SHAGALALLIYA

1.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D/AUTA*

*DEDICATE TO HANNAH SUHANA*

*Free book kuma Labarin barkwanci.*

*LAMBA TA FARKO.*

Aguje ta isa dandalin matasan ta tsaya a kansu dafe da ƙirji tana haki, yayin da take so ta yi magana amma ta kasa tsabar gudun da ta sha. Dukansu suka bi ta da kallo cike da mamaki a kan fuskokinsu, suna jiran su ji abin da ya kawo ta, saboda sanin halinta. Musamman Mani da ya kasa ɗauke idanuwansa a kanta, masu ɗauke da ƙatuwar hararar da ƙiris ya rage ya kai mata hannu, saboda bai raba ɗaya biyu a kan cewa wurin sa ta zo. Ganin hakin ya ƙi barin ta ta faɗi zaune daɓas a cikin ƙasa tana rabon ido cikin rarraba magana da haɗiyar yawu ta ce masa,

"Ka..kawu Mani, inji Kandala..wai.. wai ta ce na kira ka asiri rufe ka je ka ci kwaɗon garin kwakin da ta..."

A zabure ya miƙe tsaye yana wurga mata daƙuwa kafin ya riƙe ƙugu cikin fusata ya ce,

"Wai ke wace irin tonanniyar yarinya ce ke? To don ubanki ki je ki ce mata ba na ci na ƙoshi!"

"An gama kwaɗon yanzu yanzun nan! Kuma ai kai ka ce idan an yi a sanar da kai tun kafin ya yi ruwa ya lalac..."

Cikinta ya yi kamar zai kai mata duka, ta yi hanzarin dunƙulewa wuri guda tana ihu, haushi ya saka shi shura talkamansa zuciyarsa cike da takaici ya bar wurin. Saboda tonon sililin da ta yi masa a cikin abokan hirarsa. Hannuwansa zube a cikin aljihunsa ya sha kwana ko waige babu tsabar shaƙiyancin da abokan suke ta yi masa, a kan idan ba ya cin kwaɗon ya kawo musu tun kafin ya lalace. Amma hakan bai hana ta ɗaga murya ta sake cewa ba,

"Ɗumamen da ka ce a rage maka ma yana tukunya!"

Babu shiri wasu daga cikin abokan nasa suka fara dariya, yayin da wani daga cikinsu ya kalle ta a lalace ya ce,

"Ke kam Bintoto an yi watsatsiya! Shi kenan ba za ki iya rufa masa asirin ba, duk da jan kunnen da aka yi miki a kan ki kira shi asiri rufen?"

Ta miƙe tsaye tana turo baki ta shiga kakkaɓe zaninta da ya kwaso ƙasa tana cewa,

"To ai na faɗa masa asiri rufe ko kai ba ka ji me na ce ba?"

Ta ƙare maganar tare da murguɗa baki, zaburar da ya yi da nufin kai mata duka ya sa ta bazama da gudu tana faɗin,

"Allah Ya isana idan ƙato ya dake ni."

Ya bi ta da kalolin zagi tana yi masa gwalo. Sai da ta sha kwanar da za ta sada ta da gida ta zaro dogon kare a cikin karan da ke ƙofar wani gida, sannan ta fara yin mota da shi tana gudu tana faɗin,

"Ziiiiiiiiiih! Ba burki ba burki! Duk wanda na kaɗe yasin babu ruwana!"

Haka take ta zuba gudu da dogon karen tana nanacin babu burki har ta ci karo da wani yaro da ke ɗauke da bokitin awara a kansa, wanda fitowarsa kenan daga gida zuwa wurin talla. Babu aune sai jin ƙarar faɗuwar bokitin tare da tulin awararsa da ke cike fam ko rufuwa ba ya yi. Babu jinkiri awara ta watse gabaɗaya ta baje cikin ƙasa. Yaro ya dafe kai yana tsalle tare da ihun faɗin,

"Wayyo ni awarata! Wallahi na rantse da Allah sai an biya ni awarata!"

Kafin ka ce me mutane sun fara taruwa wurin suna tambayar mafari. Bintoto ta rike ƙugu tana kallon awarar da ke watse cikin ƙasa tana huci tare da zaro ido ta ce,

"Kam buhun uban nan kai! Me kake nufi ne? Lalle ma ni ce zan biya ka awarar? Lalle ma yaro!"

Abin da ya faɗa ya harzuƙa yaron ya yi kanta cikin zafin nama ya ruƙunƙume ta yana ihun faɗin sai ta biya shi awararsa. Ta shiga kokawar ƙwatar kanta cikin fushi tana faɗin,

"Tun farko ba sai da na faɗa maka motar babu burki ba ka ƙi ji? To ai yanzu sai na ga uban da zai sa a biya ka awarar!"

Nan take dambe ya sarƙe a tsakanin Bintoto da mai awara, mutane suka yi dafifi ana ƙoƙarin raba su suna ƙin bari, har sai da wani dattijo ya nemo kare ya fara kai musu duka, sannan suka daina yunƙurin sake yin wani damben. Daga nan aka fara tambayar ba'asin mafarin rikicin, da aka gano Bintoton ce ba ta da gaskiya kai tsaye aka kwashe sauran awarar da ta rage. Saboda tuni yara sun daka mata wawa sun cinye mara ƙasa sai kaɗan aka bari.

Ƙeyarta aka tasa sai gidansu da bokitin awarar, tare da mai awarar da ke gaba yana rantsuwar ko da bala'i sai ta biya shi kuɗin awararsa.

Ɗanɗano.

Daga Alƙalamin D/Auta✍🏻