SHAGALALLIYA

3.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D. AUTA*

*DEDICATED TO HANNAH SUHANA*

*LAMBA TA UKU*

***

Haka Kandala ta yi ta mita har zuwa yamma, inda take ta zuba idon dawowar Bintoton amman shiru kamar an shuka dusa. Dole ta saɓa zaninta ta yafa ta fita zuwa neman ta gida-gida, sai dai duk inda ta je ce mata ake yi ta zo amma ta fita, ko kukma a ce mata ba ta je ba. A jigace ta dawo gida tana sababin faɗa tare da cin alwashin irin dukan da za ta saka kawunta Mani ya yi mata idan har ta yi nasarar kama ta.

Sai dai abin da ba ta sani ba tun lokacin da za ta je wani gidan da ke maƙotaka da su; wasu yara suka shiga gidan da gudu suka sanar da ita ga Kandala nan zuwa, cikin rawar jiki ta miƙe daga wasar ƙasar da suke yi ta yi soron gidan ta ɓoye bayan ƙyaure sannan ta sha jinin jikinta. Kasancewar soron da duhu hakan ya sa har ta wuce ba ta san da ita a saƙon ɓoye ba, sai dai tana ganin Kandalar ta shige gidan da bambamin faɗa ta fito aguje ta yi gida. A miliyan ta faɗa ɗakin Kulu ta shige ƙarƙashin gado tana sauke numfashin wahala.

Leƙo kanta ta yi daga cikin ƙarƙashin gadon tana sauke numfashin kamar ta shiɗe ta ce wa Kulun,

"Don Allah Kulu idan ta zo nema na ki ce ba ki gan ni ba."

Kulu da ke zaune tana ƙullin kukar miyar da take siyarwa; wani kallon raini ta fara yi mata sannan ta samun damar cewa,

"Wallahi ni kam ba za ki saka ni yi wa Inna ƙarya ba, haka kawai ki sa ta zo ta saka ni gaba da faɗa ina zaman zamana lafiya. Don haka sawunki a likkafa ki fito, saboda duk ta tambaye ni wallahi sai na faɗa mata gaskiya ba za ki saka ni yin ƙarya ba."

Bintoto daga can ƙarƙashin gadon ta murguɗa mata baki sannan ta ce,

"Ni ko na rantse da Allah sai na kashe miki ɗiyan kaji duk kika tona mini asiri."

Babu shiri Kulu ta kafe ta da ido a lokacin da take ƙoƙarin ƙulle wata ledar kukar da ke hannunta, kai-tsaye ta ajiye ledar ta fasa ƙullewar cikin masifa ta nufo bakin gadon gadan-gadan don daman cike take da kalolin rashin kunyar da take yi mata, a zafafe ta duƙa ta janyo ta ƙii iya ƙarfinta tana faɗin,

"Fitar mini daga ɗaki marar kunyar banza fitsararriya!"

Bintoto ta ƙara komawa tare manne jikinta riƙe ƙarafunan gadon ta ƙarƙashin gadon tana faɗin,

"Ai na rantse da Allah ba zan taɓa fita ba tun da ba daga gidanku kika zo da ɗakin ba!"

Ita ko Kulu ta nace a kan dole sai ta fitar mata ɗaki ko kuma ta jibge ta, da haka rigima ta kacame a tsakaninsu har Kulu ta ci nasarar fito da ita ta ƙarfin tsiya, saboda ƙarfi ba ɗaya don ta girme ta sosai ƙarfin hali ne kawai ɓarawo da sallama.

Ai ko fitowar Bintoto ke da wuya ta yi cikin Kulu da duka kamar wata mai ƙarfin gaske. Kulu ma ta cire tsoron Kandala ta saki jiki ta dinga jibgar ta iya ƙarfinta tamkar an ba ta umarni. Wuya ta sa Bintoto ta fara ihu tare da kiran sunan Kandala a haukace tana faɗin ta yi sauri ta zo Kulu za ta kashe ta. Amma ganin Kandalar ba ta zo ba kuma ba za ta iya da ita ba; hakan ya sa ta ratumi ƙwaryar kukar Kula ta juye mata kukar duka a jikinta, tun daga fuskarta har tsakiyar ɗakin duka kukar ta barbaɗe, sannan wadda ta ƙulla ita ma ta dinga farfashe ledodin tana zubarwa a tsakar ɗakin tana faɗin,

"Ni za ki daka? B ni kika daka a banza ba! To wallahi na rama ni ma!"

Tsabar baƙinciki da takaici ya sa Kulu tsayuwa riƙe da ƙugu tana kallon ta'adin da take yi mata baki a sake. Cike da mugun jin haushin ɓarnar da ta yi mata bayan asara; Kulu ta bi ta da kallo ranta a matuƙar ɓace ta yi kanta tamkar wata zakanya, cikin matsanancin fushi ta fisgo Bintoto sai jin ƙarar rugujewar kwanonin jeren ɗakin Kulu Kandala ta jiyo rifff. Wadda shigowarta gidan ke nan daga yawon neman Bintoton ranta a ɓace tana wassafa irin dukan da za ta yi mata idan ta riƙa ta.

Gabaɗaya kwanonin da aka yi wa Kulu jere da su duk sun zubo musu a jiki, don ko da Kandala ta shigo ɗakin ta tarar da Kulu saman Bintoto a tsakiyar kwananin ta taushe ta tana ta kai mata kalolin duka inda ranta ya yi mata daɗi. Ita ko sai ihun neman ceto take saboda har da kwanonin Kulu take haɗawa wajen hushe haushin ta ga Bintoton.

Babu zato ta ji muryar Kandala a saman kanta tana salati, hakan ya sa ta yi saurin zabura ta ɗaga Bintoton da ke ta kuka iya ƙarfinta tana faman kiran sunan Kandala ta zo za a kashe ta.

A firgice ta miƙe ta yi wurin Kandala tana ihun wayyo Kulu ta karya mata hannu, Kandala kam saboda mamakin irin abin da Kulu ta aikata mata ko motsin kirki kasa yi ta yi, sai da ta ga Bintoto da hannu a sage tana ihu sannan ta dawo natsuwarta. Cikin ruɗewa ta kalli Kulu a masifance ta ce,

"Allah ya toni asirinki munafuka! Ashe daman maganar da Bintoto take faɗa mini kullum a kanki gaskiya ce? To Wallahi bari Mani ya zo kin gama zama cikin gidan nan baƙar almura mara imani... ke tun kafin ya zo ma maza ɗauki mayafinki ki bar mana gida tun da babu kuɗinki cikin ginin shi. Sannan ni Kandala uwar Mani daga yau na haramta miki zama cikinsa ki je na kore ki kuma na sake ki saki uku ringis ƙwarara. Gayyar na ayya gayyar tsiya wadda kakanki har ya bar duniya ko likkafanin da za a saka masa sai da aka bashi sadakarsa tsabar tsiya irin ta zuri'arku. Bayan ficika bai bar wa ubanki gado ba, haka ya bar shi yana watangaririya a cikin gari da riga guda ƙyalau-ƙyalau kullum rai da rai kamar fatar dabbobi."

Kulu ta fashe da kuka tana ba ta haƙuri amma Kandala ta kafe dole sai ta bar gidan, dole ta ja mayafinta ta fice tana kuka iya ƙarfinta. Bayan fitarta gidan Kandala ta dawo da kallon ta ga Bintoto hankali a tashe ta riƙo ta suka fito gidan tana ihu da kuwwar wayyo Kulu ta karya mata hannu.

Ba ta zame da ita ko'ina ba sai gidan mai ɗori, da ƙyar da walahaula aka gyara wa Bintoto hannun don Kulu ta goce ta, sannan suka dawo gida ta shinfiɗa mata tabarma ta kwanta sai nishi take yi tana sharar ƙwallah. Kandala tana mata fifita tare da jera mata sannu tana mita har ta samu ta yi bacci, sannan hankalinta ya kwanta ta dawo jimamin kuɗin da Bintoton ta sa ta kashe a wunin ranar don ta sani ficika ba za ta yi ciwon kai ba a cikin kuɗinta da ke asusu. Saboda har ta sayi wani sabo ta mayar mata da kuɗin kamar yadda ta gan su.

Tana zaune tana tsine wa Kulu a ranta, don daman can bala'in haushin kulun take ji, saboda yadda take cin zalin Bintoton a duk lokacin da ta fakaici idonta.

Sallamar Hari ce ta katse mata zancen zucin da ta ke yi, cikin sauri ta washe baki tana yi mata lale marhaban, saboda ba ƙaramin girmama Harin ake yi ba a cikin garin nasu na Maidala.

Shin wace ce Hari?

1k ne kacal ku mori laratunku babu jira. 1230094555 Access Bank Hadiza D Auta. Shaidar biya ta wannan lambar: ***.

D. Auta ce.✍️