin "aikin banza "
abdallah ya ce "wannan kuma kai ta shafa, ɗan rainin wayau " tashi fatima tayi su ka je kitchen ita da sa'ada,
"wallahi kaji kunya wai fatima zata saka kwana "
"ina ruwan ka kuma " tsaki shazim yana faɗin "girma dai ya faɗi"
"ya daɗe bai faɗi ba" mansoor ne ya fito "ina ta jiran ku shigo, naji ku shiru" ta shi su kayi su ka bi bayan mansoor ba tare da sun ce komi ba, a parlorn shi suka zauna, fira suke cikin kwanciyar hankali, nocking su kaji, mansoor ne yace wanen,"fatima ce yaya, " ok shigo kawai mansoor ya faɗa, turo ƙofar su kayi ita da sa'ada kowace hannun ta ɗauke da tray, kan center table su ka ajiye fatima na faɗin "ya dr ga dinner "tnxs abdallah yace, ficewa su kayi ita da sa'ada, mansoor ne yayi serving ɗin su. kan carpet su ka zauna suna cin abinci, da suka gama mansoor ya kira fatima ta zo ta kwashe dishes ɗin, fira su ka ɗan taɓa, sai wurin 9:30 su ka yi mansoor sallama su ka nufi part ɗin su shazim, suna tafe suna fira,suna kawo bakin part ɗin su shazim, mota ce shararo da gudu ta shigo estate ɗin ta ƙaramin gate,bin motar su kayi da kallo har tayi parking a part ɗin uncle Ibrahim, mace ce ta fito daga motar, jikin ta sanye da hijab har ƙasa,fuskar ta da face mask ,cire face mask ɗin tayi, tazo ta gaban su zata wuce,taɓo shazim abdallah yayi yana faɗin.......