SHAGALALLIYA

8.

by @princessdija

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA TAKWAS.*

A haka ta fice gidan tana ɗangishi tare da ƙara tsine wa Kulu da kajin nata. Kulu kam duk da take cikin tsoron abin da zai je ya dawo hakan bai hana ta fito da dariyar da take faman ƙumshewa ba. Musamman idan ta tuno da irin faɗuwar da Kandala ta yi mai haɗe da walle, sannan da kalar harbin da ta kai mata da ƙafa har ta faɗi kamar wata 'yar wresteling. Tuno abin da ke gabanta ya sa ta ta samo buhu cikin sauri ta dinga kama ɗiyan kajin tana sakawa, sannan ta kamo uwarsu ta damƙe a hannu da sassarfa ta fice gidan zuwa gidansu. Da nufin koma can sa zama don ita ma ta gaji da fitina tana so ta huta, saboda masifar da suke jawo mata koyaushe rigima ta tashi cikin gidan a kansu ne ake yi.

Ko da Kandala da Bintoto suka dawo gidan ba ta dawo ba, don da tsaya bayar da labarin fitintinun da kajin suke ja mata. Bintoto ɗauke da hannu Kandala dafe da ƙugu, a haka suka nemi wurin zama kowa da kalar zogin da yake ji .

Zamansu ke da wuya Kulu ta dawo gidan kai-tsaye wajensu ta nufo da nufin yi masu sannu, sannan ta ba da haƙuri duk da ta san ba lalle ne Kangala ta yafe mata ba kamar yadda ta furta. Hakan ya sa tun kafin ta ƙarasa inda suke Bintoto ta fasa wata uwar ƙara tana cewa,

"Kandala ki hana ta zuwa wurin nan wallahi ba na son ganin ta!"

Kandala ta yi saurin kallon Kulu da jar harara tana faɗin, "Kul kada ki ƙaraso wajen nan! Baƙar azzaluma! Ki tafi kawai mun bar ki da Allah, idan muka je lahira a yi mana hisabi da ke a gaban bainar jama'u!"

Kulu ta marairece fuska tana faɗin,

"Don Allah Inna ku yi haƙuri, yanzu haka ma na kwashe kajin gabaɗaya na kai su gidanmu, saboda ni ma ba da son raina suke yin abin da suke yi b.."

Kandala ta buga wani uban tsakin da ya saka Kulu dire maganarta babu shiri, saboda ganin yadda take jujjuya baki tana mayar da shi gefe kafin ta ce,

"Ke dai kawai ki ce watan mutuwarsu ne ya kama, don ko tantama babu yunwa ce za ta yi ajalinsu a gidan naku, tun da ko su masu gidan neman abin da za su ci suke yi, ballantana a samu na bai wa tsinannun kajin."

Cike da bala'in jin haushin Kandala a kan cin zarafin da take yi wa gidansu koyaushe babu alkunya, Kulu ta miƙe tana ɓata fuska cikin gunguni ta ce,

"Ai duk tsiyarmu ba za mu rasa geron da za a watsa musu ba."

Tana maganar tana tafiya Kandala ta bi ta da ƙatuwar harara tana cewa,

"Dawo ki ci gaba da zagin nawa da kika saba tabbatacciya! Ai daman can ina sane da kalolin zagin da kike shigewa ɗaki kina yi mini, to billahillazi muddin kika ci namana a bayan idona kaf zuri'arku sai Allah ya ci banten ubanku! Tun daga kan Ɗan'azumi har zuwa kan Isuhu mola mai hular gado."

Takaicin cin mutuncin da Kandala take yi wa kakanta da Babanta, ya sa ta isa ɗakinta da gudu tana kuka. Bintoto ta fashe da dariya iya ƙarfinta tana faɗin,

"Ai wallahi da ma kin yi kukan jini kin huta, idan jinin ya tsiyaye ki mutu ki bar mana gidan mu wataya mu kaɗai yadda muke so, shikenan mun mun rabu da gaibu!"

Kandala ta buge mata ƙeyar kai cikin sauri ta zuƙe jikinta tana ci gaba da dariyarta, Kandala cikin haɗe fuska ta ce mata,

"Idan ba ki daina tsokanar ta ba kika jawo ta dake ki babu ruwana don ma ki sani tun yanzu. Ni ba na goyon bayan rashin gaskiya, don haka ki bar mu mu ji da iftila'in da ta jaza mana kafin ita ma tsinuwar Allah ta hau kanta."

Sai da Bintoto ta turo baki sannan ta ce, "To Wallahi ni ko ranar da kika ga ta kayar da ni don ban shirya wa damben ba ne, amma yanzu ko da ciwon hannun nan nawa zan iya tumurmushe ta, na yi ta jibgar ta idan ta sake taɓa ni."

Kandala tana kallon ta tana juye baki gefe ta maka mata tana faɗin, "Kurin banza! Ranar ma da ta so kashe ki ai da lafiyarki amma kika saki baki ta dake ki a banza, ballantana yanzu da kika zama musaka hannu yana shirin shanyewa."

Haushin maganganun Kandala ta sa Bintoto ta rungume hannunta mai lafiya ta soke kanta cikin hannun tana gunguni, tare dasharar ƙwalla. Fahimtar ta yi fushi Kandala ta ko ma jan ta zuwa jikinta duk da zamewar da take yi, cikin sigar rarrashi ta shafo kanta tana cewa,

"Ke fa ba ki san wasa ba, to ni wasa ce nake yi miki, ai na san ko ranar don ba ki shirya ba ne shi ya sa ta lungude ki son ranta, amma tabbas da kin shirya da ta sha baƙin mamaki a kan irin ƙarfinki na zaki wanda kike kashe mutane da shi a cikin mafark.... ai kin tuna shi ko?"

A nan Bintoto ta ɗago kai tana washe baki saboda tuno mugun faɗan da ta yi da wasu mutane a cikin mafarki duk ta kashe su. Hakan ya sa ta zabura daga zaunen tana kallon Kandala ta ce,

"Wallahi fa har da wuƙaƙe na yi faɗan Kandala, kuma na yi ta soke mutane ina kashe su suna faɗuwa ƙasa suna mutuwa. To kamar haka nan zan yi wa Kulu a cikin mafarkin ko da safiya za ta yi sai dai a gan ta matacciya."

Kandala ta gimtse dariyarta tana cewa, "To wai su mutanen da kike kashewa a cikin mafarkim Musulmai ne ko Kafurai?"

Bintoto ta yi saurin faɗin, "Ohon musu! Ni dai ko su waye na yi ta kashe su yasin babu abin da ya dame ni tun da suka zo kama ni. Na san su ma idan suka samu sa'a kashe ni za su yi."

Kandala tana dariya ta ce, "Gara dai mu ji idan kafurai ne, saboda muddin aka ce Musulmai ne da kaina zan kai ki kotun Musulunci a yanke miki hukunci irin na masu kisan kai a cikin mafarki, tun kafin kisan naki ya zo kan Kulu ki ja mana bakin mutane."

Bintoto ta ƙyalƙyale da dariya Kandala ma tana taya ta, haka suka ci gaba hirarsu mai cike da shagala tare da barkwancinsu da suka saba yi a tsakaninsu koyaushe.

***

Watanni a tsakanin da rigimar kajin Bintoto ta ji sauƙi, saboda hannun nata yana samun kulawa hakan ya sa ta yi saurin warkewa, sai ɗan abin da ba a rasa ba, wani lokaci ma har tallar goro tana fita. Kandala kuma kwana biyu ne ta yi da ƙugun ya koma daidai. Da ma can buguwa ce kawai babu abin da ya same ta.

Kamar koyaushe, Bintoto tana ɗauke da tiren tallarta tare da ƙawarta Jamila, wadda ita ma tiren tallar ne a kanta za su je cin kasuwar garinsu, suna ta hirarsu a kan hanya. Babu zato suka hango wata dalleliyar mota ta nufo hanyar da suke kai, cike da ƙauyanci suka bi motar da kallo baki a sake har da tsayawa gefen hanya idonsu a kan motar har ta wuce.

A hankali motar ta fara rage gudu tana dawowa baya har ta ƙaraso inda suke tsaye ta tsaya, mamaki cike da fuskokinsu har zuwa lokacin da suka ga mai motar ya zuge gilashin motar tare da leƙo kansa yana faɗin,

"Sannun ku 'yanmata, don Allah ta wace hanya zan bi na je gidan Hakimi?"

Ƙawar Bintoto ta fara yi masa nuni da hannu Bintoto ta yi saurin tsamuke ta a cinya da ƙarfi tana yi mata signal a kan ta yi shiru, sannan bakinta yana rawa ta ce da shi,

"Bari mu zo mu nuna maka hanyar don daga nan akwai tazara sosai da gidan, kwatancen zai yi maka wahalar ganewa. Buɗe mana motar mu shiga sai mu kai ka har gidan da kanmu."

Kasancewarsa babban mutum, kai-tsaye ya gano motar take so su shiga shi ya sa ta tsiro da wayon, yana 'yar dariya ya buɗe musu motar jikin Bintoto yana rawa ta afka ciki, garin rawar jiki sannan da rashin iya shiga motar kafarta da takalmi ta fara ɗorawa ta yi tsalle ta faɗa da ƙarfi, har tiren goron ya buge mata goshi, babu shiri ta kai hannunta saman goshin tana shafawa tana faɗin,

"Wash! Allahna!"

Sannan ta yi saurin gyara zamanta tana leƙo da kanta ta kalli Jamila da ke tsaye tana kallon ta gabaɗaya ta gama tsorata, saboda tana jin fargabar ta shiga a yanke mata kai kamar yadda ta ji labarin ana yi a birni, Bintoto ta maka mata harara tana cewa,

"Ke dallah ki shigo mu je mu nuna masa gidan! Kin ga sauri yake yi kada mu ɓata masa lokaci."

Jamila ta fara ja da baya tana girgiza kai alamun tsoro, cike da jin haushin ta Bintoton ta sake magana a harzuƙe,

"Idan fa ba za ki shigo ba mu tafiya za mu yi wallahi!"

Cikin ɗari-ɗari Jamila ta shiga motar da ƙyar jikinta yana rawa saboda ita ma ba ta iya shiga motar ba, mutumin ya fito ya rufe musu ƙofa sannan ya koma mazauninsa ya tayar da motar, har ya yi gaba Bintoto ta yi saurin cewa,

"Ba ta nan ake bi ba! Juya baya akwai hanya mai sauƙi ta can inda ka fito."

Mutumin cikin aminta da zancenta ya yi ribas ya koma baya har suka ɓulle hanyar, cike da jin daɗi Bintoto ta sake nuna masa wata hanya tana cewa,

"Yawwa bi ta nan!"

Mutumin ya bi inda ta ce, suna tafe tana nuna masa hanyoyin da zai bi kamar haka;

"Miƙe wannan hanyar, yawwa sha kwana, miƙe sha waccan kwanar, ƙara miƙewa sha kwanar, yawwa bi ta nan..."

Haka ta dinga yi masa kwatance Jamila tana kallon ta cike da mamaki da fargaba har aka kai su kasuwa, cikin sauri Bintoto ta kama abin buɗewa cike da sa'a tana jawo shi ta buɗe ƙofar, jikinta yana rawa ta fito cikin sauri tana ƙumshe dariya ta kalli Jamila da ke zaune duk ta gama tsurewa ta ce da ita,

"To ai sai ki fito Malama!"

Ta fito da ƙyar sannan Bintoto ta rufe masa ƙofarsa da karfin gaske har sai da ya kai kallonsa a kan murfin. Sannan ta zo ta gefensa tana ƙumshe dariya ta ce,

"Yawwa mun gode Alhaji! Allah ya saka da alheri."

Mutumin ya zaro ido cike da mamaki Bintoto ta dafe tiren goronta da ke kanta ta manna da gudu. Jamila kam sororo ta yi tana fargaban abin da zai yi musu ta kasa motsawa daga inda take tsaye, sai da Bintoto ta waigo cikin gudun tana cewa,

"Wallahi ki zo mu je idan ya yanke miki kai babu ruwana."

Jin haka ya sa Jamila bin bayanta da gudu ita ma, yana ta kiran su amma ina ko waigo shi ba su yi ba. Sai ma ƙara ƙaimin gudun da suke yi suna ƙoƙarin shigewa cikin mutane. Bintoto tana gudu tana dariya har suka ɓace masa cikin dandazon mutanen da suka zo cin kasuwar.

Mutumin ya bi mutanen da ke kasuwar da kallo cike da tsabar mamakin da suka ba shi, babu shiri ya fashe da dariya shi ma saboda ko kaɗan bai yi tunanin za su iya yi masa wayo, hakan ya sa bai ji haushi ba. Asali ma shirmensu nasu nishaɗi ya saka shi, yana ta dariya har ya samu wani a cikin filin kasuwar ya tambaye shi ta inda zai bi ya isa gidan hakimin garin.

Mutumin ya yi masa nuni da hannu a kan ya koma cikin garin duk wanda ya tambaya zai kai shi gidan, ya yi masa godiya tare da ciro kuɗi ya yi masa alheri, sannan ya buga motarsa ya koma cikin garin.

Bintoto kam bayan sun daina gudun suka shiga sauke numfashin wahala, wata rumfa suka zauna suna dariya. Jamila tana nishi ta ce,

"Wallahi ke muguwa ce Bintoto, yanzu don mugunta kika hana mu nuna masa gidan kika saka shi ya yi wannan wahalar a banza?"

Bintoto dafe da cikinta tana dariya ta ce, "To ba mun sha lotonmu ba? Haka kawai sai mu bar banza ta wuce mu? Da fa yanzu ba mu isa zuwa kasuwar nan ba."

Jamila tana ci gaba da dariya ta ce,

"Kin san Allah; ban taɓa shiga mota ba sai yau, ashe haka ake ji idan an shiga wani shuuuuuu kamar ana tafiya cikin iska?"

Bintoto ta sake fashewa da wata arniyar dariyar sannan ta ce,

"Allah ya so ni ni kam na taɓa shiga sau ɗaya wannan ne na biyu, ai yasin da ban san ta yadda zan buɗe motar ba, da shikenan ƙaryarmu ta ƙare don wallahi tsaf zai iya tafiya da mu garinsu, ya kai mu a yanka mu da ranmu su sha daɗinsu."

Jamila ta miƙe tsaye tana faɗin, "Ni dai ta shi mu je kada ya zo ya same mu a nan mu shiga uku."

Bintoto ta miƙe tana cigaba da dariya ta ce, "Ke kam Jamila wallahi baƙar matsoraciya ce ke, shi ya sa ba koyaushe nake son fita da ke talla ba."

Jamila ta yi banza ba ita, har suka ci kasuwar suka siyar da komai ba su daina dariyar abin da suka aikata ba.

.

1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lambar; ***.

D/AUTA Ce✍🏻