4.
*SHAGALALLIYA*
*HADIZA D. AUTA.*
*LAMBA TA HUƊU.*
Jikin Kandala yana rawa ta miƙe da nufin kawo mata sabuwar tabarma, amman Hari ta nufi wata kujera 'yar tsugunno ta dawo wajen da su Kandalar suke ta ajiye ta zauna, sannan ta ce da Kandala da ke ƙoƙarin shigewa ɗaki da nufin ɗauko tamarma ta ce,
"Ki dawo kawai Inna Kandala ai na samu abin zama."
Kandala ta waigo tana washe baki ta ce,
"Da dai kin bari na kawo miki tabarmar ta fi kujerar daɗin zama, ko ba komoi kya miƙe ƙafa ki sarara ga shi kin kwaso hanya."
Hari tana dariya ta ce, "Babu komai Inna, dawo abin ki ai nan ma ya yi mini, da ma can gaishe ki kawai na zo yi sauri nake yi, saboda ana nema na a can birnin."
Kandala ta dawo tana wasar baki ta ce, "Ai kin kyauta, gara da kika biyo a yi zumunci, ko banza Hausawa sun ce a rabu a gana arziƙi ne."
Hari ta washe baki tana cewa, "Haka ne Inna, ai ya zama dole gare ni na zo gaishe ki ko don ki yi mini addu'ar da kika saba."
Tana gama maganar ta kai kallonta ga Bintoto da ke barci ta sake cewa,
"Bintoto lafiya ko? Na ga tana barci da wannan yammacin haka Inna. Ko dai ciwo ta ji ban da labari? Na ga hannunta da sabon ɗauri.
Kandala ta dawo inda take farko ta zauna, sannan ta ɗauki mafefeci ta ci gaba da yi wa Bintoto fifita sannan ta ce,
"Kin san 'yar taku da rashin jinta Hari, to yau ma garin jan maganarta ne ta jayo matar Mani saura ƙiris ta nakasa ta a banza, don dai Allah bai nufa ba kuma ya ya tsare abin ya tsaya a gocewar hannu, kin gan ta nan; yanzu muka dawo daga wurin mai ɗorin, ta sha kuka kamar babu gobe."
Hari ta ɓata fuska cikin damuwa ta ce, "Ni na rasa wa Bintoto ta gado da wannan rawar kan nata, don kowa ya san daga Habi har Buba babu wanda yake da hayaniya a cikin su, amman ita kullum daga wannan sai wancan?"
Kandala ta goge guntuwar ƙwallarta da ta taru gefen idonta sannan ta ce,
"A kan rashin jinta yau har jikka uku da rabi ta sa na salwantar, ga shi sallah ta ƙarato duk tarin kuɗin da nake yi, ina yi ne kawai a kan ɗinkin da nake so na ɗinka mata ta fito kamar kowa, amman yanzu ta jawo kuɗin sun samu mugun giɓi, ban kuma san har yaushe zan sake tara wasu kuɗin ba."
Hari ta yi shiru na ɗan lokaci tana nazari sannan ta ce,
"Wai Inna ko dai za ki ba da ita na kai ta birni ta yi aikatau? Kin ga idan ta dinga aikin za ta samo muku abin da za ku dinga ɓatarwa ke ma ki huta faɗi-tashin da kike yi. Don a ganina gara aikin ya fi, da wannan yawon ɗaukar maganar da take yi miki a cikin gari."
Kandala ta yi saurin girgiza kai tana faɗin, "Ina! Ina! Daina faɗa Hari, ai ke ma kin san ba zan iya rabuwa da Bintoto ba, saboda ita nake kallo a madadin Habi idan na rasa ta kusa da ni ban san wane irin hali zan shiga ba. Don haka gara ɗaukar maganar da a ta yi mini nisa ba zan iya ba gaskiy...."
Nan take Kandala ta fashe da kuka wiwi har da fyace majina da gunjin kuka. hankalin Hari ya tashi ta fara roƙon ta a kan don Allah ta yi haƙuri ta daina kukan, saboda girman abin bai kai yadda ta ɗauke shi ba. Saboda kukan nata Bintoto ta tashi daga barcin da take yi, ta miƙe zumbur saboda ta manta da tana da wani ciwo a jikinta, ai kuwa sai ga ta da komawa ta kwanta babu shiri tare da fasa wata uwar ƙara tana faɗin,
"Wayyo hannunta!"
Kandala ta ja ta jikinta tana ci gaba da kukanta tamkar wadda aka ce a ranar za a raba su, da ƙyar Hari ta shawo kanta ta daina kukan, sannan ta dinga ba ta baki a kan ta yi haƙuri da maganar da ta yi mata, don da a ce ta san har haka ranta zai ɓaci da tun farko ba ta yi mata ba, cikin sanyin jiki Harin ta ciro kuɗi ta ajiye a gaban Bintoto sannan ta miƙe tana yi musu sallamar tafiya, cikin rashin sukuni suka rabu ko rakiya babu.
Hari ta fita zuciyarta cike da alhinin rabuwa da ƙawarta Habi mahaifiyar Bintoto, wadda suka taso tare tun suna 'yan yara, kafin mutuwa ta yi musu katangar ƙarfen da ta shata layi a tsakaninsu. Sannan Habin ita ce auta a wurin Kandala, kuma ita ce ɗiyar da ta fi so a cikin 'ya'yanta, garin haihuwar Bintoto Allah ya yi mata rasuwa, hakan ya sa ta damƙe Bintoto a hannunta ko ƙuda ba ta so ya taɓa ta.
Sannan kuma ta ɗauki son duniya ta ɗora a Bintoto, don ko shayar da ita da ƙyar ta bari 'yarta Jimmala ta shayar da ita, wadda ta zamo yaya ga mahaifiyar Bintoton, ana yaye ta ta karɓe ta ta dawo hannunta, tun daga lokacin hidimarta ta koma kanta, don a yadda take ji ko ubanta bai isa da ita ba ganin yadda take da matsayi a wurin ta. Dole ya zuba mata ido ya bar ta da ita, tsakaninsa da su ranar da ta ga damar kai masa ita ta ya gan ta, tun tana ƙarama har girmanta ya kawo kai.
Fitar Hari ya bai wa Kandala damar ƙyalla ido ta hango 'yan dubu-dubu da Harin ta ajiye mata a kan gefen tabarma, babu shiri ta share hawayenta ta kai wa kuɗin wawura, Bintoto ma ta yi saurin damƙe kuɗin da hannunta mai lafiya, saboda sanin idan suka shiga hannun Kandala babu rabonta. Ai kuwa Kandala ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin ɓanɓare kuɗin a hannunta tana cije baki tana faɗin,
"Ai wallahi yau ƙwandala ba za ki ci a cikin kuɗin nan ba, tun da har kika jawo na yi asarar ƙudina a banza a wofi garin rashin mutuncin da kika saba."
Bintoto ta damƙe kuɗin iya ƙarfinta ita ma Kandala ba ta daina son ƙwace kuɗin ba, ganin ba za ta iya ɓanɓare kuɗin ba ta soka mata haƙorinta na gaba, wanda ya bindiro waje ko ta rufe bakin shi ba zai yiwu ya rufe ruf ba, babu shiri Bintoto ta saki kuɗin tana yarfa hannu tare da faɗin,
"Wayyo Kandala! Yanzu a kan kuɗi za ki huda mini hannu da haƙorinki mai wuƙa??"
Kandala tana haɗa kan kuɗin cikin sauri ta ce,
,"Ko mashi haƙorin nawa ya koma ba zan ji shayin soka miki shi ba a kan kuɗin nan, ballantana haƙorin da ko ko kaifi bai da shi amma kin kira shi da sunan wuƙa. To ba wuƙa ba ne zarto ne don malfar ubanki."
Bintoto tana ci gaba da yarfa hannun ta ɓata fuska ta ce,
"Ai da a ce zamanin yaƙi muke yanzu da wallahi ko shi zai yi jahadi wajen kashe miyagun arna, don tsaf zai iya komawa takobi ya kai sara ba tare da an tantance ba."
Wata muguwar dariya Kandala ta fashe da ita tare da buɗa gefen zanenta ta ƙulle ƙudin ta tsuke tsukut, sannan ta soke zanenta a jiki ta ɗauki mafefecin ta ci gaba da yi mata fifitar tana faɗin,
"Yanzu dai duk abin da za ki ce ki faɗa daidai kike. Ni dai kuɗi na haɗe musu kai na soke a jikina, idan kin isa ki tashi ki ƙwata mu gani."
Bintoto za ta yi magana kenan sai ga Kulu ta yi sallama ta shigo gidan, jiki a sanyaye ta nufo su gabanta yana faɗuwa, tana zuwa ta duƙa tana share hawayen ta ce,
"Inna, don Allah ki yi haƙuri wallahi ba da son raina na daki Bintoto ba. Tsautsayi ne da sharrin shaiɗan."
Kandala ta watsa mata wata muguwar harara sannan ta ce,
"Ai kuma tun da na riga da na sake ki to ki sani kin saku yarinya, abin da ya rage kawai ki kwashi tsommakaran haukarki ki koma gidanku, aure ya riga ya ƙare babu fashin barin gidan, ke da Mani haita-haita tun da kika dakar mini Bintoto. Don ko Mani ne ya yi mata abin da kika yi mata sai ya san ya aikata, ballantana ke 'yar karan kaɗa miya, ki zauna gidan naku ki ji idan da daɗi. Daga wannan karon Mani ya gama zama da ke, wallahi kin ji na rantse a kan Bintoto ban ƙi na tayar da garin nan ba."
Akafta😛
Na kuɗi ne. 1k kacal ku garzaya Telegram ku more karatunku babu jira. 1230094555 Access Bank Hadiza D Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan layin: ***.
D/AUTA ce✍🏻