SHAGALALLIYA

2.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D. AUTA*

*Labarin Barkwanci.*

*LAMBA TA BIYU*

***

Suna zuwa ƙofar gidan ta yi wuf ta faɗa cikin gidan tana faɗin "Wallahi Kandala ƙarya suke yi mini ba ni ce na zubar da awarar b..."

Mutumin da ya raba su faɗan ya bi bayanta da kallo cike da takaici, sannan ya fara rafka sallama wata bayan wata cikin ɗaga murya. Daga can ciki muryar Kandala ta fara tashi tana nufo soron gidan tana zuba faɗa, don tafiya take yi tana gyara zanin da ke ɗaure ƙugunta har cin tuntuɓe tana faɗin,

"Sai na ga wanda zai saka ni biyan awarar tun da an ce da ku kuɗin banza gare ni! Haka kawai a dinga ɗora wa yarinya jarfa kullum ba za a bar ta ta huta ba sai an ce ga abin da ta aikata? To ahir ɗin ku Wallahi Allah kurwar Bintotona kur take a kanku duk sharar da kuka zuba mata sai na kakkaɓe ta! Don haka gane za ku gan ta don ta Allah ba taku ba billahillazi. Awara kuma sai na ga wanda zai saka ni biyan ta a kaf faɗin garin nan na Maidala! Tun da sharri ake yi mata ta ce ba ta san ta zubar ba."

Ta ƙare maganar tare da kwance ƙullin goronta da ke gefen kallabi ta gutsura, sannan ta mayar da shi a gefen zaninta ta ɗaure shi ta sake sokewa a jikinta. Ta shiga taunar goron tana ƙarewa kowa kallo ɗaya bayan ɗaya alamun ko daidai take da zamanin wanda ya ce cas.

Mutumin da ya jagoranci zuwan baki a sake ya dinga kallon ta kafin ya yi magana cikin tausasa murya ya ce,

"Inna kin ga yaron da ta zubar wa awara, ni zan wuce ne na ga suna rigimar shi ne na raba su. Sannan kin ga bokitin fa gabaɗaya ta zubar masa da kaya, saboda Allah hakan da ta yi kin ga ta kyauta?"

Ya ƙare maganar tare da nuna mata cikin bokitin awarar, in da sauran da ta rage ita ma ta nashe da ƙasa. Kandala ta bi bokitin da kallo a lalace sannan ta yatsina fuska ta ce,

"Ta ina ko zan ga rashin kyautawarta tun da ba a gabana aka yi ba?"

Sannan ta juya gefenta ta riƙo hannun Bintoto da ke raɓe jikinta tana muzurai, ta fito da ita gaban mutumin ta sake cewa,

"Fito tsakiya ki tsaya tsaf ki yi bayanin abin da ya faru, tun da dai ba kashe ki za a yi ba don kin zubar da awara."

Bintoto ta fito gabanta ta tsaya tana muzurai tana hararar yaron sama da ƙasa sannan ta turo baki ta ce,

"Kin san Allah Inna; idan har ni ce na zubar kwarankwatsa dubu ta faɗo a kan Malam Idi. Kuma idan har ni ce na zubar ba sharri suka yi mini ba; wallahi Allah Kandala na yarda aradu ta faɗo miki duk lokacin da aka yi hadari Kandala. Saboda ban ma gan shi ba, amma ya ce ni na zubar masa da awara don yana so a ce ni na yi wannan ta'asar. Kuma fa Innarsa ce ba ya so ta dake shi shi ne ya ce ni ce..sannan ai ke ma kin sani ba zan aikata ba ko Kandala?"

Ta ƙare maganar tana langaɓe kai ta koma alamun tausayi cike da son Kandala ta amince da zancenta. Amma maimakon ta yi nasara a kai sai Mutumin ya tari numfashin Kandalar da cewa,

"Ki faɗi tsakaninki da Allah Bintoto ba ke ce kike tuƙa motar kare kika kaɗe shi ya zubar ba?"

Kowa ya zuba mata ido a lokacin da ta shiga rantse-rantsen ba ita ce ta zubar ba, amma zancenta na ƙarshe da ta dire ya tona gaskiyar ƙaryar da take ƙoƙarin kartawa domin ta wanke kanta. Saboda kallon da ta ga ana yi mata ya sa ta fashe da kuka cikin maganar tana cewa,

"Sai da na ce masa babu birki amma ya tsaya motar ta kaɗe masa awara. Kuma tun da ba ni ba ce ai ya je wurin karen da ya yi aikin sai ya biya sh...Wallahi Kandala shi ne ya ƙi janyew..."

Mugun kallon da ta wurga mata haɗe da dundu a baya ya sa ta fasa ƙara tare da barin wurin da gudu ta yi cikin gida tana zagin mai awarar, tare da jera masa kalolin ba ta yafe ba tun da ya ta sa aka dake ta a banza.

Jikin Kandala yana tsima ta fara kumfar bakin faɗin, "In dai kuɗin awarar da kika zubar ne ko nawa ne zan biya shi tun da ba da tsiya na zo duniya ba. Kuma ko gobe kika zubar zan biya ai Allah ba azzalumin Sarki ba ne ba."

Sanin halinta ya sa Mutumin ya yi tsaye sai da aka ƙididdige awarar da ke cikin bokitin sannan aka haɗa kan kuɗin da wadda ya ce an yi masa lissafi gida tun kafin ya fito. A nan Kandala ta yi tsalle ta dire a kan cewa ba za ta biya shi kuɗin duka ba, sai dai a ware wadda ke cikin bokitin ya je ya wanke tun da shi ma da laifinsa.

Da lallami da ban-baki Kandala ta biya kuɗin awarar tana masifa sannan taron ya watse. Bayan ta gama dungure wa mai awara kai a kan duk ya kuskura ya bari ta sake zubar masa da kaya babu ruwanta.

Ta juya cikin gidan tana balbala faɗa tare da ƙwala wa Bintoton kira a kan ta ɗauko asusunta a fashe ta cire kuɗinta don ba kyauta ta biya mata ba. Bintoto da ke bayi ta sha jinin jikinta ko motsi ta kasa yi. Saboda sanin idan ta fito za ta iya dukan ta, hakan ya sa duk kiran da take yi mata bai sa ta yi motsin kirki ba. Sai da ta ji ta nufo bayin tana faɗa bayan ta gama bincike ta ko'ina cikin gidan ba ta gan ta ba.

Tsul Bintoto ta kama guntuwar katangar tasu ta dira ta bayan gidan daidai lokacin da Kandala ta faɗo bayin.

"Wayyo Allahna!"

Abin da ta faɗa kenan a lokacin da ta faɗi ƙasa ƙugunta ya daki dutse tsabar tsoron ta kama ta. Kandala ta leƙo kanta tana faɗin,

"Fitinanniyar yarinya! Ko ki dawo gida ki kawo asusunki na ɗauki kuɗina; ko kuma na tattara miki kayanki ki koma gidan Ubanki."

Bintoto ta miƙe riƙe da ƙugu ta fara ɗingisa ƙafafuwa tana yi tana waigen Kandala da ke tsaye katangar tana faɗa. Tare da yi mata kashedin kada ta je ko'ina ta dawo gida sai ta biya ta kuɗinta. Amma hakan bai hana ta tsallake gidan ta faɗa wani gida ba.

Kandala ta fito bayin ta shiga neman asusun lungu da saƙon ɗakinta. Saboda ba ta san inda ta ɓoye shi ba, domin duk lokacin da ta saka kuɗinta canza masa wurin ajiya take yi. Cikin sa'a ta ga asusun ta fito da shi tsakar gida tana cigaba da faɗan, kai-tsaye ta fasa shi ta haɗa kan kuɗin sannan ta cire nata ta naɗe mata canjinta a gefen ɗankwali. Zuciyarta cike da tunanin borin da za ta yi a lokacin da ta ga asusun nata a fashe, hakan ya sa ta tanadi dogon kare sannan ta zauna zaman jiran dawowarta.

Ga mai buƙatar group ɗina ga link

Domin samun littafin a kan lokaci kuma babu jira ya biya 1k ya same shi a Telegram. 1230094555 Access Bank Hadiza D Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan layin: ***.

D. Auta ce✍️