MATAR MANYA

7

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 7

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Sallama Baba ya fara da ita ya buɗe da addu'a kafin ya shiga yi mana nasiha gaba ɗayanmu. "Alhamdulillah ina godiya ga Allah daya nuna min wannan ranar da na sauke nauyin da Allah ya ɗora min naku, Alhamdulillah nayi bakin ƙoƙarina wurin ganin na sauke nauyinku dake kaina iya yanda zan iya abinda nayi kuskure ina roƙon Allah ya yafe min. Yanzu lokaci ne da zan miƙa ko waccenku ɗakin Mijinta wanda a yanzu yafi kowa iko daku, Sabo da haka kuyiwa Mazanenku biyayya domin samun aljannarku." Dakatawa yayi ya sauke numfashi yana jin wata irin kewar yaran na kama shi.

Gyaran murya yayi yaci gaba da cewa "Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa aljanar Mace tana ƙarƙashin kafar mijinta ne, saboda haka ku dage ku samu aljanarku. Sai abu na gaba da zan ja hankalinku akai shine haƙuri, dole a zamantakewa sai anyi haƙuri musamman zamantakewar aure, ku zamo masu haƙuri da ɓoye sirrin Mazanenku."

Juyowa yayi kaina ya kira sunana "Salamatu ina so ki manta da duk wani abu daya faru a baya ki zauna da Mijinki lafiya, kiyi masa biyayya in sha Allah zakici riba. Ki sa a ranki cewar ibada zakiyi ki nemi aljannarki, ina son tunatar dake cewa ba komai ne mutum keso yake zama alkairi a gare shi ba, shi yasa ako da yaushe ake so ka nemi zaɓin Allah akan dukkanin lamuranka ba zaɓin zuciyarka ba."

Saurarawa yayi yana binmu da kallo gaba ɗayanmu kafin yace "Allah yasa albarka a cikin aurenku ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, ku tashi ku tafi a kaiku gidajen ku."

Tunda Baba ya fara magana dukkanin mu kuka muke musamman ma ni da jikina ya gama yin sanyi akan abinda na aikata da kuma fargabar abinda zai faru idan Suhail ya kasa rufa min asiri akan abinda zai tarar, duk da cewar dama shirina shine ya sake ni in auri Alhaji, amma bana so asirina ya tonu ko dan mutuncin Iyayena.

Tausayin Iyayena naji ya kamani sai dai wata zuciyar na faɗa min cewar koma me na aikata sune sila tunda na faɗa musu cewar bana son sa amma suka dage. Cikin kukan da nake wanda a zahiri za'a ɗauke shi a matsayin normal kuka da kowacce amarya keyi yayin da za'a kaita gidan Mijinta, amma a zahiri ba hakan bane kuka ne na baƙin cikin inda za'a kaini in yi zaman aure bayan na gama saka rai da inda ya lun-lunka shi sau ba adadi.

"Dan Allah Baba ka yafe min dukkan laifukana wanda ka sani da wanda baka sani ba." Na faɗa cikin kuka. Ɗan dakatawa yayi yana nazarinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "Na yafe muku gaba ɗayanku Allah yayi muku albarka."

Baba Haja da Baba Auwa ne ƴan'uwan Babanmu suka shigo suka fita damu. Karima aka fara kaiwa saboda ita ce babba har mu aka mata rakiya gidanta yayi kyau dai-dai gwargwado, sannan aka kai Sajida itama dai a cikin gari ne kuma ba laifi Mijinta yayi ƙoƙari.

Nice ƙarshen kaiwa gidan Suhail da yayi Namijin ƙoƙari ya gina gidansa na kansa kuma mai kyau dai-dai na masu rufin Asiri, ciki da parlo da ban ɗaki a ciki yayi sai kuma safaya ɗaki, kiching da store da toilet na waje sai rijiya da aka rufeta. Ko ina kuma tiles ya saka sannan hada ƙaramin gate ya saka a ƙofar gida.

Gida yayi kyau masha Allah dai-dai zaman talaka mai rufin asiri dangi nata yabawa, sai dai ni ko kaɗan bai burgeni ba sabo da gidan da Alhaji yace zai sakani tamkar aljanna yake a kan wannan, yayin da nake ganin wannan tamkar kejin ajiyar kaji.

Ƴan kawo amarya na gama tafiya na cire lulluɓin da aka min na gyara kwanciyata saman gadona wanda Babanmu yayi matuƙar ƙoƙarin saya mana tare da taimakon ƴan'uwa da abokan arziƙi, wayata na ciro na shiga dannawa ina duba abubuwa. Data na buɗe inda saƙonni suka riƙa shigowa tamkar zasu fasa wayar, kwananta biyu a kashe sabo da damun da ƙawayenmu suka rinƙa yi min akan wai da gaske Suhail zan aura.

Haushi yasa na kashe wayar saboda na san izgiline kawai yasa suke tambayata akan cika bakin da nake musu na cewar nafi ƙarfin ƙananan mutane sai Manya. Saƙonnin Whatsapp na fara dubawa ɗaya bayan ɗaya ina replying wanda ya dace in barin na shirme.

In shiga group ɗinmu na ƴan Makarantarmu naci karo da wani posting daya harzuƙani ya ƙara taso min da tsanar uren.

"Yau dai ƙarya ta ƙare wai ruwa ya ƙarewa ɗan Kada, yau ne aka ɗaura auren Salma Shehu (Matar manya) da Suhail, abin tambayar anan shine shin ina manyan Alhazan ne ko sunƙu zuwa an gaji da jira aka bawa talaka?."

Wannan shine abinda naga an rubuta an saka emojis na dariya daga ƙasa. Raina naji yayi mummunan ɓaci ina jin da zanga Yusura yanzu a gabana ba abinda zai hana ni shaƙeta in mata dukan tsiya akan wannan posting ɗin da tayi sabo da nasan don aci min mutunci ne yasa tayi hakan.

Class mate ɗinmu ce tana ɗaya daga cikin ƴammatan dake masifar son Suhail tun muna Makaranta, na san yanzu ma kishi ne yasata yin hakan don a titseni akan cika baki na in kunyata.

Ɗaya bayan ɗaya na fara bin comments ɗin da mutane keyi akan maganar da tayi, wanda saƙonnin sun kusa ɗari biyar don masifa kamar jira ake daman kowa da abinda yake tofawa, masu Allah ya ƙara In banda rashin godiyar Allah me nake nema da Suhail bashi da akwai.

Magan-ganu dai barkatai na shaƙiyanci da masu faɗa min baƙar magana, Kairiyya ce kaɗai ke ƙoƙarin kare ni wacce itama aka yi ca!!! A kanta ana cewa bata son gaskiya don ƙawata ce.

Ɓacin rai yasa na manta da cewar amaryace ni yau aka kawoni gidan miji kamata yayi in zauna cikin lulluɓi har sai ango yazo, ina tuni na watsar da lulluɓin wurinsa da ban na shiga maida martani inda rigima ta kaure sosai a group ɗin har sai da admins suka kulle gidan sannan aka saurara. A haka Suhail yazo ya same ni sai tsaki nake ina masifa ni kaɗai, da yake yasan halin abarsa bai yarda wasu sun rako shi ba duk nacin da suka yi kuwa.

Zama yayi dab dani yana mai-maita sallamarsa a karo na biyu wanda sai lokacin na lura da shigowarsa, da ƙyar na ɗaga baki na amsa masa ina matsawa daga kusa da shi. "Barka da dare." Ya faɗa yana kallon yanda na haɗe rai sosai fuskata ba alamar fara'a dama ga ɓacin ran abinda na gama gani a group ɗinmu.

Sai da na ƙara haɗe raina sannan nace masa "Barka da dare." Murmushi ne ya ƙwace masa a saman kyakykyawar fuskarsa, shifa a hakanma ya riƙa kallonta a matsayin mallakinsa ba ƙaramin farin ciki yake jiba, duk wani borenta ya bashi lokaci ne domin ya shirya tsaf don lugui-guita zuciyarta da tsaftatacciyar soyayyarsa irin wacce bata isa ta kauce mata ba.

"Ba za'a kalleni ba." Ya faɗa cikin ƙaryar da murya yana jifanta da sassanyan kallonsa, ɗagowa nayi na watsa masa harara ina ɗauke idanuna wanda hakan ya kusa wucewa da numfashin Suhail, idansa ya lumshe ya fuzgo numfashinsa da ƙyar ya buɗe baki yace "A dai tausayawa bawan Allah kar a sumar da shi."

Wato Suhail ƙarshene a wurin iya soyayya da tattalin wanda yake so, ni kaina na shaida hakan don munyi soyayya a baya wacce na bashi haɗin kai ya nuna min gata da kulawa irin wacce sai an tona ake samun Namiji mai irin wannan kulawar. A yanzu haka wancen tsohon tsumin ne ke motsa kansa a cikin zuciyata amma sai dai taurin kaina da son cikar burina ya hana ni bayyana hakan.

Duk abinda take yi yana ankare da ita yana kuma karantar duk wani motsi nata yana fassara shi saboda ya daɗe da sanin wacece ita tun tana ƙwailarta yake sonta ya san ko wane motsi nata. Tashi yayi ya fita yaje ya shigo da laidojin daya bari a parlo ya aje a gabanta ya koma kiching ya ɗauko duk wani abinda za'a buƙata wurin cin abincin ya aje kafin ya zauna a gabanta ya fitar da komai.

A natse ya fitar da danƙwaleliyar kazar dake ta nason mai tana fitar da daddaɗan ƙamshi wanda ya fisgi hankalina ba shiri na kai kallona wurin ina jin yawun bakina na tsinkewa, ta ƙasan ido yake kallonta murmushi na shirin suɓuce masa sabo yanda yaga tana satar kallon naman tana tura baki gaba. Tsokar duka ya saluɓe ya fitar da ƙashin ya yankata yanda zata yi daɗin ci sannan ya tura mata shi gabanta yana faɗin Bismillah.

Mantawa nayi da wani rashin so da nake masa na gyara zama na shiga zirawa cikina naman ina korawa da holandiya sai da naji na ƙoshi sannan na ture kwanon ina ɗagowa muka haɗa ido ya tsareni da waɗannan idanun nasa masu hana ni yi masa rashin mutunci lokuta da dama.

Harara na watsa masa na ɗauke idanuna na miƙe na shige toilet don yin wanka in kwanta saboda a gajiye nake ga bacci na fizgar idanuna. Ajiyar zuciya ya sauke bayan shihewarta ya maido da kallonsa saman plate ɗin naman data rage yayi bismillah ya fara ci cike da natsuwarsa.

Ruwa na ɗiba a cikin babban bokitin da aka cika min da ruwa a banɗakin ciki ga electric kettle na jona ruwan zafi da yake akwai wuta nayi wankana na gasa jikina sosai ina jin gajiyar dana kwasa tana sakewa a hankali.

Alwala nayi na fito na samu baya ɗakin don haka na shirya cikin gaggawa nabi lafiyar gado nayi kwanciya ta, ina jinsa ya dawo ya gama kwashe komai ya kai shi inda ya dace kafin ya shiga wanka wanda tun ina jin motsinsa har bacci yayi gaba dani ban san fitowarsa ba har ya kwanta kusa dani sai da asuba dana tashi na ganshi kwance kusa dani yana baccinsa cikin nutsuwa. Kyakykyawar innocent face ɗinsa na zubawa ido ina jin wani abu a game da shi amma zuciyata na kwaɓata akan ban dace da shiba.

"Ya ishe ki haka ko na bari ki ƙara more wa." Na tsinci muryarsa yana faɗa cikin alamun wanda ya tashi daga bacci, wata irin kunya ta kamani don ban san idonsa biyu ba da ban zuba masa ido haka ina kallonsa ba gashi ya kamani dumu-dumu ina kallonsa bayan kullum ina cika bakin cewa bana sonsa.

Mazewa nayi na miƙe ina ɓata rai nace "Meye abin kallon?."

"Kin ganshi tunda kika ɓata lokaci kina kallon kyakykyawan Mijinki mana." Ya faɗa yana buɗe idonsa gaba ɗaya ya tashi zaune ya zuba mata ido. Ɓata rai nayi na nufi bayi ina gun-guni a raina faɗi nake 'yanzu da ina can na kwana a saman bene na shiga bathroom na sakarwa kaina shower in fito in sauko daga saman bene in bada umarnin abinda za'a dafa min, amma Baba ya hana ruwa gudu yanzu ga inda na kwana a matsayin gidana wanda ban taɓa hasaso shi haka ba.'

Tsaki nayi a fili dana duba ba wuta bare in jona kettle in dafa ruwan wanka, ina tsaye ina taraddadin abin yi wanka da ruwan sanyi ko bari naji knowking ɗinsa a bakin ƙofa. Banza nayi masa tamkar ban jiba sai da yace Salma ki buɗe ruwan zafi ne na kawo maki."

Sai da ya faɗi haka sannan na buɗe na na karɓi planks ɗin ruwan zafin na maida na rufe ba tare dana tanka masa ba, murmushi kawai yayi ya juya ya zauna bakin gado yana jiran fitowar ta. Shifa hakanma ya masa don bai taɓa tunanin iya haka rikicin nata zai tsaya ba, yayi tunanin ranar da aka kawota bazata bari suyi bacci ba musamman ganin yanda ta nuna bore sosai akan ƙin auren.

Yana nan zaune har na fito nayi tsaye ina jiran ya shige in shirya amma yaƙi tashi sai kallon daya bini da shi wanda yake ratsani ba kaɗan ba. Ganin taƙi zuwa ta shirya gashi ana ƙoƙarin shiga sallah yasa shi tashi ya shige toilet ɗin bayan yace mata ta jira shi suyi jam'i.

Yana gama shigewa nayi sauri na buɗe akwatina na jawo doguwar riga na zira na saka hijab na fesa turare na kabbara sallah, raka'atanin fajri na fara gabatarwa na zauna lazumi bayan na gama nayi addu'a sosai na roƙi Allah ya yafemin akan kuskuren dana aikata. Ina nan zaune ya fito ya zira jallabiya ta maza ya saka turare ya matso ya jamu jam'i.

Muna gama sallah na tashi zan haye gado saboda baccin dake idona na tsinci muryarsa yana cewa "Barka da safiya Salma." Kunya naji ta ɗan kamani saboda nice ya kamata in gaishe shi amma na kasa har sai daya fara gaishe ni, mazewa nayi nace masa "Ina kwana." Ba tare dana juyo ba.

Cike da kulawa ya amsa min yana tambaya ya baƙunta na masa shiru na haye gado naja bargo nan da nan bacci ya kama ni.

Bai koma bacci ba yayi zaman karatun Alkur'ani sai da ya kammala sannan ya fita waje ya fara tsaftace gidan, sai daya gyara ko ina ya saka turare kafin ya shiga kiching ya haɗa musu breakfast kafin ya shiga wanka...

Akwai complete document a Naira 300

***