MATAR MANYA

8

by @oumfatima33

💓MATAR MANYA💓*

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 8

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Fitowa yayi daga toilet ɗin ɗaure da towel a ƙuunsa sai ƙarami da yake tsane ruwan dake diga daga cikin lallausar baƙar sumarsa dake ta sheƙi abin lemar dake jikinta, gaban mirrow ya ƙarasa ya jawo mai ya shiga shafawa tattausar farar fatarsa cike da nutsuwa. Yanayin yanda fatarsa take da santsi tafukan hannunsa dana ƙafarsa keda laushi bazaka ce talaka bane, kai kace a ƙasan AC yake kwana.

Yana shirin yana kai dubansa saman gadon har yanzu baccinta take hankali kwance tana sauke numfashi 'kalleta a haka very innocent amma idan ta tashi ta kama daru tamkar ba ita ba.' ya faɗa a zuciyarsa yayinda a fili yace "Ina roƙon Allah ya sanyaya min zuciyarki ki amshe ni da wuri don in nuna maki irin matsayin da kike da shi a gareni, ina roƙon Allah ya bani abinda zan kula dake da duka yaran da zaki haifa min Habeebty."

Sai da ya gama shirinsa tsaf ya baza ƙamshi ya fito angonsa tsaf sannan ya nufi bakin gadon ya zauna yana hura mata san-sanyar iskan bakinsa dake fitar da ƙamshin mouth whas ɗin daya yi amfani da shi.

Cikin baccin da nake na jiyo wani daddaɗan ƙamshi yana ratsa kofofin hancins sai kuma san-sanyar iska dake sauka saman fuskata, a hankali na shiga motsa idaduna kafin na fara buɗesu ina lumshewa har na buɗesu duka na sauke saman kyakykyawar fuskarsa da take fresh tayi fayau.

Ban san na shagala da kallonsa ba sai da ya hure m idon sannan na ƙifta na janye idona ina tsuke fuska, tattausan murmushi ya saki yana cewa "Baccin ya isa haka, ki tashi ki shirya You breakfast is ready."

Wani narkewa zuciyata take daga kwancen da nake, wato Suhail maƙura ne wurin iya soyayya, ya iya tattalin Mace da bata kulawa. Irin wannan soyayyar da kulawa nake mafarkin samu a wurin Mijina kuma ya haɗa dukansu, abinda bashi dashi kawai shine kuɗaɗen da zan fantama rayuwa yanda nake so, in saka sutura mai tsada in hau mota mai tsada ta yanda duk inda na shiga a riƙa nuna ni ana faɗar Hajiya Salma ce Matar wani hamshaƙin mai kuɗi ko ɗan siyasa.

Miƙewa nayi jikina ya gama mutuwa da shauƙin soyayyar da mutumin nan yake ƙoƙarin jefa ni, na lura so yake dole sai ya ɗauke min hankali daga ƙudurin da nake da shi wanda in nayi wasa ya samu lagona tsaf zan manta cewar ba zama nazo yi ba.

Toilet na shige bayan na ɗauki komai da nake buƙata, ajiyar zuciya ya sauke yana jin tamkar ya rungumeta ya ɓoyeta cikin ƙirjinsa ko zai ji sauƙin abinda yake ji a game da ita. Shi kam ya san soyayyar Salma jarabawa ce a gare shi da yake fatan cinye ta cikin amincin Ubangiji.

Sai da na ɓata lokaci wurin yin wanka kafin na fito na samu ya fita parlo yana amsa waya don haka nayi amfani da wannan damar na shirya cikin gaggawa kafin ya dawo, zama nayi ina duba wayata tarin saƙonni ta Whatsapp wanda duk martanin rigimar da muka yi ce jiya da aka buɗe group ɗin suka ɗora daga inda aka tsaya. Tsaki nayi a fila ina cewa "Bani da lokacinku munafukai kawai, zan baku mamaki ne."

"Su waye za'a bawa mamakin?". Na tsinci muryarsa lokacin da yake shigowa É—akin. ÆŠagowa nayi na watsa masa harara a raina ina cewa 'koma me aka min ai kai ka jawo min da shegen nacinka'. A zahiri kuwa É—auke kaina nayi na mayar kan abinda nake yi.

"Shike nan na haƙura tunda ba za'a bani amsa ba." Ya faɗa yana zama kusa da ni. Matsawa nayi yayi murmushi yana ɗaga hannu alamar saranda yace "Shike nan sauko kiyi breakfast rana nayi." Bana wasa da cikinsa don haka na sauka na haɗa shayi mai kauri na buɗe ƙwan ɗaya soya na haɗa da bread na shiga zubawa cikina a natse ba tare dana haɗa masa ba ko na kalli inda yake ma ban yiba.

Shi kuma tagumi yayi ya shiga kallonta tamkar ya samu TV yana jin daÉ—in ganinta a matsayin mallakinsa, yanda take cin abincin cike da yanga tamkar bata son taunawa shi yafi komai É—aukar hankalinsa don haka ya manta da yunwar cikinsa har sai da ta gama ta ture sannan ya haÉ—awa kansa shayin ya fara karyawa.

Tashi nayi na fita parlo na zauna ina jina duk a takure don haka nayi ta sakin tsoki lokaci zuwa lokaci ina duba wayata. Sai daya kammala sannan ya biyo ta parlon ya samu kujera ya zauna ya zuba mata ido, duk yanda yaso ya jata da hira ƙin bashi haɗin kai tayi don haka yaja bakinsa yayi shiru sai ido da yake Binta da shi har baƙi ƴan ganin ɗaki suka fara zuwa kafin ya mata sallama ya fita don basu wuri.

Sai da ƴan gida suka zo kawo min kayan gara su dubulan da cin-cin har da su Sagir sannan na sake muka yini abinmu ciki walwala da azahar Suhail yazo ya kawo mana abincin rana ya ƙara fita wanda bai dawo ba sai da dare bayan kowa ya tafi.

****** Tunda aka kai amarya aka dawo ita dai hankalinta yaƙi kwanciya da fargabar abinda Salma zata aikata da kuma zargin da take mata kar ya tabbata shi yasa ta kasa zama wuri ɗaya har sai da su Aunty Zali suka dawo ita ta ƙara kwantar mata da hankali sannan ta ɗan samu natsuwa amma dai ta kasa kunne da jiran ta inda wani abu zai iya ɓullowa.

Hankalinta bai kwanta ba har sai washe gari da Æ´an kai gara suka je suka dawo suka shaida mata cewar tana lafiya ba wata matsala sannan ta samu natsuwa ta ware ta shiga harkokin gaban ta.

Bangaren Baba Mari ma an kaiwa yara gara sosai har tana wa Mama habaici akan abinda ta kai bai kai nata ba ita mai yara biyu. "Kai Alhamdulillah na godewa Allah sana'a tayi rana yau na fita kunyar yarana na kankaro musu mutunci a wurin Mazanensu da danginsu. Kai ku kama sana'a mata!!! Macen da bata sana'a aura ce, lalee lalee maraba dake ta zinariya." Irin waɗannan magan-ganun da waƙen habaicin Baba Mari ta yini yi yau a gidan duk in zata gifta ta gaban ɗakin Mama.

Baiwar Allah ita ko ko a kanta saboda ta san tayi iya yanda zata iya Alhamdulillah kuma ta godewa Allah tunda an gama sabga lafiya ba'a kunyata ba asiri ya rufu.

****** A ɓangaren Alhaji Murtala dala kuwa tun ranar da abinda ya faru tsakaninsu ya faru ya kasa samun natsuwa, ji yake in bai mallaketa ba yayi babbar asara domin shi kaɗai yasan mai ya samu a tattare da ita don haka yake a zaƙe da son ta fito daga gidan Mijinta ya aureta. Amma a zuciyarsa fargaba yake da tunanin anya akwai wanda zai auri yarinya kamar Salma data haɗa komai ya kuma yi sakacin rabuwa da ita ko me zata masa kuwa?.

A gaskiya ba zai taɓa barinta ta zauna ba dole zai san yanda zai yi ya hanata zama a hannun wancan yaron don ba kalarsa bace tafi ƙarfinsa bashi da abinda zai iya riƙeta, amma zai bata lokaci yaga abinda zata yi don ya san ya riga ya gama lalata ta da kuɗi baza ta iya rayuwa a hannun talaka ba. Da wannan tunanin ya zuba ido yana jiran jin abinda zai je yazo.

•••••••••• Yau satina ɗaya a gidan Suhail matsayin Matarsa amma ba wata mua'amala ta aure ɗaya shiga tsakaninmu da shi domin na hana shi ko wace irin dama daya nema, saboda son da yake min yasa bai takura min ba ya rabu dani akan sai randa na shirya.

Ni kuma so nake Ya gaji da halina ya rabu dani ba tare da san cewar na rasa budurcina ba ko don rufin asirina dana iyayena, amma sai dai abinda na lura da shi shine ko shekara nawa zamu yi dashi a haka bashi da niyar rabuwa dani sai ma zage dangane da yayi wurin bani dukkan kulawar data dace duk da bana bashi haÉ—in kai amma bai fasa ba.

A haka muka kusa cinye wata ɗaya ba tare da komai ya sauya ba na zaman da muke yi, zai aje komai na kayan abincin zai kuma sayo duk abinda yasan ina so kuma zanyi farin ciki shi yake yi, tunda nazo gidan ban taɓa ɗaukar tsintsiya na share koda ɗakin da muke kwana ba da sunan aikin matar gida bare in shiga kiching in girka abinci. Kullum da safe haka zai zage ya gyara ko ina a gidan ya haɗa breakfast kafin ya fita wurin sana'arsa, idan rana tayi yana can hankalinsa a kan me taci? Haka zai ajiye uzurorinsa ya taho ya kawo mata abinci kuma ba kunya in ɗauka inci har ma in ya makara in aza masa tashin hankalin cewa ya bar ni da yunwa zata illata ni.

Haka zai yi ta bani haƙuri har sai na haƙura sannan zai samu natsuwa, duk irin wannan zaman da muke bai taɓa damunsa ba bare ya kai ƙarata wurin Iyayena ba ko ya sanar da Iyayensa ba. Kowa a cikin su ɗauka suke zaman lafiya muke yi da shi, idan ƴan uwansa suka zo gidan bana bari su san zaman da muke sakewa nake da su har su tafi.

Sai dai duk ƙoƙarin ɓoyewa da yake yi sai dai Mahaifiyarsa ta fuskanci bashi da cikakkiyar natsuwa da ya kamata ko wane mai Iyali ya kasance a cikin ta. Koda ta tambaya shi bai faɗa mata komai ba yace mata kawai gajiyar aiki ce da zirga-zirgar da yake, ba don ta yarda ba ta rabu da shi taci gaba dayi masa addu'a.

A ɓangaren abokansa sai da Huzaifa ya tambaye shi anya kuwa lafiya suke da Matarsa don sarai ya san halinta da kafiyar tsiya, duk nacin tambayar da yake masa bai sanar da shi komai ba yace suna lafiya. Ko kaɗan baya son danginsa da abokansa su tsane ta akan abinda take masa shi yaji ya gani zai iya jurewa yaci gaba da addu'a har Allah ya dai-dai tsakaninsu.

Ana haka na fara wani irin zazzaɓi mai azabar naci ga amai ban isa sakawa cikina abinci ya zauna ba, sosai hankalin Suhail ya tashi ba kaɗan ba ya shiga damuwa ko fita sai da ya daina yi. Yayi-yayi dani akan muje Asibiti amma na ƙi yarda kullum sai dai in sha paracetamol ince masa zai sauka amma abin kullum gaba yake ko ya sauka da zarar yamma tayi zai dawo ya lulluɓeni haka zan kwana ƙwara amai sai da safe kafin ya sake ni lokaci ɗaya nayi wani irin fari na ɗashe bani da aiki sai kwanciya.

Hankalinsa yaƙi kwanciya ganin yanda nayi wani uban fari yasa shi jin tsoron ko bani da jini don haka ya dage akan sai munje Asibiti wanda akan hakan ya nuna min ɓacin ran da bai taɓa nuna min ba, amma tsabar taurin kai naƙi yarda wanda yasa dole yaje gidanmu ya sanar da Mama ya kuma roƙeta akan tazo tayi min magana ko zan yarda.

Faɗa sosai Mama tayi tace shi yake lallaɓa ni shi yasa nake rashin mutuncin da naga dama, shi dai haƙuri ya riƙa badawa har Mama tace bari ta sanar da Baba. "To shike nan." Ya faɗa kansa a ƙasa.

Ƙaramar wayarta ta lalubo ta kira Baba saboda baya gidan a lokacin yaje ƙauye dubiyar ƙanin Mahaifinsu da aka kira aka shaida masa cewar bashi da lafiya. Kira biyu ya ɗaga wayar da sallama. Amsa wa tayi ta gaishe sa da tambayar mai jiki yace mata da sauƙi.

"Malam dama Mijin Salamatu ne yazo bata da lafiya yake son in je in dubata." Mama ta faɗa cike da girmamawa wanda abin yayi matuƙar burge Suhail yake fatan wata rana Salmarsa zata koya daga Mahaifiyarta.

"Subhanallah! Me ya samu Salamatun?." Baba ya tambaya daga can ɓangaren.

"Inaga ba zai wuce zazzaɓi na kuma ka santa da taurin kanta bata son allura sai anyi ta fama da ita." Mama ta faɗa tana hasaso yanda take fama da ita idan bata da lafiya.

"To kije ki ganota ɗin, Allah ya sauwaƙa."

"Ameen ya Allah." Ta faɗa tana aje wayar ta kalli Suhail tace masa "Zamu iya tafiya." Da sauri ya miƙe ya fita a ɗakin dai-dai Baba Mari na fitowa daga banɗaki ya gaisheta cike da girmamawa. A yatsine ta amsa tana ƙare masa kallo hassada na kamata sabo da Suhail ɗin yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado kuma yafi duka Mazajen yaranta. Duk da Salmar nunawa take tafi ƙarfinsa shi yasa da aka aura mata shi suka samu abin faɗa.

Fitowa Mama tayi ta sanar da Baba Mari cewar "Babar Habu zanje in dubo Salamatu bata jin daÉ—i."

"Allah ya sauwaƙa." Ta faɗa tana shigewa ɗaki, girgiza kai Mama tayi tayi waje tana mata fatan shiriya. A saman lifan ɗinsa ta same shi yana jiran fitowarta don haka tana fitowa ya ɗauketa suka tafi....

Akwai complete document a Naira 300

***

Oum Fatima