SHAGALALLIYA

7.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA BAKWAI.*

Sai da Mani ya bi ta da harara har da ƙwafa sannan ya nufi ƙofar ɗakin Kandala, wadda ke cikin ɗaki tana ƙoƙarin yi wa kuɗin mugun ɓoyo. Da sauri ta fito bayan ta adana ta tsaya bakin ƙofar ɗakin tana faɗin,

"Lafiya na gan ka a nan?"

"Bintoto ta ce kina nema n..."

"Kul...Kulu ce take neman ka tun ɗazu, ka yi tafi ka ji wataƙila kazar da ta dafa take son ba ka."

Mani ya yi tsaye yana ƙumshe dariya, saboda ya gama gano akwai abin da take ɓoyewa wanda ba ta son ya gani, cikin dariya ya fara ƙoƙarin kutsa kansa da niyyar shiga ɗakin yana cewa,

"Akwai fura a ɗakin nan na sha?"

Kandala ta tare ƙofar tana faɗin,

"Je wurin matarka yanzu ta gama dama ta da zafinta."

Mani ya juya yana dariya ya ce,

"Bari dai na je na dawo Inna, wallahi yau aljihuna ƙaf nake ko kuɗin sayen dawar da za a yi tuwo babu a gidan nan."

Kandala ta bi shi da harara sannan ta ce, "Aikin kenan ba ni-ba ni kullum kai ba ka iya wani motsin arziƙi sai na zillo da dogon wuyan a ba ka a ba ka. Sarkin maroƙan duniya ma dole ya shafa maka lafiya a wajen son banza. Wallahi dai ka san ciwon kanka tun kafin lokaci ya ƙure maka, saboda watarana ake wa gudu idan ƙasa ta shafe idona. Don haka tun yanzu ka yi ta kuka tun da kai ba ka san yadda ake juya kwabo ya koma sisi ba."

Dariya kawai Mani ya dinga yi yana sosa kai, ba tare da ya juyo ba ya nufi ɗakin Kulu don ya saba da gorinta a duk lokacin da ya nemi wani abu daga hannunta. Kuma a haka yake shanye duk abin da za ta faɗa masa matuƙar za ta ba shi abin da ya nema. Saboda zuciyarsa a mace take da kallon abin da take da shi da abin da ta samu, shi ya sa yake zaman kashe wando a majalisin hira cikin abokansa masu zaman banza, ba su da aiki sai yi da mutane wane ya samu kaza wane kaza ya rasa.

Kandala ta gama faɗanta da Mani ta juyo kan Bintoto da ke ta ƙumshe dariya, don ta san ta gama tsokano fushin Kandala dole ta kama kanta ko kuma ta saka ta ɗaki ta rufe sai ta yi kuka ta gama jigata sannan ta fito da ita, don da wuya ta dake ta gudun ta illata ta, saboda ba ta iya dukan yaro ba idan ranta ya ɓace sai ta ji masa rauni take jin sanyi.

Cikin ƙufula ta ce mata,

"Idan ma ɓakin surutunki ya jawo ya karbi kuɗin to kin yi wa kanki asarar ɗinkin sallah, kina ji kina gani kowa zai fito da sababbi kayan sallah ban da ke, tun da ke ba a rufin asiri da ke sai kin tona mutane, to ki je ki ce ya zo ga kuɗin ya ƙwata tun da uban wani ya nema mini su! Wallahi ki kiyaye ni ko a cikin kwanan nan na mayar da ke gidan ubanki na huta da halinki."

Tana gama faɗar hakan ta janyo ɗakinta ta rufe da kwaɗo ta fice gidan, Bintoto ta bi ta da wani kallo tana zunɓurar baki wai ita ta ji haushin an zagi Babanta. Ta haɗa kai da gwiwa tana ta mui-mui da baki tana gungunin faɗar duk abin da ya zo bakinta da harare-harare. Daga nan ta ɓingire tana ta barci saboda garin kwakin da ta sha ya saka ta jin daɗin yanayin har da minshari, sai dai ko'ina barcin nata bai je ba ta ji kaji a saman jikinta suna tsuwa.

"Tsui! Tsui! Tsui."

A firgice ta farka tare da kaiwa uwar kajin da ke kusa da ita wani uban duka, a bisa tsautsayi kazar ta zille ita ta naushi ƙasa. Babu shiri ta fasa ƙara saboda hannun da Kulu ta ji mata ciwo ne, Mani da ke fitowa daga ɗakin Kulun ya nufo ta cikin sauri yana tambayar,

"Lafiya? Me aka yi miki kuma yanzu?"

Bintoto ta miƙe tsaye tana kuka riƙe da hannu ta fice gidan ko kallon shi ba ta tsaya yi ba, haushi ya saka shi kai kallonsa ga ƙofar ɗakin Kandala, ganin shi a rufe ya fice yana 'yar dariya don ya san a kansa ta rufe ɗakin ta fice, don ma kada ya fito ya same ta idan ya yi mata magiya ta ba shi kuɗin da ya nema.

Minti goma sha biyar da fitar Bintoto sai ga muryar Kandala tana ta surfa ruwan bala'i da tsine-tsine, tana shiga ba ta zame ko'ina ba sai wurin kara, ta ciro wani ƙaton karen dawa mai bala'in ƙwari ta bi 'yan kajin Kulu da gudu tana duka. Kulu da ke ɗaki ta fito saboda jin kukan kajinta, ganin Kandala da gudu tana dukan kajin ya sa ta sha jinin jikinta, don ta gama gano sun jawo mata wata sabuwar fitinar da take gudu. A ckin rashin sa'a Kandala ta bi uwar kajin da gudu tana duka, sai ga ta da cin tuntuɓe da ƙatuwar tukunyar ƙarfen Kulu, wadda ke cike taf da ƙasari babu zato ta faɗi tim a ƙasa Sannan ƙasarin duka ya fantsama jikinta ya yi mata wanka. Kandala ta fasa wata arniyar ƙara dafe da ƙugunta tana faɗin,

"Wayyo ni Allah wayyo ni kaina! Ke kam Allah ya tsine miki Kulu daga ke har 'yan kajinki, wallahi yau-yau sai sun bar gidan nan ko kuma ke ki bar shi tun da ba gidan Isuhu mai mola ba ne!"

Kulu ta fito daga inda ta rakuɓe ƙirjinta yana bugawa, ganin irin faɗuwar da Kandala ta yi mai haɗe da mugun walle, cikin rawar jiki ta isa wurin tana ƙoƙarin ɗaga ta sama da niyyar taimaka mata ta miƙe, amma babu kunya Kandala ta saka ƙafa ta kai mata harbi a gefen fuskarta, babu zato Kulu ta faɗi daɓas saboda tsabar tsoron Kandalar ya shige ta ganin abubuwan da ke ta faruwa duk a sanadinta.

Da rarrafe Kandala ta miƙe da ƙyar tana faɗin wayyo, dafe da ƙugunta tana jan ƙafafu da jan numfashi ta koma faɗin,

"Dole na koma wurin Ɗantani mai gyaran karaya ni ma ya duba mini ƙuguna, wallahi Mani ka ci amanata da ka auro Kulu ka kawo mana ita a cikin gidan nan! Ke kam Kulu Allah ya wadaranki ya tsine miki albarkar dare da ta safiya. Wallahi na faɗa da babbar murya Kulu ban yafe miki ba! Saboda kin zamo mana fitina ke da tsinannun kajinki, marasa mutunci da rashin imani, kuma 'yan ƙasan wutar jahannama da ta hawiya!"

To fa! A taushi ƙugun Kandala kafin ta kasa tafiya mu shiga uku😂

1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lambar; ***.