SHAGALALLIYA

5.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA TA BIYAR*

Kulu ta sake fashewa da kuka tana yi wa Kandala magiya a kan ta yi haƙuri ba za ta sake ba, amma hakan bai sa ta karya mata zuciya ba, ba illa ɗaga kai da ta yi sama tana kumbura hanci alamun magiyarta ko a jikinta. Ana cikin hakan sai ga Mani ya shigo ransa a ɓace saboda ya samu labarin Kandala ta kori kulun, takaici ya saka shi zuwa har gidansu ya roƙi iyayenta ta dawo ɗakinta. Saboda ya tabbatar musu shi bai saki matarsa ba, kuma yana son zama da ita.

Wannan dalilin ya sa ya ƙi biyo ta ya ce ta fara zuwa, ko da ya shigo gidan kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kai, don bai bi ta kansu ba ya nufi ɗakin Kulun kansa tsaye, Kandala ta bi shi da kallo cike da mamaki sannan ta ƙwala masa kira tana cewa,

"Ban gane ba Mani! Wai an yi yamma da kare, shin kana nufin ba za ka zo ka duba Bintoto a kan aika-aikar da matarka ta yi mata ba ne ko me kake nufi?"

Ba tare da ya juyo ba yana haɗe rai ya ce,

"Allah ya ba ta lafiya! Amma ni ban saki Kulu ba kada ta sake fita ko'ina ban amince b..."

Yana maganar ya shige ɗaki, Kandala ta riƙe baki tana juya zancensa a ranta, sannan ta ajiye mafefecin da ke hannunta ta miƙe jikinta yana rawa ta bi shi har ɗakin Kulun, labule ta ɗage ranta a ɓace ta ce masa,

"Kana nufin haushi na ka ji don na kori matarka?"

Mani bai ce da ita ƙanzil ba, hakan ya sa ta sake magana a harzuƙe, "To ai tun da ka ce ba ka sake ta ba to ta dawo ta zauna, amman ka sani babu hannuna babu ƙafata da lamarinku balllantana wani abu da zai shafe ku dukanku kai da ita! Kuma wallahil'azimi a kan Bintoto zan iya bar muku gidan nan sai ku cinye shi kai da ita! Tun da ka nuna ka fi son ta a kan ɗiyar ƙanwarka uwa ɗaya uba, kuma wadda ka saki nono ta kama."

Tana gama faɗar hakan ranta a ɓace ta saki labulen ta bar wurin, kai-tsaye ƙofarta ta nufa duk da magiyar da Kulun take yi ba ta kula ba, sai ma buta da ta ɗauka ta yi bayi saboda kiraye-kirayen sallar magaribar da aka fara yi a lokacin.

Amma har ta fito bayin ta gama arwalar ta shige ɗaki bakin Kulu bai yi shiru da ban haƙurin ba. Sai da ta fara sallah ita ma ta je ta yi arwallar ta yi nata ɗakin sum-sum. Bintoto da ke kwance tana bin su da kallo ta bi ta da harara tare da murguɗa baki bayan ta yi ƙwafa a ranta ta ce,

'Munafuka! Ai ko haka aka bar ki kin sha wuya bak'ar muguwa, sai shegen baƙin ƙarfi tamkar wata zakanya, idan ban da Allah ya kawo Kandala da shi kenan sai ta ga na mutu za ta kyale ni...ai kuma wallahi sai kin sani don a kan kajinki zan huce haushina...ke duka ma sai na kashe su a gidan nan, ko kuma na yi ta jefa shegu a cikin masai suna mutuwa kowa ma ya huta.'

Gama zancen zucinta ke da wuya ta miƙe ta nufi wajen akurkin kajin Kulu ta jawo ɗiya biyu suna tsuwwa tsui-tsui, amma a haka ta je bayinsu cikin sauri ta jefa su masai, sannan ta rufe masan da murfi ta fito cike da jin daɗin ta yi ramuwar gayya.

Daren ranar suka yi kwanan takaici kowa da ƙuncin da ke damun shi, don Mani da dare sai da ya zo yana ta bai wa Kandala haƙuri amma ta ƙi kula shi, dole ya ƙyale ta ya koma wurin Kulu yana ƙara lurar da ita a kan yadda za ta zauna da Kandala da shalelenta ko don su samu zaman lafiya da su a huta da halinsu.

Haka rayuwa ta ci gaba da shurawa zaman lafiyar gidan ya yi ƙaranci, saboda kullum da sabon rikicin da Bintoto za ta jawo har ta sa a yi gagarumin faɗa a kansa.

Ana cikin hakan ne watarana ta ɗauki tallar goron da take yi idan ta ga dama, don sana'ar Kandala kenan siyar da goro da nono da man shanu, sai dai mafi akasari an fi zuwa gida a saye ba a cika fita zuwa tallar ba. Amma ranar da Bintoto ta yi sha'awar tallar don kanta tana ɗauka ta tafi yawon da ta saba yi da sunan tallar.

Hakan ta faru a ranar, Kandala ta lissafa mata goron a tire kowane da adadin kuɗinsa sannan ta rufe mata da wata raga mai riƙon ruwa. Wadda aka jiƙe sharkaf da ruwa don kada goron ya sha iska ya yi saurin bushewa.

Ta yi ɗana da tiren goron tana tafe tana wasa da wani zare a hannunta hankalinta gabaɗaya ya ɗauku a kan wasar da take yi. Babu zato ta ci karo da wani saurayi suka yi kiciɓis, Cikin tsautsayi kafin ta kamo tiren goronta tuni ya yi sama ya dawo ƙasa ya kife, kafin ta ankara ya watse ɗaiɗaya a cikin ƙasa.

A zabure ta ɗaga kanta cikin fushi ta yi magana tana zaro ido.

"Kan uban nan! Ai na rantse da Allah sai ka biya shi! Cabɗijam haka kawai ka sa na yi ɓari don ba ka da imani?"

Ɗan saurayin ya duƙa cikin rawar jiki ya fara tsince mata goron ɗaya bayan ɗaya yana sakawa a cikin tire har ya tsince duka, sannan ya ɗauko ragar ya saka mata a cikin tiren ya miƙe fuska babu yabo babu fallasa ya isa gabanta ya tsaya yana 'yar dariya ya ce,

"Don Allah ki yi haƙuri wallahi ba da gangan na yi b.."

Wani kalar kallo ta yi masa, tare da ƙura masa ido ƙur ko ƙiftawa babu riƙe da ƙugunta tana girgizar jiki, sosai ta so saka shi dariya, amma dole ya ƙumshe dariyar da ta so kufce masa saboda gudun ya ƙara tunzura ta. Ya koma gyara goron a cikin tire kamar wanda aka saka sai ya mayar da shi yadda yake. Sai da ta gaji da hararar sannan ta ja baya tana ce masa,

"Ai na rantse da Allah kuɗin gorona za ka ba ni gabaɗaya, na riga na sayar maka! Don haka ka biya ni kawai ka juye goronka sauri nake yi. Amma ka sani guda ɗaya ba zan karɓa ba don ni na sayar maka da shi duka kawai ka ba ni kuɗina na koma gida."

Ganin idan ya biye ta za ta iya tara masa mutane, hakan ya saka shi tambayar ta kuɗin goron. Sai da ta karkace kai gefe sannan ta zaftaro kuɗin da ya saka shi zaro ido yana ƙare wa goron kallo, saboda ta ce atafau ita goronta na dubu ɗaya ne, bayan kwata-kwata goron ko ɗari biyar bai kai ba. Saboda wani ma gyaran tsutsa ne wanda bai wuce ashirin naira hamsin ba, amma saboda a zauna lafiya haka ya saka hannu a aljihu ya ciro ɗari biyu guda biyu huɗu ya miƙa mata. Sai da ta kalli kuɗin sannan ta maka masa harara tana ci gaba da girgizar jiki kamar wata babbar budurwa ta ce masa,

"Ai wallahi tun da ba tsohuwa nake ba ni ko ba zan karɓi tsofaffin kuɗi ba! Haka kawai don mugunta ga sababbi nan ina gani ka ba ni su, shi ne za ka haɗa ni da waɗanda kafin na je gida sun yage? To ni kuma wallahi ba zan karɓe su ba ahe!"

Ta ƙare maganar tare da murguɗa masa baki tare da juya kai gefe, ba ƙaramar dariya ta so ba shi ba, amman ya dake ya nuna mata ko kaɗan bai ji haushi ba. Ya mayar da kuɗin ya ɗauko mata sababbin da take so ya miƙa mata, jikinta yana rawa ta fisge kuɗin sannan ta sake cewa,

"Allah Ya taimake ka ka biya da sai na yi maka dukan billahillazi, kuma ina zan juye maka goron ni sauri nake yi?"

Sai da ya mayar da sauran kuɗin a aljihunsa sannan ya ce mata ta je duka ya ba ta.

Bintoto ta zaro ido waje cike da jin daɗi da mamaki a kan fuskarta ta ce,

"Da gaske?"

Yana murmushi ya ce, "Da gaske mana, amman da sharaɗin duk lokacin da na zo gidanku za ki fito mu yi hira."

Bintoto tana dariya baki a washe ta ce masa, "Ai idan har za ka ƙara ba ni irin waɗannan kuɗin sababbi dole zan fito kai ma ka sani, don haka ka zo kawai."

Ya juya yana 'yar dariya ya fara tafiya, ta bi shi da kallo kafin ta ɗaga murya tana cewa,

."Don Allah ta wace hanya za ka bi gobe?"

Babu shiri ya waigo cike da mamaki ya jefo mata tambayar "Lafiya?"

Tana wasar baki ta ce, "So nake yi ka sake zubar da goron, ai na san za ka saya ko?"

Bakinsa ya dafe saboda dariyar da ta suɓuce masa, amma a haka ya ba ta amsa da cewa,

"Ki biyo ta nan za mu sake wani karon kamar yau. Amman fa a goben ko kin zubar da goronki ba zan biya ko ficika ba."

Bintoto ta murguɗa masa baki da hararar gefen ido ta ce,

"To na ji, shi kenan ta fi kawai."

Ya juya yana dariyar shirmenta, saboda sai da ta sake ɗaga murya ta jefo masa tambayar, "Amma dai kai ba ɗan garin nan ba ne ko?"

Ba tare da ya juyo ba ya ce mata "E, baƙunta na zo."

Ta bi bayansa da harara sannan ta ɗora tirenta a kai tana haɗa kuɗin wuri ɗaya tana cewa ,

"Ai dai na yi maka wayo, kuma duk ka kuskura muka sake haɗuwa gobe ma sai ka zubar, kuma dole sai ka sayi goron ka bayar da kuɗin sababbi. Baƙin mugu kana da kuɗi da yawa a aljhunka amma ka ce ba za ka biya ba don kada na ƙaru da kai. Hu'umm! ai yasin ba ka isa ba ma duk muka sake haɗuwa dole ma sai ka sake saya tun da wawa ne kai ba ka da wani wayo."

Haka ta yi ta sambatunta ita kaɗai kamar a gabansa take yi, sannan ta je wani gida ta wanke goron ta sake jera shi a tire yadda yake tun farko, sannan ta yi wurin tallar a ranta tana cewa,

_"Ina ma na samu wani hamagon da zai sake zubar da goron ya biya ni. Yasin da gangan zan kifa wa mutum tiren na ƙwale masa kai kuma ya biya ni kuɗin gorona."_

Ku ci gaba da biyo ni don wannan duka shimfiɗa ce a cikin littafin SHAGALALLIYA😊 1k ne kuɗin, za ku same shi a Telegram ba tare da kun yi jira ba. A WhatsApp ma ga mai buƙata PC saboda gudun hayaniya zai iya zuwa mu yi tsada. 1230094555 Access Bank Hadiza D Auta. Lambar waya don turo shaidar biya ko wani ƙarin bayani: ***.

Akafta.